Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
da iyaye na ba. To Allah ya kawo min a saukake...."
Ta katse shi "me kake nufi da wannan dogon jawabin? Kana nufin ba cikin ka bane ba ko me kake nufi?"
Ya gyada kansa "tabbas ba nawa bane ba. Amma idan kun matsa nawan ne ba zanyi dogon musu ba muje akan cewa nawan ne. Abu na farko idan har nawa ne to zai kai watanni shida zuwa sama, dan watanta shida rabonta da gidana. Cikin jikinta kuwa kasa yake da wata hudu. Idan baku yarda ba aje asibiti a gwada. Wannan kenan. Abu na gaba kuma idan ma cikina ne idan ma ba cikina bane ba kasancewarsa a jikinta ya nuna cewa babu aure a tsakanin mu, dan a musulunce ba'a yin aure da ciki. Auren da aka daura an daura a iska kenan"
Mama ta karba "tabbas. In dai da cikin sanda aka daura to an daura a iska, babu aure. In kuma an samu cikin ne bayan an daura to hakan ya tabbatar ba nashi bane ba dan yana asibiti tunda akayi auren. Yanzu abu biyu ya kamata ayi, na farko a dauki yarinyar aje asibiti a gwada cikin ta a ga watansa nawa dan a tabbatar da kasancewar aure a tsakanin su ko a'a, sai kuma a jira ta haihu sai a dauki abinda ta haifa a gwada shi dan a tabbatar da cewa nasa ne ko ba nasa bane ba"
Baba yace "idan an ga cikin ta same shi ne bayan daurin auren su, hakan yana nufin ba nasa bane ba. Kuma mu a matsayin mu na iyayensa mun cire masa takunkumin zama da ita dan hakan ya tabbatar da ba matar kirki bace ba, ba matar da za'a zauna zaman aure da ita ba ce ba, ba matar da za'a hada zuri'a da ita bace ba"
Umar ya sallami iyayensa sannan ya mike ya bar falon, murmushi kwance akan fuskar sa. Lallai duk wanda ya dogara ga Allah ya kuma mika lamuran sa ga Allah to tabbas Allah zai iya masa. Kamar yadda ya iya ws Jidda ya warware mata dukkan matsalolin ta. Kamar yadda shima yanzu da ya koma gare shi ya fara warware masa nasa matsalolin.
Ya hau saman motarsa ya zauna sannan ya dauko wayarsa ya nemo number din Jidda ya tura mata sako.
"Thank you so much Hauwa'u. Thank you for letting me know about cikin jikin yarinyar can. You have no idea how much that has helped me. Love you."
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The New Life*
**
Bayan fitar Umar daga falon ne aka cigaba da bincikar Asabe akan gaskiyar cikinta, inda ita kuma tayi bayani cewa akwai wani saurayin ta da tun tana talla tun kafin taje gidan Umar aikatau suke tare kuma yana yi mata juyen kayan tallan ta in ta dauko, wannan ne sanadiyyar lalacewar ta ba tare da sanin iyayenta ba, kuma shine dai yanzu bayan ta koma gida ya cigaba da bibiyarta inda ya kuma yin nasarar samunta kafin daurin aurenta ta Umar. Bata san da cikin ba sai bayan da suka zo gidan sannan kakarta ta lura da cikin ta kuma yi tunanin na Umar ne sannan ta barshi akan ya kara zamar musu hujjar da zai kara tabbatar da aure a tsakanin ta da Umar.
Abinda basu sani ba shine ba'a hada ilimi da jahilci a guri daya, abinda suka manta shine da masu ilimi suke harkar ba da jahilai ba. Wannan ya tabbatar da cewa babu aure tsakanin Umar da Asabe, kuma cikin jikinta ba na sa bane ba. Sai dai Baba a kokarin sa na kyautata mata sai ya nemi da su koma kauye su taho da yaron da yayi mata cikin, shi yayi alƙawarin zai dauki nauyin yi musu aure kuma ya samu aiki a cikin aiyukan cikin gidan sa ya bashi indai ya amince da auren. Itama kuma in tana da bukata zata zauna a gidan ta ke taya matan gidan aiyukan gida bisa sharadin za'a saka ta a makaranta ta arabi da boko ta samu ilimi, dan sosai Baba ya fahimci matsalar rashin ilimi ita ce take dawainiya da ita.
Wannan kenan....
Washegarin da abin ya faru Umar ya shirya ya tafi gidan sa, for the first time after months dan rabonsa da gidan tun ranar da ya saki Jidda. Mai gadin gidan yana nan har yanzu, dan Baba ne yake cigaba da biyan sa albashi saboda ya cigaba da tsare gidan duk da dai an kwashe kayan Jidda kaf daga gidan sai na Umar ne ya rage.
Yaji dadin yadda maigadin yayi ta murnar ganinsa yana kara tambayar saukin jikinsa da kuma jajanta masa. Yayi masa godiya sannan ya dauko alkhairi yayi masa ya shiga gidan.
Ya tsaya a bakin kofa yana karewa falon kallo da idonsa, images da yawa suna forming a cikin kansa, images na family dinsa, happy and so much in love with each other.
Yana iya hango Asad akan kafafun mamansa tana yi masa lilo, Yasmin kuma a kwance a jikinsa tana yin game a wayarsa yayin da shi kuma yake zura hannu lokaci zuwa lokaci yana mintsinin Jidda ita kuma ta juyo ta harare shi tare da alkawarin ramawa. And sometimes in ta gaji zata taso ta rama din shi kuma sai yayi pretending innocent yadda yayan su zasu shigar masa. Ya iya pretending ita kuma bata iya ba. Wannan yasa komai yayi mata bata iya boye bacin ranta shi kuma ya cigaba da amfani da wannan damar gurin cigaba da cisguna mata.
Ya wuce falon yana jin gidan yayi masa zafi, ba wai zafi na gari ba a'a wani irin zafi ne da yake radiating daga cikin zuciyarsa zuwa sauran gangar jikin sa. Kofar dakin ta ta bude ya tsaya yana kallon empty space din, yana tuno lokutan da suke shirya yaransu a dakin in zasu tafi school ko kuma in zasu kwanta bacci. Most of the times tana yi musu wanka yana shafa musu mai ya saka musu kaya sannan su zauna tare su karanta musu bedtime story wanda yaran suke cewa sunfi son karatun ta akan nasa wai shi murnar sa katuwa ce, Asad har ya kan kwaikwaye shi. A cikin kansa yaji kamar muryar Asad din yana kwaikwayon sa, yayi murmushi shi kadai realising shi kadai ne a tsaye a cikin dark, empty, dusty room. Babu ko kayan su ma ballantana ya gani su dauke masa kewar su, babu ko gadon Jidda ballantana ya kwanta ya yaji kamshinta a kai.
Ya juya da sauri ya bar dakin ya shiga nasa, ba tare da tunanin komai ba ya fara watso sauran kayansa da suka rage a gidan kan gado. Kamar yadda tayi ranar da zata bar gidan, ranar da ta gaya masa cewa ko akuya aka sakawa skirt aka shafawa jan baki in ya ganta sai ya bita, maganar da ta bata masa rai sosai amma kuma kamar da gaskiya a cikinta. Tunda har ya iya neman Asabe wacece ba zai nema ba kuma?
Sai daya gama fito da kayan sannan ya nemo jaka ya zuba su gabaki daya a ciki wadanda basu shiga ba kuma ya dauki wata babbar rigarsa ya daure a ciki ya kinkima ya fita dasu zuwa mota, sai kuma ya dawo ya cigaba da diban dukkan wani abun amfaninsa yana kaiwa mota including hotunan family dinsa da suke gidan, wanda ya lura Jidda ta kwashe wadanda take ita kadai ta bar wadanda suke tare da yara, shima ya san da ba zata iya cire kanta bane ba.
Sai daya gama tas sannan ya tsaya a bakin kofar falon yana kare wa gidan kallo, remembering the good memories, and the bad memories, including memories din sanda yake kawo matan banza gidan, samda suke kawo matan banza shida abokinsa, shida Bashir, cikin gidansa, gidan da later ya ajiye iyalinsa. Shin ta yaya ma yayi tunanin zai samu albarka a cikin gidan?
Ya ja kofa ya rufe da sauri sannan ya shiga mota ya zauna ya dauko wayarsa yayi kira. Wani abokinsa ya kira wanda ya ke harkar gidaje. "Hello. Idris ya kake ya family?"
"Alhamdulillah, su Yasmin suna lafiya"
"Dama gidana nake son siyarwa, shine nace bara inyi maka magana ku zo ku ganshi sai kuyi masa kudi ku nemi mai siya"
"Okay to shikenan na gode. Idan kunzo ku karbi key a gurin mai gadi"
Ya kashe wayar ya ajiye sannan yayi wa mota key ya bar gidan aguje, trying so hard not to look back.
A ranar da dare yaje ya samu Baba. Idonsa a kasa kamar yadda yake yi kullum yayi masa bayanin shawarar da ya yanke ta siyar da gidan sa, sai dai Baban ya nuna ko an siyar da gidan ba za'a bashi kudin ba.
"Ba zaka siyar da gidan ka ka kashewa mata kudin ba"
Umar ya dafe kansa, sai dai baiji haushin maganar Baban ba, ko menene ma za'a gaya masa tabbas ya san yayi deserving, kuma ya tabbatar it is going to be long kafin ya sake gaining trust din iyayensa, trust din Jidda.
Sai yace
"Na amince in an siya din a tura kudin account din ka, in an samu wani gidan a wata unguwar daban sai a siya min, shi wannan gidan ne bana son cigaba da zama a cikin sa"
Sai Baba ya amince da wannan.
Sannan kuma Umar din yace "Baba dama maganar da muka yi da Baffa ce, maganar Lagos, shine nake so inji inda maganar ta tsaya"
Baba yayi shiru yana kallon sa, a ransa yana tausaya yadda ɗan nasa ya koma, amma yana ganin rashin dacewar idea din tura shi Lagos ya zauna shi kadai a wannan lokacin, musamman saboda rashin lafiyar sa da kuma muguwar dabiar sa, amma kuma kamar yadda Halilu ya fada, a Saudiyya akwai lalatattu kuma a Lagos akwai shiryayyu, dan haka shiriya a zuciya take ba'a gurin zama ba.
Sai dai kuma duk da haka yana so yayi compensating for rashin kawar da Umar din ya samu lokacin tashin sa, kamar yadda yayi playing role wajen lalacewar dansa yana so yayi playing role wajen shiryuwar sa. Sai yace "zaka tafi Lagos din kamar yadda mukayi magana. Amma ba kai kadai zaka tafi ba, tate zamu koma da ni da kai da mamanka. Zaka karbi ragamar kasuwanci na acan ka cigaba da juyawa, ni kuma zan ke supervising dinka ina ganin yadda kake yi ina gyara maka inda kayi kuskure, ba ina maganar kuskure akan harkar kasuwanci kadai ba, ina maganar kuskure akan muamala ta rayuwa"
Umar ya gyada kai da sauri yana jin hawaye yana kawowa idonsa. Tabbas duk duniya babu wanda zai so Mutum kamar iyayensa, no matter what mutum ya zama, iyayensa will forever love him, ko da sunyi kuskure hakan baya nufin basa son ka, hakan yana nufin suma mutane ne and thay are not above mistake. Babban abu mai muhimmanci shine idan an fahimci inda aka yi kuskuren sai ayi kokarin gyarawa. Allah ya ganar da mu.
Sai dai abu ne a lokacin ya ke damun Umar, wannan abin shine family dinsa da yake kulafucin ganin sun dawo cikin rayuwarsa amma kuma wannan tafiyar da zaiyi zata kara nesanta shi da su ne, at least in suna guri daya zai iya cigaba da gwada sa'ar sa ko Allah zai sa ya dace, amma in suna nesa da shi ba shi da wannan damar, kuma ya tabbatar Jidda ba zata bashi dama ta waya ba.
But after he thought about it sai yaga kamar Jidda tana bukatar space ne a yanzu, kamar in ta cigaba da ganin sa zai cigaba da fama mata ciwuwwukan da yaji mata a cikin zuciyarta, maybe tana bukatar healing, tana bukatar ciwuwwukan su warke yadda in ta ganshi she will no longer feel the pain. But there is also the risk of loosing her completely, there is a chance that she will fall completely out of love with him when she is healing, there is a chance that someone wilk come and replace him a zuciyarta when he is away.
Wannan tunanin ya saka yaji ya fasa tafiyar ma gabakidaya, sai dai already ya riga yayi wa Baba maganar kuma ya san shi bai isa yanzu ya koma ya ce ya fasa ba. But can his already bleeding heart take it? Can he be thousands of miles away from Jidda with the thought that tana can tana soyayya da wani katon?
Ya tuna sanda ta kira shi da gardi. Sai yayi murmushi. Maganganun da ta gaya masa a lokacin hurts him but yanzu da yayu bitar su a akan sa sai ya fahimci akwai pang of jealousy acikin maganganun nata, in dai kuwa akwai kishi to tabbas akwai soyayya. Kenan akwai chance........ tiny slim little slimy chance da zai iya kubce masa any time, but that chance is what he is going to hold on to.
Babu bata lokaci ya kammala shirye shiryen tafiyarsa, ta tattara takardun sa na likitanci ya boye a gurin ajjiya dan a yanzu he no longer wants to be doctor Umar again, ge wants to first fimd himself a matsayin Umarul Faruq kafin daga baya yayi deciding if he wants to be doctor Umar again. Ko da kuwa ya dawo occupation dinsa na aikin likitanci to tabbas zai chanja field, definitely not a gynaecologist.
Yes, if you want to get rid of wata mummunar dabiar ka, abu na farko shine ka guji duk wani abu da yake da dangantaka da ita. Shi yasa annabi ya bada shawarar migration. Kayi hijira daga inda kake zuwa wani guri daban musamman inda ba'a sanka ba, inda ba za kake haduwa da abubuwan da zasu ke tuna maka da waccan dabiar ta ka ba, in da ba zaka ke haduwa da abokai ko kawayen da kuke dabiar tare ba. Wannan shine abinda Umar yayi kokarin yi.......
Abu na biyu da yayi shine he changed his phone numbers, now for real. He delete all his social media accounts and open new ones with different names and makes them very private. Yadda matan banzan da suka saba da juna da kuma abokan banxan da yake da su ba zasu same shi ta nan ba, only family and few abokansa na gari wadanda yake son ya mayar da su manyan abokansa a yanzu dan ya samu su goga masa halayensu na gari.
Sai dai kuma duk kokarin kiran number din Jidda da yayi taki dauka, daga baya ma sai kiran ya zama baya shiga abinda ya tabbatar masa da cewa tayi blocking dinsa ne, sai da ya saka sabon layin nasa sannan ya kira ta ta dauka da sallamar ta cikin daddadar muryarta. Amma tana jin muryar sa ta fara da tambayar shi abinda yake bukata sannan ta kare ta kora masa warning din kar ya sake kiranta.
"Stay away from my life!"
Sannan ta katse kiran. Next daya gani shine text daga gare ta na wata number tace in zai magana da yayansa ga number din da zai kira. Daga nan daya sake kira yaji ta kuma blocking. Ya gwada waccan number din yaji ta shiga, kuma aka dauka, muryar Yasmin cikin murna tana gaya masa mommy ta siyo musu waya mai games da yawa da zasu ke yi saboda ta hana su daukar mata waya tace suna cinye mata charge, sannan kuma in tana office da wayar take kiransu, kuma tace shima da wayar zai ke kiran su suma kuma in suna son magana da shi zasu iya kiransa.
"Daddy kayi saving number din mu. Ka rubuta Maryam da Muhammad"
Asad shi kuma yace "Daddy Muhammad da Maryam zaka rubuta, sunana ne a farko"
Yasmin tace "sunana za'a saka a farko tunda nice babba"
Umar yayi murmushi yace "shikenan. Zanyi saving da parrots, sarakan surutu" duk sukayi dariya.
A day to tafiyar su ya shirya yaje gidan su Jidda, a zuciyarsa yana ta addu'ar Allah ya bashi ikon ganinta ko da kuwa unexpectedly ne, ko da ace ta dawo daga office ne su hadu a hanya, ko da ace ita bata ganshi ba. Sai dai baiyi wannan sa'ar ba ya tarar tana gida, ya riga kuma yasan ko me zaiyi ba zata fito ba. Ya kira wayar su Yasmin sai Amira ta daga tace masa suna islamiyya amma sun kusa dawowa. Sai ya kwantar da kujerar mota ya zauna yana kallon gidan tare da addu'a ko zata leko amma shiru ko inuwar ta bai gani ba har yaran suka taso, suna ganin shi suka taho a guje gurinsa da murna.
Sai da yagan su da uniform da jaka da books sannan ya tuna duk watannin da sukayi basa tare bai taba yi musu aiken ko kwandaka ba kuma Jidda bata taɓa tambayarsa ko wani nasa wani abu ba, and they look fine, they misses him of cause amma baya jin suna da wani financial problem. Fes, fes da su, full of energy and laughter.
Sai ya tura su gida su ajiye kayan hannun su sannan su gaya wa mommyn su zai fita da su. Basu jima ba suka dawo har uniform an cire musu an kuma saka musu kaya masu kyau. Sai ya dauke su a mota suka fita, yana ta tambayar su game da rayuwar su da makarantansu su kuma suna bashi labari, a haka har sai da suka nuna masa both bokon su da islamiyyar su ya gani sannan ya tafi dasu yawo ya kashe musu kudi duk da shima ba kudin ne dashi isassu a hannunsa ba amma ya siya musu kayan abinci da kayan tea da kuma tarkacen su biscuits da sweets da juice na zuwa makaranta. Ya so ya siya musu kayan sawa ma da takalman makaranta amma kudin ba zasu ishe shi ba dan haka bai siya ba amma yayi niyyar zai turo wa Jidda kudi ta siya musu, duk da yasan already