Chapter 74 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   74 / 106

219K to 222K   out of 316K words

a guri daya tare da kwalla kara. "Mommy dan Allah kar ki dake ni dan Allah ki yi hakuri"

Sai naji na kasa dukan nata, sai shegen magiya kamar babanta, na kalli screen din wayar naga sunan Umar a jiki, kuma ita ta kira shi ba shi ya kira ba dan wayar a kashe take a cikin jaka ta, time still yana reading a kan screen din wayar meaning har yanzu yana rike da wayar kuma yana jin abinda muke yi, na saka wayar a kunnena and I heard his voice for the first time in one month. And it sounded so broken, babu wannan mazantakar da wannan takamar a ciki.

"Kar ki dake ta, dan Allah Jidda kar ki dake ta"

Na katse kiran tare da kashe wayar sannan na sunkuya na kama kunnenta na ja, tayi kara tare da rike kanta da hannu biyu "uban wa yace ki buda min jaka ki daukar min waya? Huh? Waya ce ki daukar min waya har ki kunna ta kiyi kira da ita?"

Ta fara tsiyayar hawaye "mommy am sorry, Daddy na nake so in kira, gurin Daddy nake so in je. Bana son gidan nan ni gidan mu zan tafi"

Na saki kunnen sannan na zauna a bakin gadon tare da dafe kaina. Allah kadai ya san abinda ta gaya masa. But how much did she really know? Bana jin tasan abubuwa da yawa but you can't really tell dan wasu yaran kana ganin kamar basa fahimtar abinda ake yi amma suna sane. If she did mentioned the name Diyam na tabbatar gobe zai zo gidan nan, dan sunan is unique yadda tana fada zai tuna da sunan kuma zai tambayi Mufida ita kuma zata tambayi friends din da muka yi jss tare and Ramla can take them to gidan su Diyam. Daga nan sai nan gidan.

But ban tabbatar ta fadi Diyam din ba. Naji dai ta fadi Halima. Ta kuma fadi twins, da gida mai kyau, da kuma sauran abubuwan da ban sani ba. And those are clues enough to trace us. Dole zan gaya wa Diyam but sai da safe tunda yanzu tana tare da mijinta.

Na juya ina kallon ta, ina lura da yadda jikinta yake karkarwa tana kuka, sai naji tausayin ta, so innocent, ita bata san me yake faruwa ba ita bata san kusan dan ita nake komai ba, ita kawai abinda take so shine ta ga babanta. She has always been daddy's girl tun tana Baby. Na tambayi kaina menene abin yi? amma bani da amsa a lokacin, sai nace mata ta taso ta kwanta, sai data zagaye ta can nesa da ni sannan ta kwanta tana tsoron kar kama ta inyi mata dukan da ban yi mata ba.

Na bita da kallo sannan nace "ko babu komai ubanki zai kwana da zullumin kin ci jibga yau".

Ai kam ya kwana din, dan ranar bai yi bacci ba yana tracing wacece Halima a cikin kawayen Jidda wacce take auren mai kudi kuma take da twin babies sannan suke zaune a kano? It is going to be a challenge but he is going to do it. Dan a yanzu gani yake yi babu abinda rayuwa zata yi throwing his way wanda ba zai iya handling ba. Tun da har yayi handling wannan wata gudan.

His nightmare began with a phone call from Abba bayan Jidda taje gida, yana ta tsoron abinda Jidda ta fada wa Abba da kuma abinda Abban zai ce da kuma matakin da zai dauka akai, but to his upmost surprise sai yaji Abban yace yazo ya dauki Jidda su dawo gida, kuma daga alama ma ko sauraren Jiddan Abban bai yi ba dan shima da ya fara kokarin ba da hakuri sai Abban yaki sauraren sa yace abinda ya faru sirri ne tsakanin miji da mata dan haka shi baya son ji, su bar shi a tsakanin su.

Ji yayi kamar wanda akayi wa babban albishir, yaji kamar duniya babu wandaya fishi sa'ar siriki kamar duniya babu surikin kwarai irin Abba. A take ya yanke shawarar in komai ya lafa zai samu wata kyauta ta bajinta yayi masa dan nuna jin dadin sa akan abinda yayi masa.

Ba tare da bata lokaci ba ya shiga mota ya dauki hanyar gidan su Jidda. Ya san dai ko sun dawo gida zai sha tijara a gurin ta zasuyi rigima sosai amma shi yasan kan kayarsa, yasan ta yadda zai biyo mata har ta sauko su cigaba da rayuwar su, and wannan rigimar ta su insha Allah ita zata kasance ta karshe a tsakanin su, ba zata kuma kamashi da laifi makamancin wannan ba.

Amma haka yayi ta fada mata ai........
For six years kullum haka yake ce mata wannan shine na karshe............

Haka yayi ta fada wa kansa ai.............
For more than 15 years kullum sai ya gaya wa kansa cewa wannan shine na karshe, then in ya sake yi sai yace na ƙarshe in ya kuma yi ya sake cewa na karshe.... 

Wanne ne zai zamo na karshe?????

Ya tambayi kansa. Sai kuma ya dan daki stirring "damn it. Wannan case din shine na karshe" ya fada a hankali yana so maganar da yayi tayi sinking zuwa zuciyarsa but it didn't, a fatar bakin sa ta tsaya. Ya girgiza kansa "a hankali dai. I am almost getting there. Na rage sosai kuma na kusa dainawa" ya sake fadawa kansa. But wannan shine abinda yake fadawa kansa kullum but is it really true? Da gaske ya rage din ya kusa dainawar ko kuma abinda yake gayawa kansa kenan kafin wani opportunity din yayi presenting kansa?

Zuciyarsa fes ya yi packing a kofar gidan su Jidda, ya kalli gidan yana tuno sanda yake zuwa gurinta zance da yadda take rako shi bakin mota tana ta jin kunyarsa. Yayi murmushi. She is a very special kind. Very special to him.

Ya dauko wayarsa ya nemo number dinta "Baby Dove" a ransa yana aiyana yadda take cikin fushin nan ko ya kira ma ba zata dauka ba, maybe ma tayi pretending kamar bata gani ba amma dai zai kira din ya kuma sake kira just to show her how much he cared.

Ya kira bata dauka ba kamar yadda yayi tsammani, sai ya sake kira ya kuma kira. Sai kuma ya juya yana kallon gidan, haka kawai yake jin wani irin feeling kamar basa cikin gidan, kamar something has been torn away from his heart sai wawakeken rami ne a gurin.

Yayo kokarin dauke tunanin sa daga kan abin sai kuma ya kira number din Amira, niyyar sa ya gaya mata ta gaya wa Jidda yazo, ya san zata fada a gaban mutane kuma hakan zai tirsasa wa Jiddan fitowa. Sai dai wayar Amiran bata shiga.

Ya bude kofar motar without second thought ya doshi gidan yana jin emptiness din cikin zuciyarsa yana karuwa. Ya shiga tsakar gidan yana raba idon ganin Asad ko Yasmin ko kuma jin wani motsi da ya dangancesu. "Salamu alaikum" yayi sallama, hoping to hear her voice answer him. 

Amma sai yaji muryar Amira ta amsa tare da fitowa daga dakin Umma, ta tsaya tana kallon sa sannan ta fara raba ido a tsakar gidan. "Ina yayar?" Ta tambaya. Ya kalli tsakar gidan shima cikin rashin fahimta yace "ban gane ba. Ita nazo dauka" ta bude sitting room da sauri ta shiga ta fito sannan ta shiga dakin Farhan ta fito tana kallon sa idanunta a waje "bata nan" tace, ya yamutsa fuska cikin rashin fahimta "ban gane bata nan ba. Ina ta tafi? Ina Yasmin da Asad"

Ta dan diririce kadan "muna daki tace zata yi waya da kai, ta fito kuma sai ta kira su Yasmin tace su zo suyi waya da kai. Bata kira ka ba?"

Ya bude hannu, zuciyar sa tana bugawa da karfi a kirjinsa "wanne kira kike nufi ne wai. Ina Jidda? Ina Yasmin? Ina Asad? Ina suka yi?" Amira ta juya da sauri ta koma dakin Umma, amma kafin ta gama shiga Umma ta fito da charbi a hannunta, maganganun sa ne suka fito da ita. Ta kalle shi ta kalli Amira "ina Jiddan?" Amira tace "ina jin fa guduwa tayi, da ta fito tace zatayi waya ba wayar tayi ba guduwa tayi"

Hajiya ta fito daga nata dakin itama da charbi a hannun ta, tana ja at the same time tana magana "me nake ji ana fada kamar guduwa? Waye ya gudun? Ba dai Jidda ce da tayi yaji kuma yanzu ta gudu ta shiga duniya ba? Kai kai kai! Wannan abin bai yi dadi ba, wannan abin kunya da me yayi kama?"

Umar ya juya yana kallon ta a fusace, abu daya da ya hana shi shakar wuyan ta a lokacin shine matsayin da take dashi a gurin Jidda. Amma bai jira jin sauran magana ba saboda tashin hankalin da kalaman Amira suka saka a zuciyar sa, ya fita da sauri yana kallon layin gidan up and down, babu kowa saboda yanayin sanyin da ake yi ya kori mutane gida, maganar Amira tana yawo a kansa "ina jin fa guduwa tayi"

Yayi hanyar bakin titi da saurin da yafi kama da gudu. A dai dai bakin layin ya hadu da wani yana kokarin shigowa layin, ya kama hannun sa da sauri "ka ganta? Kaga wata ta fito yanzu da yara biyu a hannunta?" Ya fada yana kwatanta tsahon Yasmin da na Asad da hannun sa.

Mutumin ya bishi da kallo sannan yace "Jidda kake nema wai? Ina ta tafi?" Sai yanzu ya kalli fuskar wanda yake tambaya din, ya tuna shi amma ya manta sunan sa, shine wanda ya ke zuwa gurin Jidda Lokacin da shima yake neman ta. Ya sake shi da sauri kamar an mintsine shi sannan cikin sauri ya karasa fita daga layin ya bi street din da kallo, babu Jidda babu mai kama da ita.

Ya tsallaka titin da sauri ba tare da ya kula motocin da suke ta yi masa horn ba. Ya doshi gurin masu furnitures din da suke da shagon su yana kallon layin gidan su Jidda, ya tarar suna kokarin shigar da kayan su cikin shago alamar sun tashi, "salamu alaikum, dan Allah kun lura da wata mata da ta fito daga layin can dazu? Da yara biyu a hannunta?" Na farko ya girgiza kai, Umar bai tsaya jiran abinda zai ce ba ya tafi gurin na biyun wanda yake tsaye yana kallon sa cikin sigar mamakin irin rudewar da yake ciki.

"Jidda kake nufi wai? Kanwar Tahir?" Umar ya karasa da sauri ya kama hannunsa guda daya a cikin nasa biyu. "Eh ita, kanwar Tahir. Ka ganta?" Ya gyada kai tare da kwace hannunsa yana yarfar wa yana yiwa Umar kallon tsoro "eh na ganta. Zan tafi masallaci na ganta ana sauke su a a daidaita suka shiga gidan su, sanda na dawo kuma sai na ganta da yaran a bakin layin su suna shiga wata adaidaita din"

Umar ya juya ya kalli inda ake nuna masa kamar mai fatan ganin su a gurin. Sannan ya juyo ya kalli mutumin "ina suka yi" mutumin ya nuna masa gabas "nan suka yi......." Umar ya juya da sauri yayi hanyar da aka nuna masa ba tare daya jira karin bayani ba ko kuma yayi wa mutumin godiya ba.

Da sauri mai kama da gudu ya bi titin har zuwa junction, inda titin ya rabu gida hudu. Ya tsaya yana bin kowanne titi da kallo kuma akan kowanne titi adaidaita sahu ne birjik kamar jumper a Jos, "she is in one of those" ya fada a hankali duk da a ransa yasan in dai ta fita kafin shigowar sa unguwar to tabbas tayi nisa, ya saka hannun sa daya aka daya kuma ya saka a aljihu ya dauko wayarsa ya sake kiran number dinta "pick up pick up pick up" ya riga maimaita wa kamar fadar ta sa ita zata saka ta dauka, ta katse ya sake kira, bayan ta katse ya kuma kira sai yaji network busy.

Hannu yaji an taba shi a bayan sa, ya juyo da sauri suka hada ido da Abba, Abba yace "Doctor ka taho gida. Mutane suna ta kallon ka anan" daga nan ya kama hannunsa basu tsaya ko ina ba sai a cikin sitting room, ya nuna masa kujera, "zauna" amma Umar bai zauna ba sai ya fara safa da marwa yana cigaba da kiran number din Jidda, sai kuma ya tsaya yana kallon Abba da yake kallon da wani irin expression mai wahalar fahimta "Tahir. Gidan Tahir zata tafi" Umar ya fada yana kirkirar murmushi, fuskar sa tana nuna jin dadi.

Abba yace "ta dauki wayar ne? Ko message ta turo maka?" Umar ya zauna "a'a bata dauka ba, amma wancan karon da muka samu matsala can taje gurinsa kuma yace in wani abu ya kuma faruwa ta gaya masa zai dauki mataki" Abba ya mike, ransa a bace "shi Tahir din? Dama shi yake daure mata gindi kenan, zai zo ya gaya min ni na haife ta ko shi ya haifar min ita?" Umar ya dafe kansa yana jin haushin kansa, wani lokacin ma dai surutu bashi da dadi.

Abba ya shiga gida yana bambamin fada "Aisha! Kina ina! Ki kira Tahir ki ce masa ya dauko yarinya ta ya dawo min da ita yanzu yanzun nan" Umma ta fito daga daki hannunta rike da wayarta, fuskar ta rubuce da tashin hankali "Tahir? Bata gidan sa, na kira shi a waya ai. Sai dai ko in ta akan hanya. Na kira Afia ma bata can. Sai dai mu jira anjina muji inda zata bulla. Ai ba zata wuce wadannan guraren ba"

Ya juya ya koma gurin Umar yana cigaba da fada. "Duk inda taje ma zata dawo ne, za kuma ta same ni ne tunda ni zata mayar mutumin banza. A baro gidan mijinta kuma in umarce ta ta koma amma ta nuna min ban isa ba, sannan ta kama hanya ta fita kuma in kira ta taki dauka"

Fada yake yi har bakinsa yana kumfa, yana yi Hajiya tana bashi hakuri "kar kaje wani ciwo ya same ka Alhaji, ba ita kadai ce yar ka ba, in ka mutu ita bata da matsala ma tunda iya yar gatan miji ce"

Umar dai yana zaune yana cigaba da kiran wayar Jidda, daga baya ya koma tura mata messages.

"Jidda please don't do this"

"In kin fi son zama anan ni zanyi wa Abba magana ya barki ki zauna anan din"

Ya cigaba da kira amma bata da niyyar dauka. Ya sake tura mata sako

"Just pick up the damn phone"

Amma bata dauka ba.

Time ya cigaba da tafiya. Duk inda zata je ya kamata ace yanzu yaje, amma kuma babu wanda ya kira yace gata nan taje gidan sa. Daga nan suka fara kiraye kirayen yan'uwa ana tambaya ko ta je, duk siblings dinta an kira su bata je ba, aka koma kiran cousins suma babu wani bayani. Farhan kuma ta yi ta kiran friends din su sji kuma Umar ya na kiran nasa dangin amma da yake mai yawo ne baya nuna Jidda yake nema sai dai kawai ya kira a gaisa, knowing in tana can za'a ce masa gata tazo, duk da dai bayan gidan yaya Mubaraka baya jin akwai gidan wanda zata je a cikin yan uwan sa. Amma babu amo babu labari.

A haka har dare yayi sosai. Lokacin Tahir yazo gidan ai kuwa Abba ya huce haushin sa akansa yayi masa tas yace shi yake ziga Jidda taki zaman aure, daga baya ma yace sai ya fito masa da yarsa, hakan ta sa dole Tahir din ya bar gidan ba tare da ya shirya ba ya fara yawon neman Jidda a duk gidan da yasan suna da alaka kuma zata iya zuwa. Sai dai duk inda yaje babu Jidda babu dalilin ta.

Dole ya hakura ya koma gidan sa, yana zama ya sake kiran number dinta still bata dauka ba sai ya tura mata message

"Jidda Call me"

Bayan wani lokaci reply ya shigo masa "I am safe. Ka gaya wa Umma".

Umar bai bar gidan Abba ba sai da Abban da kansa yace masa ya tafi gida ya huta sai da safe tukunna sai su ga abinda zasu yi, in police za'a shigar cikin maganar to, dan shi Abba ya fara tunanin ko sace su akayi tunda kusan duk wanda suka san ta sani sun kira amma basu samu ba.

Umar ya shiga motar sa ya fara driving da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kansa da shi. Bai ma san tunanin da yake yi ba amma shi dai yana da tabbacin babu wanda ya sace Jidda da yayansa, guduwa tayi, saboda shi kadai yasan irin girman laifin da yayi mata kuma shi kadai yasan irin bacin ran da ya gani a tare da ita dan baya jin ko sanda suka yi case din Mammy ranta ya baci irin haka. Guduwa tayi ya sani, so take ta hukunta shi kuma yasan yayi deserving duk hukuncin da zata yi masa koma fiye da haka. Sai dai abinda bata sani ba shine abinda take tunanin ya faru is not entirely true, amma baya jin ko yayi mata bayani zata fahimta tunda shi din tsohon mai laifi ne a gurin ta.

Gidan su ya nufa, dan baya jin zai iya zuwa gidansa a yau not without her and their kids. Amma sai dai me?

Yayi horn mai gadi ya bude masa, sai da suka hada ido sannan ya tuna da wata halitta wai ita Asabe, yayi sauri ya dauke idonsa daga cikin na maigadin yana tambayar kansa ko ina yarinyar ta tafi, ko dame dame ta je ta fada? Ko wanne sharrin kuma ta sake yi masa?

Sai dai jin maigadin bai yi masa maganar ta ba yasa ya amsa gaisuwar sa sama sama sannan ya shiga cikin gida.

Mufida kadai ya tarar a falo kwance akan kujera da waya a hannunta tana yi, sai dai tana ganinsa ta yi saurin katse wayar tare da tura ta bayan ta, idan ba rudewar da yake ciki bace tayi deceiving dinsa zai iya cewa har tsorata tayi.

"Yaya Doctor sannu da zuwa" ta fada tana kallon

74 / 106