Chapter 83 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   83 / 106

246K to 249K   out of 316K words

da sauran su. Dan haka, if I am to give an advice ga macen da take ganin ta kai karshen limit din hakurin ta da zama da mijinta har tana gudun cigaba da zaman zai iya jawo wa wani mummunan abu kuma iyayenta sun ki shiga cikin maganar shine, ta shigar da hukuma ciki, in nace hukuma ina nufin tun daga mai unguwa ko dagaci har zuwa sarki, ko kuma ta kai kukan ta gurin malamai, musamman malamin da ta yarda dashi take ganin yasan abinda yake yi kuma yana da voice din da zai tsaya mata, ko kuma ta kai hisba board, wannan kamar wata kungiya ce ta gamayyar malamai da gwamnati ta dorawa hakkin kula da irin wadannan matsalolin, ko kuma a matsayin ta na yar kasa zata iya walking direct into any court, Shari'a court ko judicial, tace ta kawo karar mijinta tana so a raba auren su. She will be heard"

"Idan misali ace hisba board ta je, zasu saurare ta first su karbi statement dinta, sannan kuma zasu dauke ta su mayar da ita gidan iyayenta kuma su tilastawa iyayen su rike ta in suka kore ta za'a kama su tunda she is bound to them by law. Sannan za'a aikawa da mijinta sammaci cewa ana nemansa, sai yazo shi da waliyansa itama tazo da waliyanta sannan sai a zauna a saurare su. Kinga a haka, iyaye irin Abba will be forced to listen."

"A haka za'a saurari matsalar, a saurari kowanne side idan akwai yiwuwar sulhu sai ayi musu, tunda shi addini dan nasiha ne, rabuwar aure shine last solution but sometimes it is the best solution. But meanwhile matar zata kasance a gidan su under the care of her parents, sai dai ko idan sulhun yayi nisa an fara shawo kan matsalar sai ace ta koma gidan mijinta da fatan zaman da zasu yi tare zai taimaka gurin sulhu a tsakanin su"

"Idan kuma sulhun yaki yiyuwa then the marriage will be dissolved. Either shi mijin ya sake ta ko kuma ta dawo masa da sadakin sa sai alkali ya sake ta. And then they will talk about the custody of the children, wanda yawanci yake tafiya hannun uwa kamar yadda addini ya tsara, ƴa mace uwarta zata rike ta har zuwa aurenta, namiji kuma har sai ya balaga sai ya zabi inda yake so, sai kuma a yankewa mijin abinda zai ke bata na ciyarwar ƴaƴan su dai dai da income dinsa"

"Wannan shine mostly abinda ake yi unless if ita uwar ceai problem kamar na rashin tarbiyya, yadda har ake tsoron in aka bata yayan tarbiyyar su zata gurbata kuma bata da uwar da zata rike on her behalf to sai a bawa uwar mijin su ta rike su"

"Dan haka mata suna da gata, gata mai yawa da addini yayi mana amma mu bamu sani ba, ko kuma mun sani mun zubar da shi a kasa su kuma maza sun take ta kanshi sun wuce"

Na girgiza kaina "da yawan mata ba hakan bane kadai, da yawan mata tsoro ne, tsoron abinda zasu tarar a gaba suke yi da kuma tsoron kallon da society zasu yi musu suke yi, tsoron kalmar bazawara suke yi, tsoron responsibility din da zasu kai gida suke yi. Iyaye da yawa responsibility din ne suke gudu shi yasa ba sa son yarinyar da suka aurar ta dawo gida da sunan zawarci"

Diyam tace "hakane, anan gabar ne kuma self dependency ya shigo ciki, ba wai ina nufin mace tayi zaman kanta ko kuma ina nufin mace ta zama bata bukatar namiji ko iyaye ta a rayuwar ta ba, a'a i a nufin mace ta kasance zata iya daukan nauyin kanta da ƴaƴanta, in terms of feeding da sauran daily bukatu. Idan har ba zaki zama liability a gidan ku ba su kansu iyayen ba zasu ƙi ki dawo gidan ba, ina nufin idan har marriage din ya kai breaking point. Idan kuma kin dawo din ba zaki zama liability ba, kannenki ba zasu raina ki ba, yayanki ba zasu wulakanta ba, shima kansa mijin da kuka rabu ba zai ke daga miki kai gurin kawo kudin feeding da yake kansa ba, sannan idan wani auren yazo miki wanda zai aure kin ba zai ke feeling cewa taimaka miki zaiyi ya aure ki ba rather sai dai taimaka wa juna zakuyi ke da shi."

"Ba wai ina nufin mace tayi kudi dole ba, ko kuma ina nufin in tanada sana'a ko aiki bata bukatar namiji ba, a'a, amma in tana da abin hannunta ta wuce wulakancin a gurin maza da matan baki daya. Dogaro da kai ba wai yana nufin lallai aikin gwamnati ba, ko kuma yana nufin lallai sai kina siyar da laces da atampopi ko kina order din dogayen riguna daga Dubai ba, akwai wadda na sani ta fara sana'a da 1k, ta siyo kayan hadin spices ta niƙa ta daddaura a leda take siyarwa naira 20 20, makota suka fara siya. Da yake ta kyautata a cikin sana'ar ta, tayi hadi mai kyau nan da nan a hankali sai gashi fa tara daurin hamsin hamsin tana kaiwa shagon unguwa ana siyar mata, daga nan sai zubawa a robobi, daga nan sai gata har da yin sticker da sunan ta tana likawa a robar, daga nan sai ta fara yi da yawa tana kaiwa stores ana siyarmata, sai tazo ta shigar da jan yaji da yajin daddawa, yajin tafarnuwa, yajin zogaye da sauransu. Wanny sana'ar ita ce a yanzu take rike da ita.

"Nasan wata mata kuma da take yi kunun aya. Ta fara yi ne tana daurawa a leda a bawa almajiri ya zagaya mata unguwa, a yanzu ta sanar min tana siyar da kunun aya a kullum musamman lokacin zafi na more than 30k, tasha tasha kasuwa kasuwa ake kai mata, har yara ta dauka aiki suke taimaka mata, da wannan kunun ayan da shi take rike kanta da yayanta"

"Misalai suna da yawa, na san ke ma kinsan wasu. Abin dai da nake nufi shine, if you can get aikin gwamnati, it is good, idan kuma sana'a zaki yi that is even better, amma idan zaki iya hada aikin gwamnati da kasuwanci that's even the best. As long as zaki tsare mutuncin ki zaki kiyaye dokokin ubangiji shikenan. Mu tuna, ko da babu mutuwar aure akwai mutuwa, naturally maza suna riga mata mutuwa, miji zai mutu ya bar ki da yaya, ya zakiyi kenan a lokacin?"

*Umar*

Tace "of course na fahimta. Kuma ina tunani ne da kwakwalwa ta sabanin da da nake tunani da zuciyata. Tabbas na fahimci Abba zai raba ni da kai which is exactly why zan je gurinsa because that's what I want with all my heart. Rabuwa da kai. Allah ya bawa Baba lafiya and I wish you best of luck a sabon auren ka. Allah ya kawo kazantar daki"

Daga nan ta kife wayar. Amma shi yasan ko da bata ajiye wayar ba baya jin zai iya kara yi mata magana ko da kalma daya ce. Maganganun ta sosai suka taba zuciyar shi fiye da yadda ita kanta da tayi su tayi tunanin zasu taba shi. Ya saki kan wayar ba tare da ya mayar gurin ajiye ta ba sannan ya juya yana tafiya duk kuwa da cewa baya ganin gabansa clear, yana jin mai gadin yana yi masa magana amma ya share shi bai juya ba dan idan ya juya zai iya kikkifa masa mari duk da babu abinda yayi masa.

Wani irin haushin Jidda yake ji, wai me take tunani ne? Ya san tana fadar abinda ta fada ne kawai dan ta bata masa rai amma yasan tana son sa, ya san kuma ba zata iya rayuwa babu shi ba kamar yadda shima ba zai iya rayuwa babu ita ba. Kuma zamanta a gidan nan ne ya jawo hakan, they are brainwashing her, suna gaggaya mata maganganu suna zuga ta suna nuna mata zata iya rabuwa da shi. Tabbas ko ba yau ba sai ya dauki mata ki akan mai gidan nan da matarsa.

Sai da ya kai karshen layin a kafa sannan ya tuna cewa da mota yazo ashe, sannan ya juya ya koma kofar gidan ya shiga motar, a ransa yana tunanin maybe maganar da mai gadin yake yi masa dazu kenan. Yana cikin tafiya a hanya wayarsa tayi kara ya duba yaga waliyin Jidda ne ya sake kiransa, sai ya katse kiran ya kuma kashe wayar ya saka a cikin aljihun mota. Su je su neme ta da kansu shi ba zai kai su ba. Sai kuma ya tuna ta ce zata kunna wayar ta ta neme su da kanta.

Ya cigaba da driving, not knowing where to go or what to do.

*Farhan*

Tana kwance a dakin ta, yau duk bata jin dadi, duk abubuwa sun cushe mata a kanta ta rasa madafa. Kuma ma yau zuciyarta duk babu dadi.

Wayarta tayi kara ta dauka ta ga sunan wannan saurayin da ya karbi number dinta a gidan su kawar Jidda. Ta tabe baki, wannan shine kira da yayi mata na uku kenan tun sa da ya karbi number dinta. Kira na farko kin dauka tayi, kira na biyu kuma ta dauka amma ta nuna masa bata gane waye shi ba duk da cewa ta gane dan tayi saving number din tun sanda ya nemi tayi saving din.

Tayi kamar ba zata dauka ba, sunanan irinsu da yawa suna damunta kusan kullum, shamarin shaho masu ado da walwali, masu daukan hankalin yammata da suke desperate for mijin aure a karshe kuma su jefa su a ramin da ba zasu iya fitowa daga ciki ba.

Sai kuma ta dauka tare da sallama murya can ciki.

"Salamu alaikum"

"Ameen wa alaikumus salam gimbiya"

Ta juya idonta.

"Waye yake magana?" Yayi dan shiru ka dan, kamar ransa bai so abinda take masa ba yace "you still did not save my number, did you?" Tace "ai ban gane waye ba ma ballantana inyi saving, waye?"

Yayi ajjiyar zuciya "okay. Mai nema ai ance baya zuciya ko? I called you yesterday and the day before that, sunana Sadiq, na karbi number din ki ne a hannun ki sanda kuka je gidan mu neman address din kawar ku Diyam. Kin gane ni yanzu? Though nayi wannan bayanin tun jiya"

Tace "ohhh okay. Nagane ka. Ya akayi?" Ya sake jin babu dadi, sannan yayi magana kamar mai hada kalmomin, daga dukkan alama bai saba ba "ammm dama address din nan dai dana tambayeki jiya shine dai zan sake tambaya yau. That's if it is okay with you. In kuma akwai damuwa just say so please so that we won't waste each other's time"

Tace "damuwa kamar yaya?" Yace "damuwa kamar banyi miki ba, tunda kin ganni, ni kinyi min ne shi yasa nake bibiyar ki, in banyi miki ba it is okay. Ko kuma maybe anyi miki miji a gida, ina ganin waɗannan sune kadai dalilan da zasu saka ki hana ni address din ki at the moment"

Tace "ko kuma maybe ina gudun halin ku na maza ba?" Sai ya danyi dariya, relaxing a little. "Halin mu na maza kuma? Me muka yi? Allah sarki mu maza bayin Allah" tace "yaudara ma na da dadin baki, yawancin ku haka kuke" yace "nooo, kar ki bari wani mutum daya ko biyu su saka kiyi generalizing din mu. Kuma idan har lissafi za'a yi na gaskiya mazan da ake yaudara sun fi matan da ake yaudara yawa"

Tace "sai dai in lissafin son zuciya za'a yi, dan ni I know a lot of matan da aka yaudara" yace "saboda ke macece ba, ni kuma I know a lot of mazan da aka yaudara" tace "da zaka tsaya mu tantance zaka fahimci ni ce da gaskiya" yace "da zaki bani address din da sai inzo mu tantance ido da ido" ta juya idonta "okay, zan turo maka. But mind you you will have to see my father first".

Tana ambatar father din taji shi ya kwalla mata kira, tayi saurin katse wayar ba tare da yi masa sallama ba sannan ta saka hijab din ta ta fita tsakar gida tana amsawa, daga sitting room ta jiyo muryar sa dan haka tayi can din, tana shiga ta tarar dashi da babban amininsa ne a zaune, gabanta ya fadi, shikenan cewa zasu yi sun fitar mata da miji tunda taki fitarwa. Ta durkusa ta gaishe su sannan ta rakube a gefe.

Abba yace "ya akayi kika san mijin Jidda ya san inda take?" Sai ta basu labarin kiran da yace Yasmin tayi masa da kuma binciken da suka yi har suka samo address din Diyam. "Shi kadai yaje gidan ba tare da mu ba, dan haka bamu tabbatar ya same ta acan din ba ko a'a" ta karasa labarin nata. Abba ya miko hannunsa bani wayarki inga address din da aka turo.

Ta fara inda inda, tana tunawa da maganar da take karshen address din "ammmmmm dama...... Abba, watooooo wayar......... Wayar tana daki bara in dauko" ta tashi da sauri ta fita suka bi ta da ido, da ta dauko wayar mata jima tana juyata a hannunta tana tunanin abinyi, in dai tayi editing zasu gane tunda zasu ga ba sending mata akayi ba kamar yadda ta fada, dan haka taje ta kai musu ta koma gefe tana sosa kai, Abba ya karanta sannan ya dago yana kallon ta, ta sunkuyar da kai waiting for ruwan fada ya fara zuba akanta amma sai taji yace "ki shirya ki je gidan, zaki iya ganewa?" Ta gyada kai, yace "ki je ki tabbatar tana can sannan ki ce mata in ji ni nace indai nine ubanta ta zo ina nemanta" ta sake gyada kai da sauri sai ya jefa mata wayarta tare da kudin mota.

*Jidda*

Cikin kankanin lokaci na gama hada mana kayan mu kaf, sannan na tafi gurin da yara suke wasa na zauna tare da su ina kallon Subay'a tana koyawa Yasmin karatu ina ta mamakin yaran yanzu da irin abubuwan da ake koya musu a school, wadansu abubuwan da suka sani a ni sai da na shiga secondary school na san su.

Muna zaune Diyam tayi joining din mu itama tana correcting din su in sunyi mistake. A haka aka zo aka sanar wai anyi bakuwa kuma tace ni take nema. Muka kalli juna ni da Diyam, abubuwa da yawa suna zuwa min rai amma sai naji nafi zargin Mufida ce Umar ya turo. Sai na aika a tambayo wacece sai aka ce Farhan. Haka kawai naji wani dadi a raina, duk da bansan abinda zai biyo bayan zuwan nata ba amma tabbas nayi missing din ta da kuma dukkan sauran ya uwana.

Tunda nace ta shigo na mike tsaye ina kallon hanyar da zata shigo din, inajin excitement da faduwar gaba a lokaci daya. Tana shigowa kuwa na tafi da gudu na rungume ta ina murna itama tana yi. Ta dago kai tana kallo na "ke ya naga kamar har kin fara cikowa ne, me suke baki a gidan ne?" Nayi murmushi "babu abinda suke bani sai kwanciyar hankali, bana fargabar me yake faruwa ko kuma menene zai faru, na riga na gama yanke shawara na mika dukkan lamura na ga Allah kuma zan bi dukkan abinda yace" tace "good for you. Mutumin ki yana can yana neman zaucewa" nayi murmushi kawai sannan na ja ta muka zauna "bani labari, ya kowa da kowa? Ya Abba?" Ta tabe baki Tace "shi ya turo ni, yace ko dai ki bini mu koma gida ko kuma ki sake wani uban" nayi murmushi "yana nan dai yadda yake kenan" tace "da dan sauki kadan, kwana biyun nan kamar baya fada sosai. Ki je kawai kiyi facing dinsa in yaso in daka ki zaiyi a turmi a tuka masa tuwo da garin ki sai yayi. Tunda dai you can't stay here forever ko?"

Sai dai kuma bai daka ni a turmin ba bayan Diyam ta kaimu gida da kanta a motar ta, asali ma bai ce min komai ba sai key din dakin umma daya jefe ni dashi sannan yace "ki bude wayarki kuma ki kira uwarki, tana can ta tashi hankalin ta tana neman ki".

A ranar da dare na kunna wayar ta wa na kuma kira auncle Muhammad wanda ya rufe ni da fada kamar zai cinye ni danya, sannan daga karshe ya turo min number din da zan samu Umma. Ranar har kusan tsakiyar dare muna waya da mutane, daga wannan sai wancan, na tambayi yaya Tahir dalilin da yasa bai gayawa Umma da Abba ina turo masa message ba sai yace "yanzu ai gashi nan ta samu ta ga yauwanta" na tambayeshi yaushe zasu dawo sai yace "ni dai zam dawo cikin satin nan, ita kuma sai ranar da Baba ya turo mata kudin jirgi" ya karasa yana dariya, nayi murmushi kawai, wato yana sane so yake ya kai Umma gurin yanuwanta kuma ya bar ta acan ta kara hutawa ta huce daga masifar Abba da ta Hajiya.

Washegari tunda assuba Umar yake kirana, wato ya gwada layin yaji yana shiga, ban kashe wayar ba kuma ban yi blocking dinsa ba sai na bar wayar tana ta ringing amma sai na saka ta a silent dan kar karar ta ta dami yara na da suke bacci abinsu. Sai da nayi baccina mai dadi na farka sannan na dauki wayar naga 21 missed calls duk daga gurin sa. Sai kuma messages din da ko karanta su banyi ba na goge su dan nasan magana daya ce a ciki, inyi hakuri ya daina halinsa, ba zai iya rayuwa babu ni ba and other stuffs.

Na dauka gari yana wayewa zan ganshi a gidan amma sai naga bai zo ba har yamma, sai na daure na karanta some of his messages sai na fahimci Abba ne ba zai iya fuskanta ba shi yasa ya kasa zuwa gidan. But he wants to see me and the kids.

A ranar ne na shiga har daki na gaishe da Hajiya, sai ta zauna a kusa dani fuskarta cike da damuwa. "Sannu Jidda. Munji dadi da Allah ya dawo mana da ke gida lafiya. Allah ya daidaita ya raba mu

83 / 106