Chapter 57 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   57 / 106

168K to 171K   out of 316K words

kunyata mu mu ƴaƴan sa a idon duniya, sai ya gaya min dalilin da yasa zai zama sanadiyyar da dole zan hakura da auren Musaddiq"

Tayi hanyar waje da sauri ranta a tsananin bace, na sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen fuskata a raina nace "good. Yau zaiyi facing abinda maybe bai taba tsammani ba. Maybe kunyar wannan abin ya zama sanadiyyar shiryuwar sa".

Ranar duk zuciyata babu dadi, har Umar yazo na gama sallamar sa na kuma gama da yara kawai sai na tafi daki na bar su tare a palo, a haka har suka yi bacci sannan ya shigo yace inje in kwantar dasu shi kuma ya shiga wanka. Ina kwantar dasu a dakina na dawo na kwanta a dakinsa na juya bayana na rufe ido na, a raina ina lissafin rayuwar da Aunty Afia tayi a baya da kuma irin alkawarirrikan da na tabbatar daddyn Aira yayi mata na cewa ya daina, maybe tun bata yarda ya daina din ba har tazo ta yarda kuma ta cigaba da yarda har yau. I can't even imagine how broken she will be in wannan labarin ya same ta. I can't imagine how broken I will be idan ni ce a matsayin ta.

Har dare ranar bana cikin walwala, har Umar ya dawo na sallame shi na kuma gama da yara suma sai na tafi daki nayi kwanciya ta na barsu a falo, sai da suka yi bacci sannan Umar ya zo ya ce inje in kwantar dasu, na kwantar dasu a dakina nayi musu addu'a sannan na dawo dakin Umar na tarar yana wanka sai na kwanta na juya bayana na rufe idona, hoping in ya fito zaiyi kwanciyar sa dan ni kam bana cikin mood kuma bana jin duk dadin bakinsa akwai abinda zai yi ya sakani in the mood.

Ina kwance ya fito, naji ya watsamin ruwan gashin kansa a fuskata. Na bude ido ina kallon sa yace "nasan dama ba bacci kike yi ba. A penny for your thoughts?" Na danyi murmushi kawai na mayar da ido na na rufe. Naji ya hawo kan gadon na sake bude ido na ganshi kwance ruf da ciki yayi tagumi da hannu daya ya zuba min ido. Na lura ko ruwan jikinsa bai goge ba nace "hey, zaka jika min gado da ruwa fa?" Yace "me yake damunki?" Na dan bata rai, there is no way da zan bashi labarin cewa tsohuwar karuwar sa yanzu ta koma karuwar mijin kanwar mamana. Nace "babu komai fa na gaya maka" ya kwaikwayi muryata "babu komai fa na gaya maka. Tun ina falo nasan in na tambayeki cewa zakiyi babu komai bayan ni nasan akwai komai. But ko ba zaki gaya min gabakidaya ba ki gaya min in yana da dangantaka da zuwan matar Bashir gidan nan"

Na yi shiru ina kallon sa sannan nace "akwai wani abu ne da zai saka ni damuwa idan Surayya ta zo gidan nan?" Ya daga hannu "nooo. Kawai dai bana jin dadin yadda kike yi ne tun ranar da ta zo din, shi yasa nake so in confirming babu abinda tace miki. Ni yaushe rabona ma da in ganta, ko mijinta?"

Na dauke kai amma bance komai ba. Sai ya kara matsowa ya dora kansa akan kirjina yace "you know, I was thinking. Kudin da nace miki na samu last month, shine nake tunanin yi mana gyaran gidan nan da shi. What do you think?" na bude idona, tun last year Baba ya matsa masa ya zuba kudi a cikin business din sa da yake yi na fata, yace masa aiki kadai ba zai rike shi ba sai ya hada da business. Shine last month aka turo masa wasu kudi a matsayin ribar daya samu na shekara daya.

Nace "gyaran gida kuma? Haka ake business din dama? Daga samun riba sai a kashe?" Yayi dariya "to dan me ake business din dama? Ba dan a samu riba a kashe ba?" Na ja kunnen sa "nooo, in aka samu riba sai a kara karfin jari, har sai jari yayi karfi sosai sannan ake fara kashewa" ya tashi zaune tare da jawo ni zaune nima "I just want to do something to make you happy, you don't seem happy" na shafa fuskar sa "ba sai ka kashe min kudi zan zama happy ba, kuma gidan nan babu abinda ya same shi"

Yace "yes, babu abinda ya same shi amma chanji yana da dadi, ko ya akayi gyaran zaki ji dadi am sure" nace "wai wanne irin gyara za'a yi ne ma?" Ya gyara zama. "Kawai tagogi da kofofi za'a chanja a mayar da su na zamani, sai ayi penti, sai kuma a chanja furnitures da curtains da carpets, if kudin zasu isa sai a chanja TV set suma"

Na girgiza kai "uhm uhm, ni furnitures dina babu abinda sukayi" yayi dariya "furnitures din ki ko furnitures din mu? They are mine as much as they are yours tunda sanda kina gida ai ba'a yi miki ba sai da aka aura miki ni sannan aka yi mana" nace "whatever. Amma dai babu abinda sukayi ai" na fada ina shafa gado na, yace "babu abinda suka yi amma chanji yana da dadi ai" nace "to su kuma wadannan din ya za'a yi dasu?" Yace "I was thinking mu kai wa Umma su ta chanja itama. Ba wai dan nata sunyi wani abu ba, saboda itama ta chanja taji dadi"

Na cigaba da kallon sa bance komai ba sai yace "common just say yes mana, why are you being difficult" na juya ido na "ba wai difficulty bane ba, kasan dai yadda muke da Mama yanzu, she is already thinking komai naka a gurina yake karewa, bana so mu......"

Yace "ai ba ke zanyi wa ba. Kaina zan yiwa da matata da yayana dan jin dadin mu. Am sure Mama will understand that" na sake bude baki zanyi magana sai yace "na gama magana. And I am the boss" na juya ido na "yes boss Sir" yayi dariya tare da jan cheeks dina "that's right. I am the boss. Now, je ki kawo min tea ki dawo sai muyi maganar color da design din da zamu yi"

Washegari da safe ina gyaran daki waya ta tayi kara, na duba naga yaya Mubaraka sai na dauka da sallama ta na fara yunkurin gaishe ta sai tace "albishirinki Jidda" nace "goro" a raina ina tunanin menene albishir din? Mama ta yarda da magana ta ko me? Sai tace "Baba ya biya miki aikin hajji" nayi kara tare da sakin waya na rufe bakina ina jin ƙwaƙwalwa ta ta toshe, Umar ya shigo dakin da sauri, ya dawo daga kai Yasmin school "lafiya?" Ya fada yana kallona, ya kasa tantance karar da nayi ta murna ce ko sabanin haka.

Wayar da take kusa da kafafuwana ya sunkuya ya dauka ya saka a kunnen sa "hello?" "Wow. Haba? Yaushe?" "Kai Baba ya biya mu, Allah ya biya shi shima. Ita da girls gabakidayan su?" Yayi dariya "zan je in samu Baba, dani ya kamata ayi tafiyar nan gaskiya. Ai ba za'a barsu su tafi babu namiji ba ko?" Ya sake dariya "kinci goron albishir. Har gida zan kawo miki" sai kuma ya kashe

Nayi tsalle na rungume shi "Baba ya biya min zanje Hajji" yayi dariya "didn't know it will make you this happy da tuni nayi insisting" nace "happy? Ana maganar one of the pillars of islam kana maganar happy, ai abinda nake ji yafi karfin happy"

Kuma da gaske nake na jima banji dadi irin na ranar nan ba.

Umar yayi ta lobbying, bayan Baba ya gama ja masa aji tare da yi masa fadan cewa shi har yanzu ya kasa girma ya kafa kansa yadda zai ke yi wa kansa komai da komai sai kuma yaci sa'a shima aka biya masa muka tafi tare, duk da dai already dama shi sun taba zuwa tare da yaya Mubaraka.

Maganar tafiya ta Hajji ta baza family na kamar gobarar daji, har gida aka yi ta zuwa ana yi min murna tun kafin in tafi, ina kuma lura da yadda yan'uwa na suke yi min kallon sha'awa kamar babu wadda rayuwarta take burge su irina. A lokacin ne mukayi waya da Surayya na bata labari kuma tayi min murna sannan tace "kiyi amfani da wannan damar Jidda, ki roka wa mazajen mu shiriya" na gyada kai kamar tana kallona "insha Allah. Yana daga cikin abu mafi muhimmanci da zanyi addu'a akai.

Cikin lokaci kankani aka gama komai muka tafi ni da Umar da Muhibbat, Muhsina da Mufida. Da zamu tafi nayi niyyar kai su Yasmin gidan mu sai ga mota Mama ta aiko da ita wai za'a dauke su, ban ce komai ba na hada musu kayansu suka tafi suna ta kuka, kuma ko airport bata je dasu ba ranar da zamu tashi tace zasu yi rigima in suka gan mu. Muka gama aikin hajjin mu successfully muka dawo, duk da dai su Muhsina suna ta sha min kamshi amma ni ibada ta kawai nayi ban damu dasu ba ballantana in saka su a raina. Nayi adduoi sosai, musamman akan Umar, na kuma yiwa kaina addu'a da iyayena da yayana.

Muna sauka na samu labarai marasa dadi guda biyu, na farko an fasa auren Aira, babu wanda ya san dalili, amma ni na sani, ka kallo daya na yiwa Aunty Afia nasan cewa ita ma ta sani and I felt her pain. Labari na biyu shine Surayya tahaihu amma dannbai zo da rai ba.

Bansan Umar ya bayar da aikin gyaran gidan mu ba sai da muka dawo, nazo na tarar da gida kamar ba namu ba, an gyara shi fes anyi fentin ko'ina an chanja furnitures din dakina da kujerun falo an saka royals masu colours brown, golden brown, da kuma golden, an saka matching rugs da curtains. Komai yayi kyau kamar dakin wata sabuwar amarya, amaryar ma yar masu kudi. Dakin baƙi ma an gyara shi an cire gadon ciki an saka twin beds na yara kowa kuma da wardrobe din sa da yar karamar dresser, dakin yayi matukar yin kyau.

Da gudu nake zagaya gidan ina bi daki daki har naje dakin sa, ina budewa na tsaya ina kallon dakin babu abinda aka chanja a ciki dan daga alama ma ko bude shi ba'a yi ba tun da muka tafi. Yazo ya tsaya a bayana ya dora kansa a wuyana yana dariya "don't comment, kar ki ce komai" na juyo "shi nan dakin laifin me yayi da ba'a gyara shi ba?" Ya shafa kansa Yace "kudi ne yayi min short, za'a gyara shi in an samu wasu, for now babu wanda ya san ba'a gyara shi ba daga ni sai ke" Na juya ido na "sai na gaya wa duk wanda yazo" yayi murmushi "ke za'a yiwa dariya ai ace dakin mijinki bai yi kyau ba" na shafa fuskarsa "I don't care, tunda mijina yana da kyau ban damu da kyan dakinsa ba" yana murmushi ya kama hips dina ya daga ni ni kuma na makale a jikinsa "da gaske? You think ina da kyau?" Nayi murmushi nima nace "the most handsome man I have ever seen"...........

Tunda muka dawo kullum sai mun samu baki masu zuwa yi mana barka da zuwa, mu kuma muka bude jaka mukayi ta rabon tsaraba. Kasancewar dawowar mu da kuma gyaran gidan mu ya faru kusan lokaci daya sai ya zamana duk wanda yazo mana sannu da zuwa sai kuma ya ga gyaran da mukayi, kowa kuma ya gani sai yayi santin yadda gidan yayi kyau musamman yan gidan mu.

Umma da Hajiya da Farhan da Amira ne sukafara zuwa, a lokacin ne suke bani labarin cewa Umar Farhan ya kira lokacin muna Saudiyya yace tazo gidan mu ta hada mana kayan mu za'a zo ayi aiki, ita da Amira ne suka kwashe mana kayan mu bayan an gama kuma suka zo suka jera mana komai suka gyara mana. Sannan kuma ya turo mota aka kwashe furnitures din da aka cire aka kaiwa Umma kamar yadda yace za'a yi. Suka nuna min hotunan yadda aka gyarawa umma dakinta ita ma da kayana, har fenti yaya Tahir ya saka akayi mata kafin a saka kayan, Bedroom din ta da falonta sunyi kyau fes kamar ba su ba.

Duk hirar da muke yi Hajiya tana jin mu, I was surprised da naji bata ce komai ba sai bin mu da kallo kawai take yi, da nace su zagaya gidan su gani ma na dauka zata ce ba zata gani ba amma sai naga ta tashi sun zagaya tare har ma dayi min murna "Allah ya sanya alkhairi yasa a kashe lafiya" nace "ameen"

Da zasu tafi sai na roki Umma ta rokar min Abba ya bar Amira tazo ta dan kwanar min biyu dan in samu in huta sosai, dan ba karamar gajiya nake ji ba ga kuma baki basa barina in samu isashshen hutu, ga yara. Ta girgiza kai "ba zai bari ba. Nima na san zaki dawo a gajiye shi yasa da zamu taho na tambayeshi zan bar miki ita amma ya hana, yace baya son kwadayi" suka yi dariya gaba daya ni kuma naji babu dadi.

Washegari sai ga Mama Sa'a tazo ita da ƴaƴan ta baki daya, na lura Mammy da jakar kaya a hannun ta. "Dama yau nace zamu zo mu yi miki sannu da zuwa sai kuma Hajiya tace in kawo miki Mammy ta taya ki zama tunda babu abinda take yi a gida, taji kina complain din gajiya kuma Abba ya hana ki Amira, na samu babanta ya barta da kyar, sai take yi miki ayyuka kuma take kula miki da yara kafin ki samu ki huta"

Naji dadi tunda nasan ina bukatar taimako, duk da dai ba Mammy naso ba nafi son Amira amma hausawa sunce a rashin uwa akan yi uwar daki. Nayi mata godiya sosai kuma na kira Hajiya ita ma nayi mata godiya "nasan yadda kike ji ai, aikin hajji ai akwai gajiyar wa, nima sanda naje da na dawo ai har sai da na yi jinya" sai ta dauko labarin zuwan su hajji ita da Abba tana bani har da dariya, abinda bana jin ni da ita mun taba zama munyi.

Naji dadin zuwan Mammy, problem din dana dauka zan samu da ita na rashin kunya da rawar kai duk ban samu ba, kullum zata gyara min gida ta kula da yara ta kuma yi mana girki, mu kuma muka samu damar hutawa ni da Umar sosai, sai dai idan munyi baki ta je ta kira ni in basu kulawa in sun tafi in koma.

A haka har na wartsake tas na fito na cigaba da harkoki na, Umar kuma ya koma aikin sa, amma ban ce Mammy ta koma gida ba sai na barta ta cigaba da zama tunda naga tana son zaman kuma bana samun problem da ita.

A lokacin ne wani abu ya faru.........

Suddenly without warning Umar ya chanja min gabakidaya ya rikice min. Rana daya ya wuni a office tun safe har magrib ba tare da ya kira ni ba ba kuma tare daya dauki kiran da nake ta jera masa ba. A ranar hankali na ya tashi nayi ta sake saken ko wani abun ne ya faru dashi, na kasa hakuri sai na kira Mufida inji ko yaje gida ko kuma sunji wani labari da banji ba, sai ta gaya min cewa yanzu taji suna waya da Mama.

Na cigaba da jira, na kuma cigaba da kira amma still bai dauka ba sai bayan magrib ya dawo gida. Ina jin tsayuwar motarsa na tashi da sauri da Asad a hannuna na bude masa kofa, glad that he is okay, yana karaso wa nayi masa murmushi "sannu da zuwa" ya amsa "yauwa sannunki" sao ya wuce ni, ignoring the hug that I was about to give him, na bi shi a baya amma da yake sauri yake yi kafin in shiga corridor har ya shiga dakin sa ya rufe kofa, ina kama handle din naji yayi locking dinta ta cikin, sai na kasa motsawa daga inda nake, mamaki ya cika min zuciyata na kuma fara tuhumar kaina idan nayi masa wani laifi ne ba tare da na sani ba dan ni kam da sanina bana jin nayi masa komai.

Yasmin wadda ta na dakina sanda ya shigo ta fito tana rarraba ido "mommy Daddy ne yazo? Ina yake?" Nace "yana dakin sa Yasmin, Daddy ya gaji zai kwanta ne" na wuce ta na shiga dakina na ajiye Asad na zauna a bakin gado tare da dafe kaina ina jin tunani na ya na tsayawa a waje daya "me yake faruwa?"

Asad ya taka ya fita shima yana kiran sunan babansa da gwaranci. "Daddy! Daddy!" Suka hadu shi da Yasmin suna ta kira suna buga masa kofa amma ko alamar budewa bai yi ba. Naje na dauko su na basu abinci, suka ci da kyar dan sun saba tare da shi muke dinner kullum, sannan nayi musu shirin bacci wanda sai da mukayi dan karamin yaki sannan sukayi wajen karfe taran dare, amma har lokacin bai bude kofa ba.

Bayan na samu sun kwanta nayi musu addu'a sai nima na dan kwanta ina tunanin abinda ya kamata inyi, inje in buga masa kofa ne in tambayeshi lafiyarsa kalau ko kuma in share shi tunda dai sanda ya shigo ban ga alamar akwai rashin lafiya a tare da shi ba.

Ina kwance ne naji kamar maganganu a falo, sai na tashi na fita da sauri, ga mamaki na sai na ganshi zaune akan dining shida Mammy ta zuba masa abinci yana ci tana masa hira yana ta zabga murmushi. Naji wani abu ya taba zuciyata. Na karasa na tsaya a bayansa "ka fito ashe. Yara sun gama rigimar neman ka har sun hakura sunyi bacci" ko kallon inda nake baiyi ba ballantana ya bani amsa, na zagayo gefen sa na ja kujera na zauna sai Mammy ta mike zata bar gurin sai yace "ina kuma zaki je muna hirar mu?" Tayi murmushi tana jujjuya ido "bacci nake ji, sai da

57 / 106