Chapter 29 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   29 / 106

84K to 87K   out of 316K words

tashi sannan ya miko min cup din da yake kai "ga wannan to, da zafin sa" na karba sannan na kai bakina a hankali na kurba ina jin zafinsa yana kona bakina amma ko kadan zafin bai kai wanda nake ji a zuciya ta ba.

Yace "yayi miki? Ko akwai abinda za'a kara?" Na girgiza kai kawai. Sai ya dauko bread din da ya sako akan tray din ya fara shafa min jam a jiki. "Ki hada da bread zaifi rike miki ciki. Na san kwan ma cewa zaki yi ba zaki ci ba" ban ce komai ba na cigaba da shan tea dina. Sai da ya gama shafawa ya miko min na karba na gutsira amma sai naji zakin jam din ya koma daci a kan harshe na.

Na ajiye na jingina kaina a jikin gado sai hawaye suka fara zarya a fuskata. Ya ajiye bread din hannunsa "Jidda! Oh my God. Wallahi da kin san yadda zuciyata take zafi in kina kukan nan da kin daina. Na fa yi miki bayanin, ya ci ace kin fahimce ni.  Zuciyata tana neman fashewa saboda takaicin taki zuciyar tana zarginta da irin wannan cin amanar. Kin san........."

Na katse shi tare da saka idona cikin nasa nace "dacin zuciya? Zafin zuciya? Fashewar zuciya kake magana?" Na kamo hannun sa na dora akan kirjina nace "ina ma dai ana musayar zuciya Umar dana baka tawa ko ta second daya ne kaji halin da take ciki akan abinda take tunanin kayi mata"

Ya marairaice kamar zaiyi kuka "na sani Jidda. Bazan iya kwatantawa ba wallahi dan idan nine maybe da yanzu ana jana'iza ta dan na tabbatar mutuwa zanyi, na tabbatar zuciyata bindiga zata yi. Amma kuma nasan da nine aka zo aka gaya min wannan maganar a kan ki Jidda wallahi ko Mama ce ta fada ba zan yarda ba ballantana wata stranger. Jidda ke mai yasa kika yarda har kika bari zuciyarki ta shiga wannan halin? Me yasa har yanzu kike shakku bayan kuma duk bayanin da nayi miki"

Na dauke idona daga cikin nasa, gabakidaya ya gama karya min zuciya naji sauran spaces din daya rage na rashin yarda da banyi dashi ba yana cikewa. Ya jawo ni jikinsa ya rungume yana jijjiga ni kamar Baby. "Dan Allah kiyi shiru haka Jidda. Kina son bpn ki ya hau ne? Kin tsorata ni da yawa fa, jiya I tot bpn ki zai hau I tot zaki fara labor ne preterm. Shi yasa nayi miki allurar bacci I was scared to death"

Na zagaye hannayena a wuyansa ina kara jawo shi jikina tare da saka fuskata a jikin wuyansa i a cigaba da kuka na. Sai ya saka hannunsa ya ciccibo bom bom dina ya dora ni akan cinyarsa gabaki daya tare da kankame ni tamkar zai hada ni ni da cikina ya saka a nasa cikin, "dan Allah ki daina kuma Baby, zuciya taba zata iya dauka ba musanman in na tuna saboda ni kike wannan kukan"

Na dago kaina ina kallon sa da kumburarrun jajayen idanuwa na nace "labarin da ka bani gaskiya ne ko?" Ya gyada kai da sauri. Na hadiye wani abu nace "Umar kasan ina son ka ko? Kasan ina sonka sosai da sosai ko?" Ya sake gyada kai da sauri yana shafa gashin kaina. Na cigaba "in kaci amana ta Allah ba zai barka ba. In kuma kayi min karya ba zan taba yafe maka ba"

Ya dora goshinsa akan nawa, hancinsa akan nawa yace "bazan iya ba ma Jidda. Believe me bazan iya ba. Dan Allah ki yarda dani"

Sai na mayar da fuskata cikin wuyan sa na cigaba da kuka na shi kuma ya cigaba da aikin lallashi har sai da nayi shiru sannan kuma ya matsa min nashanye tea din da ya hada min sannan naci two slices of bread din daya shafa min jam a jiki.

Sai kuma na sake komawa na kwanta, jiki na ya dau zafi zazzaɓi yana neman rufe ni, ya bani magani nasha sannan ya lullube ni ina jin yana waya office din sa yana gaya musu yau ba zai fito ba Madam bata da lafiya, ina jin su suna tsokanar sa akan hakan amma bai fita din ba.

Ranar kusan duk aikin gidan shi yayi. Sai da rana ne ya fita ya siyo mana abinci ya dawo nan ma ya matsa min na danci kadan, lokacin zazzabin ya sauka sai kuma ciwon kai da yake damuna. Na dauka zai gwada bp na ma amma yaki yace tsoron abinda zai gani yake yi.

Sai da dare sannan ya bude min kofa muka fita yana rike da ni muka zagaya gidan na dan motsa jikina sannan nazo nayi wanka na kwanta. Sai dai har lokacin zuciyata tayi min wani irin nauyi kuma na kasa sakar masa fuska dan haka da yazo ya kwanta a kusa dani ma sai na juya masa baya, sai kuma ya hakura bai matsa min ba.

Kwanan mu uku Umar ko office baya zuwa, sai dai kullum ya kira su ya ce ayi covering for him yana da uzuri ne. Lallabawa kuwa da tarairayar na sha ta har na gode Allah dama kuma shi gwani ne ta wannan bangaren amma na wannan lokacin extra special ne. Sai ranar da muka kwana uku da daddare na same shi.

"Ya kamata gobe kaje office, kar muje ka sami matsala fa" ya shafa kansa yana kallona "kina son inje?" Na dauke kai "aiki ai dole ne a gurin ka, tunda dole zamu ci abinci kuma kai zaka yi providing. Nima ina so inje school goben"

Ya girgiza kansa "ki bari sai monday, dazu ma fa naji kamar akwai zazzabi a jikin ki" na daga kafada "shikenan, amma kai kaje office please" sai naga kamar ransa bai so hakan ba, he seemed hesitant amma kuma sai ya gyada kai "okay, zanje".

A daren muka shirya a gado, a lokacin na fahimci ba karamin hakuri yayi a kwana ukun nan ba dan yi yayi kamar zai haukace min tare da dogon sabon bayar da hakuri hadi da dogayen alkawarirrika na cewa ba zai sake yin sakem da wani ko wata zai kuma bata min rai har haka ba. Nima kuma nayi masa alkawarin bazan kuma wasu maganganu marasa tushe su kuma shiga tsakanin mu ba saboda da gaske nima nayi missing din mijina a kwanakin nan.

Haka muka raya daren dan ma katoton ciki na yana yi mana cikas, da safe ma kamar ba zai tashi ba wai shi ya fasa zuwa office din, sai da na matsa masa na kuma gaya masa in bai tafi ba to ni zan tafi school sai dai ya zabi daya, sannan ya tashi ya shirya shaf shaf na rako shi har bakin mota kuma kamar ba zai shiga ba sai ya shiga.

Har na juya zan koma ciki sai ya sake fitowa, na juyo ina kallon sa, a raina ina tunanin abinda ya sa baya son fita din, sai ya marairaice yace min "babu inda zaki je in na tafi ko? I mean ba zaki je gidan ba ko?" Sai na fahimci fear dinsa, ya dauka har yanzu ina kan baka na na tafiya gidan mu shi yasa baya son tafiya, ya dauka so nake ya tafi dan in samu damar tafiya.

Nayi masa murmushi tare da girgiza kaina "I am not going anywhere" sai ya dawo da sauri yayi kissing din lips dina yace "thank you" and I saw his face relaxed.

Bayan na dawo ciki ne na zauna na fara wani tunani, ko da ace ina son zuwa gidan ma can I? Nasan Abba sosai na san policy din sa, yayye na ma da suka yi shekara da shekaru basu taba yin yaji ba sai ni daga yin shekara daya? Ai in naje duka na ne kadai ba zai yi ba shima dukan da albarkacin cikin jikina ne.

Sai kuma wani tunani yazo min. What if ace dukkan abinda Zuwaira ta gaya min gaskiya ne? Kuma ace Umar yayi admitting openly cewa yayi din. Kuma ace naje gida Abba ya koro ni yace in dawo gidan miji na. What would I do then?

Nayi sauri na girgiza kaina a hankali nace "Allah kar ka kawo min wannan rana ya Rabbi" amma sai nayi tunanin maybe fa akwai wadda ta taba samun kanta a irin wannan situation din ko? Ko yaya tayi?

Kusan duk bayan awa daya sai Umar ya kira ni. "You know I love you right?" Nasan duk kamun kafar kar in tafi gida ne. Da wuri ya dawo ranar na tare shi tamkar yadda na saba yi kullum, shi kuma ya taho min da sabuwar waya yayi replacing wadda na fasa ranar nan, daga ranar muka saka wannan maganar behind us muka cigaba da acting as if nothing really happened. Sai ma wani sabon babin soyayya da muka bude.

A haka har cikina ya shiga watan haihuwa. Yaya Mubaraka ya hada ni da ita muka je siyayyar kayan haihuwa tunda ni ban san abubuwan da ake bukata ba ita kuma ta san komai na kan haihuwa. Muna can ma ta kira Mama take gaya mata abinda muke yi, kafin mu gama Baba ya kira ta yace duk abinda aka siya shi zai biya.

Umar yana jin haka ya saka muka yi ta lodar kaya tunda ba kudinsa ne zasu motsa ba. Yaya Mubaraka kuma ta taya ni muka zabi kayan fitar suna masu kyau da tsada har set uku, kayan Baby kuwa babu abinda bamu siya ba har da abinda ni kaina ban san amfanin sa ba sai dai in na karanta. Bamu iya gama siyayyar a rana daya ba sai da muka yi kwana uku a jere muna fita sannan muka kammala. Amma bata bar min kayan a hannuna ba sai ta ajiye min wadansu wadanda zan bukatar immediately idan na haihu sauran kuma ta tafi dasu gida tace sai na haihu za'a kawo su a matsayin kayan barka kamar yadda yake a al'adance. Nawa kayan kuma ta kaini gurin tailor dinta zaiyi min dinkuna a jikin su.

Kwana biyu bayan nan sai Umma ta kira ni a waya take yi min zancen zuwa gida in haihu a can kuma inyi wanka kafin in dawo gidana. "Ki tambaye shi, in ya amince sai Afia tazo ta dauko ki . Ni bana jin dadi in na tuna ke kadai ce a gida ga haihuwa ba'a san sanda zata zo da yadda zata zo ba"

Nayi murmushi kawai na amsa mata da to, amma a raina nasan Umar ba zai taba yarda ba. Amma dai banyi kasa a guiwa ba sai na shigar masa da maganar lokacin da muke dinner.

Ya yamutsa fuska "menene haka din?" Nace "au kai baka san ana zuwa gida in ciki ya tsufa ba. Chafdi. Ai kuwa tafiya zanyi" yace "kwana nawa zakiyi a can?" Nace "kwana? Wata nawa zaka ce dai. Kamar wata uku haka dan sai na haihu na yi arba'in yarinya tayi kwari sannan zan dawo"

Ya fara girgiza kansa. "Ina, ina, kina so in mutu kenan" na daga hannu na nace "bani na fada ba. Umma ce ta fada" ya rike hannuna kamar zaiyi kuka "Jidda ba zan iya ba kin sani. Kiyi mata bayani yadda zata fahimta" na juya ido na. "Ni ba zanyi mata bayanin komai ba, sai dai kai kayi mata. Ai dama cewa tayi in tambaye ka in ka bari in tafi in kuma baka bari ba shikenan" ya sake marairaice wa "yanzu in nace ba zaki je ba zata ji babu dadi, ni kuma....ni kuma"

Nayi murmushi, yana ta struggling da kansa yana so ya farantawa Umma kuma baya son rabuwa da ni. Sai naji dadin hakan da yayi dan nasan da wani mijin ne da direct kawai zai fada yace ba zanje ba. Ya cigaba da bayani. "Ki gaya mata ni doctor ne, kuma so nake in dauki annual leave da zarar cikin ya cika 38 weeks yadda zan zauna a gida in kula dake irin kulawar da ko a gidan ne ba lallai ki samu wadda ta fita ba. Ko haihuwar yazo a gida zan iya karba, ko tazo da wata matsala zan sani tun kafin matsalar ta zama matsala, dan Allah Baby kiyi mata bayani yadda zata fahimta sosai" na gyada kai ina murmushi "da gaske zakaiya karbar haihuwa ta? I want to see you in action" yayi dariya "zaki sha mamakin how smartly zan karba kuwa. Ni zan fara daukan babyn mu,a hannuna zata zo duniya" ya fada dreamly. And I instantly know mai raba shi da yarinyar nan in tazo duniya sai Allah.

Tare muka je gida dashi, ya ajiye ni tare da jaddada min in yi wa Umma bayani yadda ba zata ga rashin kyautawar sa ba. Sai ya tafi ya barni yace da dare zai dawo ya dauke ni. Ina shiga tun daga tsakar gida na jiyo Abba yana fada a falon Umma "ku mata wata irin karamar kwakwalwa ce daku kuma kuce lallai sai kun yi amfani da ita kun yanke hukunci. Ta yaya zaki ce zaki dauko yarinya daga gidan mijinta ki kawo ta nan ta zauna? Mai zata yi miki anan din in ta zauna?"

Sallama ta ya saka suka juyo a tare, ya nuna ni da dan yatsa "koma inda kika fito. Kar ki sake ki karaso dakin nan" na tsaya a inda nake ban motsa ba, kawai naji hawaye ya taho min. Na farko gashi na shigo na tarar ana yiwa uwata fada duk yan gidan suna ji,na biyu kuma daga shigowa ta zai kora ni in koma. To shikenan ita mace dama bata da gidan iyaye sai gidan miji?

"Ba zaki wuce ki tafi ba?" Nace "Abba ya tafi fa, ajiye ni dama yayi ya tafi yace sai dare zai zo ya dauke ni mu koma" yace "au ho, na dauka zaman goyon cikin kika taho already. Allah ya rufa miki asiri da yanzu zaki juya ki koma" sai kuma ya fito ya bani guri na shiga shi kuma ya fice,sai daya fita sannan na tuna ko gaisheshi ban samu nayi ba"

Na zauna a kusa da Umma ina share hawaye, har yanzu ban daina wannan saurin kukan nawa ba kuma bana jin zan daina. Ta kirkiro murmushi "kar kiyi kuka, tunda babanku bai bari ba shikenan kar ma kiyi wa Umar din maganar. Kiyi zamanki kawai Allah ya sauke ki lafiya" na gyada kai na, "ameen. Kuma yace ma zai dauki annual leave dan ya zauna dani a gida, kuma kinga likita ne shi sannan bangaren daya karanta kenan dan haka zan samu kulawa sosai daga gurinsa ko da kuwa haihuwar tazo da gaggawa ne zai iya karba ko da a gidan ne".

Ta gyada kai tana fahimta, naga alamar hankalin ta ya kwanta sosai, a raina sai naji tausayinta nace Allah sarki uwa, ita duk dan ni take yi tana nema min sauki ne. Mun danyi hira da ita, na bata labarin kayan da muka siya na haihuwa ita kuma ta bani labarin admittion din da mijin Aunty Afia ya samarwa Abbah a state university wudil. Nayi mamakin da Abbah bai gaya min ba duk da muna waya kusan kullum sai tace ai basu gama musu screening ba shi yasa yaki fadawa kowa.

Muna cikin hira Farhan ta shigo gidan, tana jin muryata ta shigo dakin a guje zata fado jikina Umma tayi saurin riketa "baki ganin yadda take? In kuma kina so kiyi muku asarar ɗa ne to bismillah" na zauna a gefe na tana dariya "chaf ai kuwa da yaya Doctor ya tsire ni a kasuwa. Wannan cikin yana tabuwa ne?" Nayi shiru ban bata amsa ba tunda Umma tana gurin. Sai ta jani muka tafi dakin mu inda yanzu ita kadai ce a ciki muka fara hira.

Na lura duk ta rame, na tambayeta dalilin ramar ta tace "hmmm. Har ma zaki tambayi dalili Jidda? Kamar baki san yadda nake zaune a gidan nan ba? Yadda kika san akan kaya nake wallahi haka nake ji" nace "ke Farhan, gidan ku ne fa, in baki sake a nan ba a ina zaki sake?" Ta daga kafada "oho. Nima ban sani ba. Amma ni dai ba'a nuna min cewa anan ya kamata in sake, kullum zancen in fito da miji in fito da miji kamar akan mutane nake a zaune. Dazu ma fa sai da Abba yace wai gab yake da yin shela a masallaci akan wanda yake so na ya fito"

Na bude baki zan yi kwakwazo sai naga ta fara hawaye, sai na kwantar da murya "ke da wasa yake yi miki, Abba ba zai taba yi miki haka ba. Kawai dai yana nufin ki mayarda hankalin ki wajen samun miji" ta harare ni "dama mijin samo shi ake yi? Gaya min inda ake samu inje in samo a can"

Nayi ajjiyar zuciya "ba haka nake nufi ba sister, hausar ce banyi dai dai ba. Babu inda ake samun miji kina gida rabon ki zai tarar dake. Dan dai na yi aure da wuri ne shi yasa Abba ya saka miki ido, dan kuma dama can ya saba aurar da ƴaƴan sa da wuri. Dududu shekarar mu biyu fa da yan watanni da gama secondary school. Idan a wani gidan ne sai yanzu za'a barmu yin samari, idan a wani ne ma har yanzu bamu isa yin samarin ba"

Sai na bata labarin gidan su Umar, Mufida har yau bana jin tana da wani saurayi. Ita kanta muhibbat sai last week naji ana maganar anzo neman aurenta bayan ta gama jami'a tayi service ta samu aiki sannan aka fiyo neman aurenta. Kuma ban taba jin wani yayi mata maganar ta dade bata yi aure ba.

Muhsina kuwa anyi posting dinta service bayelsa, na dauka za'a nemi a dawo da ita kusa amma sai naji ana shirye shiryen tafiyar ta can din, da nayi complain sai Umar yace "idan mutum bai fita duniya ba ta yaya zaiyi yasan me duniya take ciki? Ki barta kawai ta tafi, experience ne ai"

Ina gama bawa Farhan labarin tace "chafdi. Wallahi Abba ko Kaduna ba zai barni inje ba in dai ba gidan miji na ne a

29 / 106