Chapter 4 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 106

9K to 12K   out of 316K words

bansan sanda nayi ba dan zuciyata bata yi shawara dani ba kawai ta bi umarnin sa. Ajjiyar zuciya naji ya sauke mai karfi "alhamdulillah. Masha Allah. Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan kyakykyawar sura. Jidda Allah yayi miki kyau, ki gode masa, fuskar ki da suffar ki mai kyau ce sosai. Kuma yanayin yadda kike ta faman gyaran hijab dinki da yadda kika makale a jikin kofar kadai ya saka naji a raina cewa kyawun ki ba'a physical kadai ya tsaya ba, har cikin zuciyarki ke kyakykyawa ce. Ni Umar Faruq naga Hauwa'u Maijidda kuma ina sonta, har cikin ruhina ina son ki. Na yaba da komai da idanuwa na suka gani, ina kuma neman alfarmar ki bani dama in gama sanin abinda ban sani ba kema kuma ki san duk abinda kike bukatar sani daga gare ni, that's in abinda kika gani physical yayi miki....."

Ya fada yana nuna kansa, na kalle shi briefly na kuma mayar da idanuna kan band dina da nake ta jujjuya wa a hannuna, ina jina kamar ina yawo a cikin gajimare.

Yace "Maijidda.......kiyi magana mana..... please zaki bani dama? Zaki bamu dama mu karanci juna sai kuma muga inda Allah zai kaimu. Me kika ce?"

Na motsa bakina amma sai na kasa magana, to me ma zance ne? Ina sonsa, kuma abinda na gani na daga suffarsa yayi min, sannan nima ina fama da irin ciwon da yake fama dashi kuma nima fuskarsa da murmushin sa sune suke ratsa cikin baccina a duk lokacin dana kwanta, wannan shine amsar dana bashi amma ba zan iya gaya masa ba, kunya da kuma pride ba zasu barni in gaya masa ba, at least not now. Na bude bakin sai kuma na mayar na rufe.

Ya rankwafo yana leka fuskata "ba zaki yi magana ba ko? Ni kadai zanyi kida na kuma inyi rawa ta ko? Shikenan to, in dai zaki saurara kuma zaki kalla I will gladly sing and dance for you, indai har hakan zai saka ki cigaba da yi min kyakykyawan murmushin ki" na sake yin murmushin, sai kuma na kama hannun motar ina kokarin budewa, naji ta a rufe, na juyo ina kallon sa "am I a prisoner?" Ya daga hannu "nooo, never. But at least say something mana, anything........ please" nace "abbana zai iya shigowa makarantar nan a kowanne lokaci, and do you know abinda zaiyi min in ya ganni a cikin motar nan?"

Ya girgiza kai, his face looking concern. Ni kaina bansan abinda zaiyi min din ba amma ba karamin aikinsa bane gobe inji an daura min aure, zaice zan dauko masa abin kunya ne, but ba zan gaya masa haka ba sai nace "zai shiga staffroom ne ya aro bulala ya fito nan ya zane ni a gaban kowa sannan ya saka ni a booth din motar sa ya tafi dani gida" ya danyi dariya, sannan yayi unlocking kofar, yace "that means akwai good upbringing. Masha Allah" na bude kofar na fita sannan na sunkuyo muna kallon juna nace "Allah ya kiyaye hanya" ya dan bata fuska "amsa ta fa? In zo gobe in karba?"

Na girgiza kai "ba gobe ba, nan da sati biyu ko wata biyu, ko kuma shekara biyu, depending on the mood din da zan samu kaina a ciki" ya lumshe ido ya bude yace "then I will make sure nayi keeping dinki as happy as possible har sai na samu amsata, daga nan kuma insha Allah I will keep you happy for the rest of our lives".

Na matsa baya sannan na rufe masa kofa, wannan ya hana min ganinsa saboda tinted glass din motar, amma shi nasan yana kallona sai na juya na fara normal catwalking dina feeling his eyes on me, fuskata dauke da madaukakin murmushi, zuciya ta tana screaming with excitement ta yadda har bana ganin gaba na sosai, da ace ni kadai ce a wajen , da ace baya kallo na da tabbas na yi tsallen dadi.

Ban ankara ba sai ji nayi munyi karo da mutum,nayi saurin dawo da hankali na jiki na ina kokarin bada hakuri sai naga Mufida ce ashe, ta bini da kallo, fuskarta dauke da wani yanayi mai wahalar fassara. Wanda yasa naji murmushin fuskata yana raguwa nace "Mufida.......ammm kije ku tafi.....sai na taho" tace "he is handsome right? Kuma ya iya kalamai ko?" Na kalle ta sharply, ina tunanin inda zanyi placing maganar ta, nace "Mufida? Menene wai? Menene problem dinki? Bakya......" Ta dakatar dani ta hanyar daga min hannu, ba dan na san Mufida kuma daga labaran da take bamu na gidan su nasan cewa Doctor yayanta bane uwa daya uba daya da zan iya yanke hukuncin cewa kishi take yi dani.

Maganar da tayi ce ta goge wancan zargin amma kuma ta dasa min wani sabon yanayi na daban "Yaya Umar yaya na ne, uwa daya uba daya muke ni da shi, yana daga cikin mutanen da nake so sosai a duniya. Ke kuma kawata ce da nake so a cikin kawaye, ban san menene a tsakanin ku ba amma koma menene, no matter how it ended, bana son in rasa ki a matsayin kawa. Yaya Umar yayi relationships da yawa, kuma he has left a trail of broken hearts, I don't want yours to add to that. I don't want you to get your heart broken" sai ta kama fuskata a hannunta ta riƙe a hankali tace "I trust you will do the right thing" sannan ta sake ni da sauri ta tafi inda yake jiranta.

Ban juya ba har naji ya tayar da motar sannan naji sun zo sun wuce, nabi motar da kallo har suka je gate aka bude musu suka fita,a lokacin ne kuma motar Abba ta shigo daukana, amma sai naji duk murnar graduation din da kuma murnar maganar Doctor tana fita daga jikina kamar yadda motar da yake ciki ta fita daga makarantar. Wani bacin rai da wasi wasi yana replacing dinsu. Na rufe ido na tare da jingina bayana da jikin bishiyar da take gurin a hankali nace "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun".


Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only






*💔 Jidda 💔*

*By*

*Maman Maama*


*Episode Three: Pilot*

Free Episode

Tun da muka fito daga makarantar, na juya ina kallon gate din amma sai naji bana jin wani excitement kamar yadda nayi tunanin zan ji. Na yi ajjiyar zuciya tare da mayar da kaina na kwantar a jikin tagar mota tare da lumshe idona.

"Bana son in rasa ki a matsayin kawa"
"He has left a trail of broken hearts"
"You will do what is right"

Wadannan maganganun su suke ta yi min yawo a kaina. Muryar yaya Tahir naji "ban taba ganin wadda bata murna da zuwa gidan su ranar candy ba sai ke. Unbelievable. Wai kuka kike yi?"

Na dago kai ina kallon sa, sannan na kalli yaya Muslim da yake driving, na dan goge idona ina kallon hawayen da ban ma san sanda suka fito ba nace "ina murna mana yayana, ina murna sosai da sosai, kawai dai ina jin babu dadi ne zan rabu da kawaye na dana saba dasu shekara da shekaru, wadansu fa shekarar mu shida tare kaga kuwa ai sabon mai yawa ne"

Yaya Muslim yace "to ba kina da numbers din su ba? Ai zaku ke waya ko? Kuma kina zaki sake wasu kawayen da har zasu mantar dake wadannan. Ni yanzu few abokai na na secondary school ne yake da contact dasu, duk kowa ya kama gabansa" sai suka cigaba da hirar abokai a tsakanin su, tunda kusan duk abokan su daya, ni kuma na koma na kwanta na rufe ido na ina ganin fuskarsa "smile please" na danyi murmushi sai kuma na bata rai, shin da gaske abinda Mufida ta fada min akan yayanta haka ne ko sharri take yi masa? Amma kuma akan wanne dalili zata yi masa sharri? In kuma gaskiya ne mai yasa ta gaya min? Kamata yayi ace ai ta kare image dinsa a matsayin sa na yayanta dan na tabbatar cewa tafi sonsa a kaina.

Amma dai whatever the case warning ne tayi min, ya kamata kuma inyi wani abu a kai, Amma me zanyi? Tace ba ta so yayi breaking heart dina, abinda ya kamata nayi shine in nisanta kaina dashi dan kar in fada cikin soyayyar sa but Oops! am already in. Sai dai zan iya fita tun kafin in nutse har kai, tun kafin inyi drowning. Menene abinyi?


Zan bawa Farhan labarin sa, nasan kuma in muka hada kai ni da ita zamu samu mafita..........amma me yasa in na hango rabuwa dashi a matsayin mafita sai inji zuciyata tana min zafi? In kuma na hango cigaba da alaka dashi a matsayin mafita sai inji murmushi yazo kan fuskata?

******************************************

Sunana Jidda. Sunan Mahaifina Alhaji Habib Mahmud wanda yake haifaffen cikin garin kano ta bangaren uwa da uba gabaki daya, malamin makaranta ne wanda a halin yanzu yake da matsayin principal a daya daga cikin manyan makarantun secondary school na jeka ka dawo na maza dake garin kano. Alhaji Habib yana da rufin asirinsa dai dai gwargwado dan gidan mu bamu taba rasa ci ko sha ko kuma wasu basic needs na rayuwar duniya ba, duk wadansu bukatun mu Abban mu ya dauke mana su dai dai gwargwado.

Ba zamu kira kanmu direct da masu kudi ba, kamar yadda ba zamu amsa sunan talakawa ba. Mata biyu Alhaji Habib yake dasu, Hajiya Maryam ita ce uwargidan sa wadda muke kira da Hajiya, sai kuma Hajiya Ayesha wadda muke kira da Umma, ita ce kuma mahaifiya ta. Mu goma sha biyu Abba ya haifa, takwas daga ciki yayan Hajiya ne wadanda suka hada da Sa'adatu (Mama Sa'a), Hadiza (Mama Hadiza), Yaya Shamsu, Yaya Aminu, Yaya Hudallah, Yaya Mukhtar, Yaya Muslim da kuma Aysha (Farhan) wadda take takwarar Umma kuma autar Hajiya.

A dakin Umma kuma mu huɗu ne, Yaya Tahir ne babba, sai Mahmud (Abbah) sannan ni Hauwa'u (Jidda) sannan autar mu Maya (Amira) wadda take autar gidan gabaki daya.

Mahaifiya ta Ayesha, yar asalin kasar Ethiopia ce, duk da cewa bata taba taka kafarta zuwa kasar ba har yanzu. Mahaifinta, Amadi, ya baro kasar su ne ya taho neman kudi har ya sauka a Nigeria kuma ya kafa kasuwancin sa anan Kano, Allah yayi anan abincinsa yake, saboda son ya koma gida ya saka iyayensa a lokacin suka nema masa auren kakata Maya, takwarar Amira, dan suna tunanin idan suka yi masa aure zai koma gida, sai dai ya koma din amma ana daura masa auren sai ya dauko matar tasa ya taho da ita Nigeria itama, suka ci gaba da zamansu anan a dole yan uwa suka hakura ya zamanto tsakanin su da juna sai dai ziyara da kuma ta hanyar waya.

Yaya uku Allah ya basu, Umma ta ce babba, sai Aunty Afia, sannan Uncle Salim, shikenan. Umma ta da yanuwanta babu wani yare ko kabilar da suka sani sai Hausawa tunda a cikin su suka taso, yaren ma sunfi iya hausa akan nasu yaren, kamanni ne kawai suke tona asirin cewa ba hausawa bane ba, bayan haka babu wanda zai iya ware su dan har birth certificate dinsu na Nigeria ne. Sai dai kamar yadda muka samu labari cewa ba'a jima da haihuwa ta ba sai Allah yayi wa kakata rasuwa anan kano, a lokacin ne babansu ya nemi ya tafi dasu gabakidaya can garin su dan dangi su gansu kuma suyi musu gaisuwa amma sai Abba ya hana Umma zuwa saboda tana jego na kuma lokacin, wannan abu ne da Umma har yau bata manta ba saboda a can ne bayan sunje Allah yayiwa babanta rasuwa shima. Wannan yasa Aunty Afia ce kadai ta dawo Nigeria dan Uncle Salim shima zamansa yayi a can cikin yan'uwa. A inda yanzu har yayi aure, sai dai lokaci zuwa lokaci ya kan kawo wa su Umma ziyara kuma aunty Afia tana dan zuwa babu laifi amma Umma har yau bata je ba, ita tayi fushi ta daina tambaya shi kuma Abba bai ma san fushi tayi ba ya dauka hakura tayi.

Umma na da yan gidan su mutane ne masu rikon addini sosai, sannan suna da dauke kai da hakuri da juriya da tawakkali duk da dai zama da Hajiya ya chanja Umma sosai, kamar yadda muke ji wani lokacin Abba yana fada "ba haka halin ki yake ba, ni bansan ki da rigima ba, ni hakuri na san ki dashi" amma yau da gobe bata bar komai ba. Tabbas duk hakurin ka indai kana zaune da mutum mai irin halin Hajiya to dole sai ka tanka mata.

Hajiya mace ce mai tsananin fada, mai tsananin kishi, fadanta kuma bai tsallake kan yayanta ba dan suma ba kyale su take yi ba idan suka yi mata abinda bata so. Bata son Umma ko kadan, ko zaman hour daya idan kayi da ita zaka fahimci bata son Umma, in kuwa kana son kaga bacin ranta to ka fadi wani alkhairi a game da Umma ko kuma abinda ya shafe ta.

Wannan rashin jituwa ya wuce daga tsakanin su ya tarar har kan mu mu yayan su. Manyan yayan Hajiya duk sunyi aure tun muna kanana. Ni da nake yar Umma ta uku nice sa'ar autar Hajiya (Farhan), wannan banbancin shekarun ne ya kara saka distance a tsakanin mu da rashin shakuwa tunda bamu taso tare ba musamman Mama Sa'a, Mama Hadiza, yaya shamsu da yaya Aminu, duk bamu wani saba dasu sosai ba dan ko mun hadu tsakanin mu ba ya wuce few words, words din ma kuma most of the times marasa dadi. "Barbarar yanyawa" shine sunan da Hajiya take kiran mu dashi ita da manyan yayanta.

Abba mutum ne mai rikakken ra'ayi, babu wanda yake saka shi kuma babu wanda yake hana shi, hakan kuma ya samo nasaba ne da cewa bashi da mahaifa a raye sai kannen mahaifan sa wadanda kuma yawanci a gurinsa suke samun kwandala dan haka babu wanda yake iya ce masa "a'a". In yayi magana abinda kawai yake bukatar yaji shine "to" baya son jayayya ballantana shawara. Baya kuma shawara da kowa idan zaiyi abinsa sai dai kawai ki ga yayi, wani lokacin ma sai yayi sannan zaku sani daga baya.

Baya wasa ko kadan. Ba wai yana takura mana bane ba ko kuma baya son mu a'a ba ya nuna mana soyayyar sa ne, typical uban bahaushe, zai providing dukkan basic needs din mu sannan zai tsaya a dukkan al'amuran mu amma babu emotions a ciki.

Sannan kuma yana da wani ra'ayi wanda da ban fahimce shi ba sai da na kara girma sannan na fahimta, sai kuma na lura ba shi kadai bane ba yawanci mazan hausawa suna da wannan ra'ayin, suna kallon mata a matsayin masu karamar kwakwalwa kuma weak ba zasu iya yin tunanin komai ba, ba zasu iya bayar da shawarar komai ba, ba kuma zasu iya tsayawa kansu ba ballantana su tsayawa wanin su sai dai su a tsaya musu.

Wannan dalilin ne ya saka baya barin ƴaƴan sa mata suyi dogon karatu kafin yayi musu aure dan yana ganin za'a iya yi musu wayo a yaudare su a lalata su, ko kuma su fitsare su daina jin magana su daina bin umarnin sa suyi tunanin dai dai suke da maza suma.

Sai dai deep inside him yana son suyi karatun su mori ilimin su, wannan ya saka duk wanda zai aura wa yarsa yana yin yarjejeniya da su cewa zasu barsu suyi karatu bayan aure, har alkawari yake yi cewa shi zai dauki nauyin kudin karatun burinsa dai kawai a bari din, amma cikin ikon Allah kaf surukan nasa babu wanda ya cika masa wannan burin, daga an shiga sai ciki, sai reno sai wani cikin, sai kuma ace an tara yaya karatu ba zai yiwu ba. Aunty Hudallah ce kawai tayi diploma a Legal, shikenan kuma bata kara komai ba.

Abba yakan yi mita akan haka wasu lokutan, amma bai taba samun surukan nasa yayi musu mitar ko kuma ya tilasta musu suyi abinda yake so ba, saboda ya riga ya saka a ransa cewa duk wanda ya auri yarsa kuma ya rike ta bai sako masa ita ba to ba karamin rufa masa asiri yayi ba.

"Dakin miji shine babban rufin asirin mace. Duk abinda kuke so na daga kudi ko wani abu ku zo ku same ni in dai ina da shi zanyi muku, amma duk wata matsala data shafi mazajen ku ku barta a cikin ku, bana son ji, ko iyayen ku mata kar ku gaya wa sirrin auren ku. Ku je ku sasanta a tsakanin ku ba tare da kowa yaji ba, wannan shine halin mace ta gari".

Wannan ita ce nasihar da mukan ji yana yiwa yayyen mu mata idan sunzo gaishe shi. Wani lokacin idan yana cikin fada yakan ce

"Duk wadda taki bin mijinta a cikin ku babu ni babu ita. Duk wadda ta yi yaji wai dan tana ganin mijinta yayi mata wani abu na rashin kyautawa to ta tafi gidan wani ba gida na ba. Duk wadda ta kashe aurenta to ta nemi wani uban bani ba. Duk wadda ta jawo min magana ta zubar min da mutunci Allah ya isa tsakani na da ita"

Wannan maganar, hatta mu da bamu yi aure ba a lokacin, mun rike ta tamkar karatu a kan mu....

Har yanzu ina iya tuno yarintar mu da irin cin zalina da yaya Muslim ya ringa yi har sai da ya kasance ko tsakar gida bana iya fitowa dan inya kama gashina ya murde sai nayi kamar zanyi fitsari a wando, sai da yaya Tahir ya ritsa shi yayi masa duka sannan na samu sa'ida amma duk da haka in dai baya kusa in ya ganni sai ya dake ni, daga nan kuma sai rigima ta balle tsakanin Umma da Hajiya.

In short, abinda nake so in nuna muku shine gidan mu babu zaman

4 / 106