Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
saka saka goshinsa a kasa yafara zubar da hawaye baya dagowa sai ya jika sallayar sa, amma a jikinsa yake jin cewa that is not enough, gani yake yi kamar tarin zunubansa sunyi yawan da bakin sa kadai yayi kadan gurin nema masa gafarar ubangiji duk kuwa da ya sani cewa shi ubangiji Algafur ne kuma Alrahim.
Sai ya dauki aniyar bawa yara sadaka dan su taya shi addu'a, ya fita yayi chanjin sababbi kudin sa tunda yara sunfi son sababbin kudi ya shiga unguwa ya ringa rabawa yara yana saka su sunayi masa addu'ar Allah ya yafe masa zunubansa ya kuma biya masa bukatun sa, bukatun sa a lokacin ba wai na samun aiki bane ba ko kuma na samun wata daukaka bane ba, bukatun sa a lokacin bayan yafiyar ubangiji sune daidaitawa da iyayensa da kuma iyalin sa. Whom he misses like crazy.
Sai dai duk kiran da zaiyi mata bata yin magana da shi, sai dai ta bawa su Yasmin da Asad su gaisa sai ta kashe. In ya tira mata message ma ba reply take masa ba, in tayi reply din kuma yawanci bakar magana ce da kuma halin ko in kula. Ya gaya mata bashi da lafiya amma ta nuna bata damu ba.
Ranar nan sai ga kira daga Baffa Halilu, ya sanar dashi ya nemi Abba da kokarin ganin an gyara maganar amma yace sam babu wannan maganar.
"Maganar yarinyar nan jikarsa ta bata masa rai sosai. Kuma kowanne magidanci mai hankali dole yaji zafin maganar. Ni banga laifinsa ba sam laifi duk naka ne Faruq. Dan haka ina umartaka da ka rubuta wa Hauwa takardar ta ka aika mata da ita"
Sai da Umar yayi minti biyu a zaune a inda yake, wayar already ta riga ta zame daga hannunsa zuwa kan cinyarsa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"
Magana ta zo karshe, ya sani, bashi da sauran mai goya masa baya, ya sani. Abinda kawai zai iya yi shine yayi ta delaying maganar ko kuma ma ya tubure yace ba zai rubuta din ba amma kamar yadda suka jima suna ta threatening dinsa ya tabbatar in bai rubuta ba zasu maka shi ne a Court, zuwa court kuma yana nufin tonon asirin sa dan ko ba'a san takamaiman abinda ya faru ba za'a ta shaci fadi har a gano dalilin da yasa matarsa ta kai shi kara ta nemi saki.
Chance dinsa daya a lokacin shine yayi kokarin shawo kan Jidda ita da kanta ta ce ta hakura zata dawo gare shi amma ta yaya?
Ya rubuta mata text ya gaya mata abinda Baffa ya ce masa, amma a reply din data turo masa na cewa
*ya dogara ga Allah, shine zai masa jagora*
Sai ya fahimci mistake din da yake yi a adduarsa, nema yake Allah ya daidaita su ba wai yana neman Allah ya zaba musu mafi alkhairi bane ba. Daga nan ya chanja akalar addu'ar sa akan auren su zuwa neman zabin Allah.
Kwana biyu bayan nan da safe ya shirya yaje gidan Yaya Mubaraka, hoping yaji labarin iyayensa da kuma halin da gidan su yake ciki duk da cewa zuciyarsa tana tsoron ko Yaya Mubaraka ta sani, ko tasan irin mugun ganin da Mama tayi masa. Sai dai bayan zuwan nashi ne ya fahimci cewa bata sani ba, fahimtar hakan ne kuma ya saka ya fahimci cewa babu wanda zai sani dan tunda Mama bata fada wa yaya Mubaraka ba to baya jin akwai wanda zata gayawa a duniya, baya jin ko Baba zata gayawa, ya fahimci cewa Mama zata rufa asirin sa sai dai ta tafi da maganar zuwa kabarin ta, lallai uwa babu ya ita kaf duniya.
Fada sosai yaya Mubaraka tayi masa, fadan da duk ya karkata ne akan halin ko in kula da take ganin yana nuna wa akan rashin lafiyar mahaifan su, sannan kuma da shaye shayen da take ganin ya fara. Bai musa ba har sai da ta gama sababin fadan ta sannan ta koma nasiha da neman yadda za'a gyara lamarin musamman lamarin auren sa da Jidda da yake kasa yake dabo
"akan halin ka ne ko? Halin nan naka baka daina shi ba har yanzu ko?"
Ya dago kansa yana kallon ta yace "na daina yaya, sai dai dainawar tawa tazo min a kurarren lokaci, na riga na rasa yarda da amincewar Jidda. Jidda ba zata yarda cewa na daina ba. Ba zata kuma yarda da ni ba"
Ta daga kafada "do you blame her? Ni dai I don't. Ta baka dukkan wata dama wadda ni personally na san ba zan bawa mijina irin ta ba, kuma ba zan bari yata ko kanwata ta bawa mijinta irin ta ba, sai dai in ban sani ba"
Ambaton kanwa da tayi ne ya saka ya dago kai ya tambaye ta abinda yake sosa zuciyarsa "ina Mufida?" Yaya Mubaraka tayi ajjiyar zuciya tare da gyara zama "yaushe rabonka da gida Umar?" Yayi shiru bai ce komai ba. Ta cigaba "ba ka san ma Mufida bata gida ba ko?" Ya kalle ta da sauri zuciyarsa tana kara gudun jini a jikin sa "bata gida? guduwa tayi ko me?" Ta harare shi "guduwa kuma wacce iri? Yakumbo Amina tazo ta tafi da ita tun Mama tana asibiti. Wai zata zauna a gidan ta na wani lokaci. Naji kuma Baba yana maganar aure za'a yi mata. Har ya fara yi min maganar kayan daki. Ni ban gane ba. Kamar Mama da Baba suna boye wata magana ne fa"
Ya sunkuyar da kansa yana wasa da band din Jidda da yake hannunsa. Aure za'a yi wa Mufida kenan. Good. Very good. Shi kuma wancan munafikin babu abinda zai ce masa sai Allah ya...... Sai kuma ya katse kansa, in Allah ya isa ne shi yayye nawa ne zasu yi masa Allah ya isa? Yadda yake takamar cewa babu wadda ya tilastawa a cikin matan da ya nema haka shima Bashir bai tilastawa Mufida ba.
Yaya Mubaraka tace "kayi shiru? Ko dama kasan da maganar ne? Ko kaima kasan abinda yake faruwa ne?" Yayi saurin girgiza kansa. Tunda iyayensu suka yi deciding binne maganar to tabbas shima zai taya su da zuba kasa ne, babu wanda zai gaya wa. Not even Jidda.
Sai ta katse masa tunanin sa ta hanyar jefo masa tambayar da bata daga cikin abubuwan da suke zuciyarsa a lokacin "ya maganar yarinyar can kuma da aka daura muku aure? Menene matsayin auren naku a gurin ka?"
Yayi blinking yana kallon ta, shi kan sa bai san amsar ba dan bai taba zama yayi tunani akan maganar ba, shi har yau ma bai taba ji a ransa cewa da gaske ne an daura masa aure ba, bai yarda a ransa cewa da gaske ne yana da mata bayan Jidda ba.
Kafin ya bata amsa kira ya shigo wayarsa. Baffa Halilu. Ya cije lips dinsa tare da runtse idonsa. Yaya Mubaraka tace "waye yake kiranka? Lafiya?" Ya bude idon da lokaci daya ya kara juyewa yana kallon ta yace "Baffa ne. Baffa Halilu. Kin san shine waliyyi na. Akan maganar Baby Dove, akan maganar Jidda. Sunce sai na sake ta. Tace sai na sake ta. Ba zan iya sakin ta ba. Ba zan iya rabuwa da ita ba. Ba zan iya rasa family na ba"
Sai ta taso ta dawo hannun kujerar da yake kai ta dora hannunta akan nasa wanda yake rike da wayar tace "shi aure rai ne dashi, Allah ne kadai yake bashi rai kuma kashe shi kamar mutum. Idan naku ya kare dole ya mutu kamar yadda idan lokacin mutum ya kare a duniya ba zai kara ko second daya ba. Sannan kuma ina so ka sani, babu wanda ba zaka iya rayuwa babu shi ba, ba Jidda ba ko da Mama da Baba ne, rayuwar ta daban ta ka daban, kaddarar ku ce tayi crossing shi yasa kuka yi aure, idan kuma roles dinku ya kare a cikin kaddarar juna dole ku rabu ko kuna so ko ba kwa so kuma dole ku ci gaba da rayuwa daban daban. Ka fahimta?"
Ya daga kai yana kallon ta, dusu dusu yake ganinta saboda ganinsa da yake ganin kamar yana disashe wa. "Ka fahimta?" Ta sake maimaita wa. Ya gyada kai a hankali sannan ta dauke hannun ta daga kan nasa shi kuma ya daga wayar ya kira number din Baffa.
"Ka taho yanzu ka same ni gidan ku, zamu je gidan surukan ka"
Gyada kai kawai yayi dan ba zai iya magana ba. Sai kuma ya mike yana kallon yaya Mubaraka yace
"zan je. Pray for me please"
Ta gyada kai da sauri a ranta tana jin tausayin kanin nata, duk da deep inside her tana jin ba abin tausayi bane ba domin shi yayi wasan kura da damarsa da har yayi sanadiyyar da zai rasa mace kamar Jidda.
Yana zuwa ya tarar har sun fito,daga alama shi kawai ake jira. Ya lura har da Mama a tafiyar amma sai ya kasa karasawa inda take ballantana ya daga kai ya kalle ta. Sai dai yaji dadin ganinta a tsaye akan kafafuwanta alamar lafiya ta same ta.
Yana karasowa suka shiga motar Baffa shi kuma ya koma motarsa yayi gaba suna binsa a baya. Daci yake ji a bakinsa, jiri yake ji yana dibansa, amma a haka ya kai su har gida sannan yayi packing yana tunowa da ranar da ya fara zuwa gidan, ranar da ta fito ta same shi ta shafa jan baki duk ya bata gefen bakin ta, ya tuna da yadda tayi kokarin gogewa ta gyara amma bai gyaru ba sai ma kuma baci da yayi.
Yana kallo Abbah yazo ya bude musu sitting room din Abba suka shiga, ya samu can gefe daga bakin kofa ya zauna yana tuno da memories din da suke cikin sitting room din, the good sweet memories and the bad final one, na last zuwansa gidan, na yadda yayi messing up everything.
Abba ne ya fara shigowa suka gaggaisa da manyan gurin shima ya gaishe shi sai ya amsa da "lafiya" daga nan bai sake ce masa komai ba.
Ba'a jima ba ta shigo, kamshin ta ne ya riga sallamar ta zuwa gare shi. Kamshin da yayi stirring something deep inside of him wanda ya kusan kawo kwalla cikin idon sa. Amma sai ya kasa daga ido ya kalle ta dan zuciyar sa ba zata iya dauka ba.
Yaji muryarta tana gaishe da mutanen gurin, bata gaishe shi ba shima bai yi mata magana ba, Baffa ya fara maganganun sa, inda ya fadi laifin da yake ganin na kowa ne, ya kuma yanke wasu shawarwari akan shi Umar din, sannan kuma ya roki alfarmar a mayarwa da Umar matarsa.
Ya rintse ido sa yana jiran amsa sai yaji Abba ya shigarwa yarsa, Yace sai ta yarda tukunna zata koma. Aka tambaye ta and she said
"ina son Umar Baffa. Amma kuyi hakuri. Allah shine shaidata bana son cigaba da auren sa, aurensa ya fita daga raina gabaki daya"
Ya bude idonsa ya sauke su a kanta. Yana ji kamar ranar ne ya fara ganinta a makarantar su sanye da uniform, amma sabanin waccan ranar yau bata kallonsa itama, sabanin waccan ranar yau bata yi masa murmushi ba. And he knew it was over.
Sama sama yaji Mama tana magana, kamar rokon Jidda take yi ta janye decision dinta. But she said
"Na yafe masa Mama, na yafe miki kema. Amma auren sa na gama"
Ya dauke idonsa daga kanta ya sauke shi zuwa hannunsa yana kallon band din ta dake hannunsa, remembering the time she gave him a cikin falon nan. Yaji Baffa Halilu yayi masa magana. Sai ya samu kansa da cewa.
"Babu komai Baffa. Allah yasa hakan shi yafi mana alkhairi. Na gode da kulawa"
Sai ya mike kamar wanda ake jansa ya fita zuwa motarsa ya bude aljihun motar ya dauko wata jotter wadda itace da kanta ta ajiye ta a gurin. Ya dauko biro ya dora akai. Ya rufe idonsa tare da sauke ajjiyar zuciya ya dube sannan yayi rubutu a ciki ya ninke da sauri ya fita daga motar ya koma inda suke ya shiga ya durkusa gabanta yana kokarin hada ido da ita one last time amma taki yarda.
Sai ya kamo hannunta ya saka mata takardar tare da fadar wani abu da bai ma san me yace ba, yaji itama ta fadi wani abu da bai fahimta ba, abinda ya fahimta kawai shine ta karbi takardar, meaning ya tabbata kenan, sannan kuma ta tsinka band din hannunsa.
How cruel!
Ya mike ba tare da ya kalli kowa a gurin ba ya fita ya shiga motarsa ya kunna ya bar unguwar.
Ya jima yana driving da hannu daya dayan hannun dafe da kurjinsa saitin zuciyarsa da take kuka, kuka mai tsanani. Shi yasan bashi da lafiya, ya kuma san cewa ciwon nasa karuwa yake yi kullum amma baya komai gurin neman magani kuma bashi da niyyar, gaya wa kansa yake yi cews ciwo ma wani bangare ne na kankarar zunubi, maybe ciwon nasa ya zame masa wani sabulu da zai rage masa dattin jikin ruhinsa.
Sai da yayi nisa sosai sannan yayi packing saboda yadda yake jin ba zai iya cigaba da tukin ba. Ya dafe kirjinsa da hannayensa duk biyun yana numfashi sama sama ga gumi duk ya lullube masa jiki, ya kwashe mintuna da yawa a haka sannan numfashin sa ya fara daidaita. Sai kuma ya dauko wayarsa ya nemo number din ta "Baby Dove"
Ya tura mata message.
"I did what you want. Ba wai dan ni ina so ba sai dan na fahimci abinda kike son proving, cewa zaki iya rabuwa da ni. Ina so ki san cewa na fahimta, kowa ma ya fahimta. Then what's next?"
*Jidda*
Na ga ya mime da sauri sannan ba tare da ya ce wa kowa komai ba ya fita daga falon sannan muka ji tashin motar sa a waje. Ina kallon Mama ta mike kamar zata bishi sai Baba yayi mata magana ta dawo ta zauna.
Baffa Halilu ne ya fara magana yace min "bani takardar in gani" na mika masa ita kamar yadda Umar ya miko min. Sai ya karanta a fili.
"Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ni Umar Faruq Muhammad Gidado na yanke igiyar aure na da Hauwa'u Mahmud guda daya. Tare da fatan hakan ya zama alkhairi a gare mu baki daya"
Ya ninke takardar ya mika wa Abba, shi kuma ya karba yayi ta juya ta a hannun sa. Baba yayi ajjiyar zuciya "Allah ya sa haka shi yafi alkhairi"
Baffa Halilu yace "insha Allahu ba karshen maganar nan kenan ba. Insha Allahu zamu dawo mu sake zama a gurin nan da murmushi a fuskokin mu" Baba yace "ameen"
Mun jima haka a zaune babu wanda ya sake iya magana a gurin sai ajjiyar zuciya da ake saukewa, sannan Baba yace "in babu damuwa Alhaji ina son yara su zauna a gurinta for the mean time, kar abin yayi musu yawa. Ni ina ji a jikina nan bada dadewa ba zamu sake dawowa"
Abba ya girgiza kai. "Bana jin hakan mai yiyuwa ce. Kayi hakuri Alhaji. Ana so muyi ta jainja da kai akan maganar nan dan Allah. Ita yanzu na riga na gama duk shirye shirye ina do ta tafi kasar mahaifiyarta tayi idda a can saboda bana son surutun mutane akan maganar nan, ni in son samu ne ma zan so yanzu a dauko muku yaran tare da kayan su ku tafi dasu kawai"
Baffa yace "haba Alhaji. Kar muyi haka mana. Ai addini ma ita ya bawa rikon yayan ta in ma aure ne zatayi nan gaba kuma ba zata tafi da yayan ba sai mahaifiyarta ta rike su, haka addini ya tsara ba wai mu muka tsara ba, saboda ubangiji ya san muhimmancin uwa ga yayanta. Dan Allah ka bar mata yaranta"
Abba yace "to tafiyar kuma fa? Yanzu mahaifiyar tata bata nan waye zai rike mata su in ta tafi?" Baba yace "sai su tafi tare. Mu zamu dauki nauyin tafiyar ta su insha Allah. Su zauna tare da ita kar abin yayi musu yawa"
Abba ya juyo yana kallona ina tattare strings din da suke kan cinyata yace "tashi kije ciki" na mike nayi musu sallama murya ta ciki ciki na shiga cikin gidan sai dai ban shiga dakin Umma ba inda na bar yara suna kallo sai na shiga dakin Farhan wadda bata gidan a lokacin, na zauna akan katifar ta ina kallon strings din da suka hannuna.
Na yi bitar takardar Umar a kaina.
"Ni Umar Faruq Muhammad Gidado na yanke igiyar aure na da Hauwa'u Mahmud guda daya....."
Na saki igiyoyin hannuna suka zube a kasa.
Guda daya yace, ni kuwa guda nawa na tsinka? Na fara irga strings din kamar tababbiya, in na kirga sai in bata a lissafin sai in sake irgawa.
Ina yi ina tuno tarin alkawarirrikan sa gare ni.
"My heart and my body belong to only you"
"I will never do it again"
Na tuno Bashir
"Dama nasan ba ka wuce tayi ai shi yasa nayi masa"
"She was your favorite pet"
Ma tuno Maryam
"Na ajiye miki sako a cikin motarsa, idan kuma baki yarda nasa bane ba ki kai asibiti ayi miki DNA test"
Na tuno Mammy
"Cewa yayi zai aure ni"
And Asabe
"Wallahi mommy sau daya ne"
Na runtse idona ina jin hawaye suna falla gudu a kan kunchina. Ban san jimawar da nayi a haka ba sai jin maganar Yasmin nayi a kusa dani
"Mommy are you crying again? Na dauka kin daina kuka yanzu"
Na dago kai ina kallon ta sannan na share hawaye na da bayan hannu na. Nayi kokarin yin magana. "Ba kuka nake ba" sai ta miko min waya ta "anyi miki message. Daddy ne. Mommy ki karanta mana. Cewa yayi zai zo mu tafi gida?"
Naji wani irin takaici ya kama ni. Message kuma? Mai zai ce min? Na dauka it is finally over na yar da kwallon mangwaro na huta da kuda.
Na karba na bude na karanta
"I did what you want. Ba wai dan ni ina so ba sai dan na fahimci abinda kike son proving, cewa zaki iya rabuwa da ni. Ina so ki san cewa na fahimta, kowa ma ya fahimta. Then what's next?"
Naja