Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
biyo bayana ya zare jakar kayan daga hannuna. Na bar masa saboda mun fito bakin layi bana son creating scene musamman saboda mutane da suke tafiya masjid dan har amfara kiraye kirayen sallah. Na ja hijab dina na rufe rabin fuskata na sunkuyar da kaina kasa ina zabga sauri. Ina jinsa suna gaisawa da mutane a duk inda muka wuce, few suna tambayarsa dalilin da suka ganmu a kasa da kaya haka, shi kuma yana bada amsa da mota ta lalace. A ciki harda wanda yayi offering zai dauko tasa motar ya kaimu.
Muna fita titi ya sauke Asad sannan ya fara kokarin tare mana Napep, wani ya tsara ya bashi address din gidan Abba sannan ya dauko kudi ya bashi yayin da ni kuma na saka yayana a ciki ina kokarin daukan kaya yazo da sauri ya dauka ya saka a ciki sannan ya bani guri na shiga, ya durkusa ya ja min skirt dina ya rufe min kafafuwana, yana kallon Yasmin yace "share hawayen ki kinji sweetheart. Zanzo an jima in taho daku gabaki dayan ku" ya karasa maganar yana kallona, Sannan ya kai hannunsa da niyyar gyara min hijab ya rufe min hanci da shi, na dauke kaina gefe, ya sauke hannunsa yace "akwai hazo jidda, kar ciwonki ya tashi" bance komai ba kuma ban kalle shi ba sai yayi taku biyu baya ya bawa mai Napep damar tayarwa muka tafi.
A hanya Asad ne yake ta hirarsa shi kadai, yana ta lissafa abokan sa da zasu yi wasa har da yayan makotan da ni ban ma san su ba. Lokaci zuwa lokaci ina bashi amsa with hope cewa zaiyi shiru ya bar ni da tunani na amma baiyi ba kamar wanda aka sakawa batir.
This is my step four, abinda na jima ina lissafin zanyi indai har abubuwa suka cigaba da tafiya a yadda suke. Amma yanzu da lokacin yazo, yanzu da na riga na dauki niyyar yin abin, sai naji dukkan confidence dina babu shi, ban san me zan ce a gida ba, ban san me zance da Abba ba, ta ina zan fara? Kuma a ina zan tsaya? Komai da komai zan fada ko kuma akwai abinda ya kamata in cire?
Ban sani ba, abinda na sani kawai shine na gama auren Umar. Ko za'a daka ni a turmi kuma a tankade ba zan koma gidan sa ba.
A haka har muka je gida. Na sauka, na sauke yaran sannan mai Napep ya sauke min kayana ya tafi. Na tsaya na seconds ina kallon gidan da anan aka haife ni anan na girma anan ne kuma iyayena suke har yanzu. Am I really ready for the life ahead of me? Are my children ready? Can I? Can they?
A tsakar gida na samu Hajiya tana alwala, na gaishe ta ina kallon dakinta tare da expecting Farhan zata leko, ko sallah take yi? Ta amsa tana tsokanar Asad shi kuma ya fara yi mata surutu, na lura da yadda take bin kayanmu da kallo fuskarta da wani yanayi da na kasa tantance wa. Na wuce zuwa dakin Umma da kayan, na tarar tana sallah a falo, Amira tana kwance akan kujera da littafin hausa a hannunta. Ta mike da sauri tana yi min sannu da zuwa sannan ta fita ta dauko Asad ta shigo dashi tana dungure masa kai "mai shegen surutun nan. Yaje sai zuba yake kamar fanfon daya lalace" ya turo baki zaiyi kuka na fita na barsu. Toilet na shiga a tsakar gida na fito nayi alwala nima na shiga na tayar da sallah. Ina cikin yi naji sallamar Abba ya shigo.
Ina idarwa ko addu'a banyi ba naji ya shigo falon. "Hauwa'u? Ina Hauwa'un take? Ke Jidda?" Umma tace "sallah take yi, bata idar ba" nayi saurin shafa addu'a na juyo. "Abba ina....." Ya daga min hannu "menene naji ance kin shigo gidan nan da kaya? Wanki za'a yi muku ko kuma kayan bayarwa ne kuka kawo?"
Na sunkuyar da kaina, hawayen nan da basa jin magana ta suka fara bin fuskata. "Kuka?" Umma ta tambaya. "Jidda me ya faru? Yaji kika yi?" "Yaji?" Naji muryar Hajiya a bakin kofa "kash! Amma wannan abu baiyi dadi ba. Yaji kika yi ko kuma sakin ki yayi? Allah dai yasa ba sakin bane ba?" Na dago kai na kalle ta ina jin wani irin zafi a zuciyata, fuskarta cike da farin ciki. Umma ta mike tana rike kugu "sai dai kiga saki akan yayanki ba dai akan Jidda ba wallahi. Aniyarki ta koma kanki"
Abba ya kama fada "to sarakan masifa, an girma ba'a san an girma ba. Kun gama yin fada a gaban yayanku kun koma yi a gaban jikoki dan abin kunya" duk suka dauke kai gefe suka yi shiru. Amira ta faki idonsa ta murguda wa Hajiya baki a hankali tace "haka kawai ba a kasa da mutum ba yazo yana diba" Yasmin ta taso ta dawo kusa dani ta zagaye ni da hannayenta ta saka fuskarta a wuyana, ina jinta tana sheshshekar kuka.
Abba ya kuma nuna ni da hannu "magana nake miki fa? Ko kin zama kurma ne yau. Kayan me kika shigo dasu? Me ya kawo ki gidan nan da magriba?" Ban amsa ba still, dan tun a hanya nake gada kalaman da zan gaya masa amma basu hadu ba. Jin nayi shiru ya saka ya dauko wayarsa daga aljihunsa sa, gaba na ya fadi, he is not going to call Umar is he? Maganar na naji yayi ta tabbatar min da fargaba ta.
"Doctor lafiya kuwa muka ga Jidda da kaya?"
"Babu abinda ta gaya mana kuma mu babu abinda muke so muji. Shi sirri na tsakanin mata da miji ai boye shi ake yi ba bayyana shi ba"
"Babu komai. Sun iso lafiya, babu komai. Ka taho kawai yanzu kazo ka dauke su ku koma. Yarinta ce irin ta Jidda, kayi hakuri"
"A'a, babu komai wallahi. Allah ya kiyaye gaba"
Ya mayar da wayar aljihu ya juyo yana kallo na "zancen banza zancen wofi. Ga iyayenki nan, shekarar mu nawa a gidan nan kuma babu irin rigimar da bama yi dasu amma babu wadda ta taba daukan kaya ta tafi gidan su da sunan yaji. Haka yayyenki duk sunsan doka ta ba'a yi min yaji a gida wallahi. Babu yarinyar da zata kashe aurenta tazo ta zauna min a gida walahi, sai dai kuma idan wani uban zaki sake bani ba. Ke banda sakarci irin naki duk dangi wacece tayi dacen miji irin naki? Duk yan uwanki wa kika ga tana rayuwa irin taki? Duk cikin surukaina wa nake ji dashi kamar mijin ki? Ji nake kwana biyu da suka wuce yazo nan ya lissafa kudin makarantar kanwarki chif ya dankamin a hannuna, shine kuma kike so ki debi kasa ki watsa min a idona? To wallahi ahir dinki, kar in kuma ji kar kuma in kuma gani. Kar ki kara tako kafarki zuwa gidan nan ba tare da izinin mijinki ba da sunan wai kinyi yaji. Marar godiyar Allah. Ki goge wannan hawayen na fuskarki ki zauna ki saurari nasihar da uwarki zata yi miki kafin mijinki yazo, na kira shi yanzu yana kan hanya ma, yana zuwa ki dauki kayan ki kamar yadda kika dauko su daga can ki dauka ku koma. Wannan kuma ya zamanto na karshe, ehe"
Ya juya ya fita. Hajiya ta bishi a baya tana cewa "sai hakuri Alhaji, ka haifi da ne baka haifi halinsa ba. Yaran zamani sai hakuri. Allah dai yasa yazo ya dauke ta su koma din kar yace yayi fushi"
Na runtse ido na, hawayena yana zuba akan hijab dina, shikenan? Duk kuri da cika bakin da nayi wa Umar akan cewa na gama aurensa amma shikenan abinda Abba zaiyi akan maganar? Few minutes after na bar gidan sa sai a kira shi yazo ya dauke ni mu koma? Babu ko bincike babu ko fada babu ko bani damar in fadi abinda yake cikin zuciyata? A matsayi na na wadda na dauki shekara shida a gidan miji ba tare da nayi yaji ba ai ina ganin yau din da nayi I deserve to be heard ko? Wannan abin da Abba yayi tamkar yana gaya wa Umar ne ya cigaba daga inda ya tsaya.
Na dago kai ina kallon Umma, hawaye yana zuba daga idona, nayi kokarin magana amma muryata taki fitowa saboda bakin ciki daya tokare makogwarona. "Kiyi hakuri Hauwa'u" Umma ta fada, "ni nasan kina hakuri amma ina kara gaya miki kiyi hakuri. Saboda mai hakuri baya taba tabewa kuma hakuri baya taba kai mutum ga halaka sai dai ya kaishi ga tsira, idan ba'a duniya ba to a lahira. Hakuri baya taba yawa, kuma yanzu ma shi zan kara baki. Shi bin miji bin Allah ne, dole ki bi mijinki in dai kina son samun tsira a lahira. Ko wacce mace in kika ganta a gidan mijinta to hakuri take yi, mazan duk haka suke kowanne da aibun sa, dole muyi hakuri da su mu kuma tayi musu addu'a......"
Nace "Umma hatta mazinaci? Dole muyi hakuri mu zauna da miji mazinaci? Umma ji nake yi annabi da kansa yace haramun ne zama da miji ko mata mazinaci" Umma tayi saurin ta katse ni "subhanallah Jidda, ya zaki ke jifan mijinki da wannan mummunar maganar? Ya zaki ke kiran mijinki da wannan sunan a gaban ƴaƴan ki? Kar ki sake, kar ki bari kowa yaji maganar nan daga bakin ki. Kar ki bari maganar nan ta fada kunnen makiyanmu Jidda. Kin san kuwa mata nawa ne suke fatan samun kansu a matsayin ki? Mata nawa ne har a cikin dangi suke fatan ki fito su su shiga gidan ki? Har a cikin yanuwan ki ma da yawa bakin ciki suke miki da samun miji irin Umar"
Na sunkuyar da kai, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, anya kuwa Umma ta jini sosai? Ko kuma dama ta sani amma take yin shiru? Tabbas biri yayi kama da mutum, tabbas Aunty Afia ta gaya mata, wannan shi yasa duk ramewar da nake yi nake kuma bushewa bata taba tambaya ta abinda yake damuna ba, saboda ta riga ta sani. Yanzu kuma shine take ce min inje in cigaba da hakuri in cigaba da zaman aure da mazinaci? Dan kar makiya suyi min dariya? Shine reason dinta?
Ta sauko gaba na ta rike hannuna. "Ki daina kukan nan Jidda, kinga, in kuka tafi gobe zan aikawa Afia taje gidan ta same ki ku sake maganar, daga nan sai ku tafi gurin Malam Murtala ayi masa bayanin komai, babu abinda ya gagari Allah, da Allah zamu hada shi, in aka yi mana addu'a a kansa ba zai kara kallon wani gurin ba"
Na karbe hannuna daga cikin nata na goge hawayena ina gyada kai. Na cire hannun Yasmin daga jikina na mike ina daukan handbag dina, ta bini da kallo "ina zaki je?" Nace "waya zanyi masa" ta danyi murmushi "yauwa. Ki gaya masa ya dan bari sai an jima kadan dan yan zaman majalisar nan su gama watsewa kar su ganku kuna fita da kaya su samu abin magana. Allah ma ya saka sanda kuka shigo suna masallaci da yanzu magana ta zagaye unguwa" na gyada kai kawai ina jin numfashi na yana rike wa a kirjina baya karasa wa cikina.
Na fita tsakar gida sannan na wuce soro na kifa kaina a jikin katanga ina jujjuya kaina zuciyata tana kuna kamar ana gasa masara a kirjina. "Am done" na fada a hankali. Na gama auren Umar. Na lissafo sanda sukayi waya da Abba nasan yanzu already yana kan hanya, maybe ma ya kusa karasowa. Na yi gyaran murya sannan na daga murya na kira Yasmin "ku zo kuyi magana da Daddy a waya" nayi shiru ina saurare, sai naji su sun fito tare, na lallaba na debo takalman su da sauri da dawo soro na saka musu na kinkimi Asad na kuma ja hannun Yasmin muka fita daga gidan da sauri.
"Mommy ina zamuje" Yasmin ta tambaya " Mommy mun fasa zama a gidan Umma? Yaushe su Muhsin din zasu zo muyi wasan?" Asad ya tambaya
Ban basu amsa ba, sai sauri nake zubawa ina waige. Muna fita bakin layi na tari Napep, yana tsayawa na saka yarana a ciki nima na shiga nace masa "muje"
Muna hawa kan titi naga motar Umar ta wuce mu, na leka naga ya saka signal ya shiga layin mu. Na dawo da kaina ciki na jingina a jikin karfen Napep din hawaye masu zafi, kwatankwacin zafin da zuciyata take yi min yana zuba daga ido na. Ban san cewa sheshsheka nake ba sai da naji muryar mai Napep yace "kiyi hakuri Hajiya. Komai yayi zafi maganin sa Allah. Ki daina kuka kinga kin saka ƴaƴan ki suna kuka suma" na kalle su, sun hada kai a guri daya suna rusa kukan da basu san dalilin yin sa ba. So innocent.
"Ina zan kai ku Hajiya?" Ya tambaya. Nayi shiru ina kallon yayana ina tunanin if I was wrong to bring them with me. Yasmin cikin kuka tace "mommy ina zamuje?" Na mayar da idona kan yatsun hannuna ina kallon su.
Ina za mu je???????
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*From the Readers*
Wadannan matan suna cikin groups din mu, dan Allah idan kinsan ba zaki fadi alkhairi a kan su ba to kiyi shiru. In kuma kina da shawara mai kyau da zaki basu to bismillah.
*1*
Assalama Alaikum
Gaskiya jidda is going thru a lot I can also feel her pain wallahi....Am also in a this kinda marriage but mine is also a Drug Abuser .... The mistake was from me daga farko gaskiya saboda tun kafin munyi aure ya gaya min cewa he was into drugs bfr and now alhamdulillahi bayayi kuma I believe SBD ban taba kamashi da abu makamancin haka ba lokacin courtship dinmu gashi antakura min nayi aure just like gidansu jidda.Haka na tsarkake zuciyata akan ya daina n yadda mukayi aure. First week was alhamdulillahi but daga second week komi ya canza ya started seeing his tru face ya ajemin abokinsa a gida for almost 3days muna just scnd week da aure and then all sort of drugs fa suna shamin a cikin gida nayi kuka nagode Allah har abokin y tafi. And that keep going ya fara shigomin d kayan maye cikin gida , ina ta masa addua da nasiha amma babu canji.haka rayuwa ta cigaba har muka sami matsala parents suka shigo ciki and that was the time dana fada cewa he's into drugs both my family became aware of that.Da farko his mum ta dauki abun so serious and tayi bani hakuri sosai wallahi (knowing she knws he's into it since dama).haka dai akayi bani hakuri aka masa fada komi ya wuce but bai fa canza ba .Ga gida , ga mota, g sutura amma wallahi basa burgeni sbd auren drug addict masifa ne wallahi nayi duk iya yina nakasa nasha cewa y sakeni just like jidda amma wallahi yace bazai taba iyawa ba koda hauka yake I shud just knw auren mu mutu ka rabane. That's how life keeps going anytime his mum ask me if akwai matsala nace mata is only drug habit ensa but bata taba daukan mataki akai wallahi, bcs sometimes tana ganinsa ya dawo a buge amma bata iya wani masa fada sai dai tayi ta fadan wai ita tama gaji yana samata ciwon kai nasan yadda zanyi da mijina n gyara shi ita bazai kasheta ba can you imagine as if nice na haife shi. Haka nake ta rayuwa cikin kunci da rashin kwanciyar hankali domin dai yanzu freely a parlour yake shan kayan mayen sa amma bani da say ...ya taba cemin dama na hakura na kyaleshi tunda mamansa ma babu yadda ta iya dashi ae. To cut it short nayi realising abun ya fara taba masa brain wallahi saboda wasu habits da naga yakeyi, the worst part am pregnant ya min duka kamar zai kasheni telling me shifa tsohon mahaukacine i should know that idan ban sani ba bfr I was so scared wannan shine karo na farko daya taba saka hannunsa a jikina and pray ya zama last..one funny thing ya gama dukana nace nikam tafiya zanyi ya biyo ni daki yana ta bani hakuri shi baisan yayi bama wallahi a tsorace nake dashi bani da wanda zan gayawa matsala ta kamar jidda ko frnds I don't trust wallahi ....ina zaune har ynz a gidansa amma cikin fargaba, tsoro da bacin rai na rasa yadda zanyi wallahi a bani shawara ...Allah ya kawo manah mafita nida jidda da duk sauran yan uwa da suke cikin irin wannan halin namu .
*2*
Wallahi ga munan for good 21yrs but still the same
My first born is 20yrs she's in the university ***l
And her brother is 18yrs he's in ***l university
See me thinking andpraying
Still
😭😭😭😭😭
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Savoir*
Kafin mu dora, let me say this.
Littafin Jidda an gina shine akan matsalolin zinace zinacen da al'ummar mu ta samu kanta a ciki, da kuma yadda wannan matsalar take rusa happy families, like jidda's family.
Wannan dalilin ne ya saka characters din cikin littafin kamar, Umar, Bashir, baban su Aira, da sauransu suka zama mazinata, saboda ma'anar labarin ta fito sosai, amma kuma hakan ba yana nufin cewa maza haka suke ba, ko kadan halin Umar baya representing halayen sauran maza.
Yes, dole in mun karanta labarin wata wadda ta samu kanta a hali kamar yadda Jidda ta samu dole zamuji babu dadi kuma zamu ji haushin miji kamar Umar, amma ba yana nufin cewa mune Jidda ba kuma mazajen mu sune Umar ba. Please we should cool down and start taking things easy. Don't start digging something that isn't there please!
Akwai maza na gari kamar yadda yake akwai bata gari,