Chapter 66 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   66 / 106

195K to 198K   out of 316K words

tsoron ta? Ke fa sokuwa ce wallahi. Yanzu kayan da na baki fa ko sau daya bana jin kin taba sakawa"

"Uhm uhm ba zan saka kayan nan ba, alkuran tagan su a jikina ubana zata ci, watakila ma ta kora ni gidan mu kuma wallahi duk abinda ta fada ta zauna kenan ba zai musa mata ba"

"Eh bai iya musa mata ba amma ai ya iya ya lallabo ya danne ki in bata nan ko?"

Suka yi dariya....

"Ke ya daina zuwa fa, tun wata rana da ta gan mu muna magana a waje, bai kara kula ni ba, na gaya miki tsoron ta yake ji kamar mala'ikan mutuwarsa alkuran. Ni tsoro nake ji ma kar alkawarin da yayi min ya bi ruwa"

"Alkawarin da yayi miki ba zai bi ruwa ba in dai har kina yin abinda nace miki, yo sau nawa anayin haka? Yar aikin gida ta auri mai gida kuma ta kori matar gida? Watarana sai dai in ce nazo gidan kawata"

Suka yi dariya.......

Cups din da suke hannuna ne suka zame suka fadi kasa suka tarwatse. Karar faduwar su ta saka suka fito daga dakin a tare suna rarraba ido, kawar tata ce ta fara ganina sai tayi hanyar waje a guje, ita kuma asaben tayi kokarin komawa ciki da gudu, na damko ta na dawo da ita baya sannan na jata zuwa cikin kitchen din na buga ta da bango.

Ta dora hannu biyu a ka ido kamar zai fado kasa "mommy wallahi ba zancen ku muke yi ba, alkuran ba maganar ku muke yi ba" na shake wuyanta nace "kashe ki zanyi dan ubanki, na haka rami na binne gawarki nace kin bata dan uwarki" ta zaro ido "alkuran mommy ba ke mommyn muke nufi ba"

Na shake wuyanta da hannu daya sannan na fara laluben abinda zan dauko da daya hannun, abinda zaiyi mata illa nake nema, hannu na ya sauka kan fork din da muka gama cin abinci dashi dazu, na dauko na dora tsinin sa a wuyanta sannan nayi mata straight tambaya "menene tsakanin ki da mijina?".

Ta tsorata sosai, idonta ya ciko da hawaye "dan Allah kiyi hakuri kar ki kashe ni, wallahi ba laifi na bane ba, yace kuma in na gaya miki sai ya kashe ni" nace "laifin uban waye to? Huh? In baki gaya min ba ni kuma zan kashe ki din, ko ki mutu yanzu ko kuma ki mutu in ya kamaki sai ki zabi daya"

Cikin rawar murya tace "sau daya ne wallahi, kuma ba laifi na bane ba, shine yazo ranar nan ba kya nan, yace in bashi kaina zai bani kudi, yace kuma in ban gaya miki ba zai aure ni, yace kuma in na gaya miki zai kashe ni"

And that was my limit..........................

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only

*From the readers*

Kamar yadda nace zan ke kawo labarai daga masu karatu, wadanda suka shiga exact or similar situation as Jidda, tare da fatan sauran masu karatu zasu dauki one or two lessons from them. Please mutanen nan suna cikin groups din mu, in kin san ba zaki fadi alkhairi ba dan Allah kiyi shiru.

*1*

Assalamu alaikum
sannu d kokari mm... jidda jarabawarta kennan Allah ya Bata ikon cin shi with Straight As amin..
Waenda ke magana ga jin Dadi ga daula Basu taba shiga irin abun bane so bazasu gane ba amma koni na salamawa umar🤮💔💔 Don abun nashi God forbid it...
 
   Na samu kaina a same situation,  Nashi was drugs 💔💔💔sai already he was a womanizer dama, so abun yayi Mana yawwa😰. babana kaman na jidda shima d munyi dare ya Fara sunturi kenan😃 Yana tsoron a koro mashi 'ya gida. Nima na gwada gayawa mamansa case din drugs din tun sanda ya fara dan muyi tacling matsalar da wuri, sai na dauki waya na kirata nace idan wane ya kwanta tun jiya sai ya wuni bai sallah, abun babu dadin Fadi, d ta dauki waya tace Mai kazo Ina nemanka sai Yana ta gujewa d ta gaji d rashin zuwanshi sai tace toh ai sai kazo Don matarkace ta kawo kararka, baya gida sai ya dawo wai me kikace ma Haj nace me kuwa? Sai ya kirata sai ta Soma cewa ita me tace nace, kuma babbar mace ce sosai da shine karamin danta, yaje ya gaya mata karya da gaskiya ni ban san me suka yi ba tunda bana gurin, a rannan ta ce wai ai bana kiranta sai zan tayar nata d  hankali🙄🤔🤔 nace ni kuwa yar mama d baba ban Kara kiranta na daina...muka koma kaman jidda d mama🥴 daga nace ki Fadi ma danki gaskiya d tun a lokacin anyi bincike d ba a kai nan b.... Kaman yanda mama ta kawo me tona mata  asiri haka baban **** made it to d dailies....

I left the house ba a zo anji why ba cz when I concluded cewa yana yi just as jidda did, na daya na biyu d next one I was ready to give up d marriage and I did, So nayi parking babu Wanda yazo yace me ya faru, muka ta saka ido tunda sun san maybe asirinsu zai tonu sai basuzo b and the mum said duk Wanda yazo Allah ya isa😊. Baba na ya bi elder brother dinshi yace me ya faru me ake ciki? he's a step bro so I think he backed out.

So d baba ya tashi he went to a sharia court yace gashi yarshi na gida 6months baya son ta koma gidan wani ya za ayi? Sai akace sai dai yayi min khulki(na mayar d sadakin d na karba lokacin aure) sai baba yace toh, but still an tura mashi sammaci akan yazo aji ta bakinshi sai basu zo b

Ran d akace mu koma naje ni kadai he didn't show up, aka Kara tura mashi still be zo b sai alkali ya ce mu dawo rana kaza sai baba yaje yazo d waliyanshi, toh tunda an bada date d za ayi finilizing sai ga waliyy yazo min da takarda wai ya rubuto min saki daya in na samu miji nayi aure and ya yafe sadakin ba sai na biya b

So sai alkali yace dole sai an bani certificate of divorce akan shi alkalin ne ya raba auren bisa khulki, alkali ya raba aure ya bani certificate showing khulki akayi yace in ba'a bani ba he can say gobe ya mayar d ni Kuma na maidu

So khulki is refunding d sadakin to the husband sai ya bama alkali ikon raba aure ama idan ya yafe it's ok in bai yafe b sai an mayar. In akayi khulki miji bashi da ikon cewa ya mayar da matarsa ko da kuwa tana idda ne, sai dai in ta gama in an daidaita sai a sake sabon daurin aure ya sake biyan wani sadakin.

Shi abun da a ke cewa sharri nayi mashi shi abun sai gashi an dora shi a goggle, ko yanxu kukayi yanzu zai fito, banji Dadi ba Don na haifi yara har biyu MAZA❤️❤️ ama sai nace toh ga sharri d akace nayi mashi shi duniyace ta wankeni😊...

D ace za a zauna d ƴa ko matar ɗa a saurari maganar su d za a shawo kan matsalan, kaman nawa tun baiyi nisa b d mahaifan sa sun dage d dua d yazo d sauki amma aka ce wace ni?😰 karku manta shine uban 'ya'ya na to an extent ai mu mata munfi iyayensu son gyaruwarsu ko akasin haka Don tsatson su d suka biyo ta mu... To cut d lonnnnnnng story short ko last week an kirani akace ai Naga wane a youtube ashe haka ya faru nace walhi mun rabu yanzu 4 years+ amma d aka tashi one random person haka ni ya Kira, I felt bad for his kids Don suma Kila a samu me kiransu yace ashe kaine Dan wane kenan💔💔😭😭 bamuzo ma wurin neman auren su ba...ko neman aiki/takara lokacin za a tuno maka d abun d ba kai kayi b😊

Nayi aure na yanzu alhamdulillah to the husband da a guri na is the best in the world, ba shi da problem sai ajizanci irin na dan adam. An I am over wancan case din. Kuma yayana suna hannuna.
 
Jidda Allah ya Baki saa ya zaba maki abun d yafi alheri
   Ki rufe kunenki Don Zaki sha zagi zaki sha magana ki dauki na dauka ki bar musu sauran,nima nasan sai nasha amma babu komai

  Kuyi hakuri d dogon sharhi na💪🏼💪🏼💪🏼
Writing this got me a lot relieved even though I'm over it. But ai jiki d Jini and seeing my boy sometimes reminds me of it. And d call na last week 😊🤔 sai naji tausayinshi dana ya kamani.

If jidda is still in this mess she needs to b strong for her kids coz d hustle out here is real 😰

*2*

Jidda touched me sosai da sosai ina karantawa ina dariyar takaici saboda tunawa da abubuwan da suka faru Dani, nikam sam ban samu mafita ba, September na gudo gida nace na gaji, karshe sai babana ne ya karba min takarda da kyar a November yanzu har na gama idda ta na fara kiba abuna



*Wannan littafin na siyarwa bisa amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*The fourth Step*

Na saki kwalar rigar Asabe daga hannuna, ko kuma ince rigar ta zame daga hannuna dan ban ma san cewa na sake ta ba sai da naga asaben ta yi baya da sauri tana neman hanyar barin kitchen din. Jiri nake ji yana dibana, yawun baki na gabakidaya yayi hijira sai bile mai daci da yayi replacing dinsa. Duhu nake gani a idona, na fara lalube ina neman abinda zan dafa dan kar in fadi, hannuna ya sauka akan cabinet din kitchen din, na dafa da hannu daya daya hannun kuma na dafe kaina dashi ina ambaton "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Allah nake kira ina neman daukin sa dan shi kadai ne zai taimaka min a lokacin saboda shi kadai ya san halin da nake ciki, shi kaɗai yasan abinda nake ji a zuciyata sai kuma wadda ta samu kanta a cikin yanayi irin wadda na samu kaina a ciki a lokacin.

Wani irin bacin rai nake ji yana tasowa daga zuciyata yana zarce wa har cikin kwakwalwa ta, a tare da bacin rai akwai tsantsar tsanar wanda da nake ji kamar nafi sonsa a duk cikin mazan duniya bayan mahaifina. Mutumin dana kwashe shekara shida ina kiran sa da mijina shi kuma yana kirana da matarsa, mutumin da a yanzu yake a matsayin uban yayana guda biyu kuma mutumin da bayan ni yayana suka fi so fiye da kowa a duniya.

Hawayena ya sauka akan hannayena da suke kan cabinet din, na kalli hawayen ina ayyanawa a raina cewa sune na karshe da zan zubar a kansa. Na zubar da hawaye sunyi cikin jarka a kansa amma wadannan sune na karshe. Na gama. Am done.

Dariyar Asad najiyo ta shigo kitchen din daga window tana ratsa cikin zurfin tunani na kamar kibiya on fire, kamar tunatarwa cewa I can't say that, I can't make that decision, kamar tunatarwa cewa ba rayuwata kadai wannan hukuncin zai taba ba har da rayuwar innocent yayana. Are they ready to face that?

Na juya ina kallon window din, a lokaci daya muka hada ido dashi shima yana kallon na da Asad a hannun sa gefensa kuma Yasmin tana rike da skipping rope a hannunta, na tsaya kawai ina kallon sa ina jin wutar kiyayyar sa tana kara ruruwa kamar ana zuba mata fetur a cikin zuciyata.
Fuskarsa da murmushi ya rada wa Asad wata magana a kunne sai Asad ya dago min hannu alamar kira "mommy come and join us, ki zo muyi wasa, Daddy zaiyi wasa tare da mu" ya karasa maganar tare da mannawa Umar kiss a goshinsa.

Nayi saurin dauke kaina tare da juya baya na na daina kallon su "in time zasu koyi rayuwa ba tare da daddyn su ba" wata zuciyar ta gaya min "Baby Dove. Come out and show us if you still have it in you" naji muryarsa ya fada da alamar dariya a muryarsa da kuma tsokana. Idona ya sauka a kan set din wukake na da suke ajjiye a maadanar su, wata zuciyar tana gaya min "dauki babbar ciki kije ki soka masa a zuciyarsa, kamar yadda ya soka miki time and time again"

Hannuna ya sauka kan wukar na dauko ta na juya ina kallon inda suke, suna iya hango ni amma ba zasu iya karanta emotions dina daga can ba. "Mommy daddy yana tsokanar ki wai ba zaki iya skipping ba" Yasmin ta sake fada da karfi. Na juya na sake kallon su, duk su ukun dariya suke and they look so happy together, na kalli hannuna rike da wuka, wukar dana dauka amma ban ma san na dauka din ba, wukar da zuciyata take gaya min in je in chakawa mijina a gaban yayan mu. Na sake ta ta fadi kasa ina jin kamar nima in bita mu fadi tare, har yanzu dariya suke yi suna cigaba da kiran sunana.

And I knew wannan daukan wukar da nayi shine na farko amma ba lallai ya zama na karshe ba in dai har na cigaba da zama da Faruq, nasan cewa there will be only two ways out of our marriage in dai na cigaba da hakurin da kullum ake gaya min a kunnuwa na, ko dai in kashe Umar ko kuma shi ya kashe ni da bakin cikin sa, either way yayan mu zasu taso da tabon cewa daya daga cikin mahaifan su ne ya kashe dayan.

"I must get out, now" zuciyata ta kuma gaya min. A hankali na ce "am sorry Yasmin, am sorry Asad" sai kuma na juya da sauri mai hade da gudu na bar kitchen din na wuce falo na tafi bedroom dina, niyya ta ina shiga in fada gado inyi kuka kamar yadda na saba a duk lokacin da Umar yayi aika aikar sa, amma wannan karon sai na ji na kasa karasawa kan gadon nawa, naji kafafuwa na sunyi giving up a tsakiyar dakin, na durkusa a gurin hannayena duk biyun a dafe da kirjina kamar mai kokarin rike zuciyata da hana ta fadowa kan cinyata, dan irin bugun da take yi da ace ba rike take da jijiyoyi ba da tabbas zan ganta a gabana and that will be the end of me. "In baki bar Faruq ba tabbas Faruq zai kashe ki wata rana, zai kashe ki da bakin cikin sa" na tuno kalaman Farhan. "In kin mutu karkarinta ayi sadakar arba'in dinki, wata zai kawo dakin ki, ya debi yayanki ya bata dan kin san babu mai hana shi karbar yaya, ita kuma ta gana musu azaba son ranta". Inji wani sashe na zuciyata

Na dauke hannayena daga kan kirjina ina girgiza kaina ina magana a hankali kamar tababbiya "ba zaka kashe ni ba Umar, I won't let you" na mike sai kuma jiri ya debe ni na sake zubewa a gurin. Wai Asabe, Umarul Faruq wai Asabe, tabbas idan bai kashe ni da bakin ciki ba zai kashe ni da cutar da zai kwaso a wani gurin ya shafa min, in yaso in mun mutu duka a rabawa dangi yayan mu.

Motsin kofa naji, ban dago kai na daga kan carpet ba amma kamshin sa da rashin sallama ya saka na fahimci shine. "Baby, muna jiran ki fa, ko kinyi giving up ne?" Ya fada cikin raha. Ban dago kai ba amma ji nake kamar wani mala'ikan mutuwa ne ya shigo dakin, tabbas in bai fita ba, in ya bari na kama shi tabbas sai na nakasa shi, in ya sake yi min magana da wannan muryar tashi tabbas zan iya fasa bedside lamp a tsakiyar kansa.

Hannunsa da naji a bayana ne ya saka na zabura da sauri kamar wadda aka dorawa garwashin wuta a jiki. Tsaye na mike ina nuna shi da hannu amma maganar ta kasa fitowa daga bakina sai hawaye da yake bin kuncina. Ido ya zaro waje yana kallon fuskata. "Jidda? Lafiya? Are You sick?" Ya jero min tambayoyin guda uku da bani da niyyar amsa ko daya daga cikin su.

"Kar ka sake" na samu harshe na ya furta, "kar ka sake ambaton sunana daga yau, kar ka sake tunanin ka sanni, in ka sake yi min magana Allah ya isa" mamaki ya bayyana a fuskarsa. "Jidda?" Ya fada da sauri cikin mamaki, da alama bai ji warning dina ba.

Bansan lokacin dana karasa gabansa ba, ban kuma san sanda na aikata ba sai dana ji karar mari a kunnena sannan na fahimci marin sa nayi. Sai a lokacin na samu kukan da yaki zuwa gabaki daya ya taho. Ya juya da sauri, a tunani na marin da nayi masa ne ya saka zai fita amma sai naga ya rufe kofar dakin da sauri ya juyo yana kallo na. Of cause, babban tashin hankalin sa shine yayansa, babban abinda zai tayar masa da hankali shine yayansa su fahimci akwai problem a cikin their lovely painted happy family.

Ya dawo da sauri yana kokarin kama hannuna. "Jidda lafiya? Mai kuma nayi? Talk to me" idan da wani zai gan mu a lokacin zai yi tunanin babu wadda tayi dacen miji iri na, mijin da zai tashi hankalin sa idan yaga kukan matarsa, mijinda matarsa zata daga hannu ta mare shi amma ko gezau bai nuna ba.

Na ture hannun sa daga jikina, har abada jikina ya haramta a gare shi kuma. An gama. Na dago ido ina kallon sa, zuciyata tana kara kuna a lokacin da idona ya sauka akan fuskarsa. It hurts so much idan mutumin da ka tattara soyayyar ka akansa ya

66 / 106