Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
yi min magana sai na murguda mata baki na cigaba da waya ta, there is no way da zan ce Mufida ta bani number din yayanta duk kuwa da kasancewar Mufida kawata ce.
Bayan mun gama wayar sai Farhan ta karbe wayar ta sake kiran Mufida "Mufida ga fa kawarki nan taki ci taki sha saboda sunyi fada da yayanki. Allah kuwa. Ki kira shi kice ko dai yazo ko kuma zuciyarta tayi bindiga" na mike tsaye da sauri na bita ita kuma ta fita a guje da wayar a hannun ta, a tsakar gida suka hadu da Umma tayi sauri ta mika mata wayar ta sannan ta shige dakin Hajiya dan tasan ba zan bita can ba.
Nayi sauri na karbi wayar a hannun Umma na saka a kunne na ina cewa "karya take yi Mufida, sharri take yi min" naji Mufida tana dariya "kwaji dashi ma daga ke har shi, dazu ma sai da ya kira ni yana tambayata wai munyi waya da ke? Ni bani na hada ku ba kuma bana son in kasance a tsakiya in kunyi fada ma sai dai ku shirya kanku ni dai ba zan shirya ku ba" nace bafa fada muka yi ba, sharrin Farhan ne" sai kuma na bata labarin abinda ya faru, tace "lah! Babbar magana, yaya Doctor ne da kishi haka? Ban taba gani ba. Zan kira shi in gaya masa kin kira kina tambayarsa" nace "ki rufa min asiri kar kiyi mini sharri ke ma" ta sake dariya, "tsokanar ki nake yi. Ki share shi zai dawo ne da kansa"
Naji dadin yadda Mufida tayi reacting, kuma na bi shawarar ta na share shi nima har sai da yayi kwana goma rabonsa da gidan mu.
Ranar nan Sulaiman ya zo gurin Farhan sai muka fita tare, muna zaune muna hira wanda mostly su biyu suke kayarsu sai dai in sun ambaci sunana sannan sai in basu amsa.
Da yake kofar waje a bude take kuma ni ce nake zaune a kujerar da take facing kofar, ina hango wulkawar mutane duk da cewa su ba zasu hango ni ba, a haka naga tsayuwar motar sa wadda ko cikin mafarki zan gane ta, tun daga nan na daina jin hirar su Farhan na koma kallonsa, komai nashi yayi min komai nashi yana burge ni, ina kallon sa ya fito daga motar ya rufe sannan ya tsaya a gaban motar yana kallon gidan mu, yana kallon kofar sitting room din da take a bude, sai kuma naga ya tako ya shigo cikin railer din still yana kallon budaddiyar kofar sannan kuma naga ya kalli takalmin Sulaiman da yake ajiye a bakin kofa.
Sai kuma naga ya daga labulen dakin da sauri yana rarraba ido a cikin dakin. Na mike tsaye da sauri ina kallon sa kamar yadda shima ya tsayar da idonsa a kaina. Cikin saurin magana nace "Yaya Doctor wannan saurayin Farhan ne, sunan sa Sulaiman".
Sai da naji Farhan tayi dariya sannan na fahimci abinda nayi, sai kuma naji kunya, ina kallon sa yayi murmushi sannan yace "hey Baby" Farhan tace "baby ce kam, dan yadda tayi ta kuka wai saboda kayi fushi da ita idan ba baby ba babu mai yin haka" na juya na harare ta, ido na yana kawo kwallar haushin tonon sililin da tayi min, yace "Allah da gaske Farhan? Da gaske tayi kuka?"
Sulaiman da yake kallon mu yace "ga wani kukan nan zata sake yi ai" nan take sai hawayen ya karasa zubowa. Na zauna ina gogewa da hijab dina, Umar ya zauna a kasa a gaba na yace "innalillahi. Kukan ne kuma? Ashe ina da aiki babba a gaba na" Sulaiman yace "ba kadan ba, sai ka shirya aikin rarrashi" na harare shi, Umar yayi sauri ya tare bangaren Sulaiman "noooo wannan hararar ni kadai za'a yi wa ita, tawa ce ni kadai" na dawo da ido na kansa sai ya koma ya zauna a gabana "na gaya miki ai, ina da tsananin kishi" na murguda masa baki sai ya lunshe idonsa yace "kara wani"
Duk suka yi dariya Sulaiman ya mika masa hannu yace "salamu alaikum, gwara mu gaisa kafin ayi maka hararar da zaka narke ban samu ladan musabaha ba" suka gaisa sai kuma muka fara hira gaba-daya mu hudun, mostly akan soyayya tsakanin yammata da samari. Ana cikin hirar ne Umar yace min "before I forget irin ta ranar nan, ina son ki bani exam number da center number din ki na waec, result din ku ya fito, gashi har na siyo scratch card zan dubo miki. Dama ina ta addu'a Allah yasa ta fito kafin a kira ku pretest, dan I was suppose to go with credentials dinki sanda zan karbi form, dan dai an daga min kafa ne"
Naji hankali na ya tashi "yaya Doctor in na fadi kuma fa? In ban samu abinda suke bukata ba fa?" Yace "sai mu jira neco ta fito, in baki ci a waec ba zaki ci a neco" nace "in ita ma banci ba fa?" Yace "common Baby, zaki ci fa, kuma in ma baki ci din ba akwai private neco da ake yi around december, sai in nemi wani in biya shi ya rubuta miki ki sami 9 distinctions, babu wani problem fa, tunda kina da ni baki da sauran matsala".
Sulaiman yace "wai maganar me kuke yi ne? Kamar makaranta kuke magana akai ko? I thought Abba baya bari ayi karatu sai bayan aure" Umar yayi saurin kallo na sai na sunkuyar da kaina kasa, Farhan tace "ya sauko ai Abban, ya bar Jidda tayi as long as Umar ne zai aure ta, tunda shine yake nema mata makarantar"
Yace "ohh okay, good" sai tace "nima zai iya barina in fara idan kai ka samo min" ya girgiza kai "a'a don't start there, mun riga mun gama magana da ke cewa sai munyi aure first year din mu zaki tafi school, wannan shine tsarin mu ni da ke bana so kuma dan kinga wasu sunyi nasu tsarin ki ce ke ma irinsa kike so. Kinji?" Ta gyada kai a hankali, amma daga gani ba haka ranta yaso ba, sai ya mike yayi mana sallama ita kuma ta bishi zata raka shi waje.
Bayan sun fita na mayar da hankali na kan Umar ina jiran ya fara jero min tambayoyi amma sai kawai naji yace "ina fatan banyi laifi a gurin Abba ba?" Na girgiza kai na, yayi ajjiyar zuciya "har na tsorata, na dauka nayi masa shishshigi" na danyi murmushi, sai yace "da na sani da na taho wa da Farhan form din ita ma ta cike, naga kamar tana so" nace "Abba ba zai barta ba ai, cewa zaiyi ai ba kai ne zaka aure ta ba" ya gyara zama "wato ya bar ki ne saboda ni zan aure ki?" Zuciyata daya ma gyada kai sai ya daga hannunsa "yes!" Sai a lokacin na lura da abinda nace, na rufe fuska shi kuma yana dariya.
Daga nan sai ya zauna ya fara min bayanin yadda tsarin neman admission a school of nursing yake "zasu kira ku kuyi pretest, daga nan wadanda suka ci zasu je ayi musu interview idan sunci sannan sai a basu admission" nan take na rude, shi kuma yana ta yi min dariya tare da kara jaddada min cewa tunda ina da shi bani da problem.
Da zai tafi yau ma har sai daya fita sannan ya tuna cewa bai karbi details din da yake nema ba, sai yace in karbo na Farhan ita ma ya dubo mata. Na koma gida na binciko a cikin takarduna na makaranta sannan naje na taya Farhan neman nata a dakin hajiya muka fita tare muka kai masa.
Washegari da rana sai ga Mufida ta kira ni tana min albishir cewa naci duk subjects ɗin da ake bukata, nayi ta murna ina tsalle itama tana tayani, sai ta bani labarin cewa itama ta ci amma ta fadi English "sai na sake resitting kafin in samu admission" sai naji babu dadi kuma na jajanta mata. Tace "mutumin ki farko cewa yayi wai in bashi number din da muke waya da ita, sai da na bashi kuma nace ta Umma ce sai gashi ya sake kira na wai ya kasa kiran ta, wai kunya yake ji, in ta dauka bai san me zai ce mata ba, gashi bama tare bare ya bani mu fara magana" ta sake dariya. "Wai yaya Doctor ne yake jin kunya"
Nayi tsaki "ke bama son rashin kunya fa, ki kama kanki ko kuma jikin ki ya gaya miki" tace "ohh, wato dan kin zama budurwar yayana shine har zaki fara dorawa kanki girma ko?" Nace "eh mana, da shekarun sa nake amfani ai yanzu ba da nawa ba" tace "yayi kyau Aunty, daga yau Aunty zan ke kiranki da shi" muka yi ta hirar mu sannan ta sake congratulating dina muka yi sallama.
Next zuwan da zaiyi ya taho min da printout na results din mu ni da Farhan kuma alhamdulillah duk munyi abin kirki sosai. Kusan kowa na gidan sai da na nuna masa, Abba ma yana zuwa naje na nuna masa kuma na gaya masa wanda ya dubo min, naga alamar yaji dadin hakan kuma yayi mana addu'ar fatan alkhairi.
Da aka saka ranar da zamu yi pretest din shi da kansa yazo ya samu Abba ya sanar masa kuma ya roke shi ya bar ni inje, Abba ya bari kuma yayi min fatan alkhairi. Da ranar tazo ma Umar din ne yazo dauka na, na shirya cikin sabuwar abaya ta maroon da Aunty Afia ta siya min, light make up tunda exam zanje, sannan nayi rolling mayafin abayar, amma dana kalli kaina a madubi sai naga nayi kyau sosai fiye ma da yadda na saka ran zanyi, sai dai na lura cikar kirjina ta bayyana sosai kuma veil din iyakacin kafada ta ya tsaya min, wannan yasa na samo bakin medium veil na yafa akan kafaduna ya sauko ya rufe kirjina. Sannan na dauki bakar jakar da na saka duk takardun da ya gaya min in tafi dasu a ciki.
Na fito ina kallon Umma ina saka ran ta kora ni tace in saka hijab amma sai naji bata ce komai ba, wannan ya tabbatar min da shigar tawa tayi dai dai. Na hau nayi wa Abba sallama sai ya hada ni da Amira yace mu tafi tare.
A waje muka samu su Umar, tare suka zo daukar mu shi da abokinsa Bashir, a ranar na fara ganin Bashir. Muna fita ya bude min baya na zauna yana ta bina da kallon dana tabbatar na birge shi ne "da motar da mai motar duk naki ne" ya rada min yadda Amira ba zata ji ba, Bashir yace "gulmar me ake yi ne? Kai fa dan iska ne" sai Umar yayi dariya ya koma gaba ya zauna Bashir yana tuka motar, "in ni dan iska ne kai kuma ai shege ne" suka sake dariya, sai naji ban ji dadin yadda suke zagin junansu a matsayin wasa ba, to ko haka maza suke tasu abotar?
A hanya ne Umar yake cewa "Baby ga abokina, ko kuma in ce oga na. Shine mai private clinic din da nace miki ina yiwa aiki, kuma senior na ne tun a school sannan kuma yana da ruwa da tsaki a cikin duganarwar makarantar ku shi yasa nake ta bragging cewa baki da problem, dan haka sai kike yi masa ladabi. Sunansa Bashir Ibrahim" nace "ina kwana Malam Bashir. Sannu da hidima fa, an gode" ya gyara mirror din motar zuwa kai na yace "da baki gaishe ni ba sai da kika ji zancen faduwa exams?" Nayi murmushi "lah ba haka bane ba fa" yace "kuma bana son Malam din nan, ki ce Bashir direct dan Malam yana saka ni inyi feeling kamar tsoho especially in ina tare da kyawawan yara irin ku" Umar ya saka hannu ya mayar da mirror din dai dai sannan yace "au kai da daukan ka kake yi yaro? Ai chus ne kai".
Haka suka cigaba da hirar su suna tsokanar juna har muka je makarantar. Ni kuwa duk na bi na tsure. Muna tsayawa Bashir ya fita, Umar ya juyo ta bangare na yana min magana a hankali "hey ba wahala fa, am sure zaki ci kinji Baby na?" Na gyada kai, tashin hankali na shine kar inje in fadi inji kunya a gaban saurayi da kuma abokin saurayi. A haka Bashir ya dawo ya kawo min attendance sheet nayi signing sannan muka fita gabaki daya suka rakani har kofar hall din da zamuyi test din sannan suka koma bakin bishiya suka zauna jira na.
Kusan duk tambayoyin da aka yi mana na san amsoshin su dan haka ban wani samu matsala ba alhamdulillah. Bayan mun gama muka yi submitting tare da photocopies na credentials din mu sannan muka fita. Ina fitowa na hango Umar ya mike sannan ya taho muka hadu a hanya bakin sa har kunne, "from the way da kike ta smiling nasan tayi sauki sosai" na gyada kai, yace "alhamdulillah" Bashir ya karaso tare da Amira a gefensa suna tambayata ya paper din, "alhamdulillah, tayi sauki sosai" Bashir yace "wow, ban taba jin wanda yace pretest tayi masa sauki ba sai ke, lallai ke din ta daban ce, and I think this calls for a celebration ko ya kace Faruq? Ya kamata mu tafi dasu mu danyi celebrating mu sha ice cream"
Sai naga fuskar Umar ta chanja yace "uhmm, I don't think so" Bashir yace "why not?" Umar ya danyi murmushi yana shafa kai yace "bana son muyi laifi a gurin Abba. Gwara mu mayar dasu gida kawai" Bashir ya sake cewa "Abba a ina zai san inda muka je? Ai bai san yaushe suka gama ba kuma ma the day is still young ba wai dare ne yayi ba" Umar ya sake girgiza kansa fuskar sa ta fara nuna alamar bacin rai "no, gida zamu kai su direct".
Ganin musu yana kokarin sarke wa a tsakanin su yasa na ja Amira muka tafi gurin mota ina bata labarin irin questions din da aka bamu. Mun dan jima muna tsaye kafin su taho, sai na lura kuma tension din tsakanin su was no longer there, kafin mu shiga mota Bashir yace "I must comment to you Jidda, ke ce mace ta farko data sace zuciyar abokina, ya saba sace zuciyoyin mata amma shi ba'a taba samun wadda ta sace ta sa zuciyar ba sai ke. Hope zaki rike min shi da amana" na kalli Umar da yake tsaye yana ta zabga murmushi nima na mayar masa sai yace "ana baki amana ta baki ce komai ba" na sunkuyar da kai na sannan nace "na karba, na kuma gode" "nine da godiya" ya fada da dariya a muryarsa.
A Oasis naga sun tsaya sannan suka yi excusing kansu suka shiga, few minutes suka fito da ledoji suka dawo muka karasa gida, bayan sunyi packing ne Umar ya bawa Amira ledojin hannunsa, ta karba yayin da ni kuma na bita da harara, yace "tunda ta harare ki kar ki bata ko dandane" tace "ai kuwa tunda ka fada ba zan bata ba, ni da Farhan zamu cinye"
Bayan ta shiga nima ban jima ba nayi musu doguwar godiya su kuma suka yi min fatan nasara sannan na bi bayan ta.
A falon Umma na tarar an baje ledojin da Amira ta shigo dasu, har da yaya Tahir da Abbah kowa ya dauki burger da ice cream. Ina shiga Abbah ya fara tsokana ta "ka ga likita matar likita, kina tafiya allura tana zuba"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Episode Nine : Engaged*
Soyayya muke yi da Umar mai ratsa zuciya da ruhi, Umar baya iyayin kwana uku ba tare da yazo gidan mu ya ganni ba haka nima duk inda ya kwana biyu bai zo basai inji ko abinci ma baya tafiyar min sosai.
Cikin kankanin lokaci duk jama'ar gidan mu da wadanda suke cikin gidan da kuma wadanda basa ma gidan a lokacin amma sun san labarin Doctor Umar saurayin Jidda, a lokacin na kuma fahimtar abinda ake kira da yan'ubanci dan kiri kiri Hajiya da yayanta suke nuna rashin jin dadin su da irin saurayin da na samu, a inda ita kuma Umma take sakin bakinta tayi ta mayar da magana a duk lokacin da aka jeho mana ita. Amma wannan sam bai taba amintakar mu da Farhan ba, su suna harkokin su mu muna namu.
A bangaren Umar shima a yanzu duk yan gidan su sun san da zama na kuma sun san abinda yake tsakanin mu, dan ranar nan kawai sai ga Mama ta kira Umma a waya wai ta kira ta su gaisa, haka Aunty ita ma ranar nan ta kira. Mufida ma yanzu ta fahimci yayanta da gaske yake dan haka ta saki jiki da maganar musamman yanzu da suka gama hutunsu a Lagos suka dawo Kano Umar ya samu damar yin amfani da ita wajen yin waya dani, ya kansa ta kirani in karbi wayar mu gaisa sai yace in rike wayar kar in mayar wa da Umma sai shi kuma ya kira ni da layinsa.
Soyayyar Umar mai dadi ce, irin mai tsayawa a rai din nan ce, kalaman sa masu dadi ne dan zan iya cewa Allah yabashi baiwar tsara kalamai yadda duk wanda aka gayawa sai sun shige shi kamar yadda kullum suke shiga ta.
Kamar yadda Umar yayi min alkawari haka ya tsaya kai da fata, da karfinsa da lokacin sa da kuma aljihunsa wajen ganin yayi min securing admission a school of nursing, har Allah ya taimaka aka samu din. Sanda aka samu da kansa ya dauki takardar ya kuma dauki mota ya tafi office din Abba yaje ya kai masa, Abba yayi murna sosai ya kuma saka albarka. Sai kuma Umar ya sake rokonsa wata alfarmar daban