Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
safe ma karasa maganar" ta juya ta tafi, and I couldn't help but noticed yadda yabi ta da kallo.
Zafin abin ya saka na kasa magana, sai kawai gani nayi ya ajiye spoon din hannunsa ya tashi ya bar min gurin, na tattare kayan gurin na kawar sannan nima na tashi na tafi, ko kallon dakinsa banyi ba na shige nawa na kwanta a raina ina cewa dani kake zancen, zaka zo ka same ni ne har inda nake a lokacin ne kuma zaka yi bayanin dalilin da yasa kayi abinda kayi din. Sai dai abinda ban sani ba a lokacin shine wannan fadan yafi karfina. Tun ina juyi ina jiran inji ya shigo karbar abinda nasan baya fushi da shi har na fitar da rai bacci ya dauke ni.
Da safe na tashi na fara aikina kamar yadda na saba, ina saka ran fitowar Mammy dan takan fito in taji ina aiki ta kama min muyi tare amma shiru har na gama hada breakfast na koma na tashi Yasmin na shiryata muka fito kusan a tare da Faruq. Yasmin ta saki hannu na ta tafi gurin sa da gudu "Daddy na!" Ya daga ta sama "uwata ta kaina. Kin tashi lafiya? Ina Asad?" Tace "yana bacci, Daddy ina ta nemanka jiya ban ganka ba" ya zauna da ita a jikinsa "to gani yanzu me zaki bani?"
Na jawo cups na fara hada musu tea sannan nace masa "barka da assuba" "lfy lau" yace ba tare da ya kalle ni ba. Na mika masa tea din ya dauka yana kalle kalle kamar mai neman wani abu "ina dota ta? Kar dai bata tashi ba" na saki baki ina kallon sa na rasa ma amsar da zan bashi. Sai kuma na zauna "Umar wai lafiya kuwa? Daga jiya zuwa yau na kasa gane kanka lafiya? Nayi wani laifi ne da ban sani ba?"
Ya ajiye cup din hannunsa yana kallon agogo "Yasmin sauri ki sha tea mu tafi zaki makara" ya mike tsaye nima na mike ina jin kamar zanyi kuka "baka yi min magana ba fa. Tun jiya kaki kayi min magana me nayi maka wai?" Yace "baki yi min komai ba fa. Kuma ni ban san abinda yasa kike wannan tambayar ba, in wani abun kika so ki bari in dawo sai ki gaya min yanzu sauri nake yi" sai ya dauki jakarsa ya tafi, yana tafiya yana waigen kofar dakin yara inda Mammy take.
Sai wajen 12 sannan Mammy ta fito, lokacin na gama komai har nayi wa Asad wanka nima nayi na shirya. Ta gaishe ni sannan ta zarce dining table ta fara zuba abinci, nace "Mammy in kin gama cin abincin ki shirya zan mayar dake gida" ta ajiye cokalin hannun ta tana kallo na "gida Aunty?" Nace "eh. Na gama hutawar ai. Zan cigaba da dukkan ayyuka na da kaina yanzu" ta zumbura baki "ni wallahi ni wallahi" na ari page daga cikin pages din Farhan "kar dai kiyi min rashin kunya. Ki shirya nace zan kaiki gida yanzu" ta dangwarar da tea din da yake hannunta har ya zube akan table din sannan ta koma dakin data fito taa kunkuni. Na bita da kallo sannan na tafi dakina na dauko kayan da na ware zan bata na fito dasu na ajiye a kusa dani tare da key din mota.
Bata jima sosai ba ta fito da jakat kayanta a hannun ta sannan tayi waje ba tare da ta ce min komai ba, wata zuciyar tace min in bar ta kawai ta tafi a motar haya tunda ita marar kunya ce amma sai dai na tashi na dauki kayan da na bata sannan na dauki Asad na fita. Tana tsaye a kusa da mota ta, na bude na shiga sannan itama ta bude ta shiga ta karbi Asad ta rike shi muka tafi. Har muka je gidan su babu wanda yayi magana a cikin mu, da niyya ta in ajiye ta a kofar gida in juya amma tunawa da nayi har gida aka kai min ita sai nima na shiga har gidan. Na gaishe da Mama Sa'a na kuma bata kayan da na hadowa Mammy sannan nayi mata godiyar zaman da Mammy tayi tare da ni. Na ga fuskarta ta nuna rashin jin dadin dawo mata da yarta da nayi amma ban bari hakan ya dame ni ba na juya na koma gida.
Ban jima da komawa gida ba sai ga wayar Umar, na dauka kiran daya saba yi min ne kullum in baya gida duk bayan wani lokaci dan yaji yadda muke ni da yara, amma ina dauka sai ya rufe ni da bala'i, abinda Umar bai taba yi min ba tunda igiyar aure ta shiga tsakanin mu. "Akan wannan dalili zaki dauki Mammy ki kaita gida? Da iznin wa ma kika fita daga gida? To ki dauki kafa kije ki dauko ta kamar yadda kika dauka kika kaita"
Sai mamaki ya kama ni, mamakin fadan da yake yi min sannan da mamakin abinda yake min fadan a kan sa. Har ya gama fadan sa tare da bayar da umarnin sa bance komai ba sai ya kashe wayar. Na zauna ina jin kaina gabakidaya ya kulle, amma ko kadan banyi niyyar cika umarnin sa ba kuma na saka a raina cewa indai har ya dauko ta ya dawo da ita ni kuma zan fita in bar musu gidan sai da ya zaba ko ni ko ita.
Sai dai kuma daya dawo din bai dawo da itan ba kuma baiyi min maganar dawo da ita din ba, sai dai na ganshi da sabuwar android phone a hannun sa, ya kwanta a falo yana ta danne dannen sa, na zauna a hannun kujerar da yake kai nace "sabuwar waya muka yi?" "Uhmm" kawai yace min, na sake cewa "kuma babu sanarwa balle mu taya ka murna, ko dan kar a bani dani" ya mike zaune yana kallo na "idan nayi niyyar yin sabuwar waya lallai sai na sanar da ke kafin inyi? Yanzu ba gashi kin gani ba"
And I asked myself "ina Umarul Faruq dina?" Dan wannan ba shi bane ba wani be mai kama da shi......
And that was just the beginning......
Weeks din da suka biyo bayan nan zan iya cewa are the worst a rayuwar auren mu. Umar ya chanja completely, ba wai cin mutunci ko zagi ko hantara ta yake yi ba, a'a, nunawa yake yi as if I am invisible. Ya daina zaman gida kwata kwata, tun yana dawowa gida bayan isha har ya koma dawowa karfe goma har ya koma wani lokacin sai cikin bacci zanji an bude masa gate ya shigo gida. Abinci ma ya daina ci sam sam ko da kuwa breakfast ne. On his bright days ne zai zauna yayi wasa da yaransa, on the worst days kuma ko su basu ishe shi kallo ba ballantana ni da ko a inches na kusa da shi baya son ganina.
In yana gida ma wayarsa tafi yi masa komai muhimmanci a cikin gidan, daga baya har ta kai Umar yana zama yayi waya da budurwa a gaba na. Na fahimci budurwa ce saboda kalamai irin "ke ma kin san in banji muryar ki ba ba zan iya bacci ba".
The first time da naji irin haka I cried myself to sleep. Na tabbatar a raina Umar budurwa yayi kuma maybe aure zaiyi, na jima kuma da saka wa a raina cewa yana da wannan right din amma ban taba tsammanin in lokacin yazo zai juya min baya irin haka ba, ban taba tunanin Umar zai iya zama a gabana yana yiwa wata mace kalamai ba, yanzu da yake neman ta ma kenan, idan ya aure ta kuma fa me zan koma a gurin sa?..
And it hurt me more than I thought it would.
Bayan nan kuma sai na lura ya dawo da abotar su da Bashir, duk da ban tabbatar ba idan ma ya yanke ta da gaske a da ko kuma dama can playing dina yake yi. Na fahimci haka ne wata rana da weekend Umar yana gida naji yana waya "hello oga bro", na juyo da sauri ina kallon sa saboda fahimtar da wanda yake waya, haka yake ce da Bashir. "Ka fito ne?" "I don't feel like driving today, ka zo ka dauke ni sai mu wuce" yayi dariya "kai ka fiya tsoro, sai kace wani mata maza. Just call me in ka shigo layi sai in fito" "okay sai ka karaso".
And I realized all my efforts are gone down the drain........
And then one day. Lokacin shekaru na 24 a duniya, lokacin shekaru na biyar a gidan Umar, Yasmin lokacin watanni ne kadai suka rage tayi shekara hudu, Asad kuma yana da shekaru biyu.
Ina falo a kwance Umar yana daki tare da Asad, sai ga Asad ya taho da wayar Umar a hannun sa yana game a ciki, na kalle shi na dauke kai na cigaba da tunanin abinda ya dame ni. Ya hau jikina ya fara rigima "mommy daddy yayi bacci, kiyi min game ni ban iya ba" na ture shi "ka rabu dani Asad" ya fara bori "ni kiyi min game, ni ban iya ba" nayi tsaki na jawo shi jiki na, haka yake, in ya samu game din da bai iya ba sai yace sai dai mutum yake yi masa shi kuma yana kalla. Ya kwanta a jikina na fara yi masa game din yana kalla, bayan wani lokaci sai naga wuyansa ya karye alamar yayi bacci, na gyara masa kwanciya nima na kwanta na cigaba da playing game din, a lokacin ne sako ya shigo wayar Umar through messenger.
Sakon ya yi showing briefly kafin ya dauke, na tsaya da abinda nake yi ina lissafin abinda ido na ya karanto min.
"Good morning my sweetheart"
But wannan ba shine problem dina da sakon ba. Problem dina shine sunan wadda ta turo sakon.
Maryam Abdulaziz Bello
Sunan Mammy ne wannan, haka take amfani da shi a facebook.
Me yasa Mammy zata kira Umar da sweetheart? Mammy fa? Niece dina? Yar yayata da muke uba daya da ita?
Yatsana ya tafi sama na jawo saman wayar. Na sake karanta sakon nata, sannan na murja idona dan in tabbatar ba gizo yake yi min ba. Tabbas ita din ce dan yanzu dana jawo sama har profile picture dinta na gani balle ince ko sunan ne yazo iri daya.
Na danna sakon nata sai ya kaini zuwa kan conversations din su.
Sakon jiya da daddare, shine ya tura mata
"Jin muryar ki kadai my dota ba zai isa ya saka ni inyi bacci mai dadi ba, ki turo min hoton ki please, na kasa bacci"
Ita kuma tayi replying
"In kana son ka ganni kazo gidan mu mana. But I guess matar ka ba zata barka ba"
"Soon my love. Very soon zan zo har sai yan gidan ku sun gaji dani sun aura min ke na taho da ke gidana"
"In gani a kasa. Kullum alƙawari har yanzu babu cikawa"
Na kasa cigaba da karantawa na dora wayar akan kirjina tare da rufe idona. Ina jin wani irin bacin rai da bana tunany na taba jin irinsa a lokacin. Ashe wani bacin ran yana gaba.
Na bude idona na sake daga screen din wayar, luckily wayar bata rufe ba dan ban san pin din wannan wayar ba. Sai nayi scrolling sama ina ta karanta hirarrakin su, soyayya ce suke yi sosai, mijina soyayya yake yi da yar sister dina. A lokacin na tabbatar ita ce yake waya da ita a gaba na. It has been her all along.
Sai kuma naga wani sakon da akayi five days ago.
"Ni dai tsoro nake ji Daddy. In Baba na ya sani wallahi kashe ni zai yi"
"Ta yaya zai sani? Ke zaki gaya masa?"
"A'a"
"To waye zai gaya masa? Ta yaya zai sani?"
"In wani ya ganmu fa? Ba aure na zaka yi ba? To kazo ayi magana mana"
"Ke ma ai kinsan dalilin da yasa har yanzu ban zo din ba. We have to be careful dan in maganar mu ta fito ba kowa ne zai fahimta ba. Kuma ni bana jin zan iya cigaba da hakura dake har lokacin. I can't help myself"
"Ni dai ina jin tsoro Daddy. Kar a kama mu fa?"
"In an kama mu din ma sai me? I will protect you with my life idan bukatar hakan ta zo. Ni dai dan Allah kar ki ce min a'a ba zan iya hakura ba komai yana iya faruwa da ni"
"To yanzu ya zamu yi kenan? Ni bansan me zan ce a gida a barni ba. Kuma wani zai iya ganina a motar ka a gaya wa Baba na"
"Yauwa. Ai ba zuwa zanyi in dauke ki ba. Gobe weekend ba kuna wuni a islamiyya ba? Idan kun tafi da siblings dinki sai kiyi wayo kar ki shiga, in sun wuce ki hau adaidaita zan turo miki address din gidan gonar baban abokina. It is safe there. Zan same ki a can. In kinje kawai ki ce da mai gadin Dr Umar ne ya turo ki zai bude miki ki shiga"
"Okay to zan gwada. Amma in naga za'a kamani zan fasa. Ina jin tsoro gaskiya"
"At least try. You have no idea what this will mean to me"
Idanuna suka kasa cigaba da karatun, kwakwalwa ta ta kasa cigaba da fahimtar abinda nake karantawa. Na mike zaune ina kallon Asad da yake kwance a jikina yana baccin sa hankalinsa a kwance, looking so much like his father.
Na zame shi daga jikina na kwantar da shi akan kujera dan gudun kar ya fadi saboda rawar da jikina yake yi. Sai kuma na zame kasan kujerar na kifa kaina a saman guiwowina ina fitar da wani numfashi mai zafi.
Babu abinda zuciyata bata yiwa Umar wishing ba, I wished daga baccin da yake zai zarce lahira, I wished dakin da yake ciki zai kama da wuta ya kone ya zama toka, I wished............I wished ban taba saninsa ba. I wished ba'a halicce ni ba ballantana inji abinda nake ji yanzu a zuciya ta.
Na sake daukan wayar, and I made screenshots of as much of their conversations as possible. Na dauko wayata a gefe na tura su through xender sannan na ajiye masa wayarsa a kusa da dansa. Wannan screenshots din sune nake saka ran zasu zamo shaidar da zata kawo min karshen alakakai din wannan auren.
But kafin nan I need to confirm something.
Na mike na shiga dakina na dauko hijab dina na saka sannan na fito na dauki wayata da key din motata na fita. A mota na zauna na shiga ta WhatsApp na tura masa screenshots din dana tura zuwa wayata with the caption "ka rubuta min takarda ta kafin in dawo"
Gidan Mama Sa'a na zarce, na tsaya a mota dan bana so in shiga a yanayin da nake sai na kira ta a waya. "Mama ina wuni ya yara. Dan Allah Mammy tana kusa? Dan turo min ita ina waje a mota zata dan rakani unguwa"
Kamar yadda nayi tsammani bata hana ba, jimawa kadan sai ga Mammy ta fito tana bina da kallo mamaki, na dauke kaina daga kallon ta trying so hard not to imagine her tare da Umar a gado. Ta shigo motar ta zauna ba tare da ta gaishe ni ba sai na dauko waya ta na bude hoto guda daya na nuna mata.
Farko ta dan fara bata fuska tana dubawa sai kumata bude ido a tsorace sannan tayi kokarin fita daga motar sai nayi locking kofar. Ta juyo tana kallona da ido a waje, nace "ina son kiyi duk abinda na saka ki idan kuma ba haka ba wallahi kinji na rantse wannan sakon sai na tura wa ubanki shi a yanzu. Ina da number dinsa ai"
Ta fara karkarwar jiki, na fahimci tana tsoron babanta sosai. Sai na kunna motar na bar layin sannan na kira wata kawata da mukayi school of nursing tare, yanzu tana aiki a asibitin Murtala Muhammad anan Kano "sister Aisha kina asibiti? Okay ganinan shigowa da wata alfarma please. Okay sai nazo"
Ban ko kalli inda Mammy take ba na kunna motar zuwa asibitin, muna packing na fita na bata umarnin ta biyo ni har office din su sister A'isha. Tana kallo na ta mike "sister Hauwa'u lafiya. Baki da lafiya ne?" Na zauna sannan nace mata "bana jin dadi sosai, amma ba wannan ne ya kawo ni ba"
Na nuna mata Mammy "wannan yar sister tace, ina so dan Allah ki duba min ita ki ga a bude take ko a rufe" Mammy ta fara ja da baya na kalle ta nace "zan ci ubanki wallahi. Kin san dai abinda nace zanyi miki ko?" Ta fara kuka "dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri, dan Allah" ban kula magiyar ta ba na saka tabi sister Aisha ciki, jimawa kadan suka fito tare, Mammy tana ta kuka.
A'isha ta kalle ni fuskar ta cike da alhini, "kiyi hakuri sister. Yarinyar nan a bude take, kamar ma ba'a jima da bude ta ba, the place is still healing" naji wani zafi beyond kwatance ya daki zuciyata, na dafe kirjina na sunkuyar da kaina, hopping babban abokina wato kuka zai zo min amma bai zo ba sai Mammy ce take ta kukan ta.
Sister Aisha ta dafa ni, "kiyi hakuri Hauwa'u. Yaran yanzu ne an haife su amma ba'a haifi halin su ba. Kuma tarbiyya yanzu sai a hankali................"
Ta cigaba da magana amma ni ba jinta nake yi ba. Na gado kai at last na kalle ta sannan nace "babu komai sister Aisha. Nagode sosai. Please let this be between you and me" ta gyada kai da sauri "insha Allah".
Sai na mike nace da Mammy "mu je" sister A'isha tace "zaki ita tuki kuwa Hauwa'u? You don't seem so well" na danyi mata murmushi nace "zan iya. Nagode."
Sai muka fito muka koma motar. A raina ina hoping zamuyi accident a hanya ko Mammy bata mutu ba ni in mutu, maybe in na mutu zuciyata zata huta.
Na dauki hanyar gidan Umar a guje, ina fatan kafin inje gidan in tarar ya rubuta min takarda ta dan ko bai rubuta ba yau a gidan