Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
ba zaki kara tsayawa ki saurari wannan mutumin mai suna Bashir ba. Na biyu shine duk wanda zaki aura ba zaki bar shi yayi treating din ki bad ba. Promise me you will be happy, ba zaki kuma daukan abinda kika dauka a gida na ba"
Na goge hawayen idona sannan na gyada kaina ina kirkirar murmushi. "Jiddan da ka sani a da ba ita bace a yanzu" yayi murmushin shima sannan da dago hannunsa ya gogi hawayen fuskata, making me feel the high temperature of his skin.
"Wannan Jiddan is acting more like Hauwa'u. Except for the tears"
Na dan matsa da kujera ta baya, forcing his hand away from my face. Sannan na mike ina kallon sa nace "tare muka zo da Yasmin da Asad. Suna waje. In shigo da su su ganka?
Ya gyada kansa bai ce komai ba, sai na juya da sauri zan fita sai ya kira sunana "Jidda" na juyo ina kallon sa yace "read your messages" ban ce komai ba na fita ina jin idonsa a kaina.
A waje na tarar da Asad da Yasmin har yanzu suna tare da Mama suna yi mata zance, da kuma Farhan a gefe a zaune itama tana kallon kofar dakin da na fito. Sai a lokacin na tuna tare muka shiga da ita ban kuma san sanda ta fito ba. Na kira yaran na durkusa na rike hannayensu nace "Daddy ne a wannan dakin bashi da lafiya" naga kyawawan fuskokin su sun bayyana alamar tashin hankali da damuwa a ciki. Na cigaba da magana. "Zaku shiga yanzu ku je ku ganshi, amma ban da surutu, gaishe shi kawai zakuyi ku tambaye shi ya jiki, banda labarin makaranta da kuma labarin TV game" na karasa ina kallon Asad, ya gyada kansa da sauri yana hura hanci irin na babansa.
Sai na mike sannan na ja hannunsu zuwa kofar dakin nace su shiga, na tsaya a gurin ina kallon su har suka je inda yake sai ya mika musu hannayensa kowa ya kama daya sannan ya jasu zuwa jikinsa. Na juya na bar gurin da sauri sannan na fita daga asibitin da sauri, sai da na bude mota na shiga sannan na tuna da cewa banyi wa Mama sallama ba.
Na kwantar da kaina a jikin kujerar motar tare da rufe idona. Ni kaina ban san tunanin me nake yi ba ban kuma san dadewar da nayi a haka ba sai jin motsin su Farhan nayi tare da yaran da na lura duk suna cikin damuwa. Farhan ta bude musu bayan motar suka shiga suka zauna sannan ta zagayo gurina tace "in ba zaki iya driving din ba ki bani inyi"
Itama da iya mota yanzu dan tana hawa ta mijinta, yanzu ma saboda cikinta ya tsufa ne shi yasa bata taho da motar ba.
Na fito na bar mata seat din driver na koma daya side din na zauna ita kuma ta tayar da motar muka dauki hanya. Har muka je gida babu wanda yayi magana. Sai da muka je yaran suka shiga ciki sannan tace min " Allah ya bashi lafiya" nace "ameen" sai tace "amma fa ni sai nake ganin ba Umar din da bane ba, duk da bai fada ba amma gani nake yi kamar ya daina halinsa" .
Na dago kai na kalle ta nayi murmushi nace "Farhan kenan. Farhan ba ki san Umar din da na sani ba. Umar zai iya yin kuka ya yi rantsuwa ya kuma yi karya a lokaci daya. Ban taba ganin mutumin da ya iya karya kamar sa ba, kamar yadda ban taba ganin mutumin da ya iya pretending kamar sa ba"
Tayi ajjiyar zuciya. "To Allah ya zaba abinda yafi alkhairi. Ki dai yi ta addu'ar Allah ya zaba abinda yafi alkhairi. Kar ki dage wai lallai ba zaki koma ba" na harare ta ina jin haushinta "yanzu ke wa kika ji yayi maganar komawa ne ma, komawa ta gidan Umar is not an option, bana jin akwai abinda zai saka Abba ya mayar da ni ko da nace ina son komawa ballantana ma bana so. Bana so kuma in bawa Umar false hope shi yasa na gaya masa gaskiya"
Muka rufe motar muka shiga gida, sai da Umma ta tambaye mu zancen kayan babyn sannan na tuna ashe kasuwa zan raka Farhan, nace tazo mu koma amma sai tace in bar shi duk sanda na samu dama naje can gidan ta mu je.
Ban kuma komawa duba Umar ba, sai dai kwana uku bayan nan na dawo daga gurin aiki kenan sai na tarar da Mama a gidan, tana dakin Umma tare da su Yasmin. Na durkusa na gaishe ta tana ta kallo na fuskar ta cike da sha'awa sai kuma na tambayeta mai jiki. Tace "da sauki. Ina shirin ma mayar da shi Dubai gurin likitan da ya duba shi wancan karon" na gyada kai. "Allah ya bashi lafiya" tace "ameen. Dama magana nazo muyi Jidda"
Sai na kalli Umma da ta bata rai sannan na kalli su Yasmin nace su tafi dakina su dauki books din su suyi homework. Sai da suka tafi sannan tace
"watakila jikinki ya baki maganar da zanyi miki tun da kika ganni, watakila kuma zaki yi tunanin ban ma chanchanci in zo miki da maganar ba, in ma hakan kika yi tunani ina ganin kina da gaskiya, amma a matsayina na uwa dole in danne duk wani nauyin ki da nake ji inzo inyi miki maganar, in gwada sa'a ta watakila ko za'a dace"
"Jidda bayan barinki gidan Umar, babu abinda ya biyo bayan hakan irin tarin masifu kala kala da suka ringa sauko wa Umar, suka ringa sauko mana gabakidaya, wadansu na san kin sani wadansu kuma baki sani ba, amma ni yau ina sanar dake cewa duk duniya babu wanda ya yarda da abinda Umar ya aikata sama da ni. Ko ke da yake gayawa da bakin sa idan ya aikata laifi baki da irin tabbacin da ni nake da shi. Amma kuma wani tabbacin da nake da shi shine na cewa ya daina, Jidda Umar ya daina halinsa bayan da halin nasa ya tarwatsa duk wani abu na farin ciki a cikin rayuwar sa"
"Jidda na san kin so Umar a baya, wannan son da kika yi masa yi ne abinda ya bani kwarin gwuiwar da nazo gurin ki a yanzu nake gaya miki halin da yake ciki. Umar bashi da komai yanzu bashi da kowa a duniya, ba ma shi da wanda zai zauna ya gaya wa abinda yake ransa kamar yadda yake gaya miki a da......"
Na katse ta ina girgiza kai "kar ki ce haka Mama. Umar yana da kowa kuma yana da komai. Yana da uwa yana da uba yana da siblings yana da abokai, yana da babban amininsa Bashir, dan na rabu da shi babu abinda zai ragu daga gare shi"
Tace "aiya, tabbas ta hausawa da suka ce rashin sani kukumi ne, a yanzu bana jin akwai wata halitta da Umar ya tsana a duniya sama da wanda kika kira da amininsa. Aminin daya taimaka gurin tarwatsewar zuriar mu. Iyayensa kuma da kike magana akai ni dai a yanzu ba zan iya tuna ranar da Umar ya zauna yayi min magana ta minti biyu ba, haka zalika yan uwan shi. Wannan bound din da kika sani a da yanzu ya gitsitstsire, yanzu babu komai sai tarin kaico da nadama"
"Jidda Umar yana nan rai a hannun Allah, bayan addu'a da kulawar likitoci babban abinda Umar yake bukata shine soyayya, kulawa, da tarairaya musamman irin na mace, abinda Umar yake bukata shine ya samu kwarin gwiwa da assurance cewa ana son shi ana bukatar sa a duniya, a bashi hope. Abubuwan da ni da babansa ba zamu iya ba. Abubuwan da babu wacce zata iya sai ke......kamar yadda nake ganin babu wacce zata iya daukan abinda kika dauka a gidan Umar haka yanzu ma nake ganin babu wadda zata iya maye gurbin ki sai ke din dai..."
Umma tayi sauri tace "ita ma ba zata koma gurbin ba. Allah ya bashi lafiya amma ba zata koma ba"
Mama tace "haba Aysha, ke fa uwa ce kuma kinsan yadda uwa take ji akan danta komai lalacewar sa kuwa, ya kamata ace kin fahimta"
Umma tace "tabbas ni uwa ce Hajiya Maryam kuma na san abinda uwa take ji akan danta, wannan kuma shi yasa nake kokarin kare tawa yar daga fadawa halaka"
Mama ta sauke idonta kasa, alamu yana nuna wa kamar hawaye ne a idonta tace "ya daina. Wallahi ya daina"
Umma tace "Allah ne masani amma mu bamu sani ba, abinda muka sani kuwa da shi muke amfani"
Sai Mama ta gyada kanta tare da gyaran murya tace "haka ne. Babu komai. Na gode da lokacin ku da kuka bani"
Ta mike zata tafi sai na tashi da niyyar rakata amma umma ta harare ni dole na koma na zauna, ina kallo ta tafi ba tare da ko sallama tayi da jikokin ta ba.
Banji dadin yadda Umma tayi wa Mama ba amma na fahimci hakan shine dai dai, dan ta fahimci cewa ba komai ne da danta yake so zata iya samar masa ba, ba kuma shi kadai ne ɗa a duniya ba muma duk yaya ne kuma duk iyayen mu suna son mu.
Da magrib muna tsakar gida a zaune sai ga dan aike nan wai ana sallama da Jidda, nace yaje ya tambayo waye dan ni banyi da kowa zai zo waje na ba, sai gashi ya dawo yace wai yace in na fita zan gani. Naji haushin maganar sai nace yayi tafiyarsa kawai. A raina nace ko waye in kafarsa ta kumbura saboda tsaiwa zai hakura ya tafi dan kansa. Sai kuma Umma ta kama yi min fada. "Wulakanci dai bashi da dadi. In ma ba zaki kula mutum ba gwara ki je ki sallame shi kawai"
Na tashi na saka hijab dina na fita amma tun a bakin kofa na gane waye, doctor Bashir, yana tsaye a jikin motarsa da wayarsa a hannunsa yana daddannawa.
Ban karasa ba sai na koma cikin gida na kuwa yi sa'a Umma ta hau kai wa Abba abinci sai na dauki waya ta na kira yaya Abbah.
"Yaya dan Allah kana kusa?" Yace "eh yanzu muke rufe shago. Wani abun ne?" Nace "dan Allah wata kwangila nake so na baka. Yara nake so ka daukar min haya as much as you can get su samo duwatsu as many as they can get akwai wani a kofar gidan nan a jikin mota suyi masa ruwan duwatsu daga shi har motar sa"
Yayi dariya "waye kuwa wannan da za'a yi masa wannan hukuncin?" Nace "believe me yayi deserving. In da kasan waye ma da ba zaka tsaya tambaya ta ba. Amma zan ba ka labarin sa in ka shigo"
Ai kuwa yan kwangila ta sunyi aikin su, dan daga inda nake ina jiyo karar fashewar glasses, am sure wadansu duwatsun sun samu goshinsa. Da kyar ya samu ya hau motar sa ya fice daga unguwar a guje ana binsa da ihu da ruwan duwatsu. Yaya Abbah yana shigowa Abba ya leko daga sama yana tambayar hayaniyar da yake ji a waje sai yace "wani ne yara suke yiwa ihu, ina jin barawo ne"
Sai daga baya na bashi labarin ko waye da kuma bibiyata da yake yi. Yace "da kin gaya min ai da ba da yara zan hada shi ba, da yan daba zan hada shi su dan rage masa tsaho kadan, ko kafa daya suka cire masa ai sun rage mana iri"
Nayi dariya kawai nace "barshi da halinsa, Allah ne zai kama shi a yadda yaso a kuma lokacin da yaso"
Sai da naje kwanciya sai na samu kaina da tunanin abinda ya faru tsakani na da Bashir, and I thought about yadda mata da yawa musamman zawarawa suke complain da cewa maza suna zuwa musu da maganganun banza. Sai naga ni so far ban samu wannan matsalar ba, for over two years da nake gida babu wanda yazo min da irin wannan maganar, me yasa?
Then I realized sai bango ya tsage kadangare yake samun hanyar shiga. Na fahimci abinda yake saka mata zawarawa da yawa fadawa wannan halin shine kwadayi da rashin dogaro da kai. Mace ta saba a gidan mijinta shi yake mata komai ita bata iya juya biyar ta koma goma, ranar da duk aka ce auren ya mutu ko kuma mijin ya mutu ta dawo gida ga yara ga rashin abinyi, wasu iyayen kuwa hatta sabulun wanka ba zasu bawa yayansu zawarawa ba. Wannan ne yake sakawa ta fara yaki halak yaki haram har ta zamanto kamar karuwar gida. Solution akan wannan shine mata mu kama sana'a, bamu san abinda gobe zata zo dashi ba
Da kuma rashin kamun kai. In kika yi shigar ki ta mutunci kika kuma kame kanki kika sauke idonki kasa dan iska tabbas zaiyi shayin yi miki magana, sai dai rikakkun yan iska irin su Bashir, su kuma irin abinda nayi wa Bashir shine maganin su.
Kwana biyu bayan nan ina off, ina kwance a dakina ina bacci sai Yasmin tazo tana tashina wai in zo inji Abba yana sitting room. Na mike zaune ina salati tare da dafe kaina da yake yi min ciwo, ina tuno mafarkin da nake yi a cikin bacci na, nayi tsaki sannan na shiga toilet na wanke fuskata na fito na tarar har lokacin Yasmin tana tsaye a tsakiyar dakin tana kallona tace "Abban fa shi da Baba ne a sitting room din" na yar da towel din hannuna ina kallon yarinyar nace "wanne Baban? Baban gidan Mama?" Tace "eh shi. Da wani ma"
Naji jikina yayi sanyi, na saka hijab dina na fita daga dakin ƙafafuwana kamar an datsa min su saboda sagewar da kafar tayi. Na shiga na tarar da su a zazzaune da Abba da Baba da Baffa Halilu. Na zauna kusa da Abba a kasa saboda ina jin idan ina kusa da shi zan kara samun kuzari da karfin gwuiwa.
Bayan na gaishe su ne Baffa Halilu yace "Hauwa'u mune muka zo muka nemi alfarmar ganin ki a gurin mahaifin ki kuma Allah ya dora mu akan sa ya bamu damar hakan duk da shi kansa bai san abinda ya kawo mu din ba, amma dai kamar yadda hausawa suke cewa in kaga kare yana shanshana takalmi to dauka zaiyi, dan haka nasan duk da bamu fadi ba already a zuciyoyin ku kunsan abinda ya kawo mu. Ni dai a nawa bangaren zance waccan damar da na roka ki bani a wadancan shekarun kika ƙi ita na sake dawowa zan sake roƙa wannan karon ma. Kamar yadda na fada wancan karon, wannan ma haka ne, ba Umar za'a bawa dama ba ni za'a bawa dama. Ni na dauke responsibility na komai. Ina rokon ki Jidda ki daure ki koma gidan Umar"
Duk suka yi shiru daga alama ni suke jira inyi magana amma nima sai naja baki na nayi shiru. Ina jin nauyin Baffa, ba zan iya watsa masa kasa a ido for the second time ba amma kuma ba zan iya amincewa ba, dan bana so. Nayi tunanin Abba zai shigar min kamar yadda yayi wancan karon amma sai naga shima ya ja bakin sa yayi shiru. Na lura duk jikinsa yayi wani sanyi tun sanda yaje duba Umar.
Jin shirun yayi yawa ne ya saka baffan ya sake magana "kinyi shiru Jidda, ko ba zaki yi min wannan alfarmar ba?" Na sake yin shiru kaina a kasa. Sai ya mike tsaye "na gane amsar ki, na kuma karba tunda babu wanda zai takura miki akan hakan, sai dai ina so kiyi tunani sosai kuma kiyi addu'a. In kin chanja shawara bayan haka sai ki gaya wa mahaifin ki, mu kuma zamuyi farin ciki idan hakan ta kasance"
Sai daya fita sannan Baba yayi magana yace "Hauwa'u. Idan da ace Umar din da ne kike gudu da dukkan mu babu wanda ba zai goya miki baya ba akan hakan. Amma ina so ki sani kamar yadda na tabbatar cewa zan mutu haka na tabbatar cewa Umar ya daina halinsa, saboda tsahon shekara biyun nan babu abinda nake yi bayan bibiyar lamuransa dan in fanshe laifina na baya, amma ko sai daya banga ya hau kan waccan hanyar da ya bari. Na kuma sani cewa Umar zai iya samun wata matar kamar yadda ke ma zaki iya samun wani mijin, amma ni nafi son ke din ki koma saboda Allah ne ya shirya Umar amma ke ce sanadiyyar shiryuwar sa, me yasa ba zaki zamanto kuma wadda zata ji dadin shiryuwar ta sa ba? Kamar yadda yaya Halilu ya fada, idan kin amince zamu ji dadi"
Sai ya tashi shima ya fita.
Har lokacin ban dago kaina ba, na jira inji comment din Abba amma sai kawai yace min in tashi in shiga ciki.
Dakina na koma na kwanta telling myself cewa bacci zan koma amma ni kaina nasan yaudarar kaina nake yi. Na gama juyi na na tashi nayi wanka na shiga dakin Umma na kunna tv, ina nan har dare, har yaya Abbah yazo ya karaci hirarsa shi kadai ban ka shi ba ya hakura ya tafi. Na duba littafan yara sannan na shirya su suka kwanta nima na kwanta sai na jawo wayata ina tuna abinda Umar ya ce min ranar da naje duba shi, "read your messages"
Na nemo number din sa da take can kasan chats dina naga messages wajen 50, na bude na koma tun daga farkon su na fara karantawa har zuwa na karshe. Labari ne ya bani, kamar mai rubuta littafi, duk da dai na fahimci labaran nasa ba'a jere suke ba amma sun fahimtar dani sakon da yake son sanar da ni. labarin duk abinda ya faru da shi tun daga ranar da na bar gidan sa har zuwa ranar da ya rubuta message na karshe wanda shine ranar da aka kwantar da shi a asibiti.
Yanzu na fahimci abinda ya faru tsakanin sa da Bashir, na fahimci abinda Mama take nufi a maganganun ta, na fahimci abinda Baba yake nufi a nasa maganganun. And I decided zanyi istikhara akan maganar komawa gidan Umar ko