Chapter 28 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 106

81K to 84K   out of 316K words

allura ka hana ni yi akan lokaci, alhaki a kanka kuma ban yafe ba"

Bai ce komai ba na shiga toilet nayi alwala na fito na tayar da sallah a zaune dan yadda nake jin kaina yana juyawa ba zan iya yi a tsaye ba. Nayi magrib nayi isha sai da na idar na fara addu'a nazodai dai gabar da nake yi wa Umar addu'a kullum sai naji n kasa, naji bansan me zan roka a gameda shi ba, shin Allah ya raba ni da shi zance ko kuma ya cire min sonsa? Ko kuma addu'ar zanyi Allah ya daidaita mu.

Naji messages din Zuwaira suna replaying a kaina kamar yanzu ne take aiko min dasu, sun saukar da wani irin daci daci yaji yaji a cikin zuciyata wanda ya kawo hawaye cikin ido na, sai na rufe fuskata da hijab dina nafara rusa kuka kamar Allah ne ya aiko ni inyi shi. Duk kukan da banyi ba jiya shi na hada nake yi yanzu. Bai rarrashe ni ba har sai da nayi ya ishe ni sannan na goge ido na na dafa gado na mike na tafi bakin kofa.

Ina murdawa naji ta a rufe, na juyo cikin dacin rai ina kallon sa "open this door" ya bini da kallo da jajayen idanuwan sa da suka yi kamar shima kukan yayi, na sake maimaita wa "ka bude min kofa nace" ya mike tsaye yana girgiza kansa. "Bazan iya barin ki ki fita ba Jidda har sai munyi magana mun fahimci juna. Kiyi hakuri ki dawo ciki"

Na saki hannun kofar sannan na dawo na wuce shi na koma kan gado na kwantana ja bargo na rufe har kaina sannan na cigaba da kuka na, sai dai ban dade ina yi ba bacci ya dauke ni tunda har lokacin akwai sauran allurar da yayi min a tare dani.

Ban kuma farkawa ba sai bayan assuba, har gari ya fara haske. Na tashi ina jin kaina ya bude sosai, jikina da zuciyata kuma sunyi nauyi. Yana zaune akan sallaya da Alqur'ani a gabansa yana karanta wa, da alama anan ta kwana dan banga alamar an kwanta a kusa da ni ba, nayi shiru ina tunanin last time da naga yayi karatun Alkur'ani.

Na sauko na shiga toilet nayi alwala na dawo na tayar da sallar asuba, ina idarwa na danyi adduoi na sannan na fara azkar wadanda narike a kaina dan dama a wayata nake karantowa kullum wanda Aunty Surayya take turo mana a group din Maman Maama novels, yanzu kuma wayar tana hannunsa kuma bani da niyyar yi masa magana ballantana in tambaye shi inda take.

Ina cikin yi naji ya katse karatun ya tashi ya mayar da Alqur'anin inda yake sannan ya bude kofa ya fita sannan naji ta rufe ta waje. Na ja tsaki na harari kofar a raina ina cewa dole dai zai bude ni kuma dole in tafi gidan mu.

Bai jima sosai ba ya kuma dawowa, ya sake rufe kofar ya saka key din a aljihun sa sannan yazo gabana ya ajiye min tray din hannunsa wanda yake dauke da cup din tea da kuma plate din da naga soyayyen kwai a ciki. Sai kuma ya zauna kusa dani, kafadar sa a jikin tawa mun jingina a jikin gado.

"Ki ci abinci dan Allah....." "ba zan ci ba" "kin san dai ba ke kadai bace ba ko? Little Jidda tana bukatar abincin ita, Idan ke kina fushi da Umar little Jidda bata yi saboda ke zaki iya chanja Umar a duk lokacin da kika so ita kuma ba zata iya ba"

"Ba zan ci ba" na sake maimaita wa. Yayi ajjiyar zuciya "okay amma zaki saurare ni ko?" Nace "kunne ne yake ji ai, kayi ta magana zasu ji ka" yace "zanyi kokarin shigar da magana ta zuwa kunnen, sannan inyi fatan zata wuce har cikin zuciyar Jidda kuma jiddan zata bawa kwakwalwar ta damar duba maganar da yi mata kyakykyawar fahimta"

"Da farko dai zan baki hakuri akan laifin da nayi miki. Laifin da nayi miki kuwa shine nayi miki karya nace ban san Zuzu ba alhalin na santa din. Sai dai ina so ki sani cewa nayi hakan ne dan gudun bacin ranki. Dan nasan in dai nace na santa sai kinja maganar har ta kaiki ga sanin abinda zai bata miki rai. Na dauka in nace ban santa ba shikenan zamu rufe babinta har abada"

Na juyo ina kallon sa, hawaye yana bin fuska ta "for how many years ka san ta?" Yace "getting to eight, kamar yadda ta gaya miki" na gyada kai. Ya fara fadar gaskiya at last.

Sai ya cigaba

"But wannan shi kadai ne gaskiya a cikin dukkan maganganun data gaya miki" na dago kai da sauri, there we go again, karyar ta dawo.

Ya gyada kai yana kokarin nuna min iyakacin gaskiyar sa kenan. Nace "kana nufin bata zauna a gidan nan ba? Baka ajiye ta a gidan nan har na tsahon shekara guda da watanni ba?" Ya dafe kai "shine maganar da nasan in nayi miki admitting na santa tun a wancan lokacin sai kin binciko kuma ba lallai bane ki fahimci yadda maganar take ba. Jidda wallahi ba irin zaman da ta gaya miki munyi bane ba, ba irin zaman da kike tunani bane ba"

Na fara girgiza kaina, "you are not ready to talk, tunda ba zaka gaya min gaskiya ba" ya kama fuskata ya juyo da ita ina kallon sa. "Look at me Jidda, ta zauna a gidan nan amma wallahi ba irin zaman da kike tunani bane ba. Budurwar Mahmud ce, suna tare tun muna buk sai ta samu matsala da iyayen ta akan lalacewar tarbiyyar ta suka kore ta, ni kuma lokacin Baba ya siya min wannan gidan babu komai a cikinsa sai ya roke ni in bata aro zata zauna ta karasa karatu anan tunda yana kusa da makaranta, shine na basu, suka zauna ita da friends dinta suna zuwa school daga nan, har lokacin da zan tafi India nace lallai su tashi dan zan bar key a gida kuma in Baba da Mama suka san da mata a gidan nan ba zasu fahimce ni ba, zasu yi min irin fahimtar da kika yi min yanzu ne"

"A lokacin ne take gaya min wai ita dama tana so na ne, kuma zata iya rabuwa da Mahmud indai har zan karbi soyayyar ta kuma zamuyi aure. Na nuna mata ni ba zan ci amanar friend dina ba, besides kuma ni tarbiyyar ta bata yi min a matsayin matar da zan aura ba."

"She kept stalking me through social media, sun bar gidan nawa amma taki rabuwa dani kullum sakon yau da ban na gobe daban ni kuma ban taba nuna mata na yarda ina son ta din ba amma ba wai ina wulakanta ta bane ba, a gurina we are just friends."

"Ina dawowa sai ta cigaba da yi min zancen aure, wai ta gaji da zama babu aure and other stuffs, kuma wai ita ni take so ta aura ba Mahmud ba, shi kuma dana gwada yi masa maganar aurenta sai ya nuna min shi ba zai iya aurenta ba cos sun riga sun lalace a waje. Wannan yasa nima kuma na kara yin baya da ita, friendship din ma na katse shi na daina replying messages din ta. But still suna tare da Mahmud din."

"Ya bude Saloon yanzu anan kan zoo road, akwai bangaren mata akwai kuma bangaren maza to sai ya bata aiki a gurin, tana yin gyaran jiki na mata, kwalliya and other girls stuff, akwai kuma inda ake aski na maza da sauran al'amuran maza. To anan ne kadai muke haduwa Jidda"

"Bayan bikin mu she complained cewa ban gaya mata zanyi aure ba ban gayyace taba amma zata zo har gida ta ga amarya ta ta kuma ga wadda ta kwace mata ni. We joked  about it na dauka da wasa take yi dan bana son mai irin tarbiyyar ta anywhere near my family amma sai tazo din. Bana son kiyi finding out ta taba zama a gidan nan shi yasa nace miki ban santa ba"

"Bayan tazo din nayi mata warning cewa in ta kuma zuwa zan hada ta da police da gaske. Sannan kuma na gaya wa shi Mahmud halin da muke ciki ni da ita da kuma abinda tayi miki nace ya ja mata kunne kar ta sake sai ya nuna min shima tuni ya sallama wa duniya ita, yanzu kawai a matsayin employee take a gurinsa babu wasu strings attached a tsakanin su, kum yayi warning dina cewa she is desperately looking for a husband, aure take so tayi ta kowacce hanya dan haka in zama careful"

"To jiyan na gaji a office, ga bacci da yake idona bana jin zan iya dogon driving shine na tsaya a gurinsa na kwanta a reception dinsa nayi bacci sannan na saka waya ta a charge a kusa dani. Wannan shine kawai abinda na sani. Ina farkawa na dauki wayata nayi masa sallama na fito na taho nan"

"Jidda wallahi wallahi wannan shine iyakacin gaskiyar magana. Na kira shi jiya da daddare na tambayeshi kuma ya tabbatar min tana gurin a lokacin da nake bacci sai dai yace bai ga sanda ta dauki waya ta ba"

"Yes, ina zama muyi magana da ita idan na shiga gurin, amma wallahi Jidda ban taba yi mata maganar ki ba ballantana maganar Abba ko wani source of income dinsa"

Ya karasa kamar zai fashe da kuka.

"Na hadiye yawu nace "a ina ta sani kenan? Ko wahayi akayi mata?"

Ya rike hannayena Yace "Jidda ke yarinya ce, so innocent, kuma background dinki ba irin na wannan rayuwar bane ba. Matar nan rikakkiyar yar duniya ce, ta san kan bariki fiye da sanin ki dan shi kansa Mahmud yanzu tafi karfinsa. She have so many sources na samun duk abinda take so including labari, zata iya sakawa a bincika mata labari a kanki and she used that to hurt you kawai dan tasan zaki yadda da abinda tace miki na cewa nine na gaya mata, tasan you are naive ba zaki fahimci zata iya bincike akan ki ba. Ta san jin nina gaya mata zai bata miki rai sosai. Wannan shi yasa ta gaya miki haka amma Jidda wallahi wallahi sunan ki ban taba furtawa a gaban taba da sunan ina bata labarin ki sai dai ko in muna magana da Mahmud ita kuma tana gurin sannan zata ji sunan ki a baki na"

"Kuma maganar wai na gaya mata bana sonki, wai sha'awar ki nake ko something like that, Jidda ba ke ba duk wanda ya sanni tabbas in yaji maganar nan ba zai yadda ba saboda soyayya ta a gare ki ba boyayyiya bace ba. Tun da ta fadi haka ya kamata ki gane cewa ita babbar makaryaciya ce. Maganar na aure ki dan na kasa samun ki a waje ai ke ya kamata ki bata kyakykyawar amsa a nan gurin tunda ke kece shaidata cewa ban taba neman ki a waje ba. Jidda ko hannu na ban taba kaiwa jikin ki ba har sai da kika zama tawa duk kuwa da cewa muna yawan kasancewa mu biyu, kuma ina yawan daukar ki a mota ta mu biyu, in da ina son wannan daga gare ki ke kin san da na samu, da nayi amfani da soyayyar da nasan kina yi min da kuma yarintar ki na samu abinda nake so na wuce gurin."

"Misali da ace na neme ki ne sai kika ki kika ce sai na aure ki, sannan sai na aure ki din, to tana fadar nace haka sai ki yarda"

"Kuma da ace bana sonki Jidda da babu yadda zan yi in bari ki samu cikin nan, amma Allah ne shaidata kuma ke ce shaidata ta irin yadda nake son wannan cikin.

"Jidda bana neman mata. Kafin ki Umar bai taba sanin wata mace da sunan mace ba, bayan ki kuma Umar bashi da bukatar wata mace daban bayan ke saboda ya samu duk abinda yake nema a gurin mace a gurin ki"

"Ke ce rayuwa ta Jidda. Ke kadai kin ishe ni rayuwa"

"Irin yadda nake nacinki kadai Jidda ya isa ace ya tabbatar miki da cewa bana neman mata"

"Da ace zan iya dawo da jiya baya da na chanja dukkan abinda suka faru har matar nan ta bata miki rai haka. Da ace zan iya dawo da baya da na koma tun ranar da ta fara ganina na shirya mata rashin mutuncin da ko hanya ba zata yadda mu hada ba"

"Wannan shine gaskiyar magana Jidda. Idan kuma har yanzu baki yarda ba zan iya daukan ki a yanzu mu tafi shagon Mahmud din in nuna miki gurin kuma in hada ki dashi da sauran ma'aikatan gurin su tabbatar miki da cewa anan nayi bacci jiya da yamma. Kuma su tabbatar miki da cewa tana gurin a lokacin".

*wannan littafin na amana ne, idan baki siya ba dan Allah kar ki karanta, idan kuma kin siya dan Allah kar kiyi sharing, idan kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*


*Yasmin*

Not Edited

Tun daya fara magana ban ce komai ba sai da naji yayi shiru sannan na zare hannuna daga cikin nasa na dora shi akan cikina sannan na rufe idona ina sauraren babyn da tun dana tashi banji ta motsa ba, maybe yunwa take ji ko kuma allurar baccin ce ba ta sake ta ba ita har yanzu.

Naji ya dora nasa hannun a saman nawa, akan cikin, sannan kuma sai ya saka yatsunsa a cikin nawa ya lankwashe su together sai ya sunkuya yayi kissing cikin. Na zare hannuna sannan na daga fuskar sa daga kan cikina na muskuta gefe, I needed space to think, to analyze things and I can't think with him looking at me, touching and kissing me like that.

"Zan ci abincin" nace, yayi saurin dauko cup din tea ya miko min "ungo, ki shanye wannan sai in karo miki wani" na karba na kurba sai nabata rai na mika masa nace "ya huce" ya karba ya kurba sai ya mike "bara in dafa miki wani" ya tashi ya fita da tea din a hannunsa.

Nayi ajjiyar zuciya tare da jingina kaina a jikin gado. Anya kuwa akwai mijin da yake kula da matarsa kamar yadda Umar yake kula da ni? Ba za'a rasa ba amma they are very few. And that makes maganganun Zuwaira so painful. I mean idan miji dama baya baka kulawa da nuna soyayya ba zaka damu sosai idan yaci amanar ka ba kamar wanda yake mayar da dukkan bukatunka his first priority.

Nayi bitar maganganun sa sannan nayi bitar maganganun Zuwaira. Na kuma dora su a scale din truth na auna su. Gabakidaya sunyi contradicting juna. Sai na fahimci ina da options guda biyu. It is either in yarda da maganar sa shi mijina kuma mutumin da nake tsananin so, mutumin da alkhairan sa a gare ni basa misaltuwa in karyata Zuwaira ko kuma in yarda da Zuwaira, matar da ban sani ba ban taba gani ba sai sau daya kuma nake da yakinin bata nufi na da alkhairi in karyata mijina.

Sai kuma nayi realising ina da third option. Zata iya yiyuwa dukkanin su sun fada min some percentage na gaskiya sun cike da karya, third option dina shine in ware gaskiyar daga cikin karyar a kowacce magana.

Sai na fara warwarewa......

Farko na dauko zancen baya so na da Zuwaira ta ce ya gaya mata, a take nayi cancelling cewa karya take yi, a idon Umar kadai nake ganin soyayya ta bama sai ya furta min ba amma duk da haka kusan kullum sai ya furta din ko da kuwa a gaban Mama ne.

Zancen ya aureni saboda yana sha'awa ta ma nayi cancelling mata shi, dan hujjojin da ya bani sun gamsar da ni kuma na tabbatar a jiyan ma da naji na yarda da ita bacin rai ne da kishi ya saka naji haka.

Zancen maganganu game da ni da Abba ma naji na maka mata wrong, anya Umar zai iya aikata min haka kuwa? Duk da son da nasan yana yi min. Nafi yarda da maganar shi ta cewa bincike tayi akan maganar ta ta cewa shi ya gaya mata

Sai zancen zaman da tayi a gidan sa. Kowane a cikin su da abinda ya fada game da hakan. Kuma version din kowanne zai iya zama gaskiya but the mere thought of Umar keeping a lady a gidan sa for his pleasure ya saka naji tamkar zuciyata zata tarwatse ta fado kan cinyata. Anya kuwa? The only way to find out the truth about that shine idan nayi bincike. Bincike kuma irin wannan yana nufin sanarwa da mutane abinda yake faruwa a gidan aure na. In ma kuma zanyi binciken ta ina zan fara? Abokan sa ko kuma kawayenta? A cikin su waye zai gaya min gaskiya? In da har abinda ta fada gaskiya ne abokan sa ba zasu fada min gaskiya ba dan zasu so su kare abokin su.

Sai maganar abinda ya faru jiya. Ita tace min yana gidan ta akwance akan kirjinta shi kuma yace min yana reception din saloon din abokin sa inda ita kuma take a matsayin maaikaciya. Waye mai gaskiya a cikin su? Shin in shi offer dinsa ne in je gurin inyi tambaya? In ce me? In kuma na sameta a gurin fa? In nuna mata tayi nasarar da sa zargin mijina a zuciya ta?

Na girgiza kai. I won't give her that satisfaction saboda a analysis din da nayi naji zuciyata tafi yarda da maganganun Umar akan nata and I think any wife in my shoe abinda zata yi kenan.

Sai dai wata tambaya data tsaya min a raina ita ce, idan da gaske babu wani abu a tsakanin tada Umar, idan dagaske budurwar Mahmud ce ba ta sa ba, idan da gaske babu wani abun daya taba shiga tsakanin su menene ribar da zata samu idan ta raba mu? Me yasa zata yi going this far wajen ganin ta raba mu? Tunda ko mun rabu ba auren ta zaiyi ba tunda babu komai a tsakanin su. Right?

Ya bude kofa ya shigo da wani tray din a hannunsa. Ya zauna a inda ya

28 / 106