Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
can din ba" nayi dariya "to ko kadunan zamu kai ki ne?" Tace "kinga kuwa yaya Hudallah ta kawo min wani Alhaji dan kaduna" muka yi dariyar yaya Hudallah da alhazawan da take kawo wa Farhan.
Ranar wuni nayi sur a gida. Dan sai wajan karfe tara na dare sannan yazo ya dauka ta sai kuma a lokacin ya shigo ya gaishe da Umma da Hajiya. Na hau sama na yiwa Abba sallama sai yace in na sauko in ce wa Amira ta shirya mu tafi tare tunda tana hutu. Na sauko na gaya wa Umma mukayi ta mamakin halin Abba idan da yana so in tafi da Amira ai da sai ya fada tun wuri ta shirya ba wai sai da muka zo tafiya ba.
Amma ko babu komai naji dadi dan zata taimak min sosai da ayyukan gida...
Bayan mun he gida ya fara tambayata yadda muka yi da Umma, wai taji haushi da bai barni ba? Sai na nuna masa kawai cewa bata ji haushi ba amma ban gaya masa already kafin inje Abba ya hana ba.
Ya karbi leave din kamar yadda ya fada, kuma ya kula dani kamar yadda yayi alkawari. Edd na saura one week na fara labor kuma ina fara wa ya gaya min cewa labor ne, haka muka yi ta yin kayan mu a gida tare har sai da yayi nisa sannan ya dauke ni da Amira rike da jakar kayan haihuwata muka tafi asibitin Dr Bashir.
Muna zuwa kamar da gaske, ya saka kayan doctors ya saka aka kawo masa duk abubuwan da zai iya bukata aka bar mu daga ni sai shi a dakin, amma haihuwar tana zuwa sai ya rikice, yadda nake karkarwa shima haka yake yi, ya ma kasa gane ina ne saman allura ina ne kuma kasanta. Dole ya kira wata midwife a gurin ta taimaka masa. Sai dai babyn tana fitowa ya saka hannu ya karbe abarsa ya rungume tun kafin a yanke cibiya balle a goge jiki.
"Welcome to the world Baby girl. You look just like your mother Yasmin"
*Wannan littafin na amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The Pictures*
Ya sunkuyo dai-dai fuskata ya nuna min babyn, "kin gan ta. Kamar ku daya ko? Ai dama na gaya miki" na dan juya na kalle ta kadan, sannan na mayar da idona na rufe. Sai dai hakan bai hana ni yin murmushi ba kadan duk kuwa da azabar da nake ciki. Fuskar yarinyar kadai ta goge min duk wahalar da nasha wajen kawo ta duniya and I was already deeply in love with her.
Yace da ni take kama, amma ni a dan kallon da nayi mata na few seconds sai naga da yan gidan su take kama dan ta fini fari sosai kuma dan siririn dogon hancin ta ma ba irin nawa bane ba.
Midwife din ce ta yanke mata cibiya sannan ta nannadeta a cikin towel yake jijjiga ta duk da cewa ba kuka take yi ba, yayin da ni kuma midwife din take kokarin gyara ni. Sai naji tana gaya masa cewa na samu tear dan yarinyar ba karama bace ba. Sai ya mika mata yaririyar yace ta gyara ta, shi zai min dinki da kansa.
Yayi kira masu allura suka yi min epidural, sai daya tabbatar ta zauna sannan yayi min dinki, taking his time har sai da ya gama sannan ya dago yana kallona yana murmushi yace "there you go. As good as new" na bata rai na harare shi sannan na juya kaina gefe ina cewa a raina da nasan haka haihuwar ta ke da ban bashi fuska ba ma ballantana yayi min ciki.
Sai yayi dariyar bata ran da yaga nayi sannan naga ya daura min drip, sannan ya gyara min kwanciya ta ya lullube ni, a take bacci ya dauke ni.
Sanda na farka Aunty Afia na gani da auntyn su Umar suna zaune suna hira da new babyn a hannun Aunty. Ina farkawa suka taso kusan a tare suna jera min sannu, sannan Aunty ta fita, jimawa kadan suka dawo tare da Umar, ya duba bp dina ya yi min yan tambayoyi sannan ya ce da aunty ta bani tea insha sannan in sha drugs din da ya kawo min. Sai kuma ya tsaya babu kunya ya dan shafa fuskar babyn sa sannan ya fita.
Suka bani tea mai zafi na sha kamar yadda yace sannan suka bani magani shima na sha, sannan suka miko min babyn suka ce in gwada feeding dinta, na karbe ta da bismillah sannan na rungume ta a kirjina side din dama na, sai kuma na fito da abincin ta na goga mata a bakinta, ta dan motsa kadan amma bata karba ba, sai na saka yatsu na biyu na dan bude dan karamin bakin ta na saka mata a ciki, ta saka harshen ta kamar zata turo shi sai kuma ta kama ta ja da karfi.
Na dan zabura kadan saboda zafin da naji, amma sai ta bude ido tana kallona kuriiii kamar ta sanni, sai naji zafin duk ya tafi murmushi ya zo fuskata. Na saka dan yatsa na ina shafa cheeks din ta ina jin wata irin soyayya da ban taba jin irin ta ba, tabbas wannan ita ake kira soyayyar uwa da ya, wadda babu irin ta kaf duniya. Lokaci daya naji a raina cewa zan iya yin komai saboda wannan yar karamar halittar da take rungume a jikina.
An gyara ta tas an saka mata kayanta da na taho mata dasu, overall mai strips pink and white, sai white hula da pink tutoci guda biyu a saman ta. Na cire hular ina kallon cikakken gashin kanta wanda ya zo tun daga keyarta har kusan rabin goshinta, tsahonsa kuma da ace za'a kama da tsaf za'a kitsa shi. A raina nace yarinya dole kiyi dashi tunda kinyo gado side biyu.
Ni gani nake kamar babu abinda take sha, dan banji alamar wani abu yana fita daga jikina ba amma tunda ta kama din sai na barta tayi ta tsotsa. A haka har ta rufe idonta ta koma baccinta. Umar ya sake dawowa, ya tsaya yana kallon mu fuskarsa kamar gonar auduga. "Aunty kinga sha take yi. Wannan yarinyar da wayon ta aka haife ta. Aunty kinga yadda take sha kuwa?"
Naja dankwali na na rufe fuska ta ina jin kamar kasa ta tsage in shige ciki, Aunty ta harare shi "to shugaban marasa kunya, in baka ji kunya ta ai kaji ta in-law din ka ko?" Sai ya dan shafa keya kadan ya fita yana murmushi. Bai jima ba ya sake dawowa lokacin na cire ta da wayarsa a hannunsa ya dauke mu hoto, sai kuma ya shiga shima ya dauke mu tare. Sannan ya dauki babyn yayi musu tare kala kala.
Su Aunty da Aunty da suka saki baki suna kallon sa, tace "da fatan dai kayi mata huduba ko sai dauke dauken hoto ka iya?" Yace "nayi mata. Sunan ta Maryam" sunan Mama. Ya ajiye ta yana shafa fuskarta. "Yasmin za'a ke kiran ta dashi"
Zuwan Umma, Hajiya da Farhan ne ya saka ya rabu da Yasmin ya mika musu ita sannan ya fita. Tun daga nan kuma dakin ya cika da hayaniya, ba'a jima ba sai ga su Mufida suma sun zo sun taho da abinci, a lokacin ne Mama ta kira ni itama daga Lagos ta duba ni sannan ta bawa Baba shima ya duba ni yana ta murna wai yayi amarya kuma ance masa tafi Mama da Aunty kyau.
Da yake haihuwar safe nayi, zuwa dare Umar da kansa ya rubuta min sallama muka taho gida gabaki daya. Bayan mun je gidan ne Abba yazo, the first time da Abba yazo gida na ya karbi Yasmin yayi mata addu'a ni ma ya duba ni sannan yace su Hajiya su zo su tafi, sai dai ya bar Farhan da Amira yace su kwana.
Washegari kuma da sassafe sai gashi ya dawo da Hajiya har da kayanta wai zata zauna tayi min wankan jego, nayi mamakin hakan dan na dauka ko yace ta zo zata ce ba zata zo ba amma sai gashi ta zo din, Amira ta gyara mata guest room din mu ta kai mata kayan ta can, kuma sai naga kamar da gaske take gurin kula da ni din, ita take yi kin wanka duk da Umar ya hana yin na ganye amma ita zata gasa min jikina sosai sannan ta saka ni in shiga cikin wani ruwan zafin in gasa kasana. Ita kuma take yiwa Yasmin wanka sai biyu a rana ta shirya ta sannan ta taimaka wa Amira gurin girkin gidan duk da dai tunda na haihu su Mufida da muhibbat kullum sai su zo gidan, kwana ne kadai basa yi amma suma suna taimaka min sosai gurin karbar baki wadanda nake ta yi ta ko'ina.
Ba ga yanuwan mu ba ba kuma ga na su Umar ba, daga ko'ina yan barka bullowa suke yi kuma kowa yazo sai ya kawo mana abin arziki. Ranar da muka kwana uku ne Mama Sa'a tazo min barka tare da yayanta gabakidaya, anan suka wuni sai dare suka tafi sai kuma ta bar Mammy anan wai zata taya Hajiya zama.
Banji dadin zaman Mammy ba saboda rashin kunyar ta bana son ta bani kunya a gaban mutane amma kuma ba zan iya hanata zama ba musamman tunda naga tana son zaman, sai suka hadu da Amira suka zauna tare tunda kusan sa'anni ne.
Na dauka zasu yi rigima tunda sun saba yi a gida amma sai naji shiru, naga Mammy ta sauko sosai tana ta yi min ladabi Aunty sama Aunty kasa har durkusa wa take in zata yi min magana.
Kwana na biyar da haihuwa Mama da Baba suka zo daga Lagos, suna sauka nan suka zarto suka ga Yasmin. A ranar ne kuma aka kawo min kayan barka daga gidan su Umar. Abin mamaki sai naga kayan sun ci uban wadanda muka siya da yaya Mubaraka, wadannan an barsu matsayin barkan Baba, sai kuma akwati guda na Mama ita ma, kayan baby masu kyau da kuma atampopi da laces masu tsada nawa, bayan nan kuma sai na sauran dangi aunties dinsa da cousins dinsa na uwa da na uba kusan kowa ya aiko min dawani abu, sai aka hada gabakidaya aka kawo a tare sai dai kowa an rubuta sunan saa jikin kayan da ya bayar. Ni wadansu ma ban gane su sosai basai da akayi min bayani.
Ni dai zance a cikin kwanakin haihuwa ta naga soyayya mai karfi daga Umar da kuma yan uwansa, tamkar ba'a taba haifa musu jika ba ko dan nashi na namiji ne? Ko kuma dan shi din shine mafi soyuwa a zukatan iyayen sa da yan'uwansa?
Umar bai taba yarda mun raba daki ba duk kuwa da idon Hajiya da ta kasa ta tsare tana comment akan komai ta gani. Duk motsin da nayi sai Umar ya tambaye ni mai nakeso? Menene yake min ciwo? Duk rigimar daren da Yasmin zata tashi tayi tare da shi muke yin ta, wani lokacin ma sai ya karbe ta yace in kwanta ina bukatar hutu shi kuma yayi ta jijjigata har sai tayi bacci sai dai in farka in ganshi kwance da ita a kirjinsa.
Ranar suna tazo aka rada mata sunan da ya fada, Maryam. Akayi kuma taron suna sosai anan gidan a lokacin ne yan uwana da kawayena suka kara tabbatar wa har kuma suka furta da bakinsu cewa babu wadda ta kai ni dacen miji a cikin su, sunga yadda mijina yake ta nan nan da ni duk da taron sunan bai hana shi nuna min kulawa ba. Duk da ya fita waje saboda mutane amma motsi kadan sai ya kira ni a waya, mintuna kadan sai ya sake kira, kawayena har tsokana ta suke da sunji karar waya ta zasu ce ga "maƙale mata mannau" nan ya kira.
But wadannan lokutan are the last peaceful days dana gani a gidan aurena......
Sati na uku da haihuwa Abba yazo da kansa ya dauki Hajiya, Umar ya hada mata goma sha tara ta arziki haka ma Mama musamman ta aiko mata da sako da taji ance zata tafi. Sai kuma nayi rashin sa'a lokacin yazo dai dai da komawar yan makaranta hutu dan haka Hajiya ta tafi tare da Amira da kuma Mammy, sai aka barni ni kadai kamar mayya. Na kama kuka Umar yana bani hakuri ina jinsa yana yi wa Mama yawa yana gaya mata ina kuka dan Hajiya ta tafi sai ta ce ya bani wayar, ta gaya min inyi hakuri zata samo min dattijuwar da zata cigaba da zama min har in karasa arba'in dina. Meanwhile Mufida zata ke zuwa muna wuni tare.
Kwana biyu bayan nan Umar yazo min da maganar tafiyar da Baba zai tura shi Lagos zai aikamasa da wadansu kayan sa zuwa waje, saboda Baban baya jin dadi sosai yan kwanakin nan shi yasa ma yake zaune a kano. Naji babu dadi kamar zanyi wani kukan amma bana so in nuna masa rashin jin dadi na dan iyayensa suna kyautata min sosai bai kamata dan sun neme shi na dan lokaci in nuna bacin raina ba. Amma kuma zan iya cewa kafin wannan lokacin bamu taba kwana ba'a makwanci daya ba ni da Umar, dan ko lokacin da muka samu sabani gado daya muke kwana kuma abin rufa daya.
Sai bayan da ya tafi ne sannan na rungume Yasmin na sha kuka na na more, zuwa yamma sai ga Mufida har da kayan ta, Mama tace tazo take kwana anan kafin Umar ya dawo, naji dadin haka dan nasan zata rage min kadaici amma ba zata debe min kewar mijina ba duk da cewa har yanzu bani da tsarki dan haka ko da yananan babu abinda zai faru amma ko babu komai ai zanji dumin jikinsa shima kuma yaji nawa, ballantana Umar baya rasa yan dabaru available.
Kwanan sa biyar a can, kwana biyar din da alokacin naji su tamkar shekara biyar dan sam bana wani samun Umar a waya baya fin sau daya muke waya dashi a rana, sai ya gaya min cewa tunda ya shiga garin network din wayarsa ya rikice sai yaje wani specific guri sannan yake samun network din kuma gashi yana ta busy baya samun zuwa gurin sosai.
Ni dai duk hankalina bai kwanta ba sai ranar da suka kwana hudu da ya kira ni ya gaya min washegari zai taho. Shi kansa naji alamar dokin ganin mu a muryarsa. Babu shiri na tashi hankalin Mufida sai data rakani saloon aka wanke min kaina aka gyara min kafata da hannaye na sannan akayi min jan lallen da yake so sosai. In wani yaga yadda nake doki zai dauka mijin nawa wata doguwar tafiya yayi ta tsahon shekara guda in anji kwana biyar ne kachal sai ayi ta min dariya.
Da safe na kira shi, and for the first time na same shi a waya. Da alama network din ya gyaru kenan. Ya dauka ya gaya min gashi nan har ya tafi airport. Da farko nayi niyyar zanje har airport din anan in dauko abina amma sai yace min cewa daga gida Baba zai je ya dauko shi da kansa, bana son ya kasance na nuna rashin kunya, dan haka nayi zamana a gida na jira shi a nan.
Muka yi kwalliyar mu ni da Yasmin. Muka kuma gyara gida ni da Mufida sannan muka yi masa girki muka aje masa, sai Mufida ta shirya ta fita school ta bar mu mu biyu muna zaman jiran mai gida.
A lokacin ne sako ya shigo wayata......
Sako daga matar da kullum zuciyata take cigaba da kokarin mantawa amma kwakwalwa ta tana ajiye da memory dinta a wani reserved space wanda a yau ta bankado ta fito.
Sako daga Zuwaira.....
Wayar tana hannuna naga notification from messenger, sai nag sunanta, Zuwaira Abdulkadir (Zuzu). Naji gaba na yayi wani irin faduwa, yawun bakina ya kafe kaf, kaina ya sara, na fara karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me wannan matar kuma take nema daga gare ni a yau ni Maijidda? Me yasa tun ranar nan banyi blocking dinta bane ba wai? Sai na shiga, da niyyar kar ma in karanta duk abinda ta rubuto min ballantana har raina ya baci da karerayin ta, na shiga da niyyar in yi blocking dinta kawai in fito.
Sai dai......
Pictures na gani guda uku da rubutu guda daya. Zuciyata ta sake warning dina akan kar in bude hoton amma ita kanta zuciyar tawa tasan ta makaro dan kuwa curiosity ba zai taba bari na in goge hotunan ba tare da na gani ba dan haka na bude din.
Na farko yana budewa naji kaina yayi wani irin sarawar da sai da na rike shi da hannu biyu na ajiye wayar. Wani duhu ne yayi replacing hoton a ido na. Ban san tsahon lokacin dana dauka rike da kaina ba ban kuma san tunanin me nake yi a lokacin ba dan ƙwaƙwalwa ta went totally blank kamar babu komai a cikinta, sannan kuma tunanin ya dawo min, tunanin hoton ne ya fara zuwa kwakwalwa ta, so nake in sake gani, so nake in tabbatar shi din ne a ciki, so nake in tabbatar ba idanuna ne suka yi min gizo ba, so nake in tabbatar ba mafarki ne nayi ba, mugun mafarki. Kuma a raina, with all my heart ina fatan mafarkin ne.
Umar ne a tsaye a wani guri that looks to me like a beach. Gajeren wando ne kawai a jikinsa, a gabansa Zuwaira ce, jikinta sanye da wata siririyar shimi da bata yi kokarin komai ba wajen boye surar jikinta dan za'a iya cewa da ita da babu duk daya, musamman da yake a jike take da ruwa. Ya zagaye hannunsa ta saman cikinta, ya dora fuskar sa a wuyanta suka kyalkyala dariya tare......
Na jima ina kallon hoton ina fatan inga kammannin sa sun chanja sun koma na wani, ko Mahmud ko wani dai, ko m wanene amma ba Umar dina ba amma babu