Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
sannan na kara reasonable riba a kai. At the end sai na samu riba da yawa.
And that was how it goes.....
Wannan kenan...
Meanwhile, Na nemi school a kusa damu inda za'a ke iya zuwa da kafa, kuma nayi sa'a na sami wata mai kyau anan kusa damu nayiwa Yasmin da Asad register. Nasan babansu ya kamata ya biya musu but I don't want to ask, musamman tunda yana asibiti, in ya samu lafiya ya biya shikenan in bai biya ba ma in dai ina da hali zan cigaba da biya, 'ya'yana ne nima.
Sai da na gama settling zancen makaranta sannan na kira Mufida na nemi yara su dawo zasu fara zuwa school. Ita da kanta ta kawo su, wannan shine ganin da nayi mata na farko tun da na bar gidan Umar and I saw that ta chanja da yawa, kamar ba ita ba, kamar wata mufidan ce aka saka a gangar jikin wadda na sani. Babu wannan tsaurin idon babu wannan gayun, babu wannan surutun. She looks calm and cool. Na tambaye ta dalili sai ta nuna min maganar auren ne, ta ce, "cousin din mu ne, ina jin zaki san Yaya Abdullahi dan Baffa Halilu" na rike baki, tabbas na san Yaya Abdullahi kusan shine babba a cikin 'ya'ya na family dinsu kuma bashi da wasa, dan haka kusan kowa tsoron sa yake ji ciki har da Umar, Mufida kuwa dama shine dodonta, dan yanzu zai wanke mutum tas, very disciplined but yana da kirki dan sai kayi ba dai dai bane ba sannan zaka ga bad side of him. Nasan yana da aure already tun ma kafin in auri Umar yana da yaya ma, kenan Mufida a ta biyu zata shiga.
Mun jima muna hirar bikin da ita wanda za'a yi in three weeks time, duk da na fahimci ba wani shiri take yi ba sai few events din da za'a yi a gida.
Sai da zata tafi sannan tace "naga kin fara sabon business, Allah ya sa albarka" nace "ameen ya Rabbi" tace "so kike dai ki koma Hajiya kwanan nan, ga aiki ga business duk ke kadai" nace "to ya za'a yi, rayuwar ce sai da haka" ta danyi shiru sannan tace "babu maganar yayana kenan ko?" Na bata rai "kar muyi haka dake Mufida, kar muyi maganar nan dake" tace "saboda menene? Ba sai kin fada min dalilin rabuwar ki da shi ba na sani, na sani fiye da abinda kika sani kuma maybe abinda na sani wanda baki sani ba shi yasa ki ka ƙi sassauta masa. Da kin sani da kin fahimci cewa ko da kudi aka ce yaje yayi abinda yake yi a da ba zai je ba. Duk da bansan yawan abinda kika sani din ba amma abinda ni na sani a yanzu shine yaya Umar din yanzu ba Yaya Doctor ɗin da bane ba. Maybe in kika ganshi zaki fahimci haka. Dan Allah Jidda zai dawo next week, please in ya dawo ki ganshi"
Ban ce mata komai ba ban kuma ji a raina cewa zan ganshi din ba, but I found myself wondering "what happened?"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*Beyond Caring*
*One Bad Chapter Does Not Mean Your Story Is Over*
Sosai na zama involved in harkokin bikin Mufida, ina gaya wa kaina cewa she deserves it from me ba wai dan yayan ta ba sai dan kawancen da yake tsakanin mu. Nina bude group a WhatsApp specifically saboda shirye shiryen bikin Mufida na saka friends din mu muka fara maganar anko da sauran su wadanda da duk ba ayi ba gashi lokaci ya kure dan haka babu bata lokaci muka fitar cikin sa'a akwai mai siyar da sutura a cikin mu dan haka ita ta kawo mana kowa har gida muka kuma fara rigimar neman tailor. Events kuma mun ma tsa wa Mufida lallai sai munyi wani abu ko guda daya ne, ta dage lallai ba tason dinner, bata son duk wani abu da zaiyi involving maza, a karshe muka tsayar da magana akan zamuyi bridal shower anan gidan su, dan ta ce ba zata je ko'ina ba. Wannan ya sa na kuma fahimtar lallai auren hadi ne za'a yi musu but I was surprised da ta karbi hadin dan nasan Mufida direct zata iya cewa bata so.
Mun gama shirye-shiryen mu tas na biki, duk da dai ba wani fita nake yi ba dan Abba yana nan a yadda na tafi na barshi in ba office ba babu inda nake zuwa, duk wani abun da zanyi sai dai in naje office kafin in dawo gida in yi in kuwa ba haka ba in na shiga na shiga kenan sai kuma wani lokacin. Na siyawa Mufida gifts dai dai gwargwado amma ima ta tunanin yadda bikin zai kasance, yadda zan shiga gidan su Umar a matsayin kawar Mufida, yadda zan fuskanci yanuwansa. I kept asking myself "sun sani kuwa? In sun sani how much did they know? Ya zasu karbe ni? Kar fa inje in kai kaina inda za'a wulakanta ni"
Wannan yasa ranar kamu kirmisisi naki zuwa. I lost the courage I thought I had. Da kawayen mu suka ishe ni da waya ma sai ma kashe wayata. Ai kuwa da dare ina kunnawa Mufida ta kira ni har da kukan ta wai ban kyauta mata ba, she then admitted to me cewa ba son mijin ta ke yi ba hadin iyayene which she can't say no to, she told me sai da na shiga cikin maganar bikin nayi supporting dinta sannan ta fara samun courage yanzu kuma duk na karbe courage din and she felt down taji bikin ya sake fita daga ranta.
I felt bad ni din ma and then promised her zan shiga washegari which is the bridal shower we organized, dan ni nayi hiring masu decorations ma suka je suka yi decorating falon Baba inda anan ne zamuyi. But then I asked her question din da rashin amsar ta ce ta kara discouraging dina akan zuwa gidan nasu.
"Ina yayan ki? Ya dawo?"
Ta danyi shiru "saboda shi kika ki zuwa? Yanzu har tsakanin ku ya kai cewa ba kya son ganin sa?" Na girgiza kaina kamar tana kallona nace "no ba haka bane ba, ina so ne dai in san ko yana nan dan in.......dan in.......taho masa da yaransa su gaisa"
Tace "tun last week ake saka ran zuwansa, amma bai samu taho wa ba though an sallame shi daga asibiti but in sha Allah cikin tsakanin gobe da jibi zai iso, dan yana son samun daurin aure" na gyada kai. "Okay. Shikenan. Zan taho dasu. Just in case"
Da wannan na shirya washegari muka tafi gidan tare da Farhan. Ina ta jan jiki na ina tunanin karbar da za'a yi min a gidan sai dai banga wani canjin fuska sosai ba, most of them suna tambayata ne akan rashin ganina jiya, wadansu kuma suna tambayata jikin Umar, akwai wadanda na lura ma suna tunanin tare muka tafi Dubai ɗin. Na jikin su sosai ne naga alamar sun sani.
Ban jima da zuwa ba Mama ta kira ni dakin ta. "Jidda naji dadi da kika zo, dama ana ta tambayar ki tun jiya. Dan Allah ina neman alfarma a gurin ki kar ki nunawa mutane wani abu, kiyi harkar ki kamar yadda kika saba duk biki a gidan nan. Bana so mutane su san abinda yake faruwa" naji maganar wani iri sai nace "amma Mama ba kya ganin fadar gaskiya ta fi? Idan basu sani yanzu ba ma ai watarana zasu sani... "
Ta katse ni "wadanda suka sani sun sani, wadanda basu sani ba kuma bana fatan su sani. Ina fatan komai zai zo ya wuce kafin su sani din" nayi shiru kawai na bar maganar dan har yau da Mama take no longer uwar mijina still ba zan iya jayayya doguwa da ita ba, na fahimci kuma har yanzu tana son in komawa Umar ne. But bana jin abinda take so din is possible.
Lafiya lau aka yi taron aka gama, Mufida ta saki jiki ta yanka cake din ta anyi mana hotuna sosai kuma duk munyi kyau Masha Allah, har aka tashi banga alamar Umar yana gidan ba dan haka na kara sakin jikina har da rawa ana yi mana video ni da amarya. Kawayen mu da suka san mun rabu da Umar suna da mamaki na wai su ba zasu iya ba ni kuma a cikin raina ina ta gaya wa kaina cewa bikin kawata nake yi ba wai bikin kanwar ex husband dina ba, dan sai da na fara sanin Mufida kafin in san Umar.
Washegari yini. Ranar da kyar Abba ya bar ni dan da farko cewa yayi ba zan je ba wanda naje musu jiya ma Allah ya sa albarka. Har na hakura, sai dai ban san abinda zan gaya wa Mufida ba sai na samu Umma ta hau saman sa ta lallaba min shi da kyar ya bar ni amma da jan kunnen kar inyi dare.
"Kar aga tana zarya a gidan ace kome take nema"
Ni dai tunda na samu aka barni sai na kama shiri, sai da na dauko dinkin ankon da Amira ta karbo min dazu a gurin tailor sannan murna ta koma ciki, gabaki daya yaki shiga jikina, daga rigar har skirt din. Na sake kallon kaina a madubi for the first time ina lura da yadda nayi kiba kamar an saka min yeast. Ina jin mutane suna fadar nayi kiba a yan kwanakin nan amma ni sam bana gani musamman saboda ban cika kallon kaina a madubi ba kuma ban fiya saka dinkakkun kaya ba mostly abaya nake dorawa akan uniform dina wadanda dama burma burma aka yi min su.
Na zauna na zabga tagumi ina kallon kayan. Sai kuma na saka su a leda na fita zuwa gurin wani tailor a bakin layin mu na roke shi ya bude min su, da kyar yayi min dan yana ganin mutuncina, amma duk da haka bai samu space sosai ba dan kadan ya samu ya kara min yace "dama yanzu Jidda sai kin sake measurements, in kika cigaba da using measurements dinki na da to za'a ke miki kayan da ba zasu shige ki ba"
Na kalli kaina ta cikin hijab sannan na kalle shi. Bama wasa da shi dan haka ban ja maganar ba na karbi kayana na koma gida na saka su da kyar ina lura da yadda suka kamani musamman ma skirt din. Wannan ya kara makarar da ni duk da ban tsaya wata kwalliya sosai ba sai abin da ba za'a rasa ba na saka hijab dina na tafi. Saurin da nake yi ya saka na manta ma da wani fargabar haduwa da Umar a gidan. Ina zuwa bayan amarya ta gama yi min mitar na makara ban zo da wuri munyi wanka tare mun shirya tare a gidan ba, sai kuma na shiga hidimar saukar kawayen mu, duk kawayen mu suna dakin Aunty kuma abincin su yana hannuna dan haka na cire hijab dina na shiga hidima.
Na lura da fuskokin mutane da yawa wadanda na sani a zamanin aure na da Umar, ciki har da Ummi kanwar Aunty da kuma Asabe. Ummi na ganta ta girma sosai ta zama cikakkiyar mace har da yar kyakykyawar babyn ta a hannun ta, nayi wa Aunty mitar kin gayyatar mu bikin Ummi da tayi kamar yadda tayi alkawari sannan na dauki babyn nayi mata wasa ina jin zuciyata fes babu wani abu na riko ko jin haushi a cikin ta.
Asabe kuma na ganta tana ta harkokin ta tare da kakarta, na lura kamar a gidan suke zaune tare a wani daki da da nasan na baki ne mata. Kallo daya nayi mata naga tayi kwalliyar ta cikin sababbin kayanta fes da ita, sai dai ko kadan kyawun kayan jikinta bai boye kauyancinta, rashin wayewa da kuma rashin ilimi ba, daga alama duniya tana zuwa mata yadda take so. Duk da na lura kamar saniyar ware take a gidan, yan uwan mijin nata da surukar tata ba sa kulata. Na lura tana ta so tayi min magana amma naki bata kofa saboda ni a ganina babu magana da ta rage tsakanin mu. Idan da son samu nane ma, idan ba dan Mufida ba, babu abinda zai kuma saka wa mu shaki iska daya da ita.
A haka har magrib tayi, mutane suka fara watsewa muka fara kokarin tattara gidan da gyaran abubuwan da aka bata ni kuma na fara shirin tafiya gida amma da niyyar zan bar su Yasmin su kwana a gidan kamar yadda Mama ta bukata.
A cikin wannan lokacin ne na shiga kitchen ina harhada soveniers din da suka rage na kawayen mu sai ga Asabe ta biyo ni kitchen din, naji an shigo amma ban waiga ba, warin kashinta na fara ji na gane ita ce, na juyo ina kallon ta bance komai ba sai ta fara jujjuya hannunta tana cewa "mommy. Dama ina ta so in ganki in sake baki hakuri akan abinda ya faru. Naji ana cewa wai kun rabu da Daddyn Yasmin ko? Ni kuma gashi an daura mana aure da shi. Shine nace zan kara baki hakuri in kara gaya miki cewa ba laifi na bane ba shine ya...."
Na daga mata hannu "kin an dalilin da yasa Umar ya sake ni?" Ta girgiza kai da sauri, nace "saboda na tona asirin abinda ya faru tsakanin ku. Duk shekarun da muka yi da shi ban taba fadar halinsa na neman mata ba shi yasa bai taba saki na ba. Amma da na fada sai ya sake ni. Kina so kema ki zauna da shi tsahon shekaru ba tare da ya sake ki ba?" Ta gyada kai da sauri nace "to ki iya bakin ki. Kar ki kuma furtawa kowa maganar nan in kuwa kika fada kuma yaji to tabbas zai sake ki kamar yadda ya sake ni"
Naga tsoro ya bayyana a fuskarta. Dama target dina kenan. So nake in tsorata ta dan nasan babu abinda take so a yanzu irin zama da Umar. Duk da Umar yanzu ba miji na bane ba tabbas har yanzu yana matsayin uban yayana kuma ba zan so wannan shashashar take yawo da zancen su a cikin mutane ba.
Ta sake matsowa kusa dani "shikenan mommy, na gode, alƙur'an ba zan sake fada ba" na dan kara matsawa ina cigaba da abin da nake yi, sai kuma na sake juyowa na sake kallonta kadan, wani abu yana daukan hankali na a tare da ita. She looks fuller and firmer.
Na sake kare mata kallo. She definitely looks pregnant. Na dauke kaina tare da gaya mata cewa ta fita ina aiki ne. But sai naji wani zafi da na jima banji ba ya soki zuciyata. Na ajiye ledar hannu na tare da dafe kaina da hannu daya. Banso su Yasmin su samu kani ko kanwa ta wannan hanyar ba.
Ina tsaye a haka naji an bude kofar kitchen din an shigo. Ban kalla ba sai rufe ido na da nayi ina kokarin daidaita yanayin fuska ta dan bana son ko waye ya lura ina cikin damuwa. Sai dai ko second biyu banyi ba na bude idon da sauri saboda kamshin da naji na juyo na sauke ido na a kansa.
Ya rame da gasken gaske. Ramar sai ta kara masa tsaho fiye da already tsahon da yake dashi kuma kananan kayan da suke jikinsa suka kara fito da tsahon. Ya aske dukkanin sajen fuskarsa ta zama smooth, abinda ban taba ganin yayi ba. Ya kuma kara fari sosai kamar wanda aka zuke jinin jikinsa.
Yana tsaye a bakin kofar fuskar sa cloudy with emotions, kofofin hancinsa suna budewa suna rufewa da sauri. His jaw strong his lips tight. Na dauke idona daga kansa na juya da sauri na cigaba da zuba kayan gabana a cikin babbar ledar hannuna.
"Jidda"
Ya kira sunana, na dan juyo kadan nace "na'am. Ya kake?"
Yayi shiru ni kuma na cigaba da aikin gabana trying so hard not to think. Kamar ba zai kuma magana ba sai yace "ya nake? Shine abinda zaki ce min kadai?" Na ajiye ledar na juyo sosai "me kake so? Akwai abinda kake bukata ne?"
Ya saka hannu ya shafa kansa looking frustrated. Sai kuma yayi gyaran murya kamar mai selecting words yace "afuwan. I kept thinking my heart and yours are the same. I kept thinking kina tunani na kamar yadda nake tunanin ki. I kept imagining you by my bed side kina jinyar zuciyarki kamar yadda naje jinyar tawa. I should have known daga lack of care dinki cewa you don't care....."
Nace "I cared and cared and cared. Now I am beyond caring. Ina yi maka fatan alkhairi. But now you must excuse me dan ina sauri ne zan tafi gida"
Bai ce komai ba sai ji nayi ya tura kofar kitchen din ya rufe. Na ajiye ledar hannu na na rike kugu zan zazzaga masifa sai kuma na tuna babu hijab a jikina kuma Umar ba muharramina bane ba.
Na nuna shi da yatsa "ka bani guri in wuce" ya jingina da kofar yana rarraba ido akan fuskata kamar mai kokarin haddace kowanne loko da sako na jikinta yace "we need to talk" nace "not now, I am busy. In magana ce da kai akan yayanka ka samu Abba ko yaya Tahir kuyi sune maza, apart from that kuma ni bani da sauran wata magana da zanyi da kai. Now, ina son zuwa in saka hijab dina dan kai ba muharramina bane ba da zan tsaya kana kare min kallo a bati"
Ya dan saki baki yana kallona daga sama zuwa kasa sannan yace "da me ya sa baki saka hijab din ba?"