Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
ka iya ganewa cewa nata ne"
Ya fara girgiza kai
"Jiddah listen to me. Ba haka bane ba...." Nace "to menene? Gaya min inji menene, ni dai a maganganun ku banji inda aka ambaci sunanta ba, I thought she is just a random unknown prostitute wacce baka sani ba kuma baka yi niyyar sani ba shi yasa baka je ba"
Yace "kawai fadar sunan nayi Jidda, nasan wata yarinyar Bashir mai wannan sunan shi yasa kawai nayi guessing ko ita ce ba wai na gane ta bane ba" na girgiza kaina nima hawayen dana dauka sun tsaya suka sake sauko min "yarinyar Bashir ko kuma yarinyar ku kai da Bashir? Wacce kuke sharing kuma kuka dade kuna sharing dinta a tsakanin ku"
Yayi shiru yana struggling da zuciyarsa, na dafe kaina ina tuno hirarsu da Bashir "ka karo dadi" na fada a fili, "abinda aka san dadinsa dama shi za'a ce ya karo dadi ba wai wanda ba'a sani ba"
Still bai ce komai ba, na goge hawaye na "there I was, thinking cewa Zuwaira ce kadai, ina ta kokarin shifting blame on adolescence da kuma rashin aure da wuri da society da shaidan da kaddara, anything but you, thinking cewa abinda ya riga ya faru ya faru kuma ya wuce kuma ba zai sake faruwa ba. Ashe suna da yawa, yanzu na san uku Allah kadai yasan yawansu kuma yasan wadanda zan sani nan gaba"
Ya fara kokarin rike hannuna yana kokarin zaro maganar da ta kasa fitowa, na zame hannuna daga cikin nasa "ba zaka gaya min gaskiya ba shine matsalar ka, rashin fadar gaskiyar kuma shine yafi komai tsaya min a rai yafi komai bata min rai Umar. If you open up to me, nasan me nake fuskanta then we can work it out together because I love you"
Ya kama fuska ta "Jidda, na gaya miki gaskiya fa, Jidda gaskiya nake gaya miki fa. Na baki labarin Zuwaira, ita kuma wannan yarinyar Bashir ce, yes I know her amma ba yanda kike tunani bane ba Jidda, daga su kuma babu wata. Na rantse miki babu wata sai ke"
Nace "sai yaya Jamila. Sai yayata jamila"
Ya rintse idonsa "that lying bitch" na nuna shi da hannu na "kar ka sake zagin ta" yace "Jidda ba tun yau ba na gaya miki wannan yarinyar karya taje yi min, so take.... " Nace "so take ta raba ka da ni? Me yasa kowa yake yi maka karya ne? Mai yasa kowa yake so ya raba ka dani ne? Saboda me? Huh?"
Na cigaba "tun lokacin da muka fara samun matsala da kai, tun farkon sanda ka fara breaking heart dina abinda na fara sakawa a raina shine alhakin yaya Jamila ne yake bi na. Sai da ta gaya min, she warn me about you amma na rufe ido na na ki sauraren ta na kuma kirata da makaryaciya, sannan naki gaya wa kowa saboda ina ganin ai karya take yi maka kuma fadar zai zamanto kamar na zubar maka da mutuncin ka a idon surukan ka"
"I can't even imagine her pain, bayan ka yaudare ta kayi mata alkawarin aure sannan ka raba ta da a abu mafi daraja a gurin ta sannan kuma kazo ka auri kanwarta. Can you even imagine how she felt?"
Ya yamutsa fuska "what? Ni fa ban gane abinda kike nufi ba, ban gane na raba ta da abu mafi daraja a gurin ta ba" nace "kasan ai abinda nake nufi Umar, kasan abinda kayi ai. You took her vaginity"
Ya sake ni "what? Jidda karya take yi wallahi. Lokacin da nasan yarinyar nan she wasn't even a virgin"
Shirun da ya biyo bayan maganar ita ta saka yayi realising abinda yace, daga dukkan alamu ranar yau bata tafiyar masa yadda ya kamata and his smart brain wasn't that smart after all.
"Umar" na kira sunan sa da karyayyiyar murya "you mean you had sex with my cousin and then you marry me duk da kasan cewa ni cousin din ta ce? Wannan wanne irin abin kunya ne Umar"
Sai ya ja da baya, sannan without another word ya sauka daga kan gadon sannan ya fita daga dakin.
Na ja pillow zuwa kirjina na rungume sannan na kifa kaina a cikin pillow din na cigaba da rera kuka marar sauti dan gudun kar in tashi yaya na da suke bacci.
Tun sanda na fahimci abinda ya faru tsakanin Umar da Zuwaira na saka a raina cewa Jamila ma ba karya tayi masa ba, ban taba yi masa maganar ba saboda ina tsoron cewa maganar zata tabbata cewa gaskiya ne, sai yau, ranar da nayi realising cewa ba Zuwaira ce kadai macen da Umar yayi ko kuma yake yin mu'amala da ita ba a ranar kuma na tabbatar har da cousin dina yar kanwar mahaifina a cikin list din matan da suka yi sharing gado da mijina kuma uban yayana. Sai naji abin yafi yi min zafi yanzu dana tabbatar akan da dana ke saka ran watakila zai iya zama ba gaskiya ba. But I am glad I did know the truth dan hakan ne kawai zai saka in samu peace of mind kuma in iya saka abin a baya na.
Nayi kuka mai yawa, amma kuma ga mamaki na sai naji kamar an dauke min wani dutse ne da ya danne zuciyata ya kasa barin ta ta sake, naji finally na samu peace a zuciyar ta wa, ba wai peace na cewa problem dina ya kare ba a'a peace na cewa na san menene problem din nawa, next step shine in san yanda zanyi tackling dinsa.
A daren nayi realising gaskiya, it was so hard on me to accept but dole nayi accepting cewa Umar, mijina, uban yayana is an adulterer. Kuma he has been at it for quite a long time, unrepentantly.
Yes, he is an adulterer. But he is also my husband who loves me dearly kamar yadda nima nake son sa, sannan kuma uban yayana ne guda biyu, na riga na haifa masa su kuma babu yadda zanyi in chanja musu uba ko da kuwa ina son inyi hakan.
Yanzu na fahimci problem din da yake cikin aure na, na fahimci tawa kaddarar kamar yadda tun kafin inyi aure nasan cewa kowanne aure yana da nasa matsalar kamar yadda na gani a gurin sisters dina, a lokacin bansan cewa nawa jarabawar zai fi nasu wahala ba sai yanzu. Next step kuma shine inga yadda zanyi tackling problem din, yadda zanci jarabawar rayuwata.
Ba zan iya chanja matsayin Umar a rayuwata ba, amma maybe zan iya chanja waye Umar din. Musamman tunda ina son sa kuma shima yana so na. Sai dai wannan son da nake yi masa da kuma wanda shima yake yi min shine ya kara rura zafi a cikin zuciyata.
It is so hard to accept that mijinki da kike so kuma wanda shima yake son ki yana mu'amala da wasu matan a waje, mu'amala bata gaisawa ko magana ko harkar aiki ko kuma soyayya ba, a'a mu'amala irin wacce ya kamata ace dani ne kadai zai ke yin irinta sai dai kuma in yayi wani auren nan gaba.
But in dai har zan iya chanja shi din ta yaya?
Ta ina zan fara.
Na jima ban yi bacci ba ina lissafin mafita, amma kuma a daren na yanke mafitar da nake ganin ita ce hanyar da zata bille da ni.
Da assuba na tashi kamar kullum nayi sallah nayi adduoi na na kai kuma na gurin ubangiji wanda nasan shine kadai zai share min hawaye na ya amsa addu'a ta ya biya min bukata ta ya shirya min mijina.
Na zauna nayi azkar zuwa wayewar gari sannan na tashi na shiga wanka na fito na shirya sannan na fita zuwa kitchen na fara hada breakfast ina lissafin yadda zan kammala kafin Yasmin ta tashi ta tayar min da Asad. Ina gamawa ne kuwa na jiyo kukan sa da yar karamar muryar sa, nayi murmushi sannan na ajiye towel din hannuna na tafi har da dan gudu na.
A kan gado na tarar dasu Yasmin tana ta kokarin wai sai ta dauke shi. Na rike hannunta "yaya Yasmin? Zaki dauki Asad ne?" Ta fara gyada kai "eh eh eh eh eh" na dauke shi sannan na gyara mata zamanta "to zauna in baki shi ki rike. Ki ce bismillah" na dora mata shi sai ta fara dariya tana taba hancinsa, shi kuma ya dauka abincin sa ne sai ya fara bude baki, da yaji babu komai sai ya kara bude baki ya cigaba da kuka.
Na dauke shi na saka a kafada ta "ya isa haka babana, yi shiru kaji rabu da yaya Yasmin dan ta ga ka fita hanci shine zata lakuce maka na ka" ta tabe fuska zata yi min kuka ita ma sai na dauke ta ita ma da daya hannun nace "taho muje mu tashi Daddy daga bacci"
Muka fita muka shiga dakin sa. Yana kwance akan gado, yayi rub da ciki ya kuma dora pillow akan sa, ko motsi baya yi, daga gani bacci mai nauyi yake yi, daga gani kuma baiyi sallar asuba ba. Na ajiye Yasmin akan gadon sannan na dauke pillow din da ya rufe fuskar sa dashi trying hard not to think of maganganun da muka yi jiya. Ina ajiye Yasmin ta sauri ta haye bayansa ta fara doki "doci, doci, doci"
Ya yamutsa fuska sannan ya bude ido yana kare haske da hannunsa. "Ka tashi ko kuma in dora maka Asad shima yayi dokin bayan Yasmin" yayi juyi without knowing Yasmin tana bayansa, ta tafi zata fadi sai yayi sauri ya rike ta da hannu daya ya gyara kwanciya ya koma rigingine sannan ya dora ta akan cikinsa.
Ta cigaba da tsallen ta "doci doci doci" sai kuma ya daga ta sama "ahh, Yasmin zaki saka inyi aman hanjina daga baki, ke baki san kullum kara girma kike yi ba ko mamana" ya karasa yana yi mata chakulkuli a wuyanta.
Na zauna a gefen gadon na fara feeding Asad. "Zuwa muka yi mu tashe ka ka shirya office, sai muka tarar ashe ko sallah ma baka tashi kayi ba" ya juyo yana kallona, muka hada ido sai yace "banyi bacci bane sosai jiya" na girgiza kaina "wannan ba excuse bane ba, da ka sani sai ka saka alarm da zai tashe ka da assuba in kayi sallah sai ka koma ka cigaba da baccin ka"
Har yanzu ni yake kallo, kuma nasan dalilin kallon dan rabon da inyi masa magana irin haka tun kafin haihuwar Asad. Maybe kuma ya dauka yau rashin maganar ta mu zata fi na kullum. Na sake kallon sa sannan na nuna masa toilet "ka tashi fa, kana ta kallo na anan" ya ajiye Yasmin ya sake juyawa ruf da ciki yana kallona sosai "kina min magana ne?" Nace "ina cewa ka tashi kayi sallah ne in ka idar kuma ka rike min daya daga cikin bundles of joys din nan kafin in wanke daya"
Ya mike da sauri "zan wanke daya ke kuma ki yi wa daya, ai tare muka haife su ko?" Ban bashi amsa ba ya shiga toilet yayin da Yasmin ta bishi tana ta buga masa kofa har ya fito ya saka riga ya shimfida sallaya, tayi sauri ta kwanta akai kamar wadda ita aka shimfidawa sai ya rabu da ita ya shimfida wata, kafin ya idar na gama feeding asad na kwantar dashi na koma kitchen na dora ruwan tea na zuba kayan kamshi sannan na dawo na tarar suna ta rigimar cire kaya da Yasmin, tana ta yi masa surutu wanda ba'a iya gane me take cewa in banda Daddy, shi kuma yana biye mata yana bata amsa, ina shiga yace "wannan zata tsaya inyi mata wankan kuwa? Duk ta gajiyar dani already" nace "ka barni inyi mata, wankan Yasmin sai da dabara, kawai ka juye ruwan tea inya tafasa a kitchen.
Yace "yes ma" yana murmushi sai kuma yazo ya tsaya a gaba na kamar mai son yin magana, na sunkuyar da kaina kasa sannan na zagaye shi na shiga toilet na fara hada wa Yasmin ruwan wanka. Sai da na gama yi mata sannan na wanke toilet na hada masa shima. Na fito na gogewa Asad jikinsa tunda har yanzu ba kullum nake yi masa wanka ba.
Kafin ya gama na gama shirya yara Asad har ya koma baccin sa, yana fitowa naje ba bude wardrobe din kayansa "me zaka saka yau? Dogayen kaya ko kanana" sai ya zagayo ta bayana ya bude towel din jikinsa ya saka ni a ciki ya rufe mu tare "wanne kike so in saka, dogaye ko kanana?" Na juyo ina kallon sa, "ya danganta da schedule dinka na yau, in akwai wani gurin da zaka je na kunya haka sai ka sa manya in kuma babu sai kasa kanana"
Ya dan zame hannun rigata daga kafada ta yayi kissing kafadar "a bani kananan to, ranki ya dade" ban ka shi ba na zame jikina daga nasa na dauko masa kayan na ajiye masa sannan na fara gyaran gadon.
Yana saka kayan yace "naga kamar kina ta sauri yau, ko akwai wani abin da zaki yi ne?" Na gyada kai "ina so ne zan fita unguwa" ya dakata da abinda yake yi, "unguwa kuma? Wacce irin unguwa bayan kin san Asad bai yi kwarin da za'a fara fita da shi ba?" Nayi shiru bance komai ba na cigaba da gyaran dakin nasa har na kammala shima ya gama sannan muka fita yin breakfast, na ga bayan ruwan tea din har sauran abubuwan da ban kawo ba duk ya kawo, ya jawo high chair din Yasmin ya saka ta a ciki ya jawo ta kusa da shi ya fara bata abinci, ni kuma na hada masa nasa na ajiye masa a gabansa sannan na hada nawa na zauna, sai ga ya ga Yasmin ta koshi sannan ya fara cin nasa yace "ina zaki je unguwar? Ni yau fa bada wuri ma zan fita ba, sai around 12 or so" nace "gidan gwoggo Habibah zan je, that's in ka bari kenan"
Ya ajiye fork din hannunsa yana kallona fuskar sa tana nuna bacin rai yace "gurin wannan yarinyar zaki je ko?" Nace "gidan gwoggo Habibah zanje, eh Yaya Jamila tana gidan dan haka definitely zan hadu da ita a can in dai ba taje unguwa bane ba ko something" ya cigaba da cin abincin "in nace ba zaki je ba fa?" Na daa kafada "shikenan sai in hakura, in kuma ci gaba da tambayar ka har sai ranar da Allah ya sa ka barni sai inje"
"Me zaki ce mata?" Ya tambaye ni, nace "ban gane me zance mata ba, yar uwata ce fa, zamu gaisa muyi hirar mu irin ta yan'uwa shikenan" yayi shiru bai ce komai ba sai na ce "idan da baka san dangantaka zaka ni na da ita, tunda ka fahimci wacece ita a gurina sai ka fasa aurena. Fakat"
Ya ajiye cup din hannunsa sannan yace "ki shirya, in zan fita sai in fita da ku in barku a can, in zan dawo sai in biya in dauko ku" nace "Nagode"
Sai 12 din muka fita tare, na saka wa Asad kaya masu kauri sosai sannan na saka shi a cikin carrier dinsa na daure shi a jikina sosai. In ba sani kayi ba ma ba zaka san da jariri a jikina ba sai dai ka daka ko kiba na kara.
Tun da muka tafi ban nuna masa hanya ba, duk da nasan cewa tunda mukayi aure bai taba kaini gidan da kansa ba amma sai gamu tiryan tiryan har kofar gidan suna ta surutun su shi da Yasmin. Ina shiga gwoggo Habibah ta tare mu ta fara'ar ta ta dauki Yasmin ni kuma na durkusa na gaishe ta. "Kune a gidan nan Maijidda? Da danyen jegon nan kika fito?" Nayi murmushi "na gaji da zama ne a gidan ni kadai gwoggo, tunda Hajiya ta tafi gidan duk babu dadi in ya fita shine yau nace ya fito da mu ya kawo mu nan mu dan yi hira, zuwa laasar sai ya dawo ya dauke mu" ta gyada kai "ina maigidan na wa?" Nace "gashi yana ta bacci" sai kuma nace "yaya Jamila tana gida kuwa?" Ta girgiza kai "kin san ta samu aiki ai har ta fara zuwa, amma kafin ku tafi insha Allah zata dawo" na gyada kai ina fatan ta dawo din kafin lokacin.
Bayan sallar azahar kuwa sai gata ta dawo din, tayi mamakin ganin mu kuwa, nima kuma nayi mamakin yadda ta chanja kamar fuskarta ta fara manyanta haka, sai dai kuma yanayin ta yana nuna ta nutsu babu rawar kai irin yadda take da.
Ta karbi Asad daga hannu na "ayyah dan jariri ban je na ganka ba har kai kazo da kanka" ta kalle ni "Umma tace sunan babanku kuka saka masa ko?" Na gyada kai "eh sunan Baba ne" ta ce "me ake ce masa?" Nace "Asad" tayi murmushi "suna mai dadi" sai ta miko min shi sannan ta shafa fuskar Yasmin "duk basu yi miki kara ba, duk da babansu suke kama"
Sai kuma ta dauki jakarta ta shiga dakin ta. Na mike nima da Asad a hannuna na bi bayanta. Bata dakin amma na jiyo motsinta a toilet, sai na zauna a bakin gado, ban dade da zama ba Yasmin ta biyo bayana ta zauna a kusa dani "mu tafi, Daddy!" Na harare ta a raina nace shegen son uba kamar ita kadai ce mai uba a duniya.
Muna zaune yaya Jamila ta fito, ta bi mu da kallo tana goge ruwan fuskar ta sai nace "gurin ki nazo yaya Jamila" sai ta ajiye towel din hannunta ta zauna a kusa dani "Allah dai yasa lafiya kanwata" sai naji hawaye ya taru a idona "zuwa nayi in baki hakuri, akan maganar nan, wannan maganar da kika gaya min ranar nan, ban yarda ba lokacin amma yanzu na yarda"
Sai tayi shiru tana wasa da hannunta sannan tace "ba sai kin bani hakuri ba Jidda, abinda kika yi a lokacin shine exactly abinda zanyi