Chapter 32 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 106

93K to 96K   out of 316K words

zaton gidan karuwar sa ne, karkarin ta yaje yace mata bata kyauta masa ba ta tona masa asiri, and they may have lover's fight and shikenan sai ya dawo ni kuma ya shirya min wata karyar.

Na bude jaka ta na dauko wayar ina kallon sunan sa "Umarul Faruq" sunan da da yake saka ni murmushi amma yanzu yake kara min kunan zuciya. Nayi cutting kiran dan wakar soyayya da na saka masa kara min bakin ciki take yi. Da sauri na shiga setting din wayar na  dubo yadda ake blocking number na danna masa block sannan na jefar da wayar akan gado. Na gama sauraren duk wasu karerayi na Umar insha Allah.

Na tabbatar na debi awanni sun kai biyar ko shida a dakin dan har duhun magrib ya fara shigowa sannan naga kiran yaya Tahir, sai jikina ya bani Umar ne ya kura shi yana nemana sai kawai naki daukan wayar ta sa shima dan in ya san inda nake zai iya dauko Umar din su taho gidan a yanzu, ni kuma alokacin babu abinda bana son gani irin fuskar Umar.

Ya cigaba da kira sai kawai na saka wayar a silent dan kar ta tashi Yasmin wadda yanzu na samu na lallaba ta ta koma bacci. An jima kadan kuma sai ga kiran Aunty Afia ita ma, itama na barta sai da ta kira har sau uku sannan naji ba zan iya cigaba da ignoring calls din ta ba. Na dauka wayar na saka a kunnena da niyyar yin magana, sai a lokacin na lura ashe tsabar kukan da nayi har murya ta ta dashe bata fita sosai.

"Kina ina?" Ta tambaye ni direct.

Daga jin yadda tayi magana nasan cewa maganar bari na gida yaje kunnenta. Sai naji hawaye na ya sake dawowa, na motsa baki na amma na kasa yi mata magana.

"Kina ina nace?" Ta saka tambaya wannan karon cikin fada. And I can swear naji muryar Umar a kusa da ita yana tambayarta "ta dauka?"

A hankali nace cikin dasashshiyar murya ta "Aunty dan Allah kar ki gaya masa inda nake" tace "wai kuka kikayi Jidda har muryar ki ta zama haka?" Ban ce komai ba sai wasu hawayen da na goge, ni da kaina ina jin yadda idanuna suka kumbura.

Ta sake cewa "kina ina?" Yanzu a hankali tayi maganar da sigar lallashi. Nace "ina gidan ki. Amma dan Allah kar ki barshi yazo nan, wallahi ba na son ganin shi Aunty" tace "okay ki zauna gani nan zuwa, amma ki daina wannan kukan tun kafin ciwon ki ya tashi" naji yace "wanne ciwon? Bata da lafiya? Me ya same ta?"

Maganganun sa naji sun kara min daci a zuciyata, he is so good at pretending ya kamata a bashi number yabo ta kasa a wannan bangaren.

Na katse wayar ba tare da naji amsar da aunty ta bashi ba. Sannan na kwanta na rufe ido na ina jin zuciyata tana bugawa da karfi. Allah yasa ba tare zasu taho ba, bana fatan sake ganin Umar har abada dan ganinsa shi zai cigaba da tunamin da hotunan sa.

Ina nan kwance naji tsayuwar mota. Na tashi da sauri na leka ta window naga motar gidan ce, Aunty da Afia suka fito, naji hankali na ya kwanta tunda ba tare suka taho ba, but then I was his car yayi packing dinta a waje, ya bude kofar ya fito sannan ya dago kai yana kallon gidan. Nayi sauri na saki labulen tun kafin in kalli fuskarsa. A raina nasan cikin biyu daya ne ya faru, ko dai hada baki suka yi da Aunty tace masa ina nan ko kuma bata gaya masa ba shine ya biyo bayanta bata sani ba.

Na ji su Aunty sun shigo sannan naji muryar ta tana kwalla min kira, na mike na fita daga dakin na tsaya a kan bene ina kallon ta amma ban amsa na, sai ta saki baki tana kallo na, da ga alama kamanni na sunyi mata kama dana wadda tayi sati tana jinya. Sai ma sauko da gudu na rungume ta na cigaba da kuka na ita kuma ta hau aikin lallashi.

Ta jani muka zauna akan kujera tana ta lallashina sannan ta aika Aira ta dauko Yasmin. Bata jima ba ta sauko da Yasmin a hannun ta ta bawa Aunty sannan tace "Aunty kin ga Yaya Doctor ashe biyo mu yayi, gashi can na hango shi a bakin gate" Aunty ta dafe kanta "sai fa dana gaya masa ya tafi gida zan kira shi a waya in na ganta, amma ashe bai yarda dani ba kenan shine ya biyo baya na"

Ta dauki wayarta sai na rike hannunta. "Aunty dan Allah. Dan Allah Aunty ki kore shi kar ki barshi ya shigo. Dan Allah kar ku mayar da ni gidan sa"

Sai naga yanayin ta duk ya chanja tausayi na ya bayyana a fuskar ta, ta kira waya sai ta kama fada

"ya akayi ka biyo mu Doctor? Kai da muka yi da kai cewa zan kira ka in na ganta ba sai ka bari in kira ka din ba?"

"Eh na ganta gata nan muna tare"

"Lafiyar ta kalau Yasmin ma haka, gata a hannuna"

Sai ta girgiza kai

"Ba zaka samu ganinsu yanzu ba gaskiya. Ita da kanta take rokona tana hada ni da Allah akan kar in barka ka shigo gidan nan bata son ganin ka"

Ta sake saurara sannan tace

"Bana jin zata saurari wani bayanin ka yanzu, ko na barkaka shigo ma bana jin zata tsaya ta ganka din, ni kuma ba zan takura mata ba"

"Ba yau ba gaskiya. Ka tafi gida kamar yadda na gaya maka. Idan ta huce zuwa jibi ko gata sai in tambaye ta tayi min bayanin abinda kayi mata, sannan sai a kira ka kaima aji naka bangaren, kafin lokacin duk kun huce. Sai a hada ku kuma a sasanta ku"

Na girgiza kaina. "Ni ba zan koma gidan sa ba aunty" na fada yadda nasan zai iya jiyo ni ta cikin wayar.

Ta kalle ni tana ce masa "ban san me kayi mata ba Doctor, amma koma menene ya bata mata rai sosai dan Jidda bata da zafi, tana da sanyin hali kamar yadda take da sanyin jiki. Allah dai ya kyauta kawai"

Sai ta katse wayar ta saka ta a jaka.

Na dauka zata saka ni a gaba da tambayoyi akan menene ya faru amma sai naga bata yi hakan ba, sai ta matsamin naci abinci. "Kina da danyen jego ba zaki zauna da yunwa ba, kin san Yasmin babu abinda take sha sai nono in baki ci abinci ba kuma ba zata samu ruwan nonon ba, dan haka ki daure ki ci ko dan saboda ita"

Na karbi plate din da take miko min na fara loma, ina taunawa ina jin kamar an hada miyar da ganyen madaci amma haka naci, for Yasmin. Na ajiye plate din na karbi juice din da ta zuba min a cup shima na shanye na ajiye mata cup din, ta kira mai aikinta ta lokacin Baba Dije tace ta kwashe kayan ni kuma tace inje in kwanta in huta.

Sai naji zuciyata ta danyi sanyi kadan, naji cewa at least da akwai inda ake sona kuma maybe zan iya samun nasara akan Umar, but sai dai ban iya yin baccin ba dan ina jin wannan ce rana ta farko a rayuwa ta dana taba kwana sir ido biyu ba tare dana rintsa ba.

Babu abinda nake yi sai saka da warwara akan abinda ya faru, da kuma akan abinda zai faru, ina ta tunanin ta yadda zan fara yi wa mutane bayanin abinda Umar ya aikata, can I really do it? Can my love for him let me do it? Sai kuma in tuna da hoton sa da Zuwaira sai inji ko gidan radiyo ne zan iya zuwa in yi sanarwa.

Da safe da kyar na tashi, ni kaina na san na fita daga hayyacina dan dana kalli mirror sai naga ma kamar bani ba ce ba, idanuwana duk sun jeme sun fada ciki, bakina ya bushe yayi kamar ma mai azumi.

Har daki Aunty ta aiko min da breakfast sannan ta dauki Yasmin ta tafi da ita dakinta tayi mata wanka ta shirya ta ta bawa Baba Dije ta goya ta sannan ta taho dakin da nake. Ta same ni nayi wanka ina shiryawa sai ta zauna a bakin gado tana jira na and I knew tazo jin dalili na na barin gidan mijina ne. But zan iya gaya mata kuwa?

Amma ai Aunty ce, kanwar mahaifiya ta ce uwa daya uba daya ina jin ita zan iya kira da second mother, kuma ina ganin a gurinta ne zan samu shawarar yadda zan tunkari wannan lamarin. Dan haka na zauna na bata labari tun daga A har Z. Tun daga zuwan Zuwaira gidan mu har hotunan data turo min.

Hankalin Aunty ya tashi, fiye da yadda nayi tunanin zai tashi, ta rinƙa jera salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne?" Na gyada kai da sauri, "wallahi Aunty, abinda ya faru kenan" sai kuma na fara kuka "Aunty ni ba zan iya cigaba da zama da Umar ba, not after what he did. Dan Allah ki taimaka min ki fada min yadda zanyi Abba ya fahimce ni ya raba auren nan"

Sai ta dafa kafada ta tana girgiza kanta "kar ki ce mu raba auren ki da Umar Jidda, Umar mutumin kirki ne kuma yana tsananin son ki duk munsan da wannan, in kince zaki rabu da Umar kika san wanda kuma zaki aura nan gaba shi menene nasa aibun. Eh ba ina nufin laifin Umar karami bane ba da zamu ture shi gefe amma ina nufin naki bangaren muma ji yanzu, watakila akwai abinda ke kanki baki sani ba tunda kafin ki taho din bai yi miki bayanin komai ba. Ki bari, daddyn Aira yana gida zan gaya masa duk halin da ake ciki, zan saka ya kira shi tunda ni macece ba zan iya wannan maganar da shi ba sai yayi masa nasa bayanin shima sannan sai mu hada ku muga yadda za'a bullowa lamarin. Amma kar ki sake zancen rabuwa, rabuwa is not a solution and will never be a solution"

Sai naji duk jikina yayi sanyi, murna ta ta koma ciki. "Aunty wallahi ba ki san halin Umar ba, in ya zauna ya kalallame ku wallahi zai iya juya maganar ma ace ni ce mai laifi"

Ta girgiza kai "ba kina da evidence dinki a hannunki ba? Sakunan da yarinyar ta turo miki da hotunan, kina da facebook account dinta dan haka za'a iya tracing dinta asan ko wacece ita. Babu wani juya magana da zai iya yi zuwa kanki" nayi shiru dai kawai na bar maganar amma a raina nasan ta fadi haka ne dan bata san waye Umar ba, bata san irin yawan fuskokin da yake da su ba. Ban kuma san menene plan dinsa mai yake shiryawa ba amma nasan tabbas yana can yana shirya wani abu.

Na lumshe ido na ina hango shi a raina, he is definitely frustrated, ya kira waya ta yafi sau dari maybe, amma nasan tashin hankalin sa ba wai nawa bane ba, tashin hankalin sa shine yawan adadin mutanen da zan gaya wa ko kuma in nunawa mummunan hotonsa. And maybe ma ba'a gida ya kwana ba, maybe a gidan Zuwaira ya kwana dan ya huce takaicin sa ya sha giyar sa ta dubu tunda yana ganin babu abinda zan iya yi masa.

Auntyn ta gaya wa daddyn Aira, bana gurin sanda ta gaya masa amma nasan abinda na fada mata shi zata gaya masa tare da fatan cewa shi zaiyi solving problem din, kamar yadda ta fada min ba ma ta son Umma ta sam da maganar ballantana Abba.

Ban san lokacin da ya nemi Umar suka yi magana ba. Ban kuma san a ina ne suka yi maganar ba sai da dare Aunty ta sake dawo wa ta same ni.

"Daddyn Aira ya kira Umar sunyi magana akan matsalar ku" sai tayi shiru bata cigaba ba, na dago kai ina kallon ta, ina ganin yadda yanayin ta ya chanja sosai sannan tace "yace shi sam bai san da wannan maganar ba"

Na dube ido "kinji ko? Kinji ko Aunty, na gaya miki da ma musawa zaiyi yace bai yi ba, wallahi kuma karya yake yi yayi din, wallahi karya yake yi Aunty" na fara kuka. Ta rike ni "kar ki tashi hankalin ki Jidda, in ma karya yake yi ai zamu tabbatar ko? Shi yace wai ita yarinyar tsohuwar budurwar sa ce tun kafin ku hadu, but sun dade da rabuwa kuma shi babu wani abu a zuciyarsa a game da ita ita kuma tana sonsa still and she sent him a message a wayarsa ke kuma kika gani shine kika tashi hankalin ki kika ce neman mata yake yi kika dauko hanya kika taho"

Na dafe kaina, bayan yi min ciki, dadin baki da yaudara, har akan karya za'a iya bawa Umar number yabo ta kasa.

Nace "Aunty wallahi karya yake yi" ta daga min hannu "ki daina cewa mijin ki yana karya, babu kyau yin hakan, idan ma ita yake yi ki bari gobe da safe daddyn Aira yace yazo zamu zauna tare da ku.

And I had another sleepless night. Yanxu ba wai abinda Umar ya aikata ne kadai ya hanani bacci ba har da ƙaryar da ya shirga. Shi gani yake yi bazan iya tona masa asiri ba ko menene? Zai sha mamaki kuwa.

Washegari ma kamar kullum da wuri Aunty ta tashe ni ta hada min ruwan wanka nayi sannan ta dauki Yasmin tayi mata wanka itama ta shirya ta, sai tace in sauka kasa muci abinci tare. Ina sauka na tarar da Aryan yana shirin fita school sai muka zauna yanata bani labarin makaranta and other stuffs da suka shafe shi wanda ni a lokacin ba wani fahimtar sa nake sosai ba dan hankali na yana wani gurin daban, haka muka ci abinci, nadan ci da yawa ranar saboda duk yunwa ta rarake min cikina kwana biyun nan.

Bayan mun gama ne Daddy ya leko daga kofar data hada wannan falon da nasa falon yace muzo Umar yazo, naji takaici ya kama ni na zuwan da yayi da sassafe wai dan ya nuna cewa ya damu dani ya damu ayi maganar. Sai na mika wa Aira Yasmin nace ta bawa Baba Dije ita ta goya ta ni kuma na hau sama da dauko wayata dana kashe na saka a cikin jaka tun da nazo gidan na yafa mayafi na nabi bayan Aunty muka tafi can.

Ina bude kofar naji kamshin turaren sa, naga yayi sauri ya mike "Jidda" ban amsa ba kuma ban kalli fuskar sa ba na tafi can karshen kujerun falon na zauna a kasa. Sai naga shima ya zauna a kasa dagadan gefe na kadan su kuma su Aunty suka zauna akan kujeru.

Daddy ya fara magana, ya fara jawo mana doguwar nasiha akan hakkokin aure da sauran su, sannan ya nuna mana muhimmancin zama muyi sulhu a tsakanin mu ba tare da mun kawo gida ba, ina jin Umar yana ta amsawa "insha Allah Daddy. Wannan shine na farko kuma insha Allah na karshe" a lokacin babu abinda naje so irin in zabga wa Umar harara amma banyi ba, my time will come.

Sai Daddy ya juyo kaina yace "auntyn ki ta fada mana duk abinda kika ce akan mijinki, shi kuma amma dana same shi da maganar sai yace min ba haka take ba, sai tace kince kina da shaida ko? Na gyada kai da sauri. "Eh Daddy, ina da shaida, akwai sakonnin da ita karuwar da yake nema ta turo min, a ciki har da hotunan su tare" hawaye ya zubo min saboda tuno wada nayi da munin hotunan

Daddy ya juya kan Umar "Doctor kaji abinda tace, ka yarda da maganar ta? Yadda ba sai munga shaidar ta ba sai mu san ta yadda zamu bullowa al'amarin" ya girgiza kai "ni bansan abinda take magana akai ba Daddy. Abinda na sani shine yarinya ce da na nema a baya ta turo min Friday message, shine ita kuma ta dauki wayata ta gani kawai sai tayi fushi, ina fita kuma sai na dawo na tarar bata nan"

Na daga kai da sauri na kalle shi, muka hada ido sai yayi saurin dauke kansa gefe.

Duk da cewa raina a tsananin bace yake sai da na lura da wata irin rama da wani irin baki da fuskar sa tayi. Bakinsa yafi nawa bushewa. Kayan jikinsa a cukurkude dan ina kyautata zaton cewa da su ya kwana a jikinsa kuma daya tashi baiyi wanka ba ballantana ya chanja su.

Amma ko kadan banji tausayin sa ba dan nafi jin tausayin kaina da kuma halin da nake ciki

Na juya ina kallon Daddy "wallahi Daddy karya...... wallahi Daddy ba haka bane ba, ba gaskiya yake fada ba" Daddy yace "kiyi shiru Jidda, kar ki sake magana sai na tambaye ki" na goge hawaye na ina jin daci a zuciyata sai daddyn yace "ina shaidar da kika ce kina da ita?"

Na dauko wayata dana ajiye a gefe na, hannuna yana karkarwa ina tambayar kaina in abinda zanyi shine dai dai, da ace ya amsa laifinsa shikenan babu wanda zai ga hoton sa amma yanzu da yaki karbar laifinsa kuma har yake min sharri tabbas bani da option daya wuce in nuna wa su Daddy maganganun da kuma hoton.

Ina jin idonsa a kaina, har yanzu maybe yana tunanin zan rufa masa asiri ne in karbi laifin da ba nawa ba duk kuwa da irin abinda yayi min?am not that stupid.

Na kunna wayar, na barta ta gama kamawa sannan na shiga facebook inda anan ne sakonnin da kuma hotunan suke, sako daya ne ba'a facebook ta turo min shi ba wanda ta kira ni da suna Baby Dove, shi kuma na rasa shi tun a waccan wayar dana fasa.

Ina shiga facebook direct messenger na shiga ina neman sunanta dan ita ce last person data turo min message kafin in kashe wayata.

Sai dai me?

Ko me irin

32 / 106