Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
agogo. Bai amsa mata ba yace "ina Mama? Shiga ki kira ta" sai ya zauna akan kujera tare da dafe kansa da hannu biyu da yake jin yana sara masa kamar zai bar jikinsa. Me Jidda take tunani ne wai? Dan me yasa zata gudu bayan aurensa kaddarar ta ne kamar yadda shima halinsa yake kaddarar sa?
Hannun mutum yaji a kafadar sa, yayi saurin dago kai yaga Mama da Mufida a tsaye a gaban sa, shi bai ma san sanda suka shigo ba. Mama tana yi masa magana amma sai yaji baya jin ta sosai, nesa nesa yake jin muryar ta amma daga dukkan alamu tambayar sa take yi me yake damunsa.
"Mama Jidda ta tafi, ta dauki Yasmin da Asad ta tafi bansan inda ta tafi ba"
Ta zauna kusa dashi itama nata hankalin ya fara tashi "ban gane ba. Ta tafi kamar yaya? Fada kuka yi? Bata gidan su?"
Sai kawai ya mayar da idonsa ya rufe sannan ya jingina kansa da jikin kafadar ta yayi shiru, tana jin yadda jikinsa yake hucin zafi, tace da Mufida ta bata aron wayarta da take hannun ta amma maimakon ta bata sai ta wuce daki ta dauko mata tata ta miko mata, Umma ta kira, ita kuma Mufida ta kira number din Jidda sai ta jita a kashe, tace "wayar bata shiga ai" a hankali yace "ta kashe ai, da wayar tana shiga amma yanzu ta kashe ta"
Mama ta fara fada "kuma dan kunyi fada sai ta debi yara ta tafi? Tayi ta tafiya mana ai ba ita kadai ce mace a duniya ba amma ta dawo maka da yayanka tunda dai ba dasu aka auro ta ba. Ni ban taba ganin irin wannan rayuwa ba. Ni ban taba ganin mata irin taka ba, mace babu abinda aka rage ta dashi amma ba zata bar mijinta ya huta ba? Jarabar yau da ban ta gobe daban? Ita bata yi kiba ba bata bar ka kayi kiba ba gashi nan duk kayi duhu ka lalace"
Sai kuma ta dora hannunta a goshinsa tana jin hankalin ta yana kara tashi "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. So take ta kashe min kai, abinda take so kenan ka mutu kabar mata duniyar"
Ya zame daga jikinta ya kwanta akan kujerar yayinda ita kuma ta kira Umma suka fara mayar da abinda ya faru
Jin bata yi masa zancen Asabe ba ya tabbatar masa da cewa yarinyar ba nan gidan ta taho ba.
Bayan Mama ta gama wayar sai ta saka Mufida ta kira Doctor Bashir tace yazo ya duba Umar bashi da lafiya sannan ita kuma ta kira Baba tana gaya masa abinda yake faruwa. Bata ma tuna da wata Asabe ba ballantana ta nemi inda take tunda matar gidan bata nan.
Umar bai taba ganin tashin hankali irin na ranar ba kamar yadda bai taba ganin dogo kuma bakin dare irin wannan ba, shi gani ma yayi kamar batteries din jikin duk agogunan gidan duk sun mutu dan gani yayi kamar daren a tsaye yake shak baya tafiya. Kamar yadda bai yi bacci ba haka bai bar mama da Mufida sunyi bacci ba, a daren bayan Bashir yazo ya duba shi sai ya saka Mufida ta rubuta masa list na dukkan kawayen Jidda da ta sani da kuma addreses din su, haka ta zauna ta rubuta masa list, gari yana wayewa ya saka ta fara bin su daya bayan daya tana kira tana tambayar su ko sun ga ko kuma sunyi waya da Jidda, sannan ta roke su da in sun ganta ko sun ji labarin wanda ya ganta su kira ta.
Wadanda kuma bata samu a waya ba sai Umar ya kira Bashir yazo suka fita tare har da Mufida suna bin su zuwa gidajen su. Daya bayan daya. Amma babu wadda take da labarin Jidda. Basu dawo gida ba sai dare, kowa ya kalli Umar a cikin kwana daya da wuni dayan nan sai ya tausaya masa, gabakidaya ya fita daga hayyacin sa in kana masa magana ma ba ganewa yake yi ba. Dole doctor Bashir ya dawo dashi gida yace ya kwanta amma Umar yaki yarda sai da ya ce masa "in ba ka kwanta nayi maka allura kayi bacci ba, zaka fadi ka mutu, ko sun dawo you won't be there to see them" wannan ya saka shi yadda akayi masa allurar, Bashir ya rufe shi a tsohon dakinsa dake gidan su tare da cewa
"Allah na gode maka da baka dora min wannan cutar ba wai ita soyayya"
Bashir da Mufida ne suka karasa zagayen sauran kawayen sannan suka dawo gida. A ranar Baba ya shigo Kano shima cikin tashin hankali da alhinin faruwar wannan abu, ya kuma zarce gidan su Jidda gurin Abba suka yi maganar sosai, sai dai daga shi har Abban basu san takamaiman abinda ya hada Jidda da Umar har yayi tsamari haka ba, a lokacin ne kuma Baba ya nuna wa Abba rashin dacewar kin sauraron korafin ta da tazo gida "da ka tsaya ka saurare ta da bamu kai ga wannan matsayin ba, yanzu rashin sanin halin da suke ciki shine babban tashin hankalin, ga rayuwa yadda ta zama duniya ta cika da marasa imani. Allah dai ya jishe mu alkhairi kawai"
Sai Abba yaji wani abu ya tsaya masa a rai, tabbas da ya tsaya ya saurare ta da ba'a kai ga hakan ba. Yanzu in wani mummunan abin ya same ta ko ya sami yayan da ta tafi dasu fa? Anya kuwa ba za'a raba alhakin har da shi ba a matsayin sa na ubanta. To wai ma menene ya hada ta da mijinta da ta gwammace ta gudu ta shiga duniya akan ta koma gidansa?
Tambayar da Baba yayi wa Umar kenan yana komawa gida. "Me ya hada ku da har tayi yaji ta tafi gida?"
Ya shafa kansa, ya shirya wa wannan tambayar tunda yasan dole za'a yi masa ita, in ma kuma ba'a yi masa ita ba Asabe zata bayyana da nata part of the story din, gwara yayi sauri ya shigar da nasa kafin nata.
Yace "nima Baba takamaimai bansan abinda ya faru ba tunda taki tsayawa tayi min bayani, kawai ta tambaye ni ne wai menene hadi na da wannan yarinyar da Mama ta kai gidan. Na gaya mata babu komai sai ta ki yarda ta kama kuka ta hada kaya ta tafi gida"
Mama tayi saurin cewa "kaji ko? Na gaya maka matsalar yarinyar nan shegen kishi ne da ita, bata son kowa ya rabe shi idan ba ita ba, dan na kai musu yar aiki wato shine take son ta tsiri maganar da zata saka a dauke yarinyar daga gidan. To Allah ya dawo da ita lafiya daga duk inda taje ma, aure zaka yi, in yaso ta hadiyi zuciya ta mutu dan bakin ciki"
Baba ya girgiza kai "uhm uhm Faruq, in babu rami me ya kawo zancen rami? Kai menene hadin ka da yarinyar" Umar ya girgiza kai kamar zai yi kuka "Baba wallahi babu komai. Yar maigadin gidan nan ce fa. Baba kaga yarinyar kuwa? Ita Jiddan ai ta san ko magana bana yiwa yarinyar ban san me tace mata ba, ban san kuma me yasa ta yarda da abinda tace mata din ba".
Sai a lokacin aka tuna da Asabe, Umar yace shi bai san inda tayi ba shi bai ma lura da ko ta fita daga gidan ko a'a ba, aka tambayi iyayenta suma bata je musu ba.
Washegari kuma Umar ya nemi sister Aisha, kawar Jidda da suka yi nursing school tare ya nemi data bincika masa kawayen su na nan bangaren ko akwai wanda yaji labarin Jidda. Ranar ita ma kamar wadda ta gabace ta, wuni suka yi suna yawo shi da Bashir, gida gida, loko loko duk inda suka san Jidda ta sani, ciki harda abokan aikin ta, duk wanda suka je kuma sai su nemi ya gaya musu wani ko wata da suka san Jidda tana mu'amala da shi.
Dogon list suka ji suna cancelling duk wanda suka gama dashi sai kuma su kara da wani sunan. Ranar ma da kyar Bashir ya dawo da Umar gida dan yaga alamar zai ce su fara bi gida gida ne, shi kuwa dama already Umar din ya fara bashi haushi, shi bai ga abin tayar da hankali ba, ai tana da hankali kuma ta san me take yi, in ta gaji da gudun ai zata dawo ne dan kanta tunda dai ba zata cigaba da rayuwa da aure a kanta ba.
But ko da Umar ya kwanta babu bacci a idonsa, sanda baccin ya sace shi kuwa munanan mafarkai yayi tayi da Jidda da yaran su a wani hali marar kyau, dole ya hakura da baccin ya tashi, zai iya bayar da ransa a lokacin in dai zai san halin da suke ciki, in dai zai san suna raye kuma suna cikin koshin lafiya.
Ya dauko wayarsa yayi ta rubutu yana aikawa number dinta, hoping ko zata kunna wayarta ta karanta ta bashi amsa ko da da alphabet daya ne, ko da da kalma daya marar ma'ana ne, burinsa kawai shine yasan cewa suna lafiya lau. A lokacin ya dauki hoton band din ta da yake hannunsa yayi posting a instagram
"Be safe. Please"
Ya rubuta, hoping ko zata gani ta tausaya masa ta yi replying messages dinsa. Shi ko da wannan kwana biyun ta barshi tabbas ya wahala, tabbas yaji jiki, amma abinda bai sani ba a lokacin shine wannan kwana biyun wasa farin girki ne.
Haka sati na daya yazo ya wuce, a cikin satin sai da Umar ya dangana da gadon asibiti, duk kuwa wanda ya san Umar inya ganshi sai ya tausaya masa, tabbas babu tashin hankalin da ya wuce ace iyalinka sun bata ba'a san inda suke ba.
Sai dai a karshen satin ne aka kira shi aka sanar da shi cewa an aiko daga sama an karbar bata leave a gurin aiki. Sakon ya kwantar masa da hankali ya fahimci cewa tana lafiya, sai dai kuma ya kara tayar masa da hankalin neman ta. Amma duk yadda yayi kokarin sanin wanda ya aiko aka karbar mata din abin ya gagara, tun daga lokacin ya kullaci one particular person da yaki bashi information din, yana ganin bai kyauta masa ba musamman tunda yasan matarsa ce, kuma ya san nemanta yake yi, amma still yaki gaya masa yace shima nasa aikin is on the line in ya fada.
Tun daga nan sai ya fara zurfafa binciken sa zuwa sama, ya fahimci duk hannun wanda take to yana da say a gwamnati ko kuma yana da kudi, bai kuma san wani wanda Jidda ya sani mai irin wannan matsayin ba, wannan ya sa kishi ya turnike shi babu abinda baya aiyanawa, maybe ma a hanya suka hadu kawai ya ga kyakykyawar mace tana bukatar taimako shine ya dauke ta ya kaita gidan sa. Wannan tunanin kadai ya kusa saka Umar ya hadiyi zuciya ya zama gawa.
Sai damuwar sa ta tashi daga kan ko suna lafiya ya koma kan abin abinda Jidda take yi a inda take.
Time went by. Har akayi wata daya da tafiyar su. A lokacin ne yaji Baba yana zancen suna shiryawa da Abba zasu tura Umma da Tahir zuws Ethiopia neman Jidda a can, duk da dai anyi waya da su kuma sunce bata je ba amma hankalin su bai kwanta ba gwara aje a gani.
Sai dai shi Umar bai damu da maganar ba dan jikin sa baya bashi ta bar kasar, yafi tunanin tana kasar nan kuma tana hannun wani babban mutum, and that's making him as frustrated as frustration goes.
Kawai kuma sai ga query daga office, wai baya zuwa aiki, shi yanzu ba aiki ne a gabansa ba dan har mantawa yake yi cewa yana da aiki. Amma abinda yafi kona masa rai shine the query was signed by the same person daya hana shi information akan inda Jidda take.
Sai kawai ya dauki mota yaje asibitin ya je har office din mutumin yayi masa kwararen naushin da suka fitar masa da jini sannan ya shiga motarsa ya dawo gida. Washegari suka aiko masa da takardar kora daga aiki.
And washegarin ne kuma da daddare yana kwance a dakin da ya mayar nasa a cikin gidan su kira ya shigo wayarsa.
Ya mike zaune a tsorace yana mayar da numfashi saboda jin kidan da yayi, kidan da ya saka mata ne. Ya dauki wayar da sauri yana kallon screen din "Baby Dove" yaga sunan ta rangadadau a jiki. Cikin karkarwar hannu yayi sliding ya dauka tare da saka wa a kunnen sa, bracing himself for anything, maybe ma ransom za'a nema or worst.
Amma sai yaji muryar diyarsa, hasken idaniyar sa "Daddy?"
Ya mike tsaye kamar wanda akayi wa allura
"Yasmin! Baby girl is this really you? Oh my God!"
"Daddy ka zo ka dauke ni, ni gurinka nake son tahowa bana son gidan nan" ta fada kamar zata yi kuka.
Yaji kamar zuciyar sa zata fito, kalmomin sun makale ma sun ki fitowa
"A ina kuke? A ina kuke Yasmin ki gaya min yanzu zan zo in taho da ku, are you okay? Ina Asad? Lfy lau kuke?"
Tace "lafiya lau muke Daddy, amma ni da Asad muna kuka kullum, mommy ma tana kuka a toilet, kuma tace ba zamu dawo ba. Shine yanzu ta fita gurin kawarta na dauko wayarta a jaka na kirawo ka kazo ka tafi da mu"
Ya lumshe idonsa ya bude, baya jin akwai wani abu da za'a gaya masa a rayuwa da ya kai wannan dadi, na farko they are okay, na biyu mentioning din kawa da Yasmin tayi ya nuna masa macece ta dauke su ba namiji ba.
"Ki gaya min a ina kuke, and I will come get you a yau kinji?"
Tace "nima bansan inda muke ba. A wani gida ne kawai" yace "kun hau jirgi da zaku je gidan?" Tace "a'a" yace "mota kuka shiga?" Ta sake cewa "a'a. Adaidaita sahu ne" ya gyada kai, suna cikin garin kano kenan.
"Kin san sunan unguwar da kuke?" Tace "a'a ban sani ba" yace "ya gidan yake? Yana da girma? Yana da kyau" Tace "eh gidan mai kyau ne daddy har da swimming pool" yace "akwai yara a gidan? Kawar mommy din tanada yaya?" Tace "eh akwai twin babies" ya sake tambaya, the most important question "ya sunan kawar mommy din? Kin sani?" Tace "sunanta Aunty Halima".
Sai kuma yaji tayi kara, sannan yaji muryar da yayi wata guda yana fatan ji, yayi wata guda rabon da yaji, muryar Jidda ta yi wa Yasmin tsawa "Yasmin!" Sai kuma yaji kukan Yasmin tana rokon kar a dake ta, ji yayi kamar zai shiga wayar, amma tunda ba zai iya haka ba sai ya bige da magiyar kar a dakar masa ya, bai sani ba ko ta jishi ko bata ji shi ba, ya dai ji ta kashe wayar.
Ya zauna akan gadon tare da dafe kansa da hannu biyu, tana can tana dukanta ya sani, Allah sarki innocent babyn girl dinsa. Sai kuma ya kuma mike wa.
"Halima" ya fada. "I am coming for you"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
Forgive the typos as always
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*Asabe 2*
A daren sai na kasa bacci, ina ta tunanin labaran da na samu yanzu daga gurin mijin Diyam, wai da gaske Umma ta tafi garin su? For the first time zata ga tushen ta da yanuwanta wadanda auren Abba ya hana ta haduwa da su? Sannan kuma wai da gaske Umar ya rasa aikin sa? I knew how much his job means to him dan yana enjoying aikinsa sosai amma me ya kai shi zuwa ya kama mutum ya daka? Saboda ya rubuta masa query akan laifin da shi ya aikata? Kamar yadda na riga na sani tun da na taho tabbas nasan zaiyi hauka amma ban dauka haukan har zai kai ga yi masa asarar aikin sa ba.
Sai kuma nayi tsaki, why did I even care ne ma ko ya mutu ko yayi rai duk daya a gurina, wani bangaren ma sai ince dama dai ya mutum, shikenan na huta da alakakai din auren sa kuma maybe his secrets will be buried with him shikenan yayana sun huta da tonon silili.
Sai kuma nayi lissafin wayar da Yasmin tayi masa, how much did she tell him? How much did she really know? Dole zan gaya wa Diyam mu san yadda zamuyi dan in dai ta gaya masa wani clue mai kyau tabbas a gobe ma zai iya zuwa gidan. Ni kuma yanzu I am not ready to face him, dan ba zance I am not ready to go back to him ba tunda na riga na yanke hukuncin ba zan koma ba kuma I will stand by it.
Da safe na samu Diyam a kitchen din kasa kamar yadda muka saba duk safiya, muka gaisa sai na karbi aikin da take yi na fara tayata sannan na fada mata abinda ya faru jiya tsakanin Yasmin da babanta. Ta tsorata sosai da maganar. "zai iya zuwa gidan nan yau" na fada mata. Ta ajiye abin hannunta "yanzu ya za'a yi kenan? Ko gurin zama zamu chanja miki? Bara in yiwa Sadauki magana in ya yarda sai mu shirya muga inda zaki koma" nayi shiru amma ni a raina bana son komawa ko ina, saboda komawa wani guri zai kara rikita yaran su kasa gane me suke ciki, kuma ba lallai ne mu samu wani gurin da zamu zauna comfortably kamar nan gidan ba.
And I told her my fear, "ni ba wai ganin nawa ne bana son yayi ba, dan ko zai daure min kafa ta yake ja na a kasa ba zan koma gidan