Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
kace kasa, babu abinda kika iya sai dai ki ci ki koshi ki kwanta kiyi ta bacci kina munshari, common abinci ba zaki iya tashi ki dafa wa yara ba bayan na fita na nemo duk abinda kuke bukata babu abinda na rage ku dashi. Ke dai Allah wadaran halinki wallahi" haka ya kare mata tatas bai kodamu da idon mu mu baki ba ballantana kishiyar ta ta lokacin balle kananan yaran da basu fara zuwa makaranta ba. Har ya gama bata ce masa komai ba ya fita sannan ta tashi ta shiga daki, na tabbatar kuka taje tayi, ni kaina da ba ni akayi wa fadan ba saboda raguwar zuciya ce da ni sai naji hawaye yana bin fuska ta.
Bayan mun shiga dakin ne muka tarar da ita ta zabga tagumi, absentmindedly tace "wallahi, ganin idon Abba ne kawai yake zaune dani a cikin gidan nan, wallahi duk ranar daya fadi ya mutu in na tafi gida na tafi kenan sai dai a raba gidan a bani rabona ko daki daya ne in zauna ni da yarana, in yaso ko kosai in ringa soyawa a bakin layi ina ciyar dasu" sai muka kalli juna ni da Farhan, duk da cewa ba zamu iya kwatanta halin da take ciki ba amma munsan abin ya munana.
A gidan Mama Hadiza kuma matsalar abinci ne, duk sun rame sun kanjame ita da ƴaƴanta kamar wasu kajin mayu. Maigidan kullum zai yi awo na shinkafa ko hatsi ya kawo daga nan kuma babu abinda zai kara akai, tun daga coal din da take girki da shi har zuwa kan maggi ita zata nema ta siya, kuma yana sane da cewa bata aikin fari balle na ja. Yawan bani banin ta ne ya saka Abba ya siya mata keken dinki duk a kokarin sa na ganin cewa ta zauna a gidan mijinta bata fito ba, to wannan ne ya taimaka mata take dan samun na biyan bukatu, ƙafafuwan ta har sun kumbura saboda zaman kan keke.
Muna zuwa bayan mun gaishe ta ta miko wa Farhan hannu "autar Hajiya ina sakon da Hajiya tace zaki kawo min?" Farhan ta dauko kudi a jakarta ta mika mata yan dubu dubu guda biyu. Ta karba tana leka hanya dan kar mijin ya gani, "yanzu idan da ace Allah ya kiyaye zai ga wadannan kudin da sai munyi sati bai bamu komai ba yace ai ya gan ni da yan dubu dubu, wannan kudin kuwa yanzu da kyar zai ishe mu siyan mai da barkonon da zamu kwana biyu muna amfani dasu, ga sabulun wankan mu ma ya kare"
Farhan tace "kai Mama Hadiza, yanzu har sabulun wanka ma baku dashi? Duk ina kudin dinkin naki?" Tace "hmmm, dinkin dai ba ina yi ne kawai ba? Duk fa a bashi yake karewa. Wani lokacin sai in hana idona bacci inyi dinki da fatan da safe in an zo karba zamu samu abin karyawa amma in an zo karba sai ace bashi, daga nan kuma shikenan sai dai ayi ta bayar da kudin kadan kadan wata ma sai dai in bita da Allah ya isa".
Gidan yaya Hudallah ne mai dan dama dama, gidan ta fes fes, ita da yarta ma haka, ga abinci nan a wadace, kuma ita kadai ce ta samu nasarar ci gaba da karatu duk da dai itama iyakacin ta diploma, sai dai kadaici. Muna zuwa ta rungume mu tana ta murna "amma dai sati biyu zakuyi ko?" Duk muka kwashe da dariya "kwana daya zamuyi" na fada ina kokarin tsayar da dariya ta amma sai na cigaba ganin yadda tayi da fuska kamar zata yi kuka "haba dai kwana daya. Ni da nake saka ran idan kunzo zan rike ku ku cigaba da zama anan tunda babu abinda kuke yi a gidan? Ni kuma gani kadaici yana neman zautani?" Mijinta a Abuja yake aiki kuma baya zuwa kano sai bayan sati bibbiyu, shtayi tayi kuma ya mayar da su can yaki yace rayuwar Abuja akwai tsada.
Ta cigaba da mita "na gaji da zama ni kadai wallahi, kuma nayi nayi dashi ya barni in nemi aiki ko private school ne in ringa teaching ina samun yar 10-15k dina amma yaki, wai private basa biyan kudi da yawa sai dai in bari ya nemar min government, aikin gwamnati kuwa a zamanin nan masu degree da masters ma nema suke yi sun rasa ballantana mu masu diploma".
A gidan tane muka fi samun sakewa mukayi hira sosai dan da kyar mukayi bacci da daddare tana ta dora mana darasi.
"Allah dai ya taimake ku ya dora ku akan Abba ya barku kuyi karatun nan na zamani kuma, dan wallahi yawancin mazan nan masu alkawarin zasu bar matan su suyi karatu karya suke yi" sai na tuno da maganar mu da Musa, ta cigaba "kuma bara in baku shawara, in kun tashi zaben miji ku zabi mai dan maiko maiko, dan shegu duk halinsu daya, amma da kiyi kuka a gaban murhun itace gwara kiyi a gaban gas cooker ko?" Duk muka yi dariya ta bata rai tace "am serious fa, ku daina dariya, duk ba kirki ne dasu ba, wani talakan ma yafi mai kudin iya shege dan idan talaucin sa ya dame shi sai ya dawo kan matar ya huce. Dan haka duk ranar da Abba ya kirawo ku yace ku fito da miji to ku duba a cikin samarin ku ku ga wanda yafi maiko sai ku zabe shi, musamman ke Jidda, dan wallahi fuskarki da jikin ki ba irin na matan talakawa bane ba, na matan manya ne" ta jawo ni na zauna kusa da ita tace "kinga, akwai wani aboki ko kuma in ce ogan Abban Sudais da suke tare a Abuja, ranar nan Abban Sudais ya gaya min wai yana neman mata yana so yayi ta biyu ya tafi da ita can dan matarsa tayi girma ta tara iyali ba zai iya tafiya can da ita ba, ga kuma tafiye tafiyen da yake yi zuwa kasashen duniya duk ba zai iya yi da matar sa ba kin gane? Shine kawai naji ina yi miki sha'awar aurensa wallahi, na san yana ganin ki zai amince dan dama irin ku yake nema, kar ki wani damu da babba ne dan sai yafi ma saurayin kula da ke da tarairayar ki........."
Ta cigaba da maganganun ta amma ni hankali na ya tafi wani gurin daban, ina duba rayuwar yayye na mata ne, irin jouney din da suka samu kansu a ciki sai na fara wondering what my own jouney will be, wanne kalubale ne ni kuma zan fuskanta a nawa gidan auren?
Mun zagaya suma mazan kamar yadda muka zagaya matan, sai dai ni duk banji wani dadin ziyarar sosai ba dan ban saba da matan su ba sai dai gidan yaya Mukhtar wanda bai jima da aure ba, amaryar sa Aunty Halima tana da kirki sosai kuma munyi dace halin mu na karatun hausa novels yazo daya, muka yi ta hirar littattafai da kuma marubuta wadanda muka sani, sai dai kuma yanzu ita ta daina karanta published novels ta dawo karanta online ones, ni kuma tunda ba waya ce dani ba ban ma san ana rubutu online din ba.
"Kuma Aunty Halima suma kamar bugaggu ne?" Tace "sosai ma, akwai online writers da suka iya labari sosai wadanda in kika fara karanta books din su ba zaki daina ba ko da kuwa sun mayar da su na siyarwa" na bata fuska nace "na siyarwa kuma Aunty Halima? Ta yaya za'a siyar da littafi online?" Ta fara yi min bayanin WhatsApp groups da Okada books da Wattpad amma ni tunda duk ba sanin su nayi ba ban wani gane sosai ba. Nace "kuma nawa kuke siya?" Tace "wani 300 wani kuma 200, most dai haka kudin yake" Farhan tace "amma yayi tsada, ji nake bugaggen ma haka ake siyar dashi, wannan kuma na waya in wayar ta bata fa shikenan ka rasa shi" Aunty Halima tace "bai yi tsada ba, ni yayi arha ma a ganina sosai saboda yawanci littafi daya suke yi babu zancen part one two three kamar yadda bigaggun littattafai suke, wasu ma har part four zaki ga, kuma ki sayi kowanne dari uku, kusan dubu daya da wani abun kenan a labari daya. Sannan kuma maganar bata ni ina siya nake kai shi e-mail dina in ajiye a can, yadda ko waya nawa na chanja yana nan a ajjiye babu inda za shi"
Na fahimci wannan bayanin duk da dai ban gane zancen e-mail din ba. Sai dai kawai nace "duk ranar da nayi waya zan zo ki koya min duk wadannan abubuwan sannan ki tura min duk books din inyi ta karantawa" tace "Allah ya kaimu kanwata" muna cikin hirar yaya Mukhtar ya shigo, sai take yi masa korafin ya kamata a ce an siya mana waya "yanxu ace yammata babu waya? Ta yaya zasu yi samari?" Ya bude baki "waya? Rufa min asiri, ai wadannan yammatan haka zaki gansu kuma haka zaki kyale su, duk wanda ya sake ya siya musu waya to rigima shi da Abba har koton koli" muka yi dariya baki daya, sai ya zauna a tare damu muka cigaba da hirar Abba da irin dokokin sa.
Daga nan munje gidan gwoggo Habiba, dukkan ƴaƴan ta sun yi aure kuma suna kula da ita sosai dan kusan babu abinda ta nema ta rasa, daga ita a gidan sai mijinta da yar autarta, Jamila.
Jamila kyakykyawar budurwa ce yar gayu mai ji da yammatanci, a lokacin tana shekarar ta ta karshe a jami'ar Bayero, tunda muka je gidan muke ta kallon ta cike da sha'awa ni da Farhan, komai na yaya Jamila burge mu yake yi, yadda take kwalliya da dressing, yadda take magana ana yi ana jefa turanci a ciki da tafiya kamar ana tausayin kasa, a ranmu sai muke ji ina ma dai mune muka samu wayewa irin tata. Sai dai kuma a cikin kwana biyun da mukayi a gidan su muka lura da irin tsananin soyayyar da yake tsakanin yaya Jamila da wayarta. Ko da yaushe tana hannunta tana daddanna wa tana murmushi, ko ita da waye oho. Cikin dare kuwa har mu farka fitsari tana cike da waya a kunne tana hira kasa kasa yadda mu da muke daki daya gado daya bama fahimtar abinda take cewa. Bamu tashi tabbatar da zargin mu a kanta ba sai da muka ga ta chanchada kwalliya ta gayawa gwoggo cewa zasu fita unguwa da wani friend dinta, irin yadda tayi maganar kamar mai sanarwa ba wai neman izni ba sannan ta fice ba tare da ta jira amsa ba, har sai da muka yi bacci sannan ta dawo ta kwanta tare da cigaba da magana a cikin wayarta tana dariya kasa kasa. "Yes, I really enjoyed myself" ta fada a hankali. Sai muka kalli juna ni da Farhan sannan muka gyada wa juna kai alamar duk irin tunani daya muke yi. Sai na kwanta ina tunani a raina "shin irin wannan wayewar da irin wannan rayuwar Abba yake gudar mana shi yasa yake takura mu? In haka ne shima yana da tasa gaskiyar kenan.
Gidan Aunty Afia (Mami) shine gida na karshe da muka je. Tun a hanya nake ta zumudin ganinta, ina balain son ta har cikin raina ita da yayanta, Aira da Aarif. Aira kusan sa'a ta ce, Aarif kuma da kadan ya girmi Amira. Ni a idona gani nake kamar Mami da yaran ta sunfi kowa kyau a duniya amma sai inji mutane suna cewa wai kamar mu daya da Aira wai kamar an tsaga kara ni kuma dariya nake yi in aka fadi haka.
Tun daga gate mai gadi ya karbi kayan mu yana mana sannu da zuwa, ya sanni kuma yasan dangantaka ta da gidan. Mijin Aunty mai kudi ne, gidan su kato mai cike da duk abinda suke bukata. Muna shiga na tafi da gudu jikinta na rungume ta ina jin hawaye yana taruwa a idona, ta rungume ni ta na shafa bayana tana dariya, sai kuma ta dago fuskata tana kalla tace "sai yau babanki ya ga damar barin ki ki zo ki ganni ko? Kema so yake ya mayar dake kamar Ayesha ko? So yake ki zama daddawar cikin daki ko? To Allah ya fishi" nayi dariya ina goge hawaye na, "kai Aunty Abba ne fa" tace "Abban ki ne ai ba nawa ba. Tun da ya raba yaruwata da kowa nata sai shi kadai ai nima ba zan raga masa ko inji nauyin sa ba. Wannan ne yasa baya son kuke zuwa gurina" na yi kokarin kawar da maganar ta hanyar fara neman yanuwana. "Aira! Arif!" Tayi dariya suna islamiyya, zasu dawo ai su same ku" sai a lokacin Farhan ta samu ta gaishe ta, ta amsa mata babu yabo babu fallasa sannan ta kira masu aiki ta bada umarnin suyi entertaining din mu. Muna cin abinci su Aira suka dawo nan take muka cika gidan da hayaniya da murnar ganin juna.
Kwana dayan da mukayi a gidan sai naji kamar second daya ne, nan da nan wai har dare yayi kuma har gari ya waye. Duk da cewa ba wani baccin kirki mukayi ba dan kusan raba dare mukayi da Aunty tana bani labarin yanuwanmu da yadda take so watarana Abba ya bar mu muje mu gansu. "insecurity ne yake damun babanku, shi kansa yasan Aysha ba sa'ar auren sa bace ba amma ta dage lallai sai shi, to tsoro yake yi kuma kar takoma cikin dangin tata guje shi, kuma kuma yana tsoron kar kuje can idon ku ya bude ku fi karfinsa, wannan shine matsalar sa. Amma kinga yanzu in kika yi aure ai kin tashi daga ikonsa kin koma ikon mijinki kuma zaki ke zumunci damu yadda kike so insha Allah. Wai in tambaye ki mana, akwai wani ne yanzu da yake zuwa gurinki?"
Nayi shiru ina tunani, Musa dai bana son sa kuma bana jin ya kamata in gayawa Aunty labarin sa, Umar kuma ban ma san menene matsaya a tsakanin mu ba. Na girgiza kai "babu kowa Aunty" ta gyada kai "to Allah ya kawo nagari. Ni in a so nane ma nafi son kiyi aure a dangin mu dan mu karfafa zumuncin mu, amma babu wanda yasan ki a can ballantana ya ce yana son ki"
A ranar da muka dawo gida, bayan mun gama murna da gaishe gaishe sai na ja Amira gefe "ke! Sanda ba ma nan babu wanda yazo nemana?" Tace "a cikin gida ko a waje?" na sosa kai "a ko'ina ma" tayi dariya "wai Musa? Zuwansa biyu fa, ana biyun Umma tace inje in gaya masa ranar da zaku dawo dan kar yayi ta zarya" naji raina ya fara baci duk da babu abinda Musa yayi na bacin rai.
"Bayan shi babu wanda ya zo?" Ta girgiza kanta. "Babu kuma wanda ya kira Umma yana nemana?" Ta kuma girgiza kai "ni dai bansan kowa ba, sai dai in Umma zaki tambaya ko an kira sanda bana nan" nayi saurin cewa "a'a, shikenan" sai kuma na wayance dan bana son tayi ta yi min tambayoyi "kinsan number dinta na bawa kawayena a makaranta, to ina tunanin ko wasu daga ciki sun kira ta ne."
Amma duk da wannan interview din da nayi wa Amira ban hakura ba sai da nayi ta duba call history din Umma wai ko ya kira bata dauka ba kuma bata bi ba, sai dai babu wadansu missed calls daga unknown number, kuma babu daga number din Mufida. Na ajiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya. "Ya fasa" na fada wa kai na, "dama karya yake yi" na maimaita. Sai dai kuma zuciya ta taki amincewa da wannan musamman idan na tuna da abinda na gani a idonsa, it looked so real.
Da dare ina tsakar gida Umma ta kira ni ta gaya min cewa Mufida ta kira ni yanzu, da sauri na karbi wayar "Allah sarki Mufida, bara in kira ta mu gaisa" sai dai a wani bangare na raina ina fatan ba Mufidan bace ba. Ina kira kuwa ta dauka, muka yi ta hira tana bani labarin hutun da suke yi a Lagos gabakidayan su, amma ko a cikin magana bata ambaci ko da sunan yaya Doctor ba nima kuma ban tambayeta ba.
Sai dai washegari da yamma ina wanke wanke sai ga dan aike. "Wai ana sallama da Jidda" naji raina ya baci, naki bashi amsa ma saboda takaici sai da Umma ta leko tace "kaje kace tana zuwa" ta kalle ni "baki ji ana magana bane ba? Yaron nan zuwansa biyu ba kya nan kuma ni nace masa ya dawo yau kafin nan kin dawo" na mike bance komai ba na wanke hannu na ina lissafin abinda zanyi masa idan na fita. Hade rai zanyi yayi hirar sa shi kadai, haka zan ke masa a haka har ya hakura ya rabu dani.
Na wanke hannuna da fuskata sannan naje daki na dauko hijab dina na fito, Umma ta bini da kallo sannan tace "ki koma ki shafa mai a kafarki duk tayi jirwaye, sannan kuma ki saka powder a fuskar ki da dan man lebe" na juya still ba tare da na ce komai ba na koma nayi abinda tace ba dan raina yaso ba, na tsaya ina kallon fuska ta a madubi ina hango kamar da ake cewa muna yi da Layla. Nayi ta gwada fuskokin bacin rai iri iri ina lura da yadda suke chanja min kamanni, so nake in samu wadda zata saka inyi muni dan in naje inyi masa yaga muni na yace ya fasa.
Ina tsaye naji kiran Umma, na fita da sauri ina lura da kallon da take min tana noticing ko nayi abinda tace, ina shiga sitting room na goge lipstick din dana shafa har da tabbatar wa cewa ya bata gefen baki na dan inyi muni. Na dan gyara sitting room din na kunna fitila da fanka sannan na bude kofar waje na fita da niyyar kiran Musa.
Sai dai me?.....
Na gane motar sa kamar yadda na gane tsayuwar sa, ya juya bayan sa yana