Chapter 46 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 106

135K to 138K   out of 316K words

maganar duk da zanyi maka ai, sauran maganganun da zasu fito daga bakina zuwa gare ka ba zasu wuce bakaken maganganu da kuma name calling ba, which I don't want to because you are my husband"

Sai naga ya danyi murmushi yace "I am your husband and you love me" naji kamar in shake shi nace "not anymore" sai ya daga kafada yace "shikenan I will be the one doing the talking in ke ba kya son yin maganar"

nace "ba wai magana ce kadai bana son yi da kai ba, har muryar ka ma bana son ji please, tana sani inji kamar zanyi amai. Please ka rike kayarka a cikin cikin ka ko kuma ka samu inda zaka fesar da ita kamar yadda kake samun inda zaka juye sauran abubuwan ka. Ni dai na gama magana, na baka sharuda guda uku da zasu saka in zauna zaman yayana a gidan nan, notice this please, ba wai zamanka zanyi ba na yaya na zanyi, shi yasa nace kayi aure dan ka samu wadda zata ke ragema nauyin kanka, ni kuma in samu wadda zamu raba bakin cikin ka tare, and maybe wadda zata iya chanja ka dan ni bazan iya ba, ban kai wannan matsayin ba"

Na karashe ina rike kugu ina jiran ya biye min muyi rigima amma sai yace "okay, na fara late, you can tell me all that in na dawo and more, duk abinda yake ranki ki fada you are welcome. Ni kuma I will show you how wrong you are akan maganar auren nan. I can't do it, shikenan, and I am the boss here"

Na zabga masa harara sai ya sake murmushi "look Baby dove, kin bani sharuda uku nayi biyu, ko exams ce ai ina ganin nayi passing ko?" Nace "exams? Abinda ka dauki maganar nan kenan? Ina magana ne fa akan rayuwar mu baki daya, rayuwar ka da tawa da ta yayan mu, menene more important than these?"

Ya sake kallon agogon hannun sa, yace "in na dawo, we will talk more. Sai mu samu wani abu da za'a iya substituting auren dashi. And maganar tafiyar nan da nace miki zamuyi in na samu annual leave dina, ina son sauko da date din ya dawo kusa, da ina da isassun kudi ma da kasar zamu bari mu dan huta ko"

Takaici ma yasa na rasa me zance masa. Sai ya dan rage tsaho yayi kissing kafada ta. "Sai na dawo" nayi sauri na dauko tissue na goge inda yayi kissing din sannan na jefe shi da tissue din, sai yayi dariya sannan ya janye towel din jikina yayi kissing tsakiyar bayana sai kuma ya ja da baya da sauri yana dariya "let's see you clean that" na dauko tissue na fara kokarin gogewa gashi kuma ina rike da towel bana son ya fadi.

Sai na juya ina kallon sa ina huci "Allah ya baki hakuri. Ni na tafi" ya juya ya fita. Na zauna a gefen gado tare da dafe kaina, it is so frustrating idan mutum ya kulla maka abin bakin ciki, kana so ka huce shi kuma yaki baka damar hucewar, pretending as if babu abinda ya faru.

Sanda ya tashi dawowa sai gashi tare da Mufida, tace min har gida yaje ya dauko ta wai yana missing dinta tazo ta kwanar mana biyu. Tana fada nasan dalilin da yasa yayi haka. Wato yasan idan Mufida tana gidan dole zan ke kulashi ko dan ganin idonta, kuma dole zan je in kwana a dakinsa ko dan ganin idonta.

Nayi kwafa ni kadai, in nayi a gaban ta ai ba zanyi a bayan idonta ba ko? Kuma ko a gaban nata ne ma magana ce kawai bana iya mayar masa amma bana wani kula shi, yayi ta kamo ni yana ta playing lovy dovy ita kuma tana ta washe baki wai ita irin yayanta ya hadu din nan.

Dare nayi ta debi yara ta tafi dakina kamar yadda ta saba duk sanda tazo gidan, bata jima da kwanciya ba na leka naga sunyi bacci sai na fito na dawo guest room na gyara nayi shimfida sannan na koma dakin na dauko Asad na kwantar dashi nayi shirin kwanciya ta na kwanta abina. Nayi bacci na mai kyau, ban farka ba sai assuba, ina juyi naji mutum a jikina, na bude ido na ganshi a cikin bargona yana ta sharar baccinsa, nayi tsaki ina jin haushin kaina da ban rufe kofar ba.

Ya bude ido yana kallona sai yace "alhamdulillahillazi ahyana ba'ada ma amata na wa ilaihin nushur. Haka ake cewa in an tashi daga bacci va tsaki akeyi ba" na mike zaune ina jan jiki na daga gare shi, a raina ina tunanin sai nayi wa jiki na wankan tsarki saboda taba nin da yayi "tsakin ai involuntarily yake zuwa, musamman idan mutum ya ga abinda ya bata masa rai da sassafe"

Na wuce na shiga toilet, sanda na fito baya nan sai na rufe kofa ta dan nasan zai iya dawo min in ya dawo daga masallaci ni kuma ganinsa ma bata min rai na yake yi ballantana magana da shi ko kuma ya kai ga taba ni.

Bayan na idar ma ban fita ba, har sai da gari ya waye sosai najiyo muryar Yasmin tana surutu sannan na fita dan nasan yanzu zata ce yunwa. A palo na same su tana zaune a kan kafafuwan sa tana masa surutu shi kuma yana sit up da sauri da sauri, na dauke kaina ina tuno lokacin da nake zama a inda ta zauna shi kuma yana kissing dina idan ya taso zaune. Those are the good old days, bana jin zamu koma kamar yadda muke a da ni da Umar, har abada.

Na shiga kitchen na fara tunanin abinda zanyi mai sauki dan yau bana jin zan iya wani dogon aiki, sai gashi ya shigo kitchen din yana goge gumin fuskarsa. Na kalle shi na dauke kai sai yace "babu gaisuwa?" Na juya na watsa masa harara sai yayi murmushi "lafiya lau na tashi, ke fa?" Still bance komai ba na kunna gas na dora ruwa.

Sai ya zo ya tsaya a gaba na.

"Maganar jiya nake so mu karasa kafin maganaɗisun can ta tashi (Mufida)" na rike kugu "ohhhhh ashe kasan maganaɗisun ce ka dauko ta a cikin wannan lokacin?" Yace "to ya zanyi? Na kasa saka murmushi a fuskar matata shi yasa na dauko ta ta tayani" nayi tsaki, yayi murmushi "bakin ki zai kara tsaho fa in kina yawan yin tsakin nan" nace "and? In ya kara tsahon ma kana da matsala ne? When there are a lot of bakunan da suke jiran ka a waje?" Yace "bani da matsala fa, I will even like it better in ya kara tsahon, I am just warning you kar nan gaba in damu bakin naki ki yi complain"

Na sake yin wani sakin, ni ban ma san sanda nake yi ba haushi ne yake isata, sai yayi dariya "wato so kike yi kenan ko? In dai kika sake to na gane kina so ya kara tsahon ne dan in kara son sa" na juyo da niyyar yi masa wani sai kuma na fasa, Umar really knows his ways with words.

"Azo a bani ruwa inyi wanka. Dan Allah" ya fada yana langwabe kai "if possible ma sai azo a taya ni wankan, kinsan bana iya wanke bayana ya fita sosai" na juya ina kallon ruwan dana dora akan wuta, zuciyata tana gaya min in dauko shi in kwara wa Umar a kyakykyawar fuskar sa, maybe ma in yayi muni ko ya nemi matan ba zasu kula shi ba, ni kuma sai in cigaba da zaman yayana.

Amma banyi hakan ba sai nace "as you can see, ina aiki ne. Akwai ruwa a toilet din ka na zafi dana sanyi, kuma Allah ya baka hannaye guda biyu da zaka kunna sannan ya baka idon da zaka ga hanya sai kuma ya baka kafafuwan da zasu kaika har cikin toilet din, sai menene kuma?"

Yace "sai yin wankan, Allah yasan na gaji ba zan iya yi ba sai ya bani matar da zata yi min" nace "watarana, ranar da kayi aure zaka samu matar da zata yi maka, idan ina aiki ita kuma sai tayi maka wanka, idan ba zaka iya yin tafiya dani ba sai ka tafi da ita. Problem solved"

Ya kamo hannu na "wannan shine dalilin ki? Kina ganin da ace ina da wata matar da da ita zan tafi in ba zan tafi da ke ba? Wannan shine dalilin da yasa kika ce inyi aure?" Na tsaya ina kallon sa amma bance komai ba, zuciyata zafi take yi min sosai idan na kalle shi shi yada nake avoiding dinsa dan babu abinda nake gani a tare da shi sai wadansu munanan screenarios na shi da wata matar da ban ma san kamannin ta ba a Zariya. Na dauke kaina daga kallonsa ina jin hawaye suna tahowa idona sai kawai naji ni a kirjinsa ya rungume ni

"I am sorry Jidda I really am sorry. Ban san ya zanyi in sanyaya miki zuciyarki ba Jidda wallahi da nasan yadda zanyi in goge miki abinda kike ji a ranki danayi, komai wahalar sa kuwa" na kwantar da kaina a kirjinsa ina cigaba da kukana silently nace "da kana son kar inji abinda nake ji, da tun farko ba zaka yi abinda kayi din ba, har rokon ka nayi Allah da Annabi ka tafi dani amma ka ki a kan wani dalili naka marar tushe ballantana madafa, ni fa matarka, duk inda aka baka ka zauna nima ai anan zan zauna ko da kuwa bakin titi ne kusa kwata. All what I wanted was to be with you. Shikenan. Amma ka ki saboda ka riga ka shiryawa kanka abinda zaka yi a can din. Yes, ka yarda kayi saboda na kama ka kayi din dan haka babu wata magana da zaka gayamin, amma zancen shine na farko tun haihuwar Asad ma bata taso ba, ka gaya min haka ne saboda wannan din kadai na sani and you want to keep it that way. Maganganun ka Umar kamar busar sarewa suke zuwa min a kunnuwa na, ga dadi, amma babu wata ma'ana a gurina" sai ma dago kaina daga kirjinsa ina kally fuskar sa "Jidda" na girgiza masa kai "don't start please, don't hurt me more please" sai kuma na hango shi rungume da wata mata, na fara kokarin kwace kaina "did you hug her like this too? Ka sake ni" na fada da dan karfi, ya cikani da sauri yana kallon kofar shigowa kitchen din, burinsa kar wani ya gani kar wani ya ji.

Na nuna masa hanyar waje "fita ka bani guri dan a yanzu zuciyata babu abinda take so irin inyi maka rauni, kuma akwai makamai da yawa a cikin kitchen din nan dan haka ka fita tun ban chanja kammannin fuskarka ba"

Ya juya ya fita ni kuma na kifa kaina akan kanta da niyyar cigaba da kuka na sai kuma nayi saurin dago kai na goge hawaye na sannan na wanke fuskata da ruwa.

Sai na dauko indomie dai dai wadda zata ishe mu na bubbude na zuba a cikin roba sannan na juye ruwan zafin dana dora akai, na dan rufe ta kadan sannan na bude na saka fork na warware ta sai na tace ruwan sannan na sake rufewa dan zafin jikinta ya saka ta yi laushi dai dai misali ba wai dahuwa ba.

Sai kuma na dauko attaruhu da albasa da koren tattasai na yayyanka, na bude na zuba akan indomie din sannan na fasa kwai mai dan yawa shima akai, sai kuma na zuba seasonings din indomie din na saka kayan kamshi na juya su sosai suka hade jikinsu sai na dora frying pan akan wuta na zuba mai kamar zan soya wainar kwai sai nake diban hadin indomie na ina zubawa ina soyawa on low heat.

Sai da na gama gabaki daya na dafa tea na hada komai na kai kan dining table, sai a lokacin na tuno da Mufida, har yanxu bata tashi ba kuma ita ba gwanar dogon bacci bace ba dan normally kamar yanzu tana kitchen tare da ni tana min zance, sai na tafi dakin na same ta shame shame tana ta sharar baccin ta, na tabe baki kawai na dawo na hadawa yasmin abinci sannan fara aikin gyaran gida na, har ta gama ci ta tafi dakin daddyn ta sai kuma gata ta dawo wai inje Daddy yana kira na.

Na juya ido, amma sai na tafi din, yana tsaye da towel a jikinsa "wanne kayan zan saka" na saki baki ina kallon sa sannan na nuna jikina nace "kayan jikina zaka cire ka saka a naka jikin" na fada cikin gatse, sai yayi murmushi "you got it" ya taho inda nake, na hade raina sosai tare da rike kugu "kar ka sake ka taba ni" yace "in na taba kin kuma fa? Huh? Nan ai babu makamin da kike magana akai"

Fahimtar da nayi cewa bani da makamin kuma ya fini karfi kuma baya jin tsoron hura hancina ya saka na juya zan bar dakin sai yayi sauri ya tare hanya tare da murda key din jikin kofar yana min murmushin da nasan ma'anar sa, na nuna shi da hannuna "don't even try it. Idan kana tunanin zaka je ka gama taba mata a waje sannan ka dawo nima ka taba ni then you have another thinking to do. Ba zai yiwu ba Umar, ni ba bola bace ba ba kuma toilet bace ba dan haka ba za'a hada ni da kazanta ba"

Yace "waye kika ji ya gaya miki haka? Ki fada min ko waye in dau mataki a kansa, because you are the purest thing ever. Kince baki yarda da magana ta ba amma ni ba zan daina gaya miki ita ba. Abinda duk na fada miki shekaran jiya shine gaskiyar magana. And you will understand hakan in kika bar kanki yayi tunanin because now you are thinking with your heart, ita kuma heart dinki yanzu is hurting dan haka komai nawa negative take ganin sa saboda ni ne nayi hurting din nata. Yes nayi abubuwa da dama a baya amma yanzu na daina, abinda ya faru da weekend din can tsautsayi ne.... "

Nace "tsautsayi? Tsautsayi fa kace Umar?" Ya daga hannu "kuskure, kuskure ne that will never be repeated" na girgiza kaina "ba kuskure ba sai dai ince ganganci, saboda abu ne da kayi shi kana sane and you are regretting only because you are caught"

Ya jawo ni jikinsa "na gaya miki, I regretted it tun kafin in ganki, nayi blocking........" "Number dinta" na karasa masa "yes, ka gaya min haka, amma sanda zaka dauki wayarka kayi unblocking number din nata ka kuma kira ta will I be there?" Yace "ina wayar? Ji nake na baki ita" nace "sanda zaka shiga shago ka sayi wata wayar da wani sim card din ka ajiye a office din ka will I be there?"

Ya girgiza kansa "you really don't trust me anymore, do you?" Na girgiza kaina "I don't, do you blame me?" Na ga alamar bacin rai a fuskar sa sai kuma ya girgiza kansa "ni kuma zan baki mamaki Jidda, ba lallai ki yarda ba amma bani da niyyar yin wata wayar har sai ranar da kika dauki wayata da kanki kika bani dan kina ganin lokaci yayi da zan rike wayar. Har sai ranar da kika yarda da ni. And yes, na rabu da Bashir, na kai masa takardar barin aiki a karkashin sa na kuma kwashe duk kayana da suke cikin asibitin sa, without a phone to contact me I think zamu iya rabuwa din gradually. It will be the hardest thing da na taba yi a rayuwa ta but I will do it for you. Don't you think I deserve something in return? Kamar yardar ki misali? Dan kin gaya min ba kyason karya na daina yi miki duk da nasan the truth will hurt you sometimes amma nake fada miki, still kuma baki yarda da gaskiyar ba uhmmm?"

Na dauke kaina gefe, sai ya saka hannu ya juyo da fuskata yana rarraba ido akan fuskar tawa yace "look into my eyes ki gaya min cewa baki sona anymore, ki gaya min cewa kin tsane ni da gaske" na kalli idon nasa, remembering the first time I saw them, sai na rufe nawa idon na rufe. Duk kokari na na ganin cewa na kalli idon nasa na gaya masa abinda yace in fada din sai na kasa ko da kallon idon ne ballantana in fada din, zuciyata bugawa take da karfi, silently crying,

Mun jima a haka, fuskata a hannun sa yana kallon na yayin da ni kuma idona yake a rufe ina sauraren yadda zuciya ta take lugude a cikin kirjina, ban ankara na sai jin bakinsa nayi akan nawa, hungrily kissing me, na kama fuskar sa da hannu biyu na tura ta baya tare da bude ido na da sauri na sauke su a kansa, "don't even think about it, in ma wani abu ne yake yi maka kaikayi sai dai kasan a inda zaka sosa shi ba anan ba"

Sai yayi dariya har da kwarewa, "my little darling, a ina kika koyi irin wannan maganar?" Na raba jiki na da nasa "oho, waya sani ne, zama da madaukin kanwa ne ya shafa min farin kai" ya sake matsowa yana langwabe kai "to yanzu ni ya zanyi da abinda yake min kaikayin?" Na daga kafada "oho maka, ko dai kayi raping dina ko kuma ka jika kanwa kasha, zabi ya rage naka" sai ya matsa daga bakin kofa sannan ya nuna min kofar "bismillah, I will never force you akan abinda ba kya so"

Ban bashi amsa ba nazo na wuce shi na koma inda na kwana dan nasan Asad ya tashi ko kuma yana gab da tashi.

Haka rayuwa ta cigaba mana har dan hutun da aka bashi na kwana biyu ya kare ya cigaba da zuwa normal gurin aikinsa, clinic din Dr Bashir ne dai ya daina zuwa dan haka

46 / 106