Chapter 27 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 106

78K to 81K   out of 316K words

da ita a yanzu, in na tabbatar da haka to zan tabbatar da cewa karya take duk sauran maganganun ta.

Wayar ta fara ringing har ta katse babu amsa, na sake kira, na sake kira duk shiru. A hankali nake cewa "pick up Umar pick up" amma umar bai yi picking up ba.

Sai naga message ya shigo min da bakuwar number

"Shshshsh. Stop calling him Baby Dove. Na gaya miki bacci yake yi. Ya gaji sosai a office shine ya taho guri na ya sauke gajiyar sa sannan yake bacci"

Baby Dove shine sunan da yayi saving number ta dashi a wayarsa.



Anan muka kawo karshen free pages na wannan littafin Jidda. A yanzu ne kuma battle din zai soma.

Shin ya zata kwashe tsakanin Umar da Jidda? Menene makomar aurensu?

Ku biyo Maman Maama dan it is going to be a long ride dan ba'a ma fara wasan ba.

This is going to be one of the best novels da kuka karanta.

This is the novel I want to be remembered with........


*Wanan littafin na amana ne, dan Allah in baki siya ba kar ki karanta in kuma kin siya kar kiyi sharing idan kuma kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*The Denial 2*

Na san dai wayar ta fadi kasa daga hannuna ta daki kan kafafuwana sannan ta sauka akan carpet, na kuma san ni ma nabi wayar ta wa na durkusa akan kafafuwana. Sai dai abinda ban sani ba shine seconds ko minutes ko kuma hours din da na dauka a haka.

Ba zan iya tuna mai nayi tunani ba a lokacin dan bana jin ƙwaƙwalwa ta ta cigaba da aiki, a lokacin bana jin ko sunana aka tambaye ni zan iya fada saboda tsananin shock da zuciya ta, ƙwaƙwalwa ta da kuma gangar jiki na suka shiga gabaki daya. Komai nawa ya tsaya, kuma bai dawo da aikiba har sai da ya bude kofa ya shigo palon.

Na dago kai daga kallon carpet din da nake yi na sauke ido na a kan sa,abu na farko dana fara lura a tattare dashi shine yadda fatar idonsa ta dan tasa exactly yadda take yi idan yayi bacci mai nauyi.

Na dafa kujera na mike a hankali, gabaki daya na ma manta da cewa ina dauke da juna biyu ballantana har in ji nauyinsa. Muka tsaya muna kallon kallo, na ga ya ajiye jakar hannunsa tare da key din motarsa sannan cikin wata irin murya yace "Jidda?" Na tabbatar yanayin kamanni na kadai sun tsoratar dashi.

Na danyi gyaran murya a hankali sannan a nutse nace masa "daga ina kake?" Yanayin fuskarsa ya chanza, a yanzu da idona ya bude sai na fahimci rashin gaskiya baro baro a cikin fuskar sa wadda da da ne ba lallai ne in fahimci hakan ba.

"What? Ba gane daga ina nake ba" na gyara tsayuwata ina a raina ina lissafo  abinda yafi komai nauyi a falon wanda kuma zan iya dauka in doka masa shi a kansa ko ya dawo cikin hayyacin sa ya fahimci am in no mood for any of his jokes.

"Daga ina kake?" Na sake maimaita wa "tambaya ce nayi maka ita cikin harshen Hausa, ko kuma baka jin hausa ne yanzu?" Ya tako da sauri zuwa i da nake yana miko hannunsa jikina "Jidda lafiyar ki kuwa? Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun" na juya a fusace da nauki pillow da yafi kusa dani na doke hannunsa dashi "don't touch me in ba haka ba wallahi sai naji maka rauni.

Ya dakata, hannunsa a makale a cikin iska yace "na shiga uku" nayi taku daya baya sannan na sake cewa "daga ina kake?" Wannan karon cikin tsawar daban san ina da irin wannan karfin da kuma muryar ba. Ya kuma kokarin miko hannunsa gare ni sannan yace "Baby daga office mana. Kinfi kowa sanin daga office nake tunda dazu ma munyi waya na gaya miki ina can. Yanzun nan muka fito daga......" "Surgery" na kara sa masa "exactly abinda tace min zaka fada min. Ohh you are so predictable Umar"

Naga mamaki a fuskarsa "what? Wacece tace miki zan gaya miki haka?" Nace "Zuwaira, karuwar ka. Zuwairan da sam baka taba da sanin ta ba, zuwairan da ka taho yanzu daga gidan ta bayan ka gama sauke gajiyar office dinka a jikinta sannan ka shaki baccinka akan kirjinta. Yes, that same Zuwaira ita ce ta gaya min"

Sai naga yayi baya da sauri tamkar wanda na watsa wa garwashin wuta sannan ya rufe bakinsa da hannayensa guda biyu idonsa kamar zai fado kasa "what!?" Ya fada da karfi. "Wacce irin magana ce wannan kike yi Jidda? Can you even listen to your self?"

Ban bashi amsa ba sai na sake daukan pillows biyu a both hannayena na fara dukan sa da su, so nake yi inyi kuka kamar yadda na saba yin kuka a duk sanda wani abu ya faru komai kankantarsa amma yau babu ko digon hawaye a idona. Na fahimci ba jin dukan yake yi da pillows din ba sai na jefar dasu na dunkule hannuna daya na fara dukan kirjinsa da shi hoping in samu zuciyarsa inyi mata rauni kamar yadda yayi wa tawa zuciyar raunin da zai zauna a cikin ta har abada.

"Why Umar? Why? Why? Why?"

"Me nayi maka da nayi deserving wannan daga gare ka?"
"Me nayi maka da zaka sakawa soyayya ta da cin amana irin wannan?"
"Me nayi maka da ka zabe ni a cikin mata kayi min wannan hukuncin?"
"Me nayi maka?"

Gabakidaya ya rikice. Fuskarsa tayi fari kal kamar takarda, fatar bakinsa ta bushe lokaci daya tamkar ya wuni bai sha ruwa ba. Farko tsayawa yayi kawai kamar gunki yana kallo na sai kuma ya fara kokarin rike ni "Jidda, listen to me. Ki fada min me yake faruwa dan Allah. Please don't hurt yourself"

Na tura shi baya da dukkan karfina amma sai ya kasance ni ce nayi bayan ba shi ba, yayi sauri ya tare ni yana kokarin hada hannayena guri daya ya rike amma na sake kwacewa na cigaba da neman abinda zan dake sji dashi. Idona ya kai kan wayata, sabuwar wayar da ya siyo min jiya a matsayin first wedding anniversary gift, na sunkuya na dauka na jefa masa ita, ya kauce ta daki bango tarwatse a gurin.

Na nuna shi da danyatsa

"wallahi da nasan abinda zai faru tsakani na da kai kenan da ranar nan ban fito daga hostel na gaishe da yan gidan su Mufida ba"

"Da nasan sakayyar da zaka yi min kenan da ban amshi fake soyayyar ka ba"

"Da ana chanja kaddara Umar da banyi kawance da kanwarka ba ballantana har in hadu da kai"

Ya sake kokarin magana. "Allahumma ajirni fi musibati. Jidda me nayi miki mai zafi haka? Wacce Zuwaira kike magana akai ne? Bayan ni na gaya miki bansan wata Zuwaira ba ballantana har tace miki wai daga gidanta nake yanzu nayi bacci a.... common Jidda......I thought you trusted me. Dan me zaki dauki words of a stranger akan na mijin ki?"

Nace "trust? Of course I trusted you tun daga ranar dana ganka har zuwa ranar da ka tarwatsa trust dina da bango, ranar da ka yi min karya kace baka san ta ba bayan kuma ka santa. Har ka rants min kace kai wallahi baka santa ba"

Yace "to waye yace miki na santa? Bayan nima har yanzu neman ta nake in hada ta da police....."

Na daga masa hannu cikin tsawa nace "stop lying damn it. Just stop lying. I saw the paper okay. Paper din da kace min ka bawa police I saw it a aljihun ka bayan ka gaya min ka bawa police, sai daga baya ka dauke ta ka fita da ita daga gidan nan"

"And I saw you on Facebook as her friend. And then she told me everything da yake tsakanin ku da kuma everything daka gaya mata akaina"

Naga ya motsa bakinsa amma sai ya kasa cewa komai.

Na koma na tsaya a gabansa nace "daga gidan ta kake, yes or no?"

Yayi saurin girgiza kai "wallahi Jidda ba daga gidan ta nake ba. Yes I know her and I lied to you about that amma wallahi abinda ta gaya miki na cewa daga gidan ta nake kuma wai..... Jidda wallahi karya take yi" na sake taku bawa ina girgiza kaina "you just won't stop lying will you?" Sai na juya na tafi hanyar corridor ina cewa

"Tunda ba zaka fada min gaskiya ba sai kaje ka fada wa Abba, dan gidan mu zan tafi kuma sai na gaya masa kaf abinda ya faru da dukkan abinda tace min"

Taku biyu yayi ya kamo ni tun kafin in shiga corridor din "innalillahi Jidda me kike cewa? Ki tsaya muyi magana ni da ke ki yardada abinda nake gaya miki. Karya take yi min, sharri take yi min, so take ta haɗa ni da ke?"

Na juyo ina kallon sa, in akwai abinda yafi karshen tashin hankali to anan gurin yake. Nace "it seems like kowa yanzu a duniya sharri yake yi maka. Kowa yanzu kokari yake yi ya hada ka dani. While kai kuma cigaba kake yi da yi min karya. Just admit cewa daga gidan ta kake"

Ya daga kafada "ta yaya zanyi admitting laifin da nasan ban aikata ba? Ni ba daga gidanta nake ba, ni ban ma san a inda gidan ta yake ba" naji raina yana cigaba da baci, zuciya ta ta a kara kuna nace "sanda na kira ka dazu kana ina? And don't tell me kana surgery"

I saw him struggling with his inner self, "ina tare da Mahmud abokina" na dafe kaina da naji yana neman sara wa tare da rintse ido na dana fara ganin duhu da su, ya samu damar rike ni. "Wallahi Jidda da gaske nake. In baki yarda ba ga wayata ki kira shi da kanki ki tambayeshi zai fada miki haka. Na taso daga aiki na gaji sosai ina jin bacci ba zan iya driving ba shine na tsaya a gurinsa nayi bacci, ina farkawa na taho nan, sai da na shigo gidan nan ma sannan naga missed calls din ki"

Na saki goshin da na rike ina kallon sa nace "shi Mahmud din shine ya dauki wayarka kenan yaga sanda na kira ka kuma ya kira ta ya gaya mata cewa na kira ka at that exact time, sannan kuma ya gaya mata sunan da kayi saving number ta dashi? Kuma ya tura mata number dina cikin wayarta?"

Ya tsaya shiru yana kallona, and i guessed he was trying to understand magana ta, sai na saukaka masa na bashi amsa "she sent me a text message and called me Baby Dove. Now, explain to me ta yaya ta samu number ta kuma ta san cewa na kira ka sannan kuma ta yaya ta san wannan sunan idan har ba kwa tare?"

Ya tsaya shiru kamar mutum mutumi ba tareda ya iya furta koda kalma daya ba. Na sake shi nace "now finally mun fahimci juna cewa daga gurinta kake, abinda ya rage shine kayi admitting dukkan abubuwan da ta fada min. Daga karshe ni kuma sai in dauki shawarar data bani in san inda dare yayi min tun kafin ka karasa tsofar dani"

Na juya na shige ciki, ina jinsa ya biyo bayana a corridor "Jidda. At least ki bani damar yi miki bayani. Ban san me tace miki ba, ammana tabbatar miki da cewa karya take yi kamar yadda take yin karya cewa daga gidan ta nake, in na miki bayani zaki fahimta. In kin bani dama zan yi miki bayani"

Na rike hannun kofar dakinana juyo "ba sai ka bata lokacin ka ba gurin yi min bayani ba na riga na fahimci komai" na nuna shi da danyatsa na "you never loved me, ka aure ni ne dan biyan buƙatar gangar jikinka, kuma I guess ka gama biya tunda har ka koma gurin karuwan ka"

Ya bude ido da baki duka "that's rediculous! Yanzu har akwai wanda zai gaya miki yace miki bana son ki kuma ki yarda?" Na juya na shige daki ina cigaba dayi masa bitar abubuwan da ta fada da karfi yadda zai shiga cikin kansa sosai kamar yadda ya shiga nawa kan

"Ba sona kake yi ba sha'awa ta kayi a wancan lokacin, Ka saka ni a makaranta saboda ka samu time din biyan mummunar buƙatar ka sai kuma Abba yayi maka cikas yace aurar dani zaiyi dan ya karbi kudin fansho baya son su kare bai yi min kayan daki ba"

Naji dukkan rage din dana ke ta kokarin rikewa ya kwace a lokaci daya, na fara diban kayan da suke kan dressing mirror dina ina jifan sa dasu ina kara "I hate you. I hate you"

"Zaka dauki magana ta kaje ka gaya wa ƙaruwar ka saboda kana son shiga tsakanin cinyoyin ta? Ka wuce kaina ma har ka tafi kan iyaye na? Me nayi maka? Me iyayena suka yi maka?"

Shock din magana ta yasa ya daskare a guri daya, wanny ya bawa wadansu daga cikin kayan da naje jifansa dasu damar samunsa, wata kwalbar turare ta daki bango ta fashe a tsakanin mu, sai a lokacin ne ya motsa ya tsallake ta da sauri ya janye ni da kar in taka. Ya fara kokarin rike ni ina tureshi.

"Menene laifin da Abba yayi maka da har zaka yi zancen sa da ƙaruwar ka? Menene laifinsa dan ya dauki kudin da yayi shekara da shekaru yana tarawa ya kuma yi wa yarsa aure da su? Halaliyar sa, gumin sa, menene laifin sa da har za'a aibanta shi har haka?"

Yace "Jidda kema kanki kinsan wannan maganar banza ce, ni kaina kin taba gaya min da wanne kudi Abban mu yayi mana kayan daki?" Na ture shi ina nuna shi da dan yatsa, "kar ka kara. Kar ka sake kiran Abba da sunan Abban ka dan bai haife ka ba, bai haifi da irin ka ba. Shi Abba talaka ne daya shafe shekaru yana koyarwa a matsayin malamin makaranta yake kuma cin gumin sa yana kula da iyalansa. Kai kuwa babanka mai kudi ne, mai kudin da har ya iya siya maka gida ya baka kai kuma ka saka karuwa a ciki ta zauna har na tsahon shekara guda ba tare da ya sani ba. To albishirinka, yanzu zai sani. Yanzu kowa zai san wanene Umar"

Sai naga ya ja da baya sannan kuma da sauri ya fita daga dakin, nayi tunanin guduwa yayi ko kuma magana tace tayi masa zafi sai na bishi da sauri dan ban gama da shi ba tukunna.

Kofar dakinsa na gani a bude dan haka nan na shiga. Yana tsaye a gaban  locker din da yake ajiye mana First aid drugs, ban lura da abinda yake yi ba dan bashi bane a gaba na ba, na tsaya a bayansa na cigaba

"Gwara ma ka nemo takarda da biro, in baka dasu ni zan ara maka dan a yau dinnan ba gobe ba zan bar gidan ka" ya juyo sai kawai naga ya rungume ni, na fara kokarin kwacewa amma sai ya matse ni sosai da dukkan karfin sa, ya saka fuskar sa a dai dai tawa, ina jin yadda fatarsa ta dauki zafi numfashin sa yana fita kamar na mai zazzabi a hankali yace

"Ba zan rabu da ke ba Jidda. Not now, not ever. Saboda ina sonki fiye da yadda nake son kaina. In kinga na rabu dake to ki tabbatar kabari aka kai ki  ko kuma ni aka kaini. Am sorry for this and for everything"

Sai naji shigar allura a cinya ta, nayi kokarin yin motsi da fatan allurar zata same ni a inda ba zan tashi ba amma ya rike ni gam gam har sai daya zare syring din ya jefar dashi.

A hankali naji jikina ya fara saki, sannan kaina ya fara juyawa ina ganin abubuwa suna rabuwa bibbiyu. Sai naji ya sake ni sannan kumaya dauke ni chak ya dora akan gadonsa, na bishi da kallo ina ganin yaddaykae gyara min kwanciya har da saka min pillow a baya na da kuma kasan marata yadda zanji dadi, sai kuma ya gyara min hannu na daya lankwashe sannan ya durkusa a gaban gadon yana shafa fuska ta.

"Am very sorry Baby, nayi miki allurar bacci saboda ina tsoron kai kiyi hurting kanki ko babyn mu" ni sai a lokacin ma na tuna akwai cikin sa a jikina. Ya cigaba "ina kuma fatan zuciyarki zata huce kafin ki farka dan in samu ki bani dama inyi miki bayanin da na tabbatar zamu fahimci juna. Amma tun kafin nan ina tabbatar miki da cewa kaso tamanin cikin dari na abinda matar can ta gaya miki karya ne. Babbar karyar kuma ita ce zancen Abba, wallahi ban gaya mata ba"

Na bude bakina zanyi magana amma shima naji yayi min nauyi, kalma dy ce ta fito daga ciki "Umar". "I am here with you. I am never going any where" ya fada yana zura yatsunsa cikin nawa, sannan ya sunkuyo yayi kissing goshina. "Umar" na sake fada, sannan hawayen da nake ta fatan suzo tun dazu suka ki zuwa sai yanzu suka zubo daga idona.

Na mayar da idon na rufe. And I slept..

Sanda na farka cikin dare ne, ba zan iya tuna karfe nawa ba ne ba amma nasan dare ya raba sosai. Abinda na fara gani shine fuskar Umar. Yana zaune a gaban gadon da yawa ta a hannun sa, daga dukkan alamu ya hado tane daga inda ta tarwatse. Tashin hankali rubuce baro baro akan fuskar sa.

Na dafe kaina da naji yana barazanar tarwatse wa, motsin da nayi ya jawo hankalin sa kaina, yayi sauri ya ajiye wayar sannan ya karaso yana kokarin mayar da ni ya kwantar. Na daga masa hannu kuma naci saa ya dakata bai karaso din ba.

Na mike zaune na ziro kafafuwana kasa ina kokarin mikewa tsaye "dan Allah ki kwanta Jidda. Kar ki je ki fadi fa ga shi ba ke kadai ba ce ba" na juya na zanga masa harara tare da dogon tsaki sannan na mike "ina zaki je?" Ya sake tambaya ta na ce "sallah zanyi, sallar magrib da isha da ka yi min

27 / 106