Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
haka?"
Sai Mama ta shigar masa "yace ai wayar ta fadi ne kuma har yanzu bau samu lokaci ya gyara layinsa ba, kasan welcome back din nan fa ance layi ake samu a gurin shi kuma ga yanayin aikinsa ba lokaci yake samu ba"
Baba yace "yanayin aikinsa? Aikin nasu ba yafi na kowa samun lokaci ba tunda suna samun off? Yar awa daya zuwa biyun da zai cire yaje ya gyara layinsa shine zai kasa samu? Kuma ma indai yasan wani a gurin ba lallai ne yabi wannan layin da kike fada ba. Shashanci ne kawai ya saka har yanzu bai yi din ba. Ji nake yanzu hutu ma yake yi"
Sai Mama tayi shiru amma duk zuciyarta ta baci kamar ita ake yiwa fadan. Sai da ya gama sannan kuma yace "yanzu idan wani abu ya faru na da iyalinka suka zo suna bukatar ka da gaggawa ta yaya zasu same ka?"
Wannan yasa bayan mun je gida na dauko masa wayarsa, "gwara ka cigaba da amfani da wayarka fa, kaga Baba yana ta fada hakan babu dadi kuma zai ga kamar kaki jin maganar sa" ya karba ya jujjuya ta a hannun sa sai ya miko min ita "naga taki ta kwana biyu, kiyi amfani da wannan kawai sai in sayi wata" na karba "zaka saya dai ko?" Yayi murmushi "Allah da gaske nake zan siya" nace "to Nagode. Allah ya kara budi"
Washegari bayan ya dawo daga office sai gashi da sabuwar waya, na karba ina dubawa sai naga yar karama ce babu abinda zata yi sai kira da sms, sai torchlight da radiyo. Na rike ta a hannu na ina kallon sa sai ya daga kafada "waya ce ita ma wadda zaku iya kirana Baba da Mama ma zasu iya kirana" na zauna a kusa dashi ina jin babu dadi, anya kuwa ban takura masa ba? Sai naga ya dauko sabon sim card yana sakawa a ciki, nace "ba layinka zaka dawo dashi ba?" Sai ya girgiza kai "sabo zan sake, akwai mutanen da bana so su cigaba da samu na a waya"
Shikenan sai na bar maganar, amma a raina sai naji na fara yarda da shi, na fara yarda da cewa da gaske yake yana son ya gyara rayuwarsa ne kuma yana iyakacin kokarin sa akan hakan.
Bayan dawowar mu aka fara shirin reunion na yan set din mu na secondary school. A lokacin shekarar mu biyar da gama makaranta dan haka muke son mu dan hadu mu ga juna a gaggaisa aci abinci tare da sauran su. Tun da aka fara zancen na gayawa Umar kuma ya yarda zan je din, sai dai yace kar in tafi da yara in barsu a gurin Umma tunda Asad ya fara cin abinci yanzu.
Da ranar taron namu tayi sai ya bani motarsa, "ki tafi da motata tafi lafiya sosai" nayi murna sosai na rungume shi i a godiya, sannan mukayi sallama, shi da kansa ya bude min gate na fita, ina fita sai ga Maryam nan tazo, tayi sauri ta tsayar dani "dama nasan da mota zaki tafi shine nace bara inzo ki bani lift, kinsan mu ko samarin da zasu kaimuna mota bamu da su ballantana mazan da zasu siya mana mota" nayi dariya "baki da dama Maryam, kika sani ko mai siya miki jirgi zaki aura nan gaba?" Ta juya ido, "a'a barni a motar dai kawai" sai na bude mata gaba "shigo mu tafi, da kin sani kin kira ni ai da sai in biya in dauke ki tunda kan hanya ne" bata ce komai ba sai sa shigo tana bin motar da kallo "wow, wai sabuwa kika yi ne haka?" Nace "no, ta Yaya Doctor ce, aro aka bani saboda tafiyar da dan nisa" ta juya ido "yar gatan yaya Doctor, to Allah ya sakamu a danshin ku muma"
Tare da ita muka biya muka dauki Mufida, tunda dama tare muka shirya zamuyi tafiyar sannan muka biya gidan mu na ajiye yara sannan muka dauki hanya, muna tafiya muna hirar rayuwar mu ta baya a school da irin wahalhalun da muka sha muna ta dariya abin mu har muka isa school din.
Mun tarar already an fara zuwa, nan da nan muka shiga mutane akayi ta murna da wasu da yawa rabona da ganin su tun muna school din, sai a WhatsApp da muke hira a group.
Bayan an gama haduwa aka bude taro da addu'a aka yi duk maganganun da za'a yi sannan aka fara cin abinci, ina zaune daga can karshe tare da Mufida muna cin abincin mu sai ga kawata Ramlah, tazo ta zauna kusa dani "albishirinki Hauwa'u" na ajjiye spoon din hannuna ina kallon ta nace "goro fari kal" tace "na ga Halima kollere"
Na bude ido "Diyam! Da gaske! Tana ina" na fara kokarin mikewa sai ta rike ni "ke dalla can ba'a nan na ganta ba a unguwar mu ne ranar nan. Ashe akwai Aunty dinta a bayan layin mu kawai ranar nan nazo wucewa sai gaa a mota zata shiga gidan Aunty din nata. Ita ce ta fara gane ni ma ni da kyar na gane ta gabakidaya ta chanja bama zaki taba cewa ita bace ba"
Naji dadi ya kama ni nace "Allah sarki Halima. Wayyo Allah na. Dama kin gayyato mana ita tazo taron nan" tace "na gaya mata sai tace wallahi ba zata samu zuwa ba dan sallama ma tazo yiwa auntyn zata bar kasar" na dafe kaina "kash banji dadi ba, amma kin karbo mana number dinta ko?" Sai ta sauko wayar ta "eh na karba, sai dai yanzu naji bata shiga ina jin sun tafi din ne" na mika mata wayata "samin number din please, zan ke ta gwadawa har Allah yasa in dace in ta shigo kasar kiran ya shiga"
Ta karbi wayar tana juyawa "wow, Jidda wannan irin waya haka? Ni ko bude ta ma ba zan iya ba ungo bude min" nayi dariya "kin cika abin dariya wallahi" sai ga Maryam nan ita ma ta zauna tana cewa "au wayar Jidda kawai kika gani Ramlah? Baki ga irin motar da tazo da ita gurin taron nan ba ko kuma baki lura da kayan data saka ba, kema kanki ai kinsan ta wuce matsayin wannan taron namu alfarma kawai tayi mana tazo"
Na juya ina kallon ta ina jin raina yana baci, bana son irin wannan abin da Maryam take min sai in yi ta feeling uncomfortable. Nace "bana so Maryam ki daina please" ta bata rai "menene abin bata rai kuma dan an fadi gaskiya? Ramla baki san mijin da Jidda take aura bane ba"
Ramla tace "na sani mana, ba wannan doctor din bane ba yayan Mufida? Ba naje bikin su ba? Menene a ciki?" Maryam tace "okay ashe kin san shi, na dauka ba ki san shi ba in baki labarin haduwar shi dan ki tabbatar Jidda is the luckiest one amongst us, ya yadda yake sonta yake kula da ita kamar kwai, wannan ma fa motarsa ce ya bata wai tafi kyau duk da cewa akwai tata tana gida a ajjiye"
Raina ya karasa baci nace "to sai menene? Ina ruwanki? Mijina ne menene dan ya kula da ni ya lallabani ina ruwan ki menene na zuwa kima gaya wa mutane, in na hau motarsa ina ruwanki dashi da motarsa dukkan su mallakata ne menene naki a ciki?"
Ta juya kai gefe "Allah ya baki hakuri naga kin dau zafi, matar gold mai mijin diamond" nace "diamond kadai? Ai ni a gurina mijina yafi daimond daraja da daukaka da kima wallahi dan diamond kowa zai iya saka kudi ya siya mijina kuwa kyauta ce daga Allah ya bani shi ta yadda kudi ba zasu iya siya min soyayyarsa ba"
Ta juyo tana harara ta "ban da dai kuri da cika baki, ni baki san duk mace mai yabon mijinta a gaban mutane haushi take bani ba?" Nace "yabo ai ke kika fara, ke kika zauna a gabana kina yabon mijina shi yasa ni kuma nake taya ki, kuma hausawa sunce yabon gwani ya zama dole shi din kuma gwani na ne dan haka dole in yaba masa"
Maryam tace "ban da dai cika baki gwara kiyi yabon saffa saffa dan wani gwanin in aka tono kazantar da yake aikatawa kuda ma ba zai bi ba"
Sai a lokacin Mufida da take ta faman daddanna wayar ta ta dago sannan ta mike tsaye "ke dalla can da dakata haka nan, kar ki ce zaki yiwa mutane maganar banza anan ina ruwanki wai da mijinta ne? Munafuka kullum kina hanyar gidan ta kullum kina bibiyarta kina kalle mata miji kuma ki zo ki ce zaki fadi maganar banza dan yace baya son ki? Ji nake nan kika same ni da magiya wai in hada ki dashi naki yarda, kika je kina ta binsa yana wulakanta ki ya kuma gaya miki baya son ki amma shine har yanzu ba zaki fita daga harkar shi ba, ba ranar nan na gaya miki kar in kara ganin kin je gidan su ba? Amma baki ji ba ko? To yau zan kunce miki zani a kasuwa munafuka"
Abinka da mata, nan da nan sai aka zagaye mu ana tambayar abinda ya jawo hayaniya, Mufida ta fara yi musu bayani wai ashe tun zuwan da Umar yayi makarantar, tun ranar da muka hadu dashi itama Maryam ta ganshi kuma tun a lokacin ta gaya wa Mufida cewa tana sonsa ita kuma Mufida tace babu ruwanta, bayan munyi graduation ma wai haka ta ringa zuwa har gidan su Mufida tana neman sa, har office take binsa sai daya gaya wa Mufida yace tayi mata warning ta fita harkar sa, tunda lokacin muna dating, ashe duk zuwan da take yi gidan mu dan ta ganshi ne ba dan ni ba.
Dama ni nayi tunanin biri yayi kama da mutum dan in dai muka hadu bata da magana sai tasa, ta ringa hirarsa kenan ta na min tambaya a kansa tun ina biye mata har abin ya fara isa ta har ta kai ga yau munyi sa'insa.
Ai kuwa nan aka yi caaa akan Maryam aka yi ta caccakar ta har da masu kiranta da mugayen suna ye, "ina ruwan ki da mijinta? In ma kina son sa a da tunda ya auri kawarki kuma ya gaya miki baya son ki ai kamata yayi ki rabu da shi. Wannan ai cin amana ne" har da masu bani shawara "duk sanda ta sake zuwa gidan ki tayi miki hirar mijinki ki gurje bakin shegiya a kasa"
A na cikin hayaniyar ashe Maryam ta sulale ta bar wajen, sai daga baya wata tace ta ganta a bakin gate ta hau babur ta tafi tasha. Sai naji a raina banji dadin rigimar da akayi ba, Mufida kuma tace "Umma ta gaida Aysha, dama ni ba'a son raina muka taho da ita ba"
Bayan mun gama mun taho a hanya ne Mufida take gaya min Baba yace ta fitar da miji a hada aurenta dana Muhsina. "Wai wani nan ma aure za'a yi min, chafdi, ai kuwa zasu san wadda zasuyi wa aure ba ni ba. Kowa sai da aka barta ta gama karatunta tayi service ta huta sannan akayi mata aure amma ni ace wai na karasa karatun a dakina? Saboda me? Saboda ni ba'a so na ko me?"
Nayi dariya "yar lelen Mama waye zai ce baya son ki? Gata ne fa za'a yi miki, ke auren fa da dadi" sai nafara yi mata hirar aure da irin albarka da take ciki da dadin damace take ji musamman inta dace da miji na gari, ita dai kawai ji na take yi tace "kyayi kya gama ma, ni ba yanzu zanyi aure ba" nace "sai yaushe to?" Tace "sai nagama zaba na gama tantancewa da gama screening sosai tukunna. Ai dai ba zasu yi min auren dole ba dai ko? Ni kuma ba zan fitar da mijin ba".
Duk a yadda nayi da Mufida ta gane cewa babu harm in aure yanzu amma bata gane ba.....
Sati daya cif bayan taron mu. Muna kwance da dare a dakin Umar bayan mun kwantar da yara a dakina. Ina kwance a jikinsa ina bashi labarin wani Hausa Novel dana karanta wai shi Maimoon, shi kuma yana game a wayata daga alama ma ba sauraron labarin da nake bashi yake yi ba amma ni ban daina ba saboda son da nake wa littafin.
Muna cikin haka aka kira wayata, ya nuna min screen din naga number ce babu suna sai nayi cutting "da daren nan ba za'a bar mace ta kwanta a jikin mijinta taji dadi ba sai a dame ta da waya?" Yayi dariya "a bar mace dau ta damu mijinta da labarin da ba gane wa yake yi ba" nayi juyi akansa "kai, labarin soyayya ne fa, ka tsaya kaji Allah da dadi" yace "ni ba zanji labarin soyayyar wasu ba sai dai ki zo muyi tamu soyayyar" ya fada yana ajiye wayar a daidai lokacin da aka sake kira, na dauka na ga waccan number din ce dai, yace "ji dauka, maybe it is important, in kinji ba important bace ba sai ki katse"
Sai na tashi zaune sannan na dauka
"Assalamu alaikum"
Sai naji muryar Maryam tace "golden wife matar diamond husband, na ajiye miki sako amma har yanzu banga alamar kin gani ba shi yasa na kira in gaya miki inda yake dan in saukaka miki nema. Ki duba bayan motar diamond husband dinki akwai sako na ajiye miki, idan kuma baki yarda da cewa abinda zaki gani nasa bane ba zaki iya kaiwa kowanne asibiti a gwada miki dan a tabbatar miki. By the way, I think it is so romantic the way ge carries a band mai sunan ki a jiki kullum a hannunsa, nasan hakan yana miki dadi sosai shi yasa na cire na saka masa nawa dan nima in gani inji dadi. Like I said, not all that glitters are gold"
Sai ta katse wayar. Na dago kaina ina kallon sa sai naga shima ni yake kallo, sai ya bude ido "what? Waye a wayar? Me akace?" Ban ce komai ba sai na kama hannunsa da sauri ina dubawa, zuciyata tana bugawa da karfi amma tun kafin in kai hannuna kan band din na fahimci ba nawa bane ba, wannan yafi nawa sabuntaka dan nawa duk color din sun goge saboda har wanka Umar yake yi da shi a jikinsa, na juyo gurin sunan da sauri "Mery G" na ga an rubuta.
Tabbas nata ne dan na tuna sanda aka bamu tana da mita cewa ita ba wannan sunan tace a saka mata ba. Ya kalla shima da sauri sai naga ya zaro ido "what? Menene wannan din?"
Bance masa komai ba sai na sauka daga kan gadon na fita da sauri na bude kofar falo, ina fita daga gidan naji ya biyo baya na "Jidda" ban amsa ba na bude kofar baya na motarsa, zuciya ta tana bugawa da sauri a raina ina cewa "God please no, don't let it be"
Da farko banga komai ba, sai dana shiga ciki sannan na ga alamun kaya a kasan kujera, na zaro su sannan na fito daga motar a lokacin da ya karaso inda nake, na daga su ina kalla, pant ne da bra. Ya fara girgiza kai "Jidda listen, dazu Yaya Mubaraka ta karbi aron motata, maybe kayan ƴaƴan ta ne" na jefa masa su "yaya Mubaraka bata da yayan da suke saka brazier, kuma na tabbatar itaba zata cire nata ta bar maka su a mota ba"
Kayan suka daki jikinsa suka zube a kasa, sai na lura wani abu ya fado daga cikin su, na sunkuya na dauka ina kallon abin a cikin hasken security light din gidan.
A used condom.
Shine abinda Maryam tace min idan ban yarda nasa bane ba inje a gwada min.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki yi sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Trash*
Ya fara girgiza kansa yana ja da baya "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda menene wannan a hannun ki? Jiddah wa ya saka min wannan a mota ta? Waye ya kira ki a waya?" Ban ba shi amsa ba sai na jefar da abin hannuna, sannan ba tare da cewa komai ba na juya nayi hanyar cikin gida.
Tafiya kawai nake yi ba wai dan ina ganin gabana ba sai dan na riga na saba da duk wani inch na gidan, har na wuce falo na shiga corridor sannan na shiga dakina, ban tsaya ba na zarce toilet na dauro alwala dama banyi sallar isha ba dan haka na fito na shimfida sallaya, ina saka hijab ya shigo dakin da waya ta a hannun sa
"Jidda kiyi min magana, waye ya kira ki a waya? Me aka ce miki kuma? Jidda kayan nan wallahi bansan yadda akayi suka shiga mota ta ba"
Na saka hijab dina na hau sallaya na tayar da sallah, shi kuma ya zauna a bakin gado da waya ta a hannun sa yana ta dannawa yana saka wa a kunne daga dukkan alama number din da Maryan ta kira ni da ita yake kira.
A sujjada ta ta karshe kamar yadda na saba kai wa Allah kuka na kullum a kowace sallah sai yanzu ma nayi kokarin yin hakan, amma sai naji na kasa jero kalaman da zanyi addu'ar dasu, sai kawai naji kuka ya zo min nan na fara yi da sheshshekar da ta saka gabakidaya jikina yake karkarwa, kadan ya rage jikina baiyi giving up na fadi ba amma ban daina kuka a gaban wanda nasan shine kadai zai share min hawayena ba, wanda ko ban ambata komai ba yasan komai kuma shi zaiyi min maganin komai.
Sai da naji numfashi yana neman