Chapter 78 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   78 / 106

231K to 234K   out of 316K words

shigo masa daga wanda yake nema. Baba

Ya daga amma kafin yayi magana Baban yace "Faruq kana ina?" Yace "ina hanya Baba, yanzu dama nake neman number din ka zan kiraka" yace "ka taho gida yanzu, ina son ganin ka. Ka same ni a falo na. Akwai maganar da zamu yi"

Kafin Umar ya amsa Baban ya katse wayar, sai kuma ya tsaya yana kallon wayar haka kawai yake jin babu dadi, kamar akwai wani abu a muryar Baba. Sai yaji jikinsa yayi sanyi, ya rasa tunanin ma da zaiyi, a haka ya karasa gida yayi packing sannan ya zarce falon Baba kamar yadda Baban ya bukata.

Sai dai me???????

Yana shiga ya tarar ba shi kadai bane ba, akwai Mama a gefensa, sannan a kasa kuma akwai Malam Adamu mai gadi, sai kuma wata mata da wata tsohuwa da bai sani ba, a can gefe kuma rakube a jikin kujera, Asabe.

Yaji kamar ya koma da baya a guje, amma kuma kafafuwan sa sai suka kasa cooperating, ya tsaya hannun sa rike da labule yana sake bin mutanen gurin da kallo kamar yadda suma duk suke kallon sa.

Baba ne yayi magana, muryar sa heavy with emotions "shigo. Zo ka zauna ko dodanni ka gani?" Ya jawo kafa kamar mai shanyayyen jiki sannan yazo nesa kadan da baban ya zauna a kasa, kansa a kasa, kwakwalwar sa a toshe. For the first time in his life, magana ta dauke daga bakinsa.

"Umar" Baba ya kira sunansa, ya dago kai yana kallon sa "na'am Baba" ya amsa da bushashshiyar murya "menene hadin ka da waccan yarinyar" Baba ya tambaya yana nuna Asabe.

Umar bai kalle ta ba sai ya kuma sunkuyar da kansa sannan yace "mai aikin Jidda ce"

Baba yace "ba cewa nayi menene tsakanin ta da matar ka ba, cewa nayi menene tsakanin ka da ita"

Ya danyi shiru sannan yace "ni babu komai tsakanin mu Baba"

Mama tace "kaji ba, ai dama na gaya maka, ya riga ya gaya mana tun farko cewa babu komai tsakanin su, ita yarinyar ce tayi masa karya, karyar da har ta jawo rigima tsakanin sa da iyalin sa"

Baba ya daga mata hannu "ba ke na tambaya ba please. Daga dukky alama idanunki sun rufewar da har ba kya ganin gaban ki. Yaron nan tun da ya shigo gurin nan na ga rashin gaskiya a lullube da shi, amma ke ba ki gani ba"

Umar yayi saurin dago kansa yana kallon Baba, babu abinda yake fada a zuciyarsa sai "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun"

"Baba rashin gaskiya kuma. Baba wallahi........."

Baba ya daga masa hannu "banason ji" sai kuma ya nuna Asabe "sake fadar abinda kika gaya mana kafin ya shigo"

Tayi shiru bata ce komai ba sai tsohuwar da suka zo tare wadda daga dukkan alamu kakarta ce tace "kiyi magana mana, ki fadi duk abinda ya faru kar kiji tsoronsa babu abinda zai iya yi miki"

Tace "shine......shine.....shine....ranar nan...... mommy bata nan, sai yazo dakina ina bacci ya danne ni kuma yace in na gaya wa mommy abinda ya faru sai ya kashe ni in kuma ban gaya mata ba zai aure ni"

Umar ya dafe kansa da hannu daya, tun da yake a rayuwar sa ta duniya bai taba jin kunya irin wadda yake ji yanzu ba, a gaban Mama da Baba? Wannan yarinyar take cewa wai ya danne ta????

Baba yace "kaji abinda tace, ka aikata ko baka aikata ba. Yes or no?"

Ya kasa dago idonsa, Muryar sa tana rawa rawar da taba taba yin irin taba yace "Baba wallahi, wallahi karya take yi, wallahi banyi abinda take nufin nayi ba, in baku yarda ba a kawo min Alqur'ani zan dafa akan hakan"

Asabe tayi saurin cewa "zaka dafa Alqur'ani a kan cewa baka shiga dakina ka danne ni ba?"

Ya dago kai yana mata wani mugun kallo, wannan kalma ta dannewa tana kona masa rai, "wallahi kika sake fadar kalmar nan sai na lahira ya fiki jin dadi" Baba ya daka masa tsawa "kai Faruq! Ka ga alamar wasa a idona? Ba zaka bani amsa ba? Ka shiga dakinta sanda matarka bata nan ka neme ta? Sannan kace zaka kashe ta in ta fada in kuma bata fada ba zaka aure ta? Yes or no? Kalma daya nake so in ka kara wata akai kuma wallahi sai na lahira ya fika jin dadi"

Ya koma ya zauna dabas a kasa, yana jin zuciyarsa tana kuna fiye da tunanin sa, wannan wacce irin sarkakiya ce ya fada ciki?

Baba ya mike tsaye, jikin sa har rawa yake saboda bacin rai sannan ya sake tambaya cikin tsawa "yes or no!?" Umar ya rufe fuskar sa da hannayensa biyu sannan a hankali ya gyada kansa.


Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only



*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, in baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*Fatherhood*

"ka bude baki kayi magana!" Baba ta sake fada cikin tsawa "ka shiga dakin yarinyar nan ka neme ta ko baka shiga ba?"
Umar ya bude fuskarsa, fuskar tayi jajur kamar an shafa masa jambaki a fuskar sannan a hankali yace "eh"

Baba ya koma ya zauna tare da dafe kansa "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun" Mama ta sauko daga kan kujerar ta dafa Umar hankalin ta a tsananin tashe "Alhaji, dan Allah kayi hakuri"
Tsohuwar da suka zo tare da Asabe tace "alhamdulillah, tunda gaskiya ta fito daga bakinsa, kafa da kafa aka roke mu mu bayar da yarinyar nan, tana cikin rufin asirin ta cikin yanuwanta muka dauko ta muka baku dan muna ganin mutuncin ku amma ga sakayyar da muka samu nan, an lalata mana yarinya sannan aka lakada mata duka aka kuma kore ta, har da bata tsoro dan kar ta fada, so yayi ya mayar da ita kamar matarsa kullum in matar bata nan yake biyan mummunar bukatar sa da ita"

Umar ya kama hannun Mama da zazzafan hannunsa, yana jin kamar ya tashi yayi ta ball da tsohuwar can da taki yin shiru ta bar shi da abinda yake damunsa. "Mama. Wallahi banyi abinda suke nufi ba. Na shiga dakinta "eh" na....na......na.....na gaya mata abinda tace na fada "eh" amma wallahi Baba" ya dago kai yana kallon Baba da har yanzu yake zaune hannunsa a dafe da kansa, "wallahi Baba........" Amma sai ya kasa cigaba da maganar, wai ma ta yaya zaiyi musu wannan bayanin ne, how do you explain going all the way and not reaching there?

Baba ya karasa masa maganar cikin sigar tambaya "amma baka neme ta ba?" Yayi shiru, nema is not the exact word da zaiyi rantsuwa akai, shi kuma yanzu he is willing to dafa Alqur'ani dan nuna gaskiyar sa. Amma ta yaya zai yi bayanin gaskiyar ta sa?

Tsohuwar ta sake cewa "ya neme ta mana Alhaji? Ba kaji ya fada ba yanzu da bakin sa amma kuma zaku sake dawo da yambayar dan a bashi damar chanja magana? Mu dai adalci muka zo ayi mana, yanzu yadda ya lalata mana yarinyar nan, dan ni bana jin ma sau daya ne ya neme ta, yanzu wa zamu aura mata kenan? Wannan abin kunya da me yayi kama?" Ta karasa tana sharar kwalla.

Umar yayi sauri sake kallon Baba, yana jin wani irin faduwar gaba, ba dai auren yarinyar suke so su lika masa ba? Ya saki hannun Mama ya dafa kafar Baba "Baba wallahi" Baba ya janye kafarsa da sauri tare da cewa "wallahi me? Me kake ta rantse rantse akai ne? Umar ka bani kunya wallahi, ko da wasa ban taba tsammanin wannan halayyar daga gare ka ba, ka tozartani yadda ba'a taba tozartani ba a duniya, ka kunyata ni irin yadda ba'a taba kunyata ni ba a duniya. Menene yayi saura? Dalilin da yasa matarka ta bar ka kenan ashe, wannan muguwar maganar taji, abinda taji ka aikata kenan a cikin gidan auren ku. Me yasa ba zata bar ka ba? Ko mu ba dan mu muka haife ka ba ai da cewa zamuyi babu mu babu kai............" Mama da take durkushe itama kusa da danta tace "dan Allah kayi hakuri Alhaji, ka tsaya ka saurare shi da akwai magana a bakin sa, ka barshi ya fada dan muji gaskiya" Baba ya sake cewa "to me zai fada ne bayan wanda ya riga ya amsa? Menene zaiyi kuma bayan wanda ya riga yayi?"

Tsohuwar tace "babu, abinda ya rage shine tunda ya karbi laifinsa sai kuma ya karasa aikin da ya fara, sai ya aure ta, tunda dai ya riga ya fara morar auren tun kafin a daura"

Umar ya bude ido da sauri ya juya yana kallon ta sannan ya sake juyowa ya kalli Baba wanda shima yake kallon tsohuwar yana gyada kai "tabbas wannan shine abinda ya dace ayi dan ayiwa yarinyar nan adalci. Dole shi zai aure ta!"

Umar yaji kafafuwan sa sunyi collapsing ya zauna dabas a kasa daga tsugunnon da yake yi, ido kamar zai fado a kasa. "Baba!" Ya fada cikin rudewa "Mama kar kuyi min haka dan Allah. Baba wallahi ban aikata laifin nan ba" Baba yace "kuma dai? Ji nake yanzu ka amsa kayi, yanzu kuma sai ka dawo ka ce ba kayi ba kuma duk a gaban shaidu daya? Me kake nufi ne? Akwai maganar da kake so ka fada me ko kuma kana so ka mayar da mu shashashai?"

Umar ya goge gumin fuskarsa da hannun sa idonsa a kasa yace "Baba na shiga dakinta, kuma na neme ta, amma.... amma... amma...ban shige ta ba" ya karasa maganar tare da kifa kansa akan kafadar Mama yana jin tamkar kasa ta tsage ya shige ciki.

Duk suka yi shiru first, sannan kuma Mama tayi magana "alhamdulillah, alhamdulillah, Allah mun gode maka, Allah mun gode maka daka bayyana gaskiya ka kuma rufa mana asiri. Alhaji kaji ko? Ka fahimci abinda yake cewa? Addu'ar mu a gare shi da tarbiyyan da muka bashi su suka kasance tare da shi suka hana shi aikata abinda ake cewa ya aikata"

Tsohuwar tace "karya yake yi, wannan daga ganin sa dama zubin makaryata ne da shi" Mama ta mike a fusace, girman shekarun matar ne kawai ya hana ta ta kwada mata mari "amma dai ke kam baki da ta ido, yanzu kina kallon yadda ubansa yake ta kokarin ganin an gano gaskiyar maganar nan duk da kasancewar sa dansa, yana so lallai yayi adalci akan maganar nan amma hakan ba zai hana ki jifan dansa da munanan maganganu ba? Ji nake an ce ko mutuwa ma ai tana jin kunyar idon mahaifi, kuma ina tabbatar miki da cewa zaki ji kunya idan gaskiya ta bayyana, zaki gane cewa yaron mu mun bashi tarbiyya jikar ki ce dai lalatacciya" itama kakar ta yunkuro "lalatacciya ai bata lalata kanta sai dai a lalata ta, ku dubi wannan yaron ku dubi wannan yarinyar ku fadi tsakani da Allah cikin su waye zai lalata wani? In dai har ana son gaskiya. Kuma na shiga ban dauka ba ai bata fidda barawo, in dai har ya amsa ya neme ta kuma karya yake yi ya dawo yace ga kuma wata magana ta daban"

Baba da tun dazu yake zaune ya dafe kansa ya mike yace "akwai yadda za'a gane ai, ana dubawa a asibiti za'a kai ta a duba ta" ya juyo yana kallon Umar yace "in dai aka samu cewa ita ce da gaskiya to ka tabbatar cewa zaka aure ta" Umar ya zaro ido "Baba ba za'a fahimci gaskiya ba a asibiti, ba za'a iya fadar wanda yayi ba. Za'a iya dora min laifin wani" Mama ta dora da cewa "musamman tunda yarinyar talla take yi kafin in karbo ta"

Baba ya kalle ta sannan ya kalli Umar yace "kamar yadda ta fada, na shiga ban dauka ba bata fidda barawo, dalilin da yasa ya shiga dakinta har kuma ya neme ta, sannan yayi threatening din ta, shine dalilin da zai saka ya cika alkawarin da ya daukar mata" daga nan ya juya ya shigewar sa daki. Yana shiga Umar ya mike da sauri ya fita daga falon ko ganin gaban sa baya yi sosai saboda yadda tashin hankali da bacin rai suka rufe masa ido.

Dakin da yake yanzu a matsayin nasa tun da ya tattaro kayan sa daga gidan sa bayan tafiyar Jidda nan ya shiga ya rufe kofa sannan ya jingina da jikin kofar ya rufe idonsa, a hankali kuma sai ya zame ya zauna a gurin tare da dafe kansa.

Tun da yake a duniya bai taba ganin tashin hankali irin na yau ba, bai taba jin kunya irin ta yau ba. Wai wannan yarinyar ta ringa fadar wai ya danne ta a gaban Baba da Mama? Wannan tsohuwar kuma, Allah da zai kamata sai ya karasa fitar da sauran hakoran da suka yi saura a bakinta.

Ya tuno maganar Baba wai zai aura masa Asabe, how? Ta yaya ma za'a aura masa Asabe? Shi kam ko sau dari za'a daura aurensa da ita to kuwa tabbas zai sake ta sau dari sai dai Baba ya saka kansa gabas ya yanka shi. Da ace ma yayi ne, da ace yayi da zai iya karbar laifinsa ya aure ta tunda yayi amma damn it bai yi ba kuma ba zai taba yarda ya amsa cewa yayi ba. Baya kuma raba dayan biyu in aka duba ta za'a same ta a bude amma ba shi bane ba, dan sanda ya neme tan ma bata yi resisting ba shi da kansa ya ce ya fasa kuma sai ta nuna rashin jin dadin fasawar ta sa, amma babu wanda zai yarda in dai ba ita ta fito ta fada da bakinta ba, especially Jidda ba zata taba yarda cewa baiyi ba.

And yasan wannan is just the beginning of his nightmare dan yanzu ne ma yake kara jin tsoron dawowar Jidda musamman yadda tayi masa magana dazu with so much bitterness, ya tabbatar in ta dawo zata juye duk abinda yake zuciyar ta ne a gaban Baba shi kuma Baban zai yarda da ita without a second thought tunda already wannan tsinanniyar yarinyar ta riga an dasa masa wannan tunanin a zuciyarsa. Sai ya fara jin haushin kansa, ya kaiwa iska naushi, damn it, menene ma ya saka shi ya bar Jidda ta fita daga gidan sa ranar nan? Me yasa bai rufe kofa ba ko kuma yayi mata allurar bacci irin ta ranar nan har sai zuciyarta ta warke sannan ya zaunar da ita yayi mata bayanin gaskiyar abinda ya faru kuma ya matsawa yarinyar ita ma ta fadi gaskiya, ranta zai baci sosai ya sani, zata yi fushi for sometimes kuma ta watakila ta kori yarinyar but that will be all, a hankali kuma komai zai wuce su cigaba da rayuwar su kamar babu abinda ya faru, yes she always forgives because she have a big heart.

Amma yanzu kam komai ya chakude. Ya dauka tana missing dinsa kamar yadda yake tsananin missing dinta, but bai ji hakan ba ko da a muryarta ne kuma bai ga alamar hakan ba dan da tana missing dinsa zata fito dazu ta ganshi, in yaso ko fada ne suyi, ko maganganu ne ta gaya masa, at least dai ta kula shi, at least ta ganshi shima kuma ya ganta.

Ya saka dan yatsa ya shafa band din ta na hannun sa, ya tuno sanda take masa mitar ya kamata ya yar da shi haka dan ya tsufa shi kuma yace ba zai yar ba sai ta sake masa wani, ta kuma yi alkawarin zata yi masa wanin "da kaina zan hada maka, irin na zamani ma mai kyawun da zai dace da kyakykyawan mijina"

Yayi murmushi yana jin tsananin kewarta irin wadda bai taba ji ba, he needs her now more than ever, ya san kuma chance dinsa daya shine ya samu ya riga kowa a family ganinta, yayi mata bayanin situation din da yake ciki tare da rokon ta da kar ta karasa datse yar guntuwar yardar da take tsakanin sa da iyayensa, but ta yaya zaiyi achieving hakan with that closed gate in between them?

Karar wayarsa ce ta dawo dashi daga tunanin sa, ya zaro ta daga aljihunsa sannan ya rintse idonsa saboda sunan Mama da ya gani a jikin wayar, sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka amma kafin yayi magana sai tace "kazo ka same ni a dakin babanka" daga haka ta kashe.

Ya mike tsaye yana tunanin dalilin kiran, shin zasu ce masa "ka bamu kunya Umar bamu yi tsammanin haka daga gare ka ba" ko kuma zasu cigaba ne dayi masa maganar auren Asabe? Ya cire rigar jikinsa da ta jike da gumi sannan ya saka wata a ransa yana tunanin ranar da Jidda ta siya masa rigar "zata yi maka kyau sosai".

Da sauri ya fita ya doshi palon da ya baro dazu, amma yana shiga sai ya tarar babu kowa a ciki sai Mama ita kadai a zaune a inda ya bar ta, babu Asabe babu iyayen ta balle kakarta, kp sun tafi asibitin ne?

Kafin ya zauna ko kuma yayi wata magana sai ta mike da sauri ta kama hannunsa ta jashi zuwa bedroom din Baba suna zuwa suka tarar dashi zaune akan gado hannun sa biyu dafe
da kansa, Umar ya durkusa a gaban sa idonsa a kasa, Mama kuma ta zauna a kusa da shi.

"Alhaji, dan Allah ka zauna ka saurari yaron nan, kar ka yanke masa hukumcin laifin da baiyi ba, nasan ka fahimci abinda ya faru ba sai an sake maimaita wa ba ni kuma nasan duk duniya a yanzu babu wanda yafi karfin kaddara da sharrin shaidan, babu yadda banyi da matarsa akan ta hakura da aikin ta ta zauna a gidan ta ta kula da mijinta tunda babu abinda ya rage ta dashi amma taki, ta

78 / 106