Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
matsorata a tsakanin barebari da fulani"
Suka cigaba da hirar su tare da wasa da dariya, ni kam san na dauki abinda zan bukata na koma daki nayi zamana zuwa can ma bacci ya dauke ni, sai dai cikin baccin naji ana taba ni, na bude ido naga Asma'u sai tace "wai kizo, mutumin jiya ne ya dawo" naji gabana ya fadi amma sai na mike zaune wata zuciyar ta ce min ince da Asma'u tace masa ba zan zo ba kuma ba zanyi magana da shi ba.
Amma kuma sai na kasa fadar hakan na mike na bi bayan ta zuwa inda wayar da suke communicating da gate take. Na dauka, "Hello?" Naji muryar "Jidda, please don't hang off. I need to see you, I need to talk to you"
Nace "I don't want to see you or talk to you"
Yace "naji. Just listen to me then. I will do the talking in dai zaki saurara"
Nace "you have thirty seconds. Ka fadi abinda kake so ka fada ka kara gaba"
Yace "Jidda please. This is serious. Baba da Abba sun san komai. Har maganar Mammy, I don't know yadda akayi suka sani. Baba yana asibiti, jininsa ya hau"
Na lumshe idona na bude nace "it has always been serious Faruq, kai ne dai baka dauki maganar serious ba. Amma a gurina tun ranar farko da ma sani na san serious ce"
Yace "na sani Jidda, na samy serious ce tuntuni but ina gaya miki Baba yana asibiti, jininsa ya hau akan maganar........."
Nace "nima jinina ya jima da hawa, kuma akan maganar, har yanzu kuma ban warke ba"
Naji muryar sa kamar zaiyi kuka "Jidda please listen, kin ce ba zaki yi magana dani ba to listen to me mana. Maganar babba ce fa sosai. Ban sam ya zanyi ba Jidda please ki taimaka min, Baba da Abba sunce in baki takarda and you of all people know that is not possible. Ba zan iya rabuwa dake ba Jidda because I love you and you love me too"
Nace "loved. I loved you. But not anymore. Kaje ka rubuta ka basu"
Yace "I don't believe that. I know you love me kuma dalilin hakan ne yasa kike buya a cikin wannan gidan. If you truly don't love me fitowa zakiyi gabana ki tsaya ki kalli idona ki gaya min. Jidda mutuwa zanyi, very soon. In dai suka matsa sai na sake ki zan shiga duniya irin yadda kika yi, but at least ki barni in ganki ko sau daya ne kafin in mutun ko in shiga duniya"
Na rufe ido na ina sauraron sa, ba kalaman dayake yi ne suke taba ni ba sai yanayin da naji muryar sa a ciki. Ya cigaba
"Baba yace zai daura min aure da wannan yarinyar, wannan yar aikin naki. And Abba will soon come and take you away. Please Jidda don't let them take you away from me. You and the kids are the only thing I have left. Please Jidda don't let them take you away"
Na bude bakina a hankali nayi magana, ina jin taste din hawaye a cikin bakina, nace
"no body is taking me away from you Umar. You already pushed me away"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*Back Home*
Yace "nooo Jidda, kin sani ai, kin fi kowa sanin cewa I will never do that to you. I will never hurt you. I never meant to hurt you. Nasan nayi hurting dinki but it was never intentional, kuma a yanzu babu abinda ba zan iya bayarwa ba dan in dawo da rayuwata baya in gaya ta. Amma ba zai yiwu ba, sai dai in gyara gaba kawai. Dan Allah Jidda ki dawo. Ki dawo gidan ki muci gaba da rayuwar mu tare da yayan mu. Please come back home"
Na goge hawayen da na fahimci suna zuba daga idona nace "ina ne home din? Home is where the heart is and my heart is no longer with you Zuciyata yanzu already tana gidan babana, daga nan kuma sai gidan next mijina insha Allah. Ka je ka rubuta ka basu sai yafi maka sauki, sai yafi mana sauki gabakidayan mu"
Yayi shiru har na dauka ma ya ajiye wayar sai kuma naji yace "kina fadar haka ne dan ki bata min rai na sani, amma ina so in gaya miki ce wa ba kya bukatar bata min rai dan a halin da zuciyata take ciki bana jin akwai wata magana da zaki fada da zata bata min rai. Baba da Abba have only two options, ko dai su hakura su mayar da ke gidan ki dan ba zan sake ki ba, ko kuma su barki a gida kiyi ta zama da igiyar aure na har sai sun gaji sannan su mayar da ke, either option ends with you back to my house"
Sai nayi murmushi, yace ban bata masa rai ba amma na fahimci na bata din, and I am looking forward to more of bacin ransa sai nace "ka manta cewa suna da third option, zasu iya kaiwa alkali ya raba auren with or without your consent, and then sai suyi min aure with someone much better than you in all the ways, ka kaji dadin ka ma ba zaka gan mu ni da shi naked in bed ba in dai ba leken mu zaka je kayi ba, maybe dai kan mu holding hands a hanya, which I guess won't hurt you much tunda a lokacin babu aure a tsakanin mu kuma ba farka na bane ba aure na yake yi, ka ga kai ka ji dadi ba kamar ni ba da naga abubuwan da na gani a lokacin da muke da igiyar aure a tsakanin mu....."
Yace "shut up! Just shut up"
Nace "why? Dan na fadi gaskiya? Ina yi maka fatan alkhairi Umarul Faruq, ina yi maka fatan samun haske a rayuwar ka, kuma na gode maka sosai da kazo ka sanar da ni cewa komai ya daidaita a gida yanzu zan iya komawa. Now I can finally switch on my phone and call Abba in gaya masa inda nake yazo yayi musu godiya ya dauke ni"
Yace "Jidda! You are not understanding are you? You are thinking with your heart kuma your heart is still hurting, idan Abba ya zo ya dauke ki ba zai mayar min da ke ba fa. Zai raba auren mu ne. Zai raba ki da ni ne. Do you understand?"
Nace "of course na fahimta. Kuma ina tunani ne da kwakwalwa ta sabanin da da nake tunani da zuciyata. Tabbas na fahimci Abba zai raba ni da kai which is exactly why zan je gurinsa because that's what I want with all my heart. Rabuwa da kai. Allah ya bawa Baba lafiya and I wish you best of luck a sabon auren ka. Allah ya kawo kazantar daki"
Sai na kife wayar tun kafin ya ce komai. Sai kuma na jingina kaina da jikin bango tare da rufe idona ina jin hawayena yana zuba cikin rigata.
"Mommy are you crying?"
Naji muryar Yasmin a gefe na, nayi saurin goge hawayen fuskata da hannaye na biyu sannan na juya da sauri na bar gurin ita kuma ta biyo ni a baya tana cigaba da tambaya ta "mommy kuka kike yi? Waye ya saka ki kuka? Da wa kuke waya? Daddy ne? Daddy ne ya saka ki kuka? Mommy mai yace? Zai zo ya dauke mu yace?"
Ban ce mata komai ba na dauko jakar da Diyam ta zubo mana kayan da ta siyo mana a ciki na fara zuba mana kayan mu a ciki, ta sake kama skirt dina "mommy tafiya zamu sake yi, gida zamu koma? Gurin Daddy zamu koma" na ajiye jakar na rike kafadar ta nace "Yasmin. Tafiya zamuyi. Amma ba gidan Daddy zamu koma ba gidan Abba zamu koma. A can zamu cigaba da zama. Daddy zai ke zuwa yana ganin ku kuma kuma zaku ke zuwa gidan sa da gidan Mama kuna ganin su. Amma ba zamu cigaba da zama a gidan sa ba. Kin fahimta?" Sai ta girgiza kai idonta yana cikowa da hawaye, "ni dai ban fahimta ba mommy. Ni ban gane ba. Ni nafi son mu koma gidan Daddy mu cigaba da zama a can tare da ke tare da Daddy" na sake ta na cigaba da ninke kaya ina saka wa a jakar "ba komai ne da kake so kake samu ba a rayuwa Yasmin, ba kuma komai ne da kake so yake zama alkhairi a gare ka ba" amma ni kaina nasan ba da ita nake maganar ba da kaina nake, ina kara karfafa wa kaina guiwar cigaba da bin hanyar da na dauka.
Diyam ta shigo dakin tana kallona tare da jakar kayan da take gaba na. Sai ta zauna akan side drawer tace da Yasmin "Yasmin share hawayen ki kinji, rabu da mommy, ki je falo maza kuyi wasa da Asad gashi can yana wasansa" Yasmin tayi kamar ba zata fita ba kuma sai ta fita.
Diyam ta juyo tana kallona "tafiya zaki yi?" Na gyada mata kai ina jin babu dadi na fara hada kaya ba tare da munyi magana ba "gidan Umar zaki koma?" Ta sake tambayata, na juyo da sauri ina kallon ta "of course not. Me yasa kika yi tunanin zan koma gidan sa?" Tace "well, yazo, kunyi magana a waya, and you started crying kina hada kaya. Kuma nasan kina son sa. Me yasa ba zanyi tunanin kina shirin koma masa bane ba?".
Na danyi murmushin takaici nace "tabbas munyi magana da Umar kuma ya gaya min maganganun da suka taba zuciyata suka saka ni kuka. Amma hakan ba wai yana nufin cewa zan koma gidansa bane ba" na zauna ina wasa da hannuna "ya gaya min cewa gaskiya ta bayyana. I think Abba ya karanta sakon da na tura masa kuma ya yarda, har ya gaya wa Baban Umar, kuma sun gane abinda ya faru da Asabe. Jinin Baban Umar ya hau yanzu yana asibiti. Mutumin kirki ne dan tun da na sanshi wani abu bai taba hada mu ba face alkhairi. But now he is reaping abinda dansa ya shuka. Shine abinda ya saka ni kuka. Ba wai Umar ba. And yes, tabbas ina son Umar, amma bana jin son da nake yi masa ya kai kashi goma cikin darin wanda nayi masa a baya. Shima kuma goman nafi tunanin kyautatawar sa gare ni ce ta saka har yanzu yake zuciyata. Amma aurensa na gama kamar yadda na fada. Na gama auren Umar. Yanzu ne ma kuma na sake tabbatarwa kaina da cewa na gama din. Tun da nake gidan sa kullum addu'a ta itace Allah ya shirye shi, Allah ya gyara masa halin sa dan mu zauna lafiya, amma Umar bai shiryu ba sai cigaba da lalacewa da yake yi. Tun da na bar gidan sa kuma sai na koma yin addu'ar Allah ya zaba min mafi alkhairi a rayuwata, sai gashi cikin sauki al'amurra suna warwarewa toward rabuwar mu, meaning rabuwar mu itace alkhairi a gare ni. And I will not resist. Zan karbi rayuwa duk a yadda tazo min tare da fatan shine mafi alkhairi a gare ni"
Nayi shiru ina tunani sannan na dora da cewa "ba wai na fitar da ran cewa Umar zai shiryu ba ne a'a shiriya ta Allah ce kuma shiryar sa tana hannun Allah. Amma Allah ba zai shiryar da shi ba har sai shi yayi nadamar abinda ya aikata ya daina aikatawa kuma yayi taubatun nasuha, a lokacin Allah zai yafe masa sannan ya shiryar da shi. No matter how much matan da mazajen su suke da hali irin na Umar suke san su shiryu, no matter how much they pray cewa su shiryu, ba zasu shiryu ba har sai su mazan sun yadda cewa laifi suke yi kuma sun tuba sun koma ga Allah, sannan Allah zai shiryar da su dan shine kadai zai iya shiryar da su ba wai matan su ba"
Diyam tayi ajjiyar zuciya tace "haka ne Jidda. Tabbas labarin ki wata aya ce da ya kamata matan da suka samu kansu a irin rayuwar ki su gane, is not their fault, ba laifin su bane ba dan haka duk gyaran da zasu yi mijin ba zai gyaru ba har sai shi mai laifin ya gyara da kansa. Yes, yin hakuri da yin addu'a da danne zuciya da karbar kaddara duk abubuwa ne masu kyau, amma hakan ba zai taba chanja miki al'amuran ki direct ba, ita kanta addu'a tana aiki ne based on actions dinka, misali ace talauci yana damunka babu cin yau babu na gobe shikenan sai kayi folding hannunka kayi da addu'a kana hakuri tare da daukan cewa talauci kaddarar ka ce? Shin ba zaka fita ka nema ba sai ka hada da addu'ar sai Allah ya albarkaci neman naka? Ko kuma wanda yake fama da cuta, shin zai zaune ne yayi ta addu'a tare da daukan cewa ciwon jarabawar sa ne ba zai fita ya nemi magani ba? Ina ganin neman mafita ba wai yana nufin baka dauki kaddara bane ba, ka ki yin addu'a kuma ka dage akan cewa lallai abu kaza kake so baka son kaza a ganina shine rashin daukan kaddara"
Nace "haka ne. Duk abinda kika fada haka ne. Allah yasa mu gane" tace "ameen. Yanzu gidan zaki tafi kenan?" Na dan yi shiru ina tunanin in kai kaina ne ko in barsu su zo inda nake da kansu? Kamar tasan tunanin da nake yi sai tace "ina ganin ki barsu su zo. Let them have the satisfaction of finding you. Whatever way am happy for you, naji miki dadin yadda abubuwa suke warware miki, haka Allah dama yake ikonsa. Trust him and He will find a way for you" na gyada kai, maganar ta tana tuno min da wani ironi da ya faru, na tuno sanda nake ta bin Umar ina rokon sa Allah da annabi yayi aure dan a lokacin ina ganin kamar aurensa zai iya sakawa ya gyaru amma sai ya shafa wa fuskar sa toka yaki, yace shi bai ga wadda tayi masa da har zai iya auren ta ba, sai gashi yanzu za'a hada shi aure da Asabe, Asabe for God's sake.
Sai nayi murmushi na bawa Diyam labarin sabon auren da Umar zai yi, ina ambatar sunan wadda za'a aura masa sai ta kwashe da dariya har da faduwa kasa tana rike ciki, nima sai na samu kaina da darawa, but abinda nake da tabbaci shine Umar ba zai zauna da ita ba except if Baba yace zai tsine masa ko something like that, but either way I don't see auren Umar da Asabe a matsayin mafita ga Umar sai dai ko a matsayin sakayyar na yaruwar yaran da Umar ya bata.
But thinking about that also got me thinking. Rayuwar Umar da halayyar sa ba wai laifinsa bane ba shi kadai, it is equally laifin sa da na matan, cos I don't think ya taba raping wata banajin that will be his style cos he is a romantic guy not a rogue. Ba wai ina justifying actions din Umar da masu halayya irin ta sa ba amma ai karfe da ya baya amo, ko da sun sami yarinya da yaudara da kalaman cewa zasu aure ta she should be wise enough to say no, in dai har zasu aure tan su bari ayi auren mana. Those girls should blame themselves dan zunubin bana mazan bane su kadai ba equally za'a basu.
Diyam tace "wani tunani nake yi Jidda, ranar da kika bar gidan Umar kika je gidan ku Abba ya kore ki ki ka gudu, misali idan da ace ban kira ki a lokacin har na fahimci kina cikin problem nace ki taho nan ba, ya zakiyi?"
Nayi shiru ina juya maganar, and I realized there may be matan da suka taba shiga irin problem dina kuma iyayen su irin nawa ne, Misali baban su mai tsatstsauran ra'ayi uwar kuma mai gudun abin da take gani as abin kunya, they may not be as lucky as me to have a friend that will take them in and support them, me zasu yi? Menene mafita a gare su?
Sai na girgiza kaina "ban sani ba Diyam, ban san menene zanyi ba a lokacin, maybe I could have ended up a gidan one of my relatives wanda kuma dole a karshe Abba zai mayar dani tare da yi min fadan da yafi wanda yayi min, ba zai bani listening ear ba, zai mayar da ni gidan Umar kuma yadda nake ji a raina a lokacin in aka mayar da ni gidan Umar komai zai iya faruwa, zan iya ji masa ciwo or worst"
Ta dawo ta zauna kusa dani ba tace komai ba sai ni na tambaye ta. "Menene kike ganin zan iya yi a lokacin? Menene shawarar ki ga mata iri na wanda basu samu wanda zai tsaya musu ba?" Tace "kin san na gaya miki cewa ina karantar law ko? Kuma nafi bada karfi a bangaren family laws haka da kuma kare hakkin mata, saboda I was once in a family crises shigen wanda kike ciki yanzu and I thought duk rashin sanin hakkoki na ne ya saka ma na sha duk wahalar da nasha. Wannan yasa nake karatu akai dan in samu license din da zanke tsayawa mata i a karbar musu hakkin su a duk lokacin da naga an take musu shi. Ban gama karatu ba yanzu so am still just a student ba ni da damar tsayawa a gaban judge haka. But still ina da dan sani akan abin, sannan wannan zuwan nawa Nigeria ina zuwa na fara bincike a kan cases din marital abuses haka