Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
ku amma ba zaki gaya min ba? Ko message ai ya kamata ace kin tura min in ba zaki iya kirana ba" nace "ban dauka kana bukatar sani ba" yace "ina bukatar sani? Yasmin ce fa babu lafiya, ƴata ce fa a asibitin" da sauri nace "yanzu ai ka san an sallame ta ko? Sai me kake bukata kuma? Akwai wani abu ne da kake so?"
Sai ya danyi shiru, daga alama ya rasa abinda zai ce ne, Umar of all people ya rasa abinda zai ce? Sai kuma yace "kiyi hakuri in tambayar da nayi laifi ce. Allah ya huci ziciyarki" na juya idona ina mamakin yadda zai making maganar to sound as if I am the bad guy. Nace "ameen tunda haka ka dauka amma ni ina da more important things to do than jin haushinka, na kuma fadawa yanuwanka da suke asibitin dan haka na dauka zaka ji a gurin su. In yarka kake son gani you are always welcome ka zo ka aiko a kira maka ita ka ganta, in kuma muryar su kake son ji I suggest ka siya musu karamar waya ka basu yadda zaka ke kiran su duk sanda kake so"
Sai na katse kiran tare da yin tsaki, wai shi ya dauka dan zaman da mukayi a asibiti hakan yana nufin mun shirya kenan?
Bai daddara ba da sassafe sai gashi ya sake kira, lokacin Yasmin ma bata tashi daga bacci ba sai na dauki kiran na mikawa Asad wayar, ai kuwa ya kama zance kamar an bude pampo sai da yayi iyakacin yin sa sannan ya miko min wayar wai Daddy yace ya bani. Na karba sai na kashe na ajiye. Jimawa kadan sai ga sako ya shigo daga gare shi.
"I lost everything Jidda. My job, my dignity, my parents and my daughter's dignity. Ke kadai kika yi min saura. Please kar ki bari in rasa ki kema"
Na karanta na ajiye wayar ina jin zafi a raina, sai kuma na dauka na aika masa da reply
"You lost me tun kafin ka rasa wadancan. It is over. Get over it"
Na aika masa sai kuma na zauna ina tunanin abinda yake nufi da cewa ya rasa iyayensa dan ni nasan har jiya suna nan da ransu duk su biyun sai dai in yanzu da safe suka wuce. But ai dai ba zai kira ni har suyi hira da Asad ba idan har iyayen sa sun mutu da safen nan.
Sai ya turo min da wani sakon
"Bani da lafiya Jidda"
Nayi masa reply
"Allah ya baka lafiya yasa kaffara ce"
"Bana jin zan tashi Jidda. Nafi tunanin mutuwa zanyi"
"Allah yaji kanka ya yafe kurakuran ka"
Sai kawai na kashe wayar dan nasan ba rabuwa zai yi dani ba.
Da yamma yayan Hajiya suka zo gidan gabakidayan su, ina ganin su babu wanda yace min wani abu bayan gaisuwa nima babu wanda na cewa komai, daga baya kuma sai na ga sun hau saman Abba gabakidayan su, tun daga inda nake ina jiwo fadan Abba muryar sa har dashewa tayi akan fada amma bana gane me yake cewa sosai, sai daga baya sai gasu sun sauko. Amira ta leka ta tsakanin labule tana tsegumi sai tace min Mama Sa'a suna ta kuka ita da Hajiya, sai nace ta duba min ko anzo da Mammy, ta duba tace bata ganta ba.
Sai dare duk suka watse, a lokacin ne Farhan ta shigo inda muke ta saka ni a gaba da tambaya wai tana son jin gaskiyar abinda ya hada ni da su Hajiya, wai Abba yace sune silar da na baro gidan mijina nake zaune a gida, wai Abba yace asiri suka yi suna son Umar ya sake ni ya auri Mammy, wai kuma tana son ta ji gaskiyar me ye tsakanin Umar da Mammy.
Na girgiza kaina "Farhan Hajiya mahaifiyar ki ce, ko me tayi marar kyau ba zaki so ki ji shi ba, da ma dai ace abin bai riga ya faru ba shine zan iya gaya miki ko zaki iya preventing amma ya riga ya faru daga ni har ke babu abinda zamu iya yi akai sai dai mu dauki darasi daga abinda ya faru dan gudun faruwar sa a gaba. shima Abba na gaya masa ne ba dan ya dauki mataki ba sai dan yasan gaskiyar abinda ya faru. Sunyi min ba dai dai ba tabbas, amma Allah ya riga ya saka min tun kafin ma insan sunyi din. Dan haka ni babu wani abu a tsakani na da su sai fatan alkhairi"
Ta yi shiru duk zuciyarta babu dadi, sai tace " yanzu me kike ciki? Zaki koma gidan Umar ne?" Sai na girgiza kai da sauri. "Ban san me Allah ya rubuta min ba, amma ni in a zabi nane zance na gama auren Umar Farhan, auren Umar ya fitar min daga raina gabaki daya. Sai dai ko da mun rabun ina so ki san cewa ba saboda Hajiya ko Mammy ko wani ne daban ba ne, zan rabu da shi ne saboda shi, saboda na gaji da halin sa" ta dafa ni "amma fa ni ina ganin kamar ya bari da gaske, naga yayi laushi da yawa Allah kuwa, kin san dai am not a fan of Umar tun kuna dating ballantana kuma da nasan halin sa amma still ina jin tausayin sa kwanan nan duk sanda na ganshi ballantana ma a asibitin nan" tayi murmushi ta kara da cewa "duk da dai ance "kowa ya tuba dan wuya ba lada" nayi murmushi nima nace "fadin hausawa ne kawai. Tuba duk tuba ne idan dai har mutum ya tuba ne daga zuciyarsa kuma tsakanin sa da Allah. Kuma ni a iyakacin sanina ma da wahala ki ga mutumin da yayi nisa a aikata sabo kawai ya tuba yana cikin jin dadin aikata sabon, da yawa sai wani abu ya faru mai taba zuciyarsu sannan imani yake dawo musu, kuma in sun tuba in dai har taubatun nasuha ne ana saka ran Allah zai karba insha Allah, tsakanin su ne da shi. In dai har taubatun nasuha Umar yayi ina masa fatan alkhairi, komawa gidansa ne dai kuma ba zanyi ba"
Haka kwanaki suka ja. Kullum Umar sai ya kira ni ni kuma in bawa yaransa suyi magana. Sai ya cigaba da yi min messages ta text message da kuma through WhatsApp amma sai na daina kula shi, sometimes ma bana karantawa sai in goge dan bana son ya fadi abinda zai dame ni. He kept saying bashi da kowa sai ni, kuma bashi da lafiya and other stuffs, and I ignored him.
Ranar nan he texted me cewa wai Baffa Halilu ya kira shi yace wai yana umartar sa da ya rubuta takarda ya bani.
"Jidda I don't know what to do. Baba yaki saurara ta. And I can't even talk to Mama. Ban san ma wa zanyi wa magana ba dan bani da kowa sai Allah sai ke"
And I replied
"If you trust Him then He will guide you"
Daga nan ya dauke min wuta, ya daina text din, sai dai ya kan kira in hada shi da yayansa suyi magana shikenan.
Sai kuma ranar nan ina kwance ina baccin rana kamar yadda na saba sai naji muryar Abba yana kira na. Na tashi da sauri na amsa sai ya leko palon Umma yace in shirya in je sitting room munyi baki. Na koma toilet na wanke fuskata sannan na saka hijab na gaya wa Amira ta kula da yara zanje in dawo sannan na fita.
A sitting room din na samu bakin, Abba da Baba da Baffa halilu da Mama, sai kuma Umar a can bakin kofar shigowa a zaune. Na durkusa daga bakin kofar da na shigo na gaishe su suka amsa min, Baba har da tambayata yara, sai na zauna ina lissafa yatsun hannuna ina lura da yadda Umar ko dago kai bai yi ya kalle ni ba.
Baffa Halilu ne ya fara magana "to kusan dai nasan kowa ya san maganar da ta kawo mu nan, amma ba wai zuwa mukayi dan muyi ta mayar da magana ba, zuwa muka yi dan mu tura abinda ya faru ya wuce mu kuma fuskanci abinda yake gaban mu"
"Ni dai nine waliyin Umar, ni nazo na nema masa aure kuma ni na riko sadakin sa na bayar na karbar masa aure, amma kuma ban san duk matsalar da ake ciki ba sai yanzu. Sai yanzu da mahaifin yarinyar nan yayi min magana yace wai yana bukatar a bashi takardar ƴar sa shi baya so ta cigaba da zama da aure a kanta, sai a lokacin ya ke gaya min duk abubuwan da suka faru wadanda ni ban sani ba saboda bana gari. Bayan ya gaya min ne kuma na samu mahaifin Umar shima ya gaya min nasa bangaren naji. Bana bukatar jin magana daga bakin ki ke Jidda ko kuma daga gurinka kai Umar dan ina ganin kusan duk abinda zaku fada din an riga an fada. Kuma dukkan bangarori biyun sun yadda akan magana daya ba wai an samu rashin fahimta bane ba. Wannan ya sa naxe zan zaunar daku a tare gabakidaya ni kuma in fadi tawa fahimtar watakila ko za'a samu maslaha"
"Tabbas abinda ya faru dukkan mu mun amince cewa laifi na Umar ne, shima kuma da nayi magana dashi ya karbi laifin sa, amma ni kuma sai nake ganin kamar laifin iyayensa yafi yawa akan nasa, amma hakan ba yana nufin cewa bashi da laifi ba dan laifin su a gurin Allah sam bai kai yawan nasa laifin ba dan duk abinda ya aikata da hankalinsa ya aikata shi. Sai dai abinda nake nuna mana shine da ace iyayen sa sun kyautata gurin tarbiyyar sa da bamu samu kan mu a inda muke a yanzu ba. Kuma a ganina laifin mahaifin sa yafi yawa akan na mahaifiyar sa tunda ita mahaifiyar sa at least zamu ce tayi iyakacin kokarin ta shi kuma mahaifin sa shine ya saki tarbiyyar gabaki daya ya mayar da hankalinsa kan kasuwancin sa"
Daga nan kuma a laifi sai shi mahaifin Jidda, wanda maybe da ya tsaurara bincike a lokacin aurar da yarsa da ya bankado halin Umar da bamu sani ba, watakila da yayi haka da ya ankarar da iyayen Umar halin dansu kuma da sun dauki mataki tun a lokacin, laifin sa ma biyu kuma shine rashin jan yayansa a jiki yadda zasu iya gaya masa abinda yake damun su, da ace da akwai kyakykyawar dangantaka a tsakaninsu da tun farko da ta fahimci halin mijinta da gurin iyayenta zata zo, maybe da tun lokacin za'a yi maganin matsalar. Sai ita kuma kuma Jidda, she should have try ta samu hanyar gayawa magabata ba wai ta rike abin a ranta tana tunanin zai wuce ba, abinda addini ya tsara shine irin wannan maganar sai a gaya wa magabata su kuma sai su bi tsarin shari'ar wajen ganin an samu dai dai to"
Mama tayi gyaran murya tace "akwai laifina a nan" duk suka juyo suna kallon ta ban da ni da Umar sai tace "Jidda ta gaya min. Ta aiko babbar yar mu ta gaya min. Amma sai zuciyata ta ki yarda da maganar a karshe ma sai nayi kokarin dora laifi a kanta dan ina ganin kamar zuciyata ba zata dauki kasancewar maganar gaskiya ba, dana binciki maganar tun a lokacin watakila da na samo gaskiya, wata kila da bamu zo inda muke a yanzu ba, da abubuwan da suka faru ba su faru ba, watakila da ban ga abinda na gani ba"
Ta karasa maganar tana kuka, Baba ya yunkuro da bacin rai kamar zaiyi mata fada akan cewa na gaya mata amma bata dauki mataki ba kuma bata gaya masa ba sai Baffa ya dakatar da shi. "Kamar yadda na fada tun farko, ba mu zo gurin nan dan mayar da magana ba. Nazo ne dan in fada wa kowa laifinsa sai kuma mu san matakin da zamu dauka"
"Yanzu na gama fadar laifi, sai kuma abinda nake ganin shine a kamata muyi. Abu na farko shine dole mu gyara tushen matsalar, ma'ana Umar, abinda bamu bashi a da ba wato tarbiyya dole ita zamu bashi a yanzu, bashi tarbiyya kuwa ba yana nufin ignoring dinsa ba kamar yadda iyayensa suke yi a yanzu, ba shi tarbiyya ba yana nufin aura masa mai aikin matarsa wadda ake zargin sa da cewa ya lalata ba, bashi tarbiyya a gani na yana nufin jan shi a jiki, keeping him busy with something good, samar masa aikin yi, dora shi akan tafarkin Allah da kuma tunatar da shi girman laifin da yake yi"
"A ganina wannan auren da kuka yi masa bashi da wata ma'ana, ta yaya mutumin da yake auren kamilalliyar mace, kyakykyawa mai tarbiyya da ilimin addini da kuma na zamani dadin dadawa kuma wadda yake so amma bai daina halin sa ba sai kuma a aura masa wadda take totally opposite sannan ayi tunanin zai daina? Ta yaya? Tabbas Umar ba yaro bane ba yasan dai dai ya san ba dai dai na amma a ganina there is no harm in guiding him, making it easier for him to do the right thing"
Baba yace "ni ban yiwa Umar aure dan wai ya daina halinsa ba, nayi aura masa yarinyar can ne dan in koya masa darasi kuma dan in cika alkawarin da na dauka wa iyayen yarinyar wanda a ganina idan ba'a yi haka ba tamkar an zalinci yarinyar ne. Daina halin shi ko rashin daina wa is all up to him, shi kadai zaiyi deciding zai daina kuma ya daina din"
Baffa yace "but we can still help him ai, with prayers, nasiha and guidance. A ganina ita case din yar aikin ba dai iyayenta suna gudun abin kunya bane ba shi yasa suka dage akan ya aure ta? To an daura auren. Zama da ita ko rashin zama da ita ku barshi a matsayin choice din Umar. In yaga zai zauna da ita a matsayin mata fine in kuma ba zai zauna da ita ba kar ku takura masa a bisa hakan dan takura masan will do more harm than good a ganina. Idan ana maganar aure ana maganar zuri'a ne, idan kuwa ana neman kyakykyawar zuri'a to ana neman tsatso ne mai kyau. A shawarce Iyayenta su kawo ta nan gidan ku a bata daki ta zauna, sai shi kuma ku bashi lokaci idan a cikin lokacin ya ga zai zauna da ita fine, idan kuma ba zai zauna da ita ba sai ya sauwake mata ta koma gidan iyayenta a matsayin bazawara kunga an yi musu maganin wannan abin kunyar da suka ce suna tsoro. Shi kuma ba'a sake tura shi ga halaka ba"
"Abu na gaba kuma shine a shawarce gabaki dayan ku kuna bukatar break from each other, Umar kansa yana bukatar break daga gare ku ku iyayen sa kuma kuma haka, idan har kuna tare maganar ba lallai ta mutu a zuciyoyin ku ba amma ku bashi space yaje yayi tunani akan girman laifuffukan sa sannan ya fahimci inda ya tsaya da kuma inda zai dora a rayuwa. Ku ma kuma ku huce ku daina ganinsa for sometimes, duk da nasan abubuwan ba zasu wuce a zukatan ku ba amma zaku huce kadan"
Baba yace "ina zai je kenan a ganinka?" Baffa yace "Lagos" ba Mama ba har ni sai da muka dago kai muka kalle shi. Mama tace "Lagos? Ji nake zaman Lagos din yana daya daga cikin abinda ya kai shi inda yake a yanzu? Sai kuma ya sake komawa a yanzu da ya kamata ya kara nisa da garin?"
Baffa yace "ita shiriya ai ba a gari take ko a cikin mutanen garin take ba, ita shiriya a zuciya ta ke. Idan har Umar da gaske yake abinda ya fada cewa yayi tuba na gaskiya then zaman Lagos ba zai saka ya dawo ba. Eh tabbas gari yana da tasiri a wajen bayar da tarbiyya amma Umar already yana da tarbiyya, already tasan right and wrong ba wai yaro bane ba shi. Kuma ina so mu sani cewa akwai shiryayyun mutane a Lagos kamar wadda yake da akwai lalatattun mutane a Saudiyya. Abinda ya sa nake son ka tura shi Lagos din dan a can ne zaiyi fighting temptations din sa sosai, kuma a can ne zai samu abin yi. Tunda anan ba aiki yake yi ba kawai zaman kashe wando yake yi. Mahaifin sa kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Dukkan harkokin kasuwancin sa na can sai ya damka masa a hannunsa ya barshi ya cigaba shi kuma ya zauna a gefe ya saka masa ido akai. In ya ga dama ma zai iya komawa makarantar addini a can din dan akwai su da yawa, in bai ga dama ba ya bari, wannan a zuciya yake in an tilasta masa yaje din ma in babu abin a zuciyarsa karatun da wa'azin duk ba zasu ke shigar sa ba. Amma in akwai abin a zuciyarsa ko bai koma makaranta ba zai gyara rayuwarsa, ko sallah ya tsayar yake yi akan lokaci zata gyara masa rayuwar sa".
"Sai maganar data kawo mu nan baki daya, maganar auren Umar da Jidda. Duk abubuwan da suka faru a gidan auren su mu waliyansu bamu sani ba sai yanzu. Dan haka ni a matsayina na waliyyin Umar ina nema masa alfarma a gurin iyayen Hauwa'u da suyi hakuri. Su sake bamu wata damar. Mu zasu bawa dama ba Umar ba. Idan har Umar yayi wasa da damarsa ko ince damar mu dan tamu ce ba tasa ba, ni da kaina zan karbi takardarta a hannunsa in bata"
Abba ya girgiza kai "gyara muke kokarin yi. Gyaran dan ku kuke kokarin yi. Gyaran kuskuren ku kuke kokarin yi kamar yadda ni ma nake kokarin gyaran nawa kuskuren" Baba yayi saurin cewa "Dan Allah Alhaji kar ka ce ba zata koma ba. Nauyin ka da girman laifin yaron nan ya saka na kasa zuwa tunda abin nan ya faru ballantana in baka hakuri, amma yanzu ka duba darajar mu......"
Abba yace "ita na duba a lokacin da na bada