Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
da abubuwan da suka faru. Kalma daya biyu zasu fadi mommy, idan mommy tazo, in muka dauko mommy daga gidan Abba, shima kuma Umar din haka "me mommy tayi?" "Mai mommy tace?" Duk shine hirar tasu. Tabbas in zasu cire ta daga ransu ma ba da sauki ba.
Daga nan ya dauki yaran suka fice, basu dawo gidan ba sai dare, da ta tuna masa maganar gyaran dakin da zasu zauna sai yace "Mama su zauna a dakin ki mana for the time being, in Jidda ta dawo ai zasu koma gida ne" bai jira abinda zata ce ba ya fice.
A ranar a dakin ta ta shirya su suka kwanta, addu'ar Yasmin ta bacci ita ce "Allah Allah Allah ka sa gobe muje da Daddy mu dauko Mommy mu koma gida" sai ta shafa ta kwanta ta juya baya.
Asad kuma ya tashi zaune ya fara jera wa Mama tambayoyi
"Mama anan dakin zamu kwana?"
"Eh"
"A ina zamu kwanta? Akan dago ko a kan carpet?"
"Akan gado"
"Damu da wa zamu kwanta?"
"Da kai da Yasmin"
"Daddy kuma fa?"
"Ba'a nan zai kwanta ba"
"Mommy fa?"
"Itama ba anan zata kwana ba"
"To ke kuma fa? A ina zaki kwana?"
Ta nuna kan carpet
Ya zaro ido "a'a ki hawo kan gado ki kwanta kar dodo ya zuro hannunsa ta kasan gado ya kamaki. Amma kuma in kika yi addu'a dodon ba zai zo ba, mommy tace idan mutum yayi addu'a dodo baya zuwa, kullum sai sunyi mana addu'a ita da Daddy ni da Yasmin in zamu yi bacci, mu biyu muke kwana a dakin mommy ita kuma mommy sai ta tafi dakin Daddy amma sai su bar kofa a bude saboda cikin dare in munji tsoro sai mu falfala da gudu mu shiga dakin su mu buya"
Mama ta rufe baki tana dariya, "kai Asad ka fiya surutu ka kwanta kayi bacci" ya kwanta ya rufe idonsa "mommy tana karanta mana story sannan tayi mana addu'a kullum kafin muyi bacci" ta zauna a kusa dashi tana kallon sa, sosai yake tuna mata da yarintar Umar dinta, kamar su daya kuma surutun su daya.
Sai data samu yayi bacci sannan yi fita ta tafi dakin Mufida tana so ta tuna mata da zancen bikin yar kawarta da akeyi gobe juma'a kuma tana so suje tare, dan mufidan ta tashi da wuri saboda in bata gaya mata ba zata makarar dasu da wannan shegen baccin safen nata da sai azahar take tashi.
Dakin a bude yake, mufidan tana kwance a kan gado ruf da ciki da waya a kunnen ta ta juya bayan ta can daya side din tana magana kasa kasa yadda ita kanta Maman da ta shigo dakin badan yadda gari yayi tsit ba daba zata ji abinda take fada ba.
"Kayi hakuri, gobe insha Allah zan san dabarar da zanyi. Kasan dai halin da nake ciki a gidan nan"
"Eh tace gobe zan raka ta wani event na wani biki, zan ce mata cikina yana ciwo ba zan je ba in ta tafi sai in fito"
"Okay in ta tafin zanyi maka waya kai ma ka fito. Around 12-1 zata fita"
Ta danyi dariya
"Babu wani wuni fa. Nasan na zata dade sosai ba Kasan saboda rashin lafiyar Baba lekawa kawai zata yi"
"So sharp sharp kawai please"
"Okay mu hadu a kofar gidan zoo"
"Can't wait to see you too"
Ta sake dariya.
Mama ta juya ta koma falo tana dafe bango tare da rike kirjinta. Menene wannan taji? Waye suke waya da Mufida? Akan me suke magana? Mai zasu yi in sun hadu? Saurayinta ne? Me yasa ba zai zo gida ya ganta ba har sai tayi karya ta saci jiki ta je sun hadu?
Taji kamar ta koma dakin ta chakumi mufidan tayi ta dukan ta har sai ta gaya mata gaskiya amma kuma ta san cewa ba zata samu cikakkiyar gaskiyar daga haka ba, dan kusan shekara guda kenan Umar da kansa yazo gida ya kwakwkwada wa mufidan mari ya cevya ganta tana shiga motar wani, sannan ya saka mata takunkumin fita wanda ita Maman ta cigaba da ensuring, amma kuma har yanzu sun kasa gano kan mufidan ta kasa tsayar da hankalin ta guri daya ta fitar da mijin aure ga kuma kumbiya kumbiyar da take tayi wadda tafi kama da ta marasa gaskiya.
Sai maman ta ga kamar wannan chance ne nata na sanin gaskiyar halin da yar autar tata take ciki, na sanin waye wanda suka yi waya yanzu kuma menene hadin sa da Mufida da har take shirin yi mata karya dan ta hadu da shi. Bayan an bata damar yin saurayi da kuma kawo shi gida suyi zance.
Ranar bata samu baccin kirki ba tana tunani, zuwa safe ta yanke shawarar abinda zata yi. Shawarar kuma ita ce; zata bi Mufida a baya ta ga gurin wanda zata je da kuma abinda zata yi a can din.
Ranar Friday din da safe bayan sun kammala komai na routine din gida, ya saka anyi wa yara wanka sai ga Umar nan ya shigo a gaggauce kamar mai sauri yana ta duba agogo, ta lura yau yayi wanka ya saka kaya masu kyau har Aunty ta a tsokanar sa
"ango ka sha kamshi"
A tare suka watsa mata mugun kallo da shi da Mama, ita Mama ma har ta manta wai yau ne Baban yake da niyyar daura wa Umar aure dan ko maganar basu kuma yi da shi ba ballantana da Umar.
Briefly ya dan zauna da yaransa sannan kuma ya danci abincin da ta ajiye a gabansa ta matsa masa yaci kamar yadda take yi kullum tunda abin ya faru a matsayin ta na uwar da take son danta, kuma in dai bata yi masa haka din ba ba ci yake yi ba.
Yau ma bai fi loma uku yayi ba ya mike ya ce zai he je unguwa ya dawo. Ta lura kamar yau ransa da dadi sai ta fara tambayar kanta ko dai gurin Jidda zashi? Ko dai sun fara daidaitawa?
Bayan ya fita ne ta aika a taso Mufida tazo tayi breakfast ta shirya zasu fita unguwa amma sai ga sako daga mufidan cewa bata jin dadi cikinta ne yake yi mata ciwo, mama tayi shiru tana tabbatar da abinda taji jiya. Sai ta je ta shirya kamar mai fita unguwa tazo dakin Mufida tace "ki tashi ki ci abinci ki sha magani sai ki koma ki kwanta, ni zan leƙa gidan bikin"
Mufida ta dago kai tana kallon ta tare da yamutsa fuska tace "to Mama. A dawo lafiya" sai ta koma ta kwanta. Mama ta fita tare da jan kunnen su Yasmin akan kar su fita waje su yi zamansu suyi wasa ko kallo kafin ta dawo ko kuma daddyn su ya dawo, daga nan ta fita waje inda already driver yake cikin mota yana jiran ta suka fita aka rufe gate. Sai dai suna fita din sai tace da drivern ya shiga layin da yake facing din gidan su ya samu guri daga gefe yayi packing sannan ya taya ta duba gate din gidan su ya kuma gaya mata idan Mufida ta fito.
Basu wuce minti talatin ba mufidan ta fito taci kwalliya fes da ita, ta tari adaidaita sahu ta hau ta tafi, nan take Mama ta bawa drivern umarnin yabi adaidaitan, suka yi ta bin sa tiryan tiryan har gaban gidan zoo sai ya tsaya Mufida ta sauka su kuma suka tsaya can nesa da ita, bata dade da sauka ba sai ga mota ta tsaya a gabanta, ta bude gaba ta shiga motar ta tafi su Mama kuma suka bi bayanta.
A lokacin gabakidaya hankalin Mama ya gama tashi, gabanta faduwa yake yi sosai tana tsoron abinda zata yi finding in ta cigaba da bin Mufida but she couldn't stop, tana so ta sani, waye Mufida take tare da shi kuma menene tsakanin su?
Sai taga sun dauki hanyar barin gari, zuwa wata unguwa da bata da cikowa sosai sannan suka shiga wani layi suka kuma tsaya a kofar wani gida da Mama ta ga yafi mata kama da gidan gona, shi kuma drivern Mama yayi packing a can bayan su a karkashin inuwar wata bishiya yadda ko da Mufida ta juyo ba zata gane motar ba. Motar da Mufida take ciki tayi horn da karfi, ta sake yi, sai kuma na cikin motar ya fito da alama ransa a bace yake yaje ta tura gate din ya fara kokarin bude shi.
Mama ta dafe kirjinta da hannu biyu "Doctor Bashir?" Ta fada cikin mamaki, kamar ya ji ta sai ya juyo da fuskar sa side din ta yadda zata gane shi sosai sannan ya koma cikin motar ya shigar da ita cikin gidan gonar tare da barin gate din a bude da niyyar idan mai gadin ya dawo daga yawon da ya tafi yi ya tabbatar cewa yayi laifi.
Mama ta balle murfin mota ta fito. Ranta a matukar bace, wannan wanne irin cin amana ne? Bashir din da yake aminin Umar wanda Umar yake kai wa har cikin gidan su cikin yanuwansa amma shine mai daukan kanwarsa zuwa gidan gona a bayan gari? To ma wai uban me yake yi mata a cikin gidan gonar?
Zuciyarta ta san amsar.......
Amma zuciyarta bata son ta yarda da amsar.......
Da sauri ta fara tafiya a kafa zuwa gidan, yar tazarar da take tsakanin inda suka yi packing da kuma gidan gonar ya saka ta dan dauki lokaci kafin ta je, babu kowa a bakin gate din dan haka ta shiga, ta ga motar anyi packing din ta a gaban wani gini a ciki amma babu kowa a ciki, ta tabbatar suna cikin ginin, amma abinda baya tabbatar ba shine abinda suke yi a cikin ginin. Shine kuma abinda take so ta tabbatar
Ta tura kofa a hankali ta shiga falon tana lura da kofofi biyu da suke facin dinta amma babu kowa a falon sai kamshin turaren Mufida, turaren yarta. Ta doshi ɗakunan guda biyu tana tunanin wanne ne suke ciki, tana kuma fatan ta shiga ta tarar ba abinda take tunani bane ba, amma idan ba shi bane ba to menene? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Kofar farko ta tura da dukkan karfin ta cikin karfin halin da bata san tana da shi ba ta shiga, sai dai kamar yadda tayi addu'a ba abinda take tunanin gani ta gani ba, instead abinda ta gani yafi karfin abinda take tunani. Mace da namiji ne a kwance akan gado, turmida tabarya, suna aikata abin da miji da mata ne kadai aka halatta wa aikatawa, amma duk ba wannan ne tashin hankalin ta ba, tashin hankalin ta shine tasan namijin, danta ne, Umar din ta ne, tsirara tamkar yadda ta haife shi.
"Umar!!!!!!!" Ta ambaci sunansa, wanda hakan ne ma ya ankarar da shi da kuma abokiyar alfashar sa da shigowar ta dakin.
Bai san sanda yayi tsalle daga kan yarinyar zuwa karshen dakin ba, cikin tsananin tsorata da razana, idonsa cikin idon mahaifiyarsa.
Sai kuma ta rufe idonta da sauri sannan ta juya cikin laluben hanya ta fita daga dakin ba tare da ta san inda kanta yake ba. A cikin rudewar tata ne ta bude next door ta fada cikin dakin
Abinda ta gani a dakin ne ya saka ta fara tantamar anya kuwa ba ta mutu bane ta bar duniya, anya kuwa ba hisabi ne ake yi mata ba?
Yar autar ta ce Mufida kwance akan gadon itama kamar yadda ta haifo ta, samanta kuma babban aminin yayanta ne.
"Mufida!!!!!"
Ta kira sunan ta itama, sannan dan sauran ganin da ya rage a idonta ya kauce, bakin duhu yayi replacing din sa, sai kuma ta zube a kofar dakin cikin halin sumewa.
*Ina sake tunawa masu karanta littafin nan ba tare da sun siya ba cewa na siyarwa ne, idan har baki biya ni anan ba to kuwa tabbas zaki biya ni a garin da babu kudin biya, dan hakkinane, Allah kuma baya yafe hakkin wani sai in shi ya yafe da kansa*
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing. In kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*Black Friday 2*
*Umar*
"Umar!!!!!" Kamar daga sama yaji an kira sunan sa da karfi, kiran da ya ji shi tamkar saukar mari akan fuskar sa. Ba kiran sunan ne ya firgita shi ba, ba kuma jin da yayi tamkar mari a fuskar sa ne ya firgita shi ba, a'a muryar da yaji an kira sunan nasa da ita ita ce ta firgita shi.
Ya juyo a razane zuwa bakin kofar dakin da yake aikata alfashar sa a ciki, dakin da ya rufe da hannunsa wai dan ya hana wani shigowa ya ga abinda yake yi, forgetting cewa babban wanda yake sabawa yana ganinsa komai killacewar da yayi kuma komai duhun gurin da yake. Kuma shi mai ganin nasa shine wanda zai hukunta shi duniya da kuma lahira.
Sai dai abinda ya gani a bakin kofa shi ya tsorata shi tsoratar da tunda uwarsa, matar da take tsaye a bakin kofar, ta haife shi bai taba yin irinta ba.
Mama ce, a tsaye a bakin kofar idanuwan ta a cikin nasa, maman sa, mahaifiyarsa, matar da yafi so fiye da kowa a duniya, matar da yafi jin nauyi fiye da kowa a duniya, matar da tafi sonsa fiye da kowa a duniya.
Bai san sanda yaje bayan gadon ba sai kawai ganinsa yayi a can, bugun zuciyarsa tana tsayawa chak kamar yadda kwakwalwar sa ta daina aiki gabaki daya, ya ga ta runtse idonta sannan ta juya da sauri tana laluben hanya ta fita daga dakin, ya runtse nasa idon shima yana tabbatar wa a ransa cewa mafarki yake yi, mugun mafarki yake yi. A take kuma ya gaya wa kansa cewa ba zai taba yadda wannan mugun mafarkin ya zama gaskiya ba, ba zai kuma aikata abinda yake aikatawa ba.
Sai dai jin muryar ta da ya sake yi ta sake yin wata karar cikin ambaton sunan kanwar sa, mafi soyuwa a zuciyarsa a saman dukkan sauran yan'uwansa shi ya saka ya bude idonsa da sauri, hoping ya ganshi akan gadon sa na dakinsa da yake gidan su, ko kuma ya ganshi a kan gadonsa na gidansa rungume da matar sa, ko kuma ma ya ganshi a dakinsa zamanin yarintar sa, hoping dukkan abinda ya faru mafarki ne, dukkan mummunar rayuwarsa mafarki ce.
Amma sai ya ganshi still a cikin mafarkin sa, a cikin mummunan mafarkinsa durkushe a can bayan gado a cikin dakin da ya aikata da yawa daga cikin alfashar da ya aikata a rayuwar sa. A cikin mummunar rayuwarsa.
But was she really there????
Was his mother really there???
Did see really see him????
Ko dai hallucinations yake yi?? Ko dai ya fara samun matsala a kwakwalwa?
A lokacin babu abinda ba zai iya bayarwa ba dan ya kasance cewa da gaske matsala ya samu a kwakwalwa ba wai abinda yake tunani bane ba.
But what if abinda yake tunanin ne?
Ya rarumi wandonsa ya saka ignoring matar da take ta babatun tambayar sa wacece ta shigo, ya fita da sauri a dai dai lokacin da Mama ta sulale ta fadi a kofar dakin da yake kusa da inda ya fito.
Ya tsaya yana kallon ta, yana tabbatar wa cewa ita din ce ko aljana bace ba ko kuma mai kama da ita bace ba, sai kuma ya daga kansa a daidai lokacin da yaji an kwalla kara da muryar da tayi kama da ta kanwarsa Mufida. Mufidan ce a zaune akan gado hannunta rike da bedsheet tana kokarin kare tsiraicin ta, idonta kamar zai fado kasa saboda tsoro da razana, a gefen gadon, hannun sa rine da wandonsa yana kokarin karasa daure tazugen wandon, babban abokinsa ne a mu'amalance, kuma amininsa a harkar lalatarsu. Bashir.
Duk da toshewar da kwakwalwar sa tayi amma image din da ya gani ya tabbatar masa da abinda ya faru. Ko kuma daga dukkan alamu, abinda ya dade yana faruwa. Bashir, amininsa da suka jima suna jagorantar junansu zuwa ga aikata alfasha shine yake aikata alfasha da kanwarsa uwa daya uba daya.
A dai dai lokacin da yake daki yake aikata zina, zinar da ansha gaya masa kuma ya sani cewa bashi ce, a dai dai lokacin few meters away from him ake karbar bashin da yake dauka daga gurin kanwarsa. Kuma babban aminin sa ne mai karbar.
Hada idon da suka yi da Mufida shi ya saka ta fadowa daga kan gadon itama, tana kara nannade jikinta a cikin bedsheet din, babu inda baya rawa a jikin ta, yayinda shi kuma Bashir ya tsaya a inda yake kamar statue, gabakidayan su babu wanda ya tantance mai yake faruwa.
Umar ya fahimci mai yake faruwa tsakanin Bashir da Mufida amma bai fahimci mai ya kawo Mama gurin ba. Bashir ya fahimci cewa ashe Umar yana cikin gidan sanda suka shigo da Mufida, dan dama ya ga kofar falon a bude sai dai bai kawo Umar din bane ba dan ya jima rabon da yazo, tunda Jidda ta bar gidan sa, amma shima bai san ya akayi Mama tazo gidan ba. Mufida farko ta dauka Umar tare da Mama suka shigo, amma kuma ya akayi babu riga a jikinsa?
"Bashirrrr?"
Umar ya ambata cikin muryar da ta ratsa dukkanin ilahirin gidan sannan yayi kukan kura ya tsallake gadon da yake tsakiyar sakin ya damki Bashir ya buga shi da jikin dogon mirror din da yake dakin, mirror din ya tarwatse a gurin, sannan ya dunkule hannunsa ya fara nausar bakin Bashir din, burin sa ya fitar masa da hakoran gaba gabakidayan su dan ya kasance har abada in dai ya bude bakinsa sai ya tuna da abinda yayi. Sai ya tuna da cewa ya bata rayuwar kanwarsa.
Amma abinda yayi ne ko kuma abinda suka yi????
Sannan kuma shi kannen mutane nawa ya bata???
Kuma it doesn't look like forcing Mufida yayi, it looks