Chapter 79 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   79 / 106

234K to 237K   out of 316K words

gwammace ta fita ta bar mijinta da yar aiki a gida, babu wanda yafi karfin shaidan, even the most purest of hearts....."

Ya dakatar da ita "Hajiya Maryam, idan komai zamu ringa jingina shi zuwa ga kaddara kuma komai zamu ke dangantaka shi da laifin shaidan then me yasa akayi wuta kuma akayi aljanna? Mr yasa ranar alkiyama za'a ware yan wuta a kuma ware yan aljanna? Me yasa ba za'a bar shaidan shi kadai ya shiga wuta ba tunda komai laifinsa ne ba namu bane ba?" Ya juya yana kallon Umar yace "shi shaidan ai yana shiga ziciyar wanda ya bar masa gurbin da zai zauna a ciki bai cika zuciyar tasa da abubuwa masu muhimmanci ba, kamar soyayya Allah da Manzonsa, kamar yawan ibadu da aiyuka masu kyau, kamar tunane tunane masu ma'ana ba gurbatattu ba. Amma in dai mutum ya kusanci sabo, in dai mutum ya saka a ransa yana son aikata sabo, to tamkar ya aikawa da shaidan katin gayyata ne zuwa zuciyarsa"

"Na shiga ban dauka ba bata fidda barawo Umar, shiga dakinta kawai da kayi da kuma maganganun da ka gaya mata kawai sun daure ka da jijiyoyin jikinka. Gaskiyar Abinda ya faru a dakin mu bamu sani ba ku kadai kuka sani sai kuma Allahn daya halicce ku.shi yasa Allah ya ce mana kar mu kusanci zina, dan kusantar tata shine yake jawo yin nata. Yanzu kuwa in dai binciken abinda muka tura ayi bincike akansa ya bamu amsar da ba ita muke so ba, ko kai kayi ko ba kai kayi ba zaka aureta tunda kayi mata alkawari nima kuma yanzu na fada a gaban iyayenta" Umar yayi sauri ya dago kai yana kallon sa, zai fara magiya, sai ya juya kansa gefe yace "Amma abinda nake so in tambayeka yanzu shine, sanda ta gaya wa matarka, har matarka ta tuhumeka da maganar, ka fada mata abinda ka gaya mana yanzu? Cewa ba ka yi ba?"

Umar da hankalin sa gabaki daya ya tafi kan maganar auren Asabe, yace "nayi kokarin gaya mata Baba, amma bata saurareni ba, kuma ko na gaya matan ma ba lallai ne ta yarda ba" Baba yace "saboda me?" Umar ya dago yana kallon sa bai ce komai ba, Baba ya sake cewa "Saboda menene ba zata yarda ba? Matarka tana sonka duk mun sani, kuma kai uban ƴaƴan ta ne, kuma babu wanda zai rufa maka asiri duk duniya bayan mu sama da ita, amma me yasa kace ko ka gaya mata ba zata yarda ba?" Umar ya sake yin shiru bai bayar da amsa ba, yana sauraren yadda zuciyarsa take lugude a kirjinsa. Baba ya sake tambaya

"ko kun taba samun matsala ne mai kama da wannan?"

Umar yayi sauri ya dago kai amma bai ce komai ba. Mama tace "Baban Faruq ya kuma zaka ke neman wani laifin daban bayan ga wanda yake gaban mu?" Sai ya juyo yana kallon ta sannan yace "Hajiya Maryam, tashi ki fita" tayi shiru fuskarta na nuna rashin jin dadin abinda yayi mata sai ya sake cewa "ki tashi ki fita nace, inaso zanyi magana da ɗa na" sai ta mike kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ta dan kalli Umar kadan sannan ta fita tana jan kafa.

Baba ya dawo da hankalin sa kan Umar yace "ina jin ka, akwai wani abu daya kamata in sani? Akwai wata matsalar da kuka taba samu da matarka irin wannan? And be very careful when answering me, idan kayi min karya kuma na bincika na fahimci gaskiya hukuncin da zan yanke akan ka sai yafi wanda zanyi maka idan naji gaskiya daga bakin ka"

Umar ya rufe idonsa ya bude, sannan ya saka yatsansa yana shafar sunan Jidda da yake hannunsa, a ransa yana tunanin me yasa ya iya gaya wa Jidda? Me yasa duk laifin da yayi yake amsawa Jidda? Me yasa ya iya gaya mata har wadanda bata sani ba duk kuwa da yasan ranta sai yafi na kowa baci akan maganar a matsayin ta na matarsa, me yasa yake iya zubar da hawaye a gabanta amma yanzu ya kasa yi a bayan idonta ballantana yaji sanyin suyar da zuciyarsa take yi a cikin kirjinsa.

"Ina jin ka" Baba ya sake magana "akwai wata matsala da kuka samun da ita kafin wannan wadda take kama da wannan? Wadda har ta saka ba zata yarda da kai ba ko da kayi mata bayani?"

Umar ya sunkuyar da kansa kasa yana lissafo cases din da sukayi ta samu da Jidda, wacce zai fada wacce zai bari? Anya ma kuwa zai iya fadar?

Tabbas akwai abubuwa da dama na miji wanda matarsa ce kadai ta sani, akwai maganganu da dama wa'danda miji zai iya gayawa matarsa amma ko uwar da ta haife shi ba zai iya gaya wa ba balle uba. Anya zai iya? Babu abinda yake so a lokacin irin Jidda's touch, ina ma dai tana kusa da shi ta rike hannunsa ta rada masa cewa "you can do it" amma yasan ba zai samu ba hakan ba dan haka sai ya hada hannayensa guri daya ya rike su together sannan ya gaya wa kansa a hankali "you can do it".

Baba yace "me kace? Ka daga murya kayi min magana, akwai wata maganar kafin wannan?"

Ya dago kai "eh akwai Baba" sannan ya mayar da kansa kasa, bayajin zai iya kara wata kalma bayan wannan, yaji Baba ya ja doguwar ajjiyar zuciya tare da ambaton "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" sai Umar ya runtse idonsa as he felt his heart breaking into thousand pieces.

Shima kenan, shi kuma Baban fa mai yaji?

Sun jima a haka sannan Baba yayi magana ba tare da ya kalle shi ba "tashi ka fita daga gabana. Bana son ganinka a kusa da ni"

Umar ya mike da sauri har ƙafarsa tana hardewa kamar zai fadi ya fita daga dakin tare da jan kofa ya rufe sannan ya rufe idonsa ya jingina kansa da jikin kofar. Muryar Mama yaji a bayan sa "ya kuka yi? Ya fasa hada auren ko?" Ta fada muryar ta dauke da tashin hankalin yanayin da taga dan lelen nata a ciki. Umar yaji tayi mishi fami a ciwon da yake cikin zuciyarsa, shi har ya manta ma da wani batun aure da Asabe, matsalolin sa kamar kara gaba suke with each second. Wannan wacce irin rana ce? Ya juyo amma sai ya kasa hada ido da ita yace "nima ban sani ba Mama" sai kuma ya fice daga falon da sauri kamar yadda ya shigo da sauri.

Motarsa ya nufa yayi mata key sannan ya fice daga gidan, a ransa yana lissafin abinda zaiyi, anya kuwa shima ba zai bi irin hanyar da Jidda ta dauka ba? Anya ba zai hada kayansa shima ya gudu a neme shi a rasa ba, ya ga guduwar is kind of working out for her tunda gashi nan maganganu suna fitowa tun kafin ta yi magana.

Gidan sa ya tafi, gidan su shi da Jidda. Ya shiga falo ya kwanta akan kujera ba tare daya damu da kurar da kujerar tayi ba, sannan ya fara bin falon da kallo yana tuno memories din yayansa yadda suke hargitsa falon ita kuma uwar tana yi musu fadan sun bata mata guri, Jidda akwai tsafta, tun daga jikinta har gidanta har yayanta har shi kansa mijinta kullum sai ta gyara su fes, kuma tsaftar yana tunanin har zuciyarta haka take.

Ya tuna da yadda shari'ar dazu ta kasance, yadda gashi yana da gaskiya amma bashi da yadda zaiyi yayi bayanin da za'a yarda da shi kuma ya tabbatar ya fada cikin ramin da bashi da kalaman da zasu fito da shi daga ciki, and that hurts a lot, wai dana haka Jidda taji a lokacin da take da gaskiya a gaban Aunty Afia amma ya juya magana ya goge evidence dole aka ba shi gaskiya ita kuma aka dora mata laifi? Haka taji wai a gaban Mama sanda ta kai maganar sa kuma ita ce mai gaskiya amma ya juya maganar ta koma ita ce mai laifi shine mai gaskiya? Shi duk a lokacin a nasa tunanin gani yake yi it won't hurt her that much tunda abin zai wuce and it will cover his dignity, wanda bayan family dinsa shine babban abinda ya damu da shi.

Sai ya dauko wayarsa a aljihun sa ya shiga messages ya nemo number din ta sannan ya tura mata sako kamar haka

"Am sorry Jidda. Am sorry for deleting those pictures daga wayar ki, and for saying the things I said about you to Aunty Afia and to Mama. I am sorry"

Ya tura mata sannan ya dora wayar a kirjinsa yana jin kalmar sorry din tana amsawa a zuciyarsa saboda daga can ta fito.

Ya jima a haka sannan yaji kiraye kirayen sallar laasar, sai ya tuna da maganar da Baba ya fada dazu cewa in ba'a cika zuciya da ibada da ayyukan alkhairi ba shine shaidan yake samun gurin zama a cikin ta, gashi shi ko azahar ma baiyi ba. Ya mike ya shiga cikin dakinsa ya zarce toilet yayi alwala sannan ya fito ya kuma daukan wayarsa da key din motarsa ya fita, a masallaci ya tsaya yayi sallar azahar sannan akayi laasar tare da shi.

Daga nan motarsa ya koma yana lissafin abubuwan da ya rasa so far, his job and his dignity, ga kuma auren da ake neman kakaba masa, menene kuma next?.

Ya girgiza kansa da sauri a hankali yace "not my family, no!" Sai ya juya motar zuwa hanyar gidan da Jidda take. At least zuwa kofar gidan will make him feel closer to her ko da kuwa bai samu ganin ta ko yayan su ba. A kofar gidan yayi packing yana kallon gidan, yana kallon windows din sama yana aiyanawa ko akwai wadda take a dakin da Jidda take zaune a yanzu? Ko zata ji a jikinta yana gurin ta leko ya ganta ko da na second daya ne?

Bai jima da tsayawa ba aka bude kofa aka fito, one of the security guards din da suka yi rigima da su dazu, dazu ne abin ya faru but it feels like an jima da yin abin saboda yawan abubuwan da suka faru after it. Ya zo gaban motar tare da yi masa knocking a jikin glass, ya sauke yana kallon sa sai yace "da Allah malam ka dan ja motar ka gefe, ba'a packing anan, kofar gidan mutane ce" Umar ya dauke idonsa daga kansa, in normal days zai fito ne suyi rigima but today, now, rigima is the last thing a mind dinsa dan haka sai ya saka motar a giya ya kara gaba kamar yadda security din ya fada.

Ya jingina kansa da kujerar motar ya rufe idonsa. Bai jima ba wata mota tazo gate din ya ga an bude mata da gudu ta shiga, hakan ya tabbatar masa da cewa mai gidan ne ya dawo amma sai yaji baya jin haushin sa yanzu kamar yadda yake ji dazu, ko babu komai he took his family in and put a roof over their heads and food in their bellies.

Sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib sannan ya kunna motar ya bar gurin, yana sake kallon windows din da fatan zai hango ko da inuwar ta ce amma ko inuwa mai kama da tata bai gani ba. Gidan su ya dosa, sai dai kuma gabansa sai mugun faduwa yake yi har daci yake ji a bakin sa, gani yake yi kamar da akwai wata sabuwar rigimar da take jiran sa a gidan amma sai yayi saurin kawar da maganar da cewa yasan case din Asabe ne kawai za'a cigaba a kansa, maybe sun dawo daga asibitin.

Yayi tsaki, ko yayi tafiyar sa wani gurin ne ma kar yaje gidan? In basu ganshi ba ai ba zasu yi masa maganar ba ko? Amma kuma dai sai ya tafi gidan..........


*Baba*

Ranar kamar kullum yaje sallar asuba, sannan ya dawo ya zauna a dakin sa akan sallaya yana ta adduoin sa kamar yadda ya saba, a lokacin ne yaji karar wayarsa kamar sako ya shigo, ya share ya cigaba da harkokin sa dan yasan ba zai wuce network providers din sa ba da basu da aiki sai damun mutum da sakonni marasa ma'ana. Har sai daya kammala sannan ya tashi ya dauki wayar sa da take gefe ya koma kan gado da niyyar sake komawa bacci kafin gari ya karasa wayewa kuma ya fita yaga abinda hali zai yi. Ya tsani wannan rashin aikin nasa, ya saba shekara da shekaru kullum ya tashi zai je gurin aiki, kullum yana da abinda yake looking forward to doing, amma yanzu dai yayi ta zaman gida in ya gaji kuma sai ya fita yayi ta yawon da babu gurin zuwa. Tun yana kai wa abokai da yan'uwa ziyara har ya hakura ya daina zuwa dan gudun kar ace yana zuwa kwadayi.

Zaman banzan kuma shi yake haddasa masa tunane tunane marasa ma'ana, musamman yanzu akan batan Hauwa'u da yayanta. Kullum da ita yake kwana da kuma ita yake tashi a ransa, menene ya faru da har zata zani ta bijire masa ta bijirewa mijinta sannan ta debi yaya ta tafi wata duniyar da babu wanda ya san inda take. Anya kuwa ba wani mugun abu ne ya faru da su ba? Duniyar nan fa bata da kyau, mugaye mun kusan fin mutane na garin yawa a gari.

Wannan ya saka yayi abinda bai taba tunanin zaiyi ba, ya tura amaryar sa garin su da niyyar ta bincika ko can ta tafi tunda ta taba zuwa ta san hanya. Amma har yanzu suma shiru, duk inda suke tunanin zata je acan din sun je amma bata je ba. Ya tuna cewa jiya da suka yi waya Tahir ya gaya masa akwai gurin da zasu je a jiyan ko Allah zai saka a dace ko ta je can, gidan wata cousin din su Umma ce.

Ya gyara kwanciyar sa sannan ya jawo wayarsa da niyyar ya kira Tahir din yaji ko sun je can din kuma menene suka samu. Sai dai sunan da ya gani akan wayar ta sa ya saka ya tashi zaune da sauri, sannan ya nemo eye glasses dinsa ya saka dan ya tabbatar ba wai idonsa ne yake yi masa gizo ba.

Hauwa'u

Ya maimaita sunan "Hauwa'u?" Saboda rikice wa ma sai ya kasa tantancewa ko missed call ne ko kuma message, sai daya danna sannan yaga message ya bude. Ya tashi zaune sosai yana gyara glasses din idonsa sannan kuma ya karanta sakon nata. Sai kuma ya zauna sosai ya sauko da kafafuwan sa kasa ya sake karantawa.

Wannan yarinyar me take nufi ne? Me take cewa ne? Ta nan ta bullo kuma dan tayi justifying guduwar da tayi?

Amma kuma anya? Mijinta ne fa kuma uban yayanta, sannan shi kansa shaida ne na irin soyayyar da take tsakanin su, sannan kuma tun tashin ta Jidda ba mai karya bace ba, ita ba mai surutu bace ba ma tana da sanyi sosai. Da dai Farhan ce ko Amira sune masu zance sosai, mai surutu kuwa yawanci yana da karya.

Amma kuma anya???????

Ba wai maganar da ta fada ce ta tayar masa da hankali ta saka ya cire hularsa ya fara firfita fuskar sa da ita duk da yanayin sanyi ne bana zafi ba, sunayen da ta ambata ta kula alakanta su da mijinta akan wannan maganar, wannan mummunar maganar.

Baccin da bai koma ba kenan, ya ringa sakawa yana warwarewa. Yaji dadin jin suna lafiya amma kuma Yana so ya tabbatar gaskiya yar ta sa ta fada ba wai zargi ne irin nasu na mata ba dan wadansu matan basa tantancewa tsakanin mijin da yake neman aure da kuma manemin mata, wata matar da ta ga mijinta yana waya ko chatting da mata sai ta fara zargin shi da zina. And a cikin zuciyarsa sai yaji yana wishing hakan ne ya faru, yadda za'a iya zaunar dasu ayi musu fada ayi musu nasiha shikenan maganar ta wuce, amma kuma deep inside him sai yake jin cewa maganar ta wuce zargi, yanayin yadda Jidda tayi maganar akwai wani assurance da yake nuni da kamar she is sure of what she is saying.

Ta ce yayi bincike, sai dai shi bai san ta inda zai fara binciken ba, Jamilar da ta ambata tayi aure tana gidan mijinta, ta yaya kuma zai je ya bincike ta da wannan maganar? Sai kuma Mammy, sai dai shi bai ma tabbatar wacce mamyn take nufi ba, Mammy daya ya sani kuma baya jin ita take nufi, it can't be........

Amma in dai gaskiya ne tun dadewa mai yasa Jidda bata gaya masa ba sai yanzu? Yanzun ma sai data gudu uwa duniya sannan zata aiko masa da sako?

Haka ya wuni ranar a daki, ya rasa mai zaiyi ya rasa tunanin mai zaiyi. Sai can yamma ya fito barandar gaban dakinsa ya tsaya yana kallon tsakar gidan nasa, a lokacin ne yaga shigowar Farhan har tana sanda, takalman ta a hannun ta dan kar yaji shigowar ta

"ke!" Ya daka mata tsawa. Ta yarda takalman hannunta ta diririce ta rasa wanne dakin zata shiga. Sai abin ya bashi mamaki, wai dama haka suke tsoron sa? Wannan tsoron ne ya saka Jidda ta kasa zuwa ta gaya masa matsalar ta ayi wa tufkar hanci har sai da ta saka mata hawan jini tana kyar kankanuwar ta?

"Zo nan!" Yace da karfi.

Ta saki jakar hannunta sannan ta fara hawowa stairs din, yana lura da yadda bakinta yake motsawa amma ya kasa gane karkarwar sanyi take yi ko kuma magana take yi a hankali? Tazo dai-dai shi kunnen sa ya jiyo masa........... ".,............subhanaka inni kuntu minaz zalimin"

Mamaki ya kama shi, wato addu'a take yi da neman tsarin Allah daga abinda zai yi mata. Dama tsoron sa da suke ji har ya kai haka? Ya shiga falo ta biyo bayansa ta rakube a gefe

"Abba dan Allah kayi hakuri. Wallahi ba nisa nayi ba nan makota na shiga gurin kawata na karbo aron phone charger din ta"

Ya zauna yana kallon ta, ya tuna

79 / 106