Chapter 31 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 106

90K to 93K   out of 316K words

abinda ya faru sai ma kamannin nasa da suke kara fitowa har ma yan kara yi min kama da jaririyar yarsa da take kwance a kusa dani cikin kyalliyar tarar babanta.

Hannuna ya sauka akan hoto na biyu.......

A wani daki ne da yafi yi min kama da dakin hotel. Ta madubi aka dauki hoton kuma ita zuwairan ce ta dauka. Tana kwance akan gado sanye da pant da bra only, shima yana kwance akan gadon, hoton bai nuna min dukkan jikinsa ba amma samansa babu komai, ya dora kansa a cikinta hannunsa a saman kirjinta, idonsa a lumshe, fuskarsa dauke da kyakykyawan murmushin da yake nuna irin tsananin farin cikin da yake ciki.

Na jima ina kallon fuskar tasa. Har kara zooming nayi na kare masa kallo, yana yinsa kadai ya nuna min irin yadda yake cikin jin dadin yanayin da suke ciki.

Sai na uku. A cikin jirgi suke, yana ta kokarin bata wani abu a baki ita kuma tana dariya, hoton yayi rawa kuma daga gani shima ita ta dauka amma shi bai san ta dauka din ba.

Sai kuma sakon text din ta.

"I hope kinyi enjoying kwanakin nan kamar yadda mu mukayi enjoying sosai. I hope kuma wannan ya tabbatar miki da cewa ko ma me ya gaya miki kwanaki karya yake yi. I hope yanzu kin fahimci cewa Faruq is mine, ni kadai"

Na ajiye wayar a gefe na ban bata amsar komai ba, to menene zance mata ma? Cewa ni din shashasha ce sakarai wadda Umar ya mayar makikiya yake kuma raina mata hankali? Ko kuma admitting zanyi in gaya mata cewa na kasa rike mijina na barwa karuwa shi? Amma da gaske na kasa din? A ina na kasa? A ina na gaza? Menene aibu na? Wanne gurbi ne ban cike ba? Wanne laifi nayi? Wanne laifi na yiwa Umar da har ya zabe ni a cikin mata ya kuma saka ni a cikin wannan ukubar?

A lokacin naji shigowar mota gidan, naji an bude an fito sannan naji muryar sa yana rafka min kira " My Baby. Baby Dove!" Ban motsa daga inda nake ba sai jin maganar sa nake yi tamkar sukar kibiya a cikin zuciyata. Wato plan din sa kenan yaje ya gama sheke ayarsa sannan ya dawo ni kuma in jawo shi jikina in rungume, alhalin karuwar sa tana can tana min kallon sakarai.

Tamkar Yasmin taji maganar babanta sai ta challara kuka, ban ko kalli inda take ba idona kasa kawai yake kalla numfashi na yana fita da sauri sauri.

Ya budo kofar falon da karfi ya shigo, muryar sa cike da doki yace "Baby where are you. Am home" na daga ido na ina kallon sa, ina tuno fuskarsa akan cikin Zuwaira. Wasu hawaye masu zafin da bansan sanda suka fito daga idona ba suka zubo akan cinyata. Ya tsaya yana kallona sannan kuma nan da nan yana yinsa ya juya ya rikide zuwa tashin hankali.

"Jidda?" Ya ambata da rawar baki "lafiya? Mutuwa akayi"

Na mike tsaye sannan calmly na goge hawayen idona da bayan hannuna. "Mutuwa akayi Umar" na fada da sanyin murya and I can swear I saw him relaxed. Ya karaso kusa da ni fuskar sa cike da concern "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, waye ya mutu Jidda?"

Na saka ido na cikin nasa, sai naga kamar ba Umar dina bane ba, kamar ba Umar din dana sani kuma nake tsananin so bane ba, kamar wani abu ya chanja amma ba a jikinsa ba a zuciyata. Nace "abu uku ne suka mutu Umar. Son da nake maka. Yarda da nayi da kai. Da kuma mutuncika da nake gani"

Calmness din da nayi magana dashi ne ya sa sai da yayi blinking idonsa ya girgiza kansa sannan yace "what?"

Na tabbatar ya dauka mafarki yake yi ko kuma kunnuwan sa ne suka samu matsala. Kukan da Yasmin take yi ne ya saka yayi kokarin daukan ta, nayi sauri na riga shi dauka ina ja baya da ita a hannuna nace "kar ka taba min ya, kar ka shafa mata dattin da yake jikin ka"

Ya bude idonsa "Jidda? Me kike fada ne haka, ni Umar kike gaya wa haka? Me nayi miki? Me kuma aka ce nayi this time around?" Na girgiza kaina "ba gaya min akayi ba this time around, saboda wancan karon an gaya min ka shirya karya kaima ka gaya min ni kuma da yake sakarai ce kuma idona ya rufe da soyayyar ka sai na karbi karyar ka na ajiye gaskiyar. Wannan karon nuna min akayi, dan hausawa sunce gani ya kori ji"

"Ni fa bansan me kike magana akai ba Jidda. Ki bani Yasmin kinga kuka take yi. Sai mu zauna muyi magana kiyi min bayanin abinda kike fada sai in fahimtar dake abinda baki fahimta ba"

Na sake girgiza kaina. "Lokutan zaunawa in saurare ka sun wuce Umar. Dan a yanzu kaf duniya idan da akwai wanda in yayi magana ba zan yarda da shi ba ko da kuwa zaiyi rantsuwa cikin tsarbi ne to kaine. Ba zan kum yarda da duk wata kalmar data fito daga bakin ka ba ballantana in fahimci abinda kake so in fahimta ba. I am done being your fool"

Ya kuma kawo hannu zai karbi Yasmin da take cigaba da kukan ta ni kuma bani da niyyar rarrashin ta, na lura da yadda hannunsa yake rawa kamar ana karkada shi, na tabbatar yasan in da magana ta ta dosa kuma na kara tabbatarwa ya aikata din.

"Jidda, dan girman Allah ki bani ita" ya fada muryar sa kamar zai yi kuka. Na saka hannu na fara dan dukan bayan ta kadan cikin sigar lallashi, ta dan yi shiru, sai yace "ki gaya min inda maganar ki ta dosa Jidda dan Allah. Duk kin tayar min da hankali na wallahi" na dago ina kallon sa. "Ka san inda magana ta ta dosa ai Umar. Kawai dai kana son in gaya maka ya akayi na sani, shima kuma ina jin ka riga kasan ta yadda zan sani din"

Ya daga hannu koma dai menene aka gaya miki ki gaya min and I am sure I can explain, zaki fahimci cewa misunderstanding ne...." Nace "Kamar yadda kayi min wancan bayanin? Ka tuna abinda nace maka a lokacin? Ka tuna nace maka idan karya kake min bazan taba yafe maka ba? To yau na tabbatar da cewa karyar ce ka shirga min kuma Umar ba zan taba yafe maka ba, har abada, ba zan taba yafe cin amanar ka gare ni ba, ba zan taba yafe yadda ka yaudare ni ka tozarta ni a idon duniya ba, ba zan taba yake......" Sai kuka ya kwace min, na kasa cigaba da maganar. Ya karaso ya karbi Yasmin a hannu na ya kwantar da ita akan kujera, idonsa ya kada yayi ja.

"Jidda, banyi miki karya ba, duk abinda na gaya miki a lokacin haka ne yanzu ma kuma......" Nace "duk abinda ka gaya min a lokacin karya ne, duk abinda ta gaya min a lokacin gaskiya ne. Har maganar cewa baka sona gaskiya ne. Har maganganun da ka gaya mata akaina da Abba gaskiya ne ka fada din" ya bude ido "Jidda kar ki ce haka, kar ki tayar da maganar da muka riga muka wuce ta dan Allah. Ta yaya ma za'a yi ki ce bana son ko..."

Nace "bani na fada ba Umar kai ka fada" ya yi saurin cewa "a ina? Yaushe?" Na dauko waya ta hannuna yana rawa na bude hoton sa a kwance akan ruwan cikin mace na nuna masa "fuskarka ce ta gaya min amsars dina"

Ya kalli hoton, sannan ya kalle ni sannan ya kuma kallon hoton. Sai ya fara ja da baya yana girgiza kai. Na tura hoton na nuna masa dayan sannan dayan na jirgin dana tabbatar an dauke shi ne few hours da suka wuce dan har kayan jikinsa sune a hoton, har yanzu tafiya yake da baya yana girgiza kai ni kuma ina binsa ina cigaba da nuna masa

"Ko zaka iya yi min bayanin cewa ba kai bane ba a hoton nan, ko Mahmud ne? Ko kuma fuskar ka da jikin ka aka saka a jikin wani, ko zaka ce tilasta maka tayi ka aikata hakan ko kuma zaka ce tsafi ne tayi maka?" Na juyo wayar ina kallon fuskar sa nace "da wannan murmushin a fuskar ka zaka iya gaya mata komai Umar, including magana ta data iyaye na"

Ya fara girgiza kansa da sauri "wallahi bana sonta Jidda, wallahi ke nake so Jidda" sai na zauna a kujera na ajiye wayar a kusa dani nace "additional karya. Bara in gaya maka gaskiyar yadda maganar take. Kana son ta, sosai da sosai, son da ba zaka ma iya hada shi da wanda kake yi min ba tunda har zata iya zuwa har gidan nan ta fadi maganganu sannan ta sake aiko min da sako ta fada min maganganu ni da iyaye na amma still ka dauke ta a jirgi ku tafi yawon shakatawa. Abinda yasa ka aure ni ba ita ba shine, na farko kasan su Baba in dai suka yi bincike akanta ba zasu bari ka aure ta ba, na biyu kuma kana bukatar innocent well mannered girl din da zaka yi fooling son ranka, wadda kuma zata haifa maka yaya ta kuma basu tarbiyya. Wannan shine dalilin da yasa ka aure ni Umar, ba wai dan kana so na ba"

Ya taho da sauri zuwa gaba na " You are wrong. Very wrong" na sake daukan wayar ina kallon hoton. "Fuskar ka ta nuna min I am right, very right" ya kawo hannu zai karbi wayar na yi sauri na dauke nace "wa? Wannan hoton har gaban Baba zai je wallahi sai dai in bani da rai. Yadda ka saka zuciyata a tsinken tsire ka gasa haka zan yi wa taka"

Ya girgiza kansa da sauri tare da saka guiwowin sa a kasa "Jidda, we can solve this ni da ke, babu wani abin da zai gagare mu if we stick together, if you give me a chance to explain this zaki fahimci duk ma ba haka bane ba"

Na mike na zagaye shi. "Sai dai kayi wa kanka explaining kai kadai, amma ba tare dani ba. Am done listening to your lies" na shige corridor sannan na shiga dakina, sai na samu kaina da tsayawa a gaban mirror ina kallon kaina, ina kallon kyaliyar da nayi saboda shi, saboda wanda nake mutuwar so wanda shi kuma ko digo baya kaunata. Sai na dora goshina akan mirron na fara rusa kuka kamar raina zai fita, banji shigowar saba sai ji nayi ya dago ni yana kokarin saka ni a kirjinsa. Na tura shi baya da dukkan karfina sannan cikin buda murya nace "fita! Ka fita ka bani waye bana son ganinka. I hate you"

Sai ya juya ya fita da sauri ya banko kofar, na ji ya shiga dakinsa sannan na ji shi yana watsi da kayan dakin. Na fito na tafi falo na tuna na bar Yasmin ita kadai, ina daukan ta ya fito daga dakin sa a fusace yazo ya wuce mu da key din mota a hannunsa. Naji ya tashi motar yaci taya sannan yabar gidan.

Minti goma bayan fitarsa daga gidan nima na fita da karamar jaka a hannuna. Yadda Umar ya wulakanta ni a idon karuwarsa nima sai na wulakanta shi. Sai kowa ya san wanene shi.


*Wannan littafin na amana ne, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika yi inci amana kuma ke d Allah*

*The Denial 3*

Na saka Yasmin a car seat din ta da aka riga aka yi installing a seat din baya na motata, ta riga tayi bacci dan haka ban samu problem da ita ba sai na zagaya na shiga seat din driver na dauko handbag dina ina neman key, sai da na dauko shi sannan na lura da yadda hannayena suke karkarwa dan da kyar na iya saita key din na saka a ignition amma kuma sai na kasa kunna motar na dora kaina akwan wheel ina kuka mai tsuma zuciya.

Ban taba dauka rayuwa zata zo min a haka ba, ban taba dauka ni tawa kaddarar kenan ba, ban taba dauka ko da wasa cewa Umar zai iya cin amanata har haka ba.

Yes, ban taba sakawa a raina cewa nawa ne ni kadai ba musanman yaddana lura da cewa yana da farin jinin yammata, kuma ina gaya wa zuciyata ina preferring din ta na kan cewa at any time zai iya haduwa da wadda ta kwanta masa kuma yaji yana son aurenta, ba zan so hakan ba tabbas amma in yazo da hakan na shirya karba kuma in taya shi kokari gurin ganin yaya adalci a tsakanin mu. But ban taba tunanin zaiyi zina ba.

Zina fa....  
Umar......
Umar dina wanda nake so kamar rai shine na gani a hoto kwance a kan ruwan cikin mace........
Macen ma kuma matar data iya bude baki ta gaggaya min maganganu.......

In na rufe idona babu abinda nake gani sai fuskokinsu da suke dauke da farin ciki da annashuwa. Hankalin su a kwance suna aikata zina, tamkar ba su san ma'anar ta ba ko kuma tamkar ba zasu mutu ba.

Gwara ma ita....
Ni ban damu da ita ba
Amma Umar, Umar da aure na a kanshi, yana da ni, yana da mace kamar ni, ni din da yake iƙrarin yana so, ni din da nake iyakacin kokari na wajen ganin nayi satisfying dukkan bukasunsa in bed and out of bed, ni din da yasan cewa I am pure dan shi ya bude ni a leda ta kuma shi kadai ne ya taba ko da taba ni ne, shi kadai, amma ya tsallake ni ya tafi gurin karuwa.

Me nene zai samu a gurinta wanda ni bani da shi?

Ko kusa bata kai ni kyau ba. Kyan jikin ma ni a hoton tsiraicin nata dana gani ban ga wani kyawu a jikin ta wanda zai iya sakawa wanda yake da ni ya kalle ta ba. Idan shekaru ne kuwa in jin in bata kamo Umar ba da  kadan ya girme ta, dan haka babu maganar yarinta.

Na dago kaina ina kallon Yasmin ta mirror na tuna har yarinya na haifa masa ballantana yace ko bana haihuwa ne.

Me yasa yayi min haka......

Amsa daya na bawa kaina a lokacin ita ce saboda baya sona ita zuwairan ita yake so, ya aure ni ne saboda in haifa masa yaya in basu tarbiyya in kuma zama shield din da zaka kare martabar sa.

Na danyi murmushi. Yayi kuskure. Martabar sa tamkar kasa take yanzu a idona, kasar da zan tattaka da takalmi na in wuce in bar masa gidan sa.

Amma in na tafi ina zanje?

Ko giyar wake na sha ba zanje gidan mu ba. Amm kuwa anya wannan bai isa dalilin zuwa gida ba? Anya sauran sisters dina da basu taba yaji ba sun taba haduwa da irin wannan matsalar kuwa? Anya bai kamata Abba ya dube ni ba in yaji abinda Umar yake aikatawa?

Sai dai nasan ba lallai ne ya bani listening ear ba ballantana har yaji abinda Umar din yake yi.

Wani tunani yazo min kaina. Aunty Afia. In tafi gidan ta in zauna da ita in warware mata komai na abinda ya faru, ita zata san ta yadda zata doshi Abba da maganar har in samu ya saurare ni, na tabbatar in yaji abinda Umar yayi kuma yake kanyi shi da kansa zai karbo min takarda ta a hannun sa.

Na tayar da motar na fita, ina tuki a hankali dan nasan hankali na baya tare dani kar inje inyi accident ko ba dan ni ba ko dan Yasmin da bata da wani laifi acikin maganar nan. Ni ce mai laifi, ni ina jin ma nafi kowa laifi da na rufe idona tun sanda yaya Jamila ta zo min da magana irin wannan akan Umar ammana karyata ta saboda ina son shi, saboda ina tsananin son shi, saboda na yarda dashi kuma wannan shi yasa abinda na gani yayi min ciwo fiye da kima.

Babu wanda zai fahimci abinda nake ji a raina sai wadda ta samu kanta a irin halin da nake ciki. Duk kwatancen mutum ba zai iya kwatanta wa ba, duk hasashen mutum ba zai iya hasasowa ba......

Allah ya kai mu gidan Aunty Afia lafiya. Na shiga da mota ta ciki amma sai mai gadi yake gaya min sun fita gabaki dayan su tun safe "kamar biki suke yi a dangin Alhaji. Dan tace sai dare zasu dawo" na gyada kai, "babu komai. Zan jira su. Akwai spare key ai ko?"

Ya shiga dakin sa ya fito min da key ya bani, na dauki Yasmin da jakar kayan mu muka shiga ciki. Direct sama na hau na bude dakin Aira na shiga na rufe. Sannan na kwantar da Yasmin akan gado ni kuma na kwanta a gaban gadon na bude sabon babi na kuka. Tabbas da ace hawaye yana karewa da tabbas nawa ya kare a ranar.

Ban san adadin lokacin da na dauka a hakan ba, na dai ji an kira sallar sai na tashi zaune na kaiwa Allah kuka na tare da gaya masa bukata ba. Ni bukata ta a lokacin kawai ita ce Allah yasa iyayena su fahimce ni su kuma goya min bayana sannan su raba ni da auren Umar duk kuwa da tsananin son da nake masa, babban burina a lokacin shine in rabu da aurensa ko da kuwa son sa zai zama ajalina, dan nafi kaunar mutuwa ta akan in sake ganinsa irin ganin da nayi masa a hoto shi da Zuwaira.

Bayan na idar ne wayata ta fara ringing da kidan Umar, naji wani kolulun bakin ciki ya tsaya min a makoshi, wato har yana da karfin halin da zai kira ni? To yace min me? Kiyi hakuri dan Allah ki dawo gida ba zan iya rayuwa ba sai dake? Ko kuma yace wallahi sharri take yi min bani bane a hoton wani ne mai kama da ni?

Na tabbatar yanzu ya dawo daga inda ya figi mota ya tafi wanda nake kyautata

31 / 106