Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
mu zan kwana, ko kuma a gefen titi.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
Forgive the typos please.....,
*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*Enchanted*
Gudu nake zubawa a motar kamar wadda zan tashi sama, ina kakkaucewa motoci da babura ne badan bana so inyi accident ba sai dan bana so inyi accident intentionally dan in na mutu zai zamanto kamar na kashe kaina kenan. Amma at the back of my mind da akwai wani voice da yake hoping muyi accident din ko na samu in mutu in huta. Ba zan kwatanta yadda zuciyata take kuna ba kuma bana fatan ku fahimta dan babu wadda zata fahimta sai wadda mijinta ya nemi yar yayarta, bana kuma fatan hakan ta kasance ga duk wata yar uwata musulma ko da kuwa makiyiya ta ce.
Tun Mammy tana dauriya har ta tsorata sosai da uban gudun da nake zubawa, ta kankame jikinta ta cure a guri daya tana kuka "dan Allah Aunty Jidda kar ki yar damu, wallahi bana so in mutu, in na mutu wuta zan tafi wallahi" nayi kamar ban ji ta ba, na cigaba da abinda yake gabana ina godewa Allah da ban taho da Asad ba yadda ko da munyi accident din babu shi. But ya rayuwar sa zata kasance idan babu ni a duniya? Ya rayuwar su zata kasance shi da yaruwarsa? Na tabbatar uban su za'a barwa su a matsayinsa na kammallen cikakken mutum. Ya tarbiyyar su zata kasance a hannun Faruq kuma a bayan ido na? Tun da Faruq ya iya neman Mammy, bashi da shamaki akan wadda zai nema nan gaba, ko da kuwa Yasmin ce.
Na sassauta gudun da nake yi ba fara controlling motar a hankali, now hoping not to die but inje gidan Umar in karbi takarda ta da nake saka ran by now ya riga ya rubuta min sannan in debi yarana mu tafi gida. Sai dai na kasa barin ƙwaƙwalwa ta tayi tunanin yadda zuwan namu gida zai kasance.....
Muna zuwa gida nayi packing, abinda na fara lura da shi shine rashin motar Umar a compound. Amma ban karaya ba sai na bude kofa na fito sannan na zagayo na bude gaba na damki hannun Mammy da har yanzu take rakube tana karkarwa na finciko ta daga cikin motar nayi cikin gidan da ita, not minding kallon da maigadi ya bimu da shi.
Ina shiga falo na fara rafka masa kira "Umar Muhammad Gidado. Umar Faruq Gidado" da muryar da naji ta kamar ba tawa ba. "Ka fito duk a inda kake ka bani takarda ta, ka fito ga ta na kawo maka ka bani takarda ta in matsa in baku guri" sai dai babu shi babu alamun sa, daki daki nabi da Mammy a hannuna har da su bude toilet amma ko inuwar sa ban gani ba.
Na jawo ta muka dawo falo, taa ta kokarin karbe hannunta daga cikin nawa tana cigaba da kukan ta "dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri, dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri" .
Na saki hannun da sauri sannan na sauke shi a fuskar ta cikin karfin da ban san ina da shi ba, karfin marin ya saka ta durkushe a kasa tare da rike kuncinta. Na nuna ta da yatsa "kar ki sake ambatar sunana ballantana ki ambaci kalmar hakuri" naji a raina babu kalmar da na tsana irin ta hakuri. Na cigaba "tunda babban munafikin baya nan zan fara settling ki ke karamar munafukar. Ki tashi mu koma gidan ku in je in damka ki a hannun wannan mugun uban naki in kuma gaya masa duk abinda kika yi tare da nuna masa shaida, in yaso ya saka gabanki gabas ya yanka ki, in uwarki tayi magana itama ya dora ta akan gawarki ya yanka ta, all of you can go to hell for all I care".
Ta saki fuskar da sauri tana zare ido cikin tsoro "na shiga uku, Aunty Jidda ki rufa min asiri kiyi min rai kamar yadda Allah yayi miki, wallahi da gaske nake kashe ni zaiyi in yaji maganar nan, wallahi in na mutu Allah kona ni zaiyi. Kin ce in banyi abinda kika ce ba ne zaki gaya masa kuma nayi duk abinda kika ce" nace "ai bance in kika yi ba zan nuna masa ba, ko na fada? Munafuka. Kina tsoron mutuwar kika aikata abinda kika aikata? Ai ke ba yarinya bace ba da hankalin ki kina sane kin san abinda kike yi kuma kinsan girman abinda kika yi"
Ta cigaba da kuka da sheshsheka "wallahi ba laifi na bane ba. Cewa yayi zai aure ni. Dan Allah Aunty Jidda ki rufa min asiri. Wallahi na fasa auren sa ma ni. Zan gaya masa in ce ya rabu da ni babu ni babu shi" na girgiza kaina "ko kadan bana so ki rabu dashi. So nake ki aure shi din dan the two of you deserve each other. Ki tashi mu tafi gidan ku wallahi tun kafin inyi miki dukan da zaki kasa tashi" ta sake rike kafata tana girgiza kai "dan Allah, dan Allah" na dauko wayata "okay tunda ba zaki je ba bara in kira uban naki shi yazo nan gidan da kansa, maybe ma kafin nan surukin nasa ya dawo sai ya bashi sadaki kawai ya daura muku aure a yau" ta mike da sauri tana rike hannuna da yake rike da wayar.
"Dan Allah ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki. Wallahi zan gaya miki komai in kinyi alkawarin ba zaki gaya masa ba, dan Allah kar ki kira shi wallahi zan gaya miki duk abinda ya faru"
Na kwace hannu na daga nata "waye ya gaya miki ina so inji komai? Ku rike kazantar ku ke da shi, wanda na sani ma da zan iya zuwa a goge min memory na da naje anyi min" na fada cikin zafin zuciya. Sai ta girgiza kai tace "ba maganar shi zan gaya miki ba. Wata maganar ce. In dai ba zaki fadawa kowa abinda ya faru ba"
Nace "oh ba maganar shi ba? Maganar ki kenan zaki yi min? Yadda kike kokarin maye gurbi na a cikin rayuwata tun kafin in mutu? Maganar......." Tace "bani ba ce ba wallahi. Hajiya ce"
Na dakata da maganar da nake yi na juyo ina kallon ta "Hajiya? Ita ce ta saka ki cusa kanki a gurin mijina kuma tace ki kwanta dashi?" Tace "ita ce ta bani magani tace in binne"
Na saki wayar hannu na ta fadi kasa ina jin numfashi na yana tsayawa a kirjina, sai ta zame ta durkusa a kusa da kafafuwana tace "dan Allah, dan Allah, kar ki fada wa kowa wallahi tsoro nake ji. Zan fada miki duk abinda ya faru kuma zan rabu da mijinki amma dan Allah kar ki gayawa kowa abinda kika sani wallahi nayi nadama kuma danay na gaya masa ba zan kara zuwa gidan gonar nan ba" na runtse idona na bude, har yanzu hawaye basu zo min ba, sannan nace "menene zaki gaya min?"
Tace "Hajiya ce wallahi, ta jima tana cewa in ringa yi masa kirki ina kiran sa a waya ina kuma zuwa gidan ku, ita ce take matsawa wai in ringa zama a gidan nan ina yi masa magana to shine kuma sanda kuka dawo daga Saudiya sai ta je gidan mu ta kirani ta bani wani abu tace za'a kawo ni gidan nan tace in binne a kofar palon ku in da zai ke tsallaka wa kullum, ta kuma bani wani turare tace in ke shafawa kullum in kuma tabbatar zai zo kusa dani yaji kamshin, kuma ta bani wani magani tace in saka masa a abinci amma shi kadai, ta tabbatar min wai in nayi haka soyayyar da yake yi miki zata dawo ni yake yiwa ita, zai ji idan bai aure ni ba kamar zai mutu ne, tace zai rabu dake kuma ni ya aure ni in zama ni ce matarsa ni zan cigaba da zama a gidan nan ke kuma ki fita, ni za'a ke saiwa mota kuma ake kaini Makka"
"Bayan nazo shine ranar nan kuna bacci na binne abin da ta bani, kuma nake saka turaren data bani kullum da dare lokacin da muke zama muyi kallo tare a falo, na abincin ne tunda tare kuke ci da kyar na samu na zuba masa wataray da yaci abinci shi kadai. To shine sai yake turo min text yake ce min wai ina da kyau, ko yace min yana son ganina, ko kuma ya kira ni a waya yace yana son jin muryata. Shine ke kuma kika mayar da ni gida. Sai muka cigaba da magana a waya. Yace min yana sona sosai kuma yana son ya aure ni. Ni kuma nace masa ya sake ki kamar yadda Hajiya tace in ke gaya masa, kullum sai yace min to zaiyi amma yaki yi din, kullum yace zai zo gidan mu amma bai taba zuwa ba sai dai yace in turo masa hotona ya ganni. Shine ranar nan ya fara yi min zancen abin nan, yace shi mutuwa zaiyi idan bai yi ba, kuma yace ai aure na zaiyi in yayi din, yace in na yarda munyi zai sake ki ni kuma ya aure ni"
Ta rufe fuskarta tana kuka "na gaya masa dama ni tsoro nake ji, ina tsoron kar a kama mu. Nace masa ya bari muyi auren amma yaki. Dan Allah Aunty Jidda kiyi hakuri. Dan Allah ki rufa min asiri"
Na mike tsaye ba tare da na kalli inda take ba na wuce kitchen na dauko the closest wuka da na gani, ina fitowa falon sai ta mike da gudu ta shige dakin yara ta turo kofa. Na wuce kofar dakin da take na bude kofar falon na tsaya ina kallon kasan kofar, inda kullum za'a tsallaka kafin a fita daga gidan kuma za'a tsallaka idan za'a shigo.
Flowers ne a jere a gaban yar karamar varandar da kofar falon take ciki, a cikin ramin flowers din aka yi matakala biyu da zaka taka ka hau varandar, hakan ya saka kasan stairs din ya zama kasa ce, amma mostly tsallakewa akeyi dan space din ma kafa ba zata iya shiga ba.
Na durkusa a gaban gurin na fara tone kasan gurin da wukar hannu na a rikice, ban jima ina hakar ba na ga abinda nake nema.
Wani abu ne mai suffar kwai, amma yafi kwai girma sai dai jikinsa kamar shell din kwai. Na dauka a hannuna ina kalla, jikina gabakidaya yana karkarwa, rubutu ne a jiki kacakaca da larabci wani kan wani wani kan wani, a ciki na tsinci sunayen Umar, da nawa dana Mammy.
Na mike tsaye da abin a hannuna, jiki na yana karkarwa kamar ana kadani, karkarwar da nake yi ce ta saka abin ya zame daga hannuna ya fadi a edge din barandar sannan ya tarwatse a cikin flowers, wasu layu suka bayyana, yan kanana kanana har babu kyan gani wadanda aka dinka su wata a jikin wata wata a jikin wata.
Naji wani amai ya taso min, na koma cikin gidan da sauri sannan na shige dakina na shiga toilet nayi amai kamar zan fitar da yayan hanjina. Na dawo daki na zauna a gaban gado na dafe kaina ina mayar da numfashi, sai a lokacin kukan da nake nema yazo min, na hada kai da guiwa kuwa nayi shi kamar raina zai fita.
Farko kaina ya kulle ban ma san tunanin menene zanyi ba, tunanin mijina ya kwanta da yar yayata ko kuma tunanin matar babana da kuma yan uwana da muke uba daya, duk da ban tabbatar da hadin bakin su ko kuma hadin Hajiya ne ita kadai ba, sun shirya rabani da mijina da yayana da gidana sannan su saka yar yayata a madadi na.
Wannan wanne irin tashin hankali ne?
Wannan wacce irin rayuwa ce.....
Na sani cewa tun ina karama ta Hajiya da yayanta basa sona, with exception of Farhan, na kuma sani cewa tun sanda Umar ya fara neman aure na basa son auren na mu either, na kuma sani dan ina gani a idon su cewaa suna hassadar irin rayuwar da suke tunanin ina yi a gidan mijina amma ban taba tunanin har abin ya kai wannan matsayin ba. Ban taba tunanin they can stoop this low ba.
Sai da nayi kuka na na koshi sannan ƙwaƙwalwa ta ta fara aiki. Na fahimci motive dinsu shine su cirewa Umar so na su saka masa son Mammy, su saka ya sake ni sannan ya aure ta. In koma gida ita kuma ta shiga rayuwar da suke tunanin ina yi.
Sai dai abin nasu sai yazo musu ba yadda suka shirya ba, sai Umar din yaki sakina da wuri kamar yadda suka saka rai, sannan kuma asirin nasu ya tarar da halinsa wannan ya hadu har ya kai shi ga neman Mammy. Yes, sunyi masa asiri amma halin sa ne ya kai shi ga neman Mammy. Abinda suka kawata masa suka ce zaiji idan baiyi ba kamar zai mutu, sun dauka zai aure ta ne kafin yayi, shi kuma yayi ba tare da ya aure ta din ba.
Maybe da sun san ainahin halin Umar, da ba zasu kawata masa Mammy har haka ba. Tabbas sun haka min ramin mugunta ne amma sai ya rufta da su tunda Allah ya ga zuciyata ya kuma san bana nufin kowa da sharri, ko kuma in ce ya rufta da Mammy tunda stain din yanzu a jikinta yake, and will forever be on her.
Tunowa da nayi da Mammy ya saka na mike na wanke fuskata a toilet na fita, sai dai babu ita babu alamun ta a cikin gidan, ta gudu, na fita bakin kofa, layun da suka zubo daga cikin kwan suma basa gurin, ko tantama kuma bana yi cewa ita ce ta dauka ta tafi dasu. Na juya na koma falo, sai na kalli agogo nayi realising lokacin dauko Yasmin daga makaranta yayi har ma ya wuce, na koma na shiga mota naje na dauko ta na dawo. Muna shigowa na hada mata cornflakes na kunna mata tv sannan na wuce dakina na fara gada kayana a jikin yar karamar jaka.
Tabbas duk abinda Umar yayi yayi ne under the influence of asiri amma kuma that did not change the fact that yayi din, he slept with my niece, and that is something I will neither forget nor forgive. Dole my step four will happen. Dole zan je gida kuma zan gaya wa iyayena halin da aurena yake ciki ya rage nasu su fahimta kuma su dau makaki ko kuma su ki fahimta kuma suki daukan mataki ni kuma in shiga step five dina.
Na dan debi kaya na kadan, na wuce dakin yara na debar musu suma wadanda zasu dan kwana biyu a raina ina lissafin kafin a aiko a kwashe min kayana daga gidan Umar. Amma kuma a son samu na nafi son in tafi da takarda ta a hannuna yadda Abba will have no choice then to listen to me, sai dai kuma Umar din babu shi babu alamun yana da niyyar zuwa gida yanzu, ni kuma ba zan iya cigaba da zama har in jira shi yazo ba dan iskar gidan kanta ji nake yi tana min yaji yaji kamar zata yi suffocating dina.
Sai da na gama diban iyakacin wadanda zan diba sannan na juyo zan fito daga dakin, sai wani siririn voice a cikin kaina ya tambaye ni "idan kin je gidan me zaki ce ya faru?" Na dakata da tafiyar tawa ina lissafa tambayar, sai na bada amsa "zan bada labarin duk abinda ya faru ga duk wanda zai saurara" "zaki ce Umar mijinki uban yayanki ya kwanta da yar yayarki? and then what?" Na kuma tambayar kai na..
Sai na zame kasa na zauna na dora kaina akan jakar da na hada mana kaya. Tabbas Hajiya tayi wa Umar asiri kuma sanadiyyar hakan hadi da halinsa, ya saka ya kwanta da Mammy. Amma babu wanda ya san hakan sai su da suka yi asirin sai kuma ni da Mammy ta gaya wa, and I realized a yanzu bani da shaida ta cewa asiri suka yi masa, ina dai da shaidar yiyuwar kwanciyar sa da ita, but in na nuna wannan laifin toward wa zai yi pointing? Toward Umar, dan a hirar tasu shi yake ta hillatarta har tana nuna masa tana tsoro shi kuma yana kara insisting, har da cewa zaiyi protecting dinta with his life.
A yanzu na san maybe labari ya iske Hajiya na cewa na tone na kuma fada asirin su, meaning asirin ya karye kenan, meaning babu zancen soyayya tsakanin Umar da Mammy, kuma na tabbatar the Umar I know ba zai auri Mammy ba ko da kuwa ya sake ni din kamar yadda nake fata, dan haka burin su bai cika ba kenan, and their next target will be to destroy me, Umar da duk wani abin da ya shafe mu, including yayan mu.
Da zarar wannan maganar ta shiga kunnen su, they will turn it around, knowing the Hajiya I know zata ma iya cewa raping Mammy yayi, yayi amfani da yarintar ta ya yaudare ta sannan yayi mata fyade. They will play the victim, and destroy Umar to the core.
Wannan ba shine damuwata ba. My concern are my children. Hajiya will make sure duk wanda ya sanni yasan abinda Umar yayi, za ta yi ta jan maganar ne kuma babu yadda zanyi da ita, har girman yayana the stain will forever be on them. Knowing the society I live in, the stain will be on me too amma bana jin hakan zai dame ni kamar yadda kasancewar sa on my children zai dame ni.
Hakan yana nufin cewa I can't even talk about