Chapter 51 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 106

150K to 153K   out of 316K words

hannuna na rike ba "innalillahi. Me ya faru?" Tace "to waya sani ne? An saka rana har lokaci yazo kuma kawai sai mijin ya aiko wai a bashi kudin sa ya fasa" na fara girgiza kaina cikin takaici, ina jin babu dadi har cikin raina.

"Allah ya kawo mata wani wanda ya fishi alkhairi" tace "ameen fa. Ni tausayin ta nake ji Allah. Ta kusa tsufa a gida fa. Ni kaina da nake kanwar bayanta ina ji na kamar nafi kowa dadewa a duniya banyi aure ba ballantana ita. Ban san ya take ji a ranta ba dan ma babansu babu ruwansa da Abba ne da tuni ya yayyanka ta yayi farfesunta ya raba wa makota"

Umar yayi dariya, na juya ina hararar sa, wato har ma bakin dariya yake dashi kenan, nace "ke Farhan. Abba fa duk cika baki ne yake yi. Ke yanzu sanda muka gama secondary school mun taba saka ran cewa zakiyi shekara biyar a gida ba tare da aure ba?" Amira tace "Abba fa duk yayi sanyi yanzu fa. Gashi nima Umma ta tambayar min kuma ya barni in nemi makaranta in na samu in shiga. Dama tunda ya bar Farhan nima na saka ran zai barni" Farhan tace "babu wani sanyi da yayi fa, gigin tsufa ne kawai ya fara kama shi" Umar yace "ke! Ki kiyaye ni fa, baban nawa kike gayawa haka?" Duk suka yi dariya sannan ya koma kan maganar da Amira tayi na zancen makaranta, yayi uwa yayi makarbiya, ya karbi takardun ta kuma yace shi zai samo mata makarantar.

Duk maganar da suke yi ban saka musu baki ba, sai da nayi realising yayana basa tare da mu sannan na tambayi inda suke sai aka ce min suna gurin Hajiya wai ta kira su, nayi mamakin amma kuma sai na tuna hajiyar kamar ta chanja kamar ba irin ta da bace ba. Sai da aka kira sallar laaasar sannan Umar ya tashi yace zai dawo ya dauke mu da magrib, na fito zan raka shi sai ga Hajiya ta fito daga dakin ta ya durkusa ya gaishe ta "naji har zaka tafi ai, ita kuma yar tawa ko dan kara ba zata yi ta kawo ka gurina ka gaishe ni ba" ya shafa kai yana kallo na yace "ta gaya min in shigo ai, nine nace ta bari sai na dawo dan an kira ni ne yanzu ana nemana da gaggawa" banyi mamakin karyarsa ba dan in da sabo na saba, shi a ganinsa yayi ne dan ya kare ni kar Hajiya ta ga laifina,ni kuma a ganina wannan bai kai dalilin yin karya ba.

Sai ga su Yasmin sun fito hannu rike da alawa da biscuits, har zai fita sai da Hajiya ta ja hankalin sa lallai sai da yaga abinda ta bawa yayansa, shi kuma ya nuna jin dadinsa har da yi mata godiya sannan ya fita na bishi a baya.

A gaban motar sa ya tsaya, nace "sai ka dawo" na juya zan koma sai yarike hannu na, na juyo da sauri ina kalle kalle a layin, na hango majalisar maza da take bakin layin mu kuma na tabbatar suna hango mu suma, nace "dan Allah ka sake ni a waje fa muke" yace "kin tuna ranar da na fara ruke hannun ki? Adai dai gurin nan?"

Na sunkuyar da kaina ina tuna ranar, ranar da aka daura auren mu, yace "lokacin ba kya fushi dani, lokacin kina sona sosai, lokacin bana jin akwai wanda zai iya shiga tsakanin mu" ba dago kai ins kallon sa "to yanzu mai ta faru?" Ya langwabe kai "nima ban sani ba, banajin dadin yanayin fuskar ki sam. Dan Allah ki saki ranki. Kiyi hira da Umma kiji dadin ki, in akwai wani abu da kike so bayan ganin Umma ki fada min ko menene zanyi miki shi Jidda. Ni dai kawai so nake inga kina farin ciki"

Nace "kayi duk abinda zaka yi min. Nagode kuma" ya sake bata rai "amma baki yi min murmushi ba ai" na kirkiri murmushi nayi sai yace "that one is fake, bana son sa" ya kama daya hannun yana kokarin jawo ni jikinsa, na bude ido "yaya Faruq a titi fa muke, akwai mutane fa"

Ya daga kafada "ina ruwana da su? Matata ce fa" nace "dan Allah ka cika ni ni inajin kunyar su wallahi, har fa da abokan Abba a gurin" ya dan sake ni kadan yana murmushi "to kiyi min murmushi in ba haka ba ba zan tafi ba" na sake yi masa wani, "dan Allah ka tafi" ya saki hannuna "shikenan, na tafi din but in na dawo ko? In baki saki ranki ba ko? Ni kadai nasan me zan miki" na ja da baya ina satar kallon yan majalisar, a raina ina cewa suna can suna gulmar mu maybe, sai kuma nayi masa murmushi tare da daga masa hannu, yayi min blowing kisses sannan ya tafi.

Ina komawa gida na tarar Umma ta fito ta bawa Farhan da Amira sun fara aikin kajin da muka zo dasu "wannan manya manyan kaji haka ai sai mun kwana biyu muna ci, gaskiya yaron nan akwai kokari, ga kirki ga sakin fuska ga girmama mutane" nace "uhm" na kwanta akan kujera na rufe ido na ina tunanin abinda ya dame ni, amma basu barni nayi tunanin ba sai da Farhan ta jawo ni tsakar gida mukayi aikin kajin tare, muna ta hirar shirye-shiryen bikin yaya Tahir da za'a yi kwanan nan. A lokacin ne Umma take bani labarin ita ma Aira (yar Aunty Afia) an aiko tambayar auren ta.

Har magrib muna tsakar gida, mun soya kajin anyi farfesun wasu kuma za'a ci a matsayin abincin dare, Farhan tana ta tsokanar Umma wai ta kira Abba tace ya taho da bread "ke ce amarya, zaki iya lallaba shi" nace "ke fa Farhan baki da kunya, halin ku daya da Umar" sai na fara bata labarin ranar da nake ce masa naga Aunty kamar tana fushi sai yake wai ko period take yi, mukayi ta dariya, Abbah (yayan Jidda) ya shigo shima yayi joining hirar sai ga yaya Muslim nan da yaya Tahir sun shigo tare suma duk aka hadu aka shimfida tabarma anan tsakar gida, Umma ta zubawa Hajiya nata naman aka kai mata daki sannan yaya Tahir ya siyo mana bread din muka hadu muka ci abincin tare sai naji duk stress din da nake ciki ya barni, sai naji kamar inyi ta zama na anan gida kar in koma gidan Umar, sai naji kamar in dawo da hannun agogo baya in dawo lokacin da nake gida.

Mun gama cin abinci kenan sai muka ji sallamar Mammy, duk muka bita da kallon mamaki, yaya Muslim ya kalli ogogon wayarsa yace "ke daga ina kike haka da daddaren nan?" Ta zauna a bakin tabarmar da muke kai ta ajiye yar karamar jakar kayanta sannan tace "daga gida" ya bata rai "kawai su iyayen naki sai suka barki kika fito da magriba? In zaki zo ba sai kizo tun safe ba? Ko kwana zaki yi?" Ta kalle ni "aunty Jidda gidan ki zan tafi, binki zanyi"

Na bude ido "gida na kuma?" Ta gyada kai "eh wallahi. Na gaji da zama babu abinda nake yi, tunda muka yi candy ni ba makaranta ba ni ba aiki ba ni ba sana'a ba sai dai in kwanta in tashi. Gidan ki zanje in taya ki zama"

Nace "gidan nawa ma Mammy in kinje ai babu abinda zakiyi, shima dai zaman ne zakiyi tayi. In maganin zaman banza kike so sai ki nemi sana'a ko ki samu makaranta" ta sake turo baki "ni dai nafi son can, ko aikin gida nake taya ki kinga sai ki koya kin girki irin na yan gayu" na juya na kalli Umma sai ta girgiza min kai a hankali, na juyo ina kallon Mammy nace "to sai dai kya zo wata rana. Amma kinga yanzu daga nan ba gida zamu tafi ba unguwa zamu je, kuma gobe zamuyi tafiya dan yanzu ma sallama muka zo yi wa su Umma, sai dai watarana sai ki zo mu zauna din"

Tayi kamar zata yi kuka "to ba sai ku tafi dani inda zaku je ba? Ai dai shi daddyn Yasmin bashi da problem ba zai yi complain dan kin tafi da ni ba" Farhan ta dungure ta "dalla ki rufe wa mutane wannan bakin rashin kunyar naki, basu shirya tafiya da ke ba kawai lokaci daya sai ki zo ki ce sai kin bisu? Ko tace zata tafi dake ma wallahi ba zaki je ba kinji na gaya miki" ta dauki jakar ta tana kunkuni ta tafi dakin Hajiya, Farhan tace "kar dai ki zage ni, in ba haka ba inzo in balla kafar ki daya"

Sai bayan ta shige sannan nayi realising babu wanda ta gaisar a cikin mu, har Umma.

Sai wajen karfe takwas Umar yazo, sai ya tsaya a waje kawai ya kira ni na dauko yara Asad har yayi bacci, nayi wa Umma sallama ina jin babu dadi, na kuma yiwa Hajiya sallama tana min mitar Mammy ta taho takanas tun daga gidan su dan ta bini gida na amma naki tafiya da ita, ban ja maganar ba sai kawai nayi dariya na mike na fita, Farhan da Amira suka raka ni na saka yara na a bayan mota na shiga gaba muka tafi. Muna tafiya ya leko fuska ta, "muga fuskar" na harare shi sai yayi murmushi "that's a little bit better"

Kwana biyu bayan nan yaya Mubaraka tazo kamar yadda tayi min alkawari zata zo, daga office take dan haka na fara gabatar mata da abinci ta kuma ci sosai sannan na kunna wa yara cartoons mu kuma muka tafi dakina muka zauna.

Ta kama hannuna "Jidda kin ce zamu yi magana, kuma tun a wayar na fahimci magana ce mai muhimmanci zamuyi din menene? Naga kamar kina cikin damuwa ki gaya min menene yake damunki? Wani abu ne ya faru ko yake faruwa?"

Tun kafin in amsa mata sai naji hawaye ya fara taho min, it felt so good a tambaye ka abinda yake damun ka ba wai a kawai a kalleka ayi assuming you are okay ba. Ta bude ido "innalillahi, Jidda kuka kike yi ai, abin har yayi girma haka? Dan Allah ki gaya min menene ya faru? Faruq ne yayi miki wani abu?" Na dago kai ina kallon ta, ina jin nauyin abinda zan gaya mata, sai kuma na tuna tsakanin su da Umar tabbas ba zata tona asirin sa ba.

"Yaya... Faruq....... Umar neman mata yake yi"

Na saki hannu na sannan ta rufe bakinta tana matsawa daga kusa dani "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda? Kin tabbatar? Ya akayi kika sani? Wani ne ya gaya miki? Kama shi kika yi?"

Ta jero min tambayoyin. Farko sai na rikice na rasa amsar da zan bata. Sai kuma na tattaro nutsuwa ta na fara bata labari "tun farkon auren mu na sani. Tun da cikin Yasmin"

Sai na bata labarin zuwan Zuwaira gidan da duk abinda ya wakana har zuwa munanan hotunan su da zuwairan ta turo min waɗanda har yau basu bar cikin kai na ba. Sai kuma na cigaba da bayani "tun a lokacin ya yarda, har ma ya tabbatar min da cewa sun dade tare, har ma a gidan nan ya taba ajiye ta na tsahon lokaci sanda yana karatu a buk, amma kuma sai yayi min alkawarin ya daina tunda ya aure ni ya daina wannan karon ma tsautsayi ne da sharrin shaidan"

Sai na cigaba da bata labarin abubuwan da suka cigaba da faruwa, bayan nan, yadda ya ringa yi min karya, yadda ya dinga yi min alkawarin ya daina kuma yazo ya karya da kansa, irin munanan hirarrakin su shida Bashir dana ringa gani har zuwa case din Maryam.

"Shi yasa na yanke shawarar in gaya miki ke kuma ki gaya wa su Mama dan su san halin da yake ciki suyi masa fada da nasiha sannan kuma suke saka shi a cikin adduoin su dan na fahimci ni kadai ba zan iya ba, ina bukatar taimako, ina bukatar taimakon ku Yaya Mubaraka tun kafin ya zama too late. Lamarin Umar gaba yake yi yaya Mubaraka tunda har zai iya neman kawata nan gaba ban san wadda zai sake nema ba kuma. Na gaji, zuciyata ta gaji, ki taimaka min dan Allah..........."

Kuka nake yi sosai, itama kukan take yi......"har akayi har abin nan yayi nisa bamu sani ba? Ni dai ban taba sani ba Jidda ban taba ko tunanin jingina wannan mummunar halayyar akan Umar ba" na share hawaye na "ya dade fa sosai, ya gaya min tun yana Lagos, tun yana secondary school"

Ta dafe kai "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda shi ya gaya miki hakan da bakinsa? Da kansa ya amince da laifukan sa kuma har ya iya furta miki da bakin sa?"

Na gyada kai "shi ya gaya min. Yace he is addicted to it. Amma sai yace yana iyakacin kokarin sa wajen ganin ya daina, abinda yasa kullum nake ta lallashin zuciyata nake kuma gaya wa kaina cewa zai daina din tun da yana iyakacin kokarin sa, kinga na hana shi social media kuma ya daina, na ce ya rabu da Bashir kuma ya rabu dashi, then I have no reason to think cewa bashi da niyyar dainawar, amma sai ya saka min da neman kawata. Bayan kuma ta tona musu asiri a giri na shine ya kala mata sharrin sata ya saka aka kamata, duk da laifinta ne amma hakan ai ba dai dai bane ba kuma yana da alhakin ta"

Yaya Mubaraka ta gyada kai "tabbas naji maganar a gida, mamanta ta je gurin Mama jiya ni kuma na shiga gidan sai naji suna zancen da Mufida bayan uwar yarinyar ta fita cewa kawarku ce taje office dinsa tayi masa sata, har muke zancen abin kunya ki je office din mijin kawarki kiyi sata"

Na girgiza kaina nace "ba sata tayi masa ba" na sake yi mata bayanin abinda ya faru.

Yadda nayi tunanin hankalin yaya Mubaraka zai tashi sai naga yafi ma hakan tashi, tayi ta rantse min akan cewa basu sani ba.

"Mu dai munsan shi da wayan yammata, tun farkon shigarsa jami'a yake da yammata wasun su har gida suke zuwa nemansa, dan tun ina gida nasan akwai wasu da Mama ta taba zagewa tas da ta gansu sunzo gurinsa amma bamu taba tunanin abinda yake tsakanin su kenan ba. Gidan nan kuwa tunda aka siye shi Baba yace ba zai zauna a ciki ba sai yayi aure,dan na tuna lokacin har sai da yayi ta nacin a barshi ya dawo nan tunda yafi kusa da school amma Baba ya hana yace a gida zai cigaba da zama sai yayi aure tukunna. Ashe shi akwai abinda yake yi a gidan"

"Abinda kawai zan iya ce miki na sani shine case din Ummi"

Na bude ido "Ummi. Me ya faru da Ummi kuma? Wani abu ya faru tsakanin Umar da Ummi? Na shiga uku ni Hauwa'u"

Sai naga hankalin ta ya kara tashi "baki sani ba? Bai gaya miki ba? Ni na dauka kin sani da ba zanyi mentioning ba"

Na sake rikicewa, kar dai Umar har lalacewar sa ta kai ya nemi Ummi, Ummin da yace min is like a sister to him, in har ya nemi Ummi to tabbas babu wadda ba zai iya nema ba kenan "dan Allah ki gaya min Yaya, tunda kin riga kinyi mentioning hankali na ba zai jwnta ba sai naji gaskiyar magana in ba haka ba zanyi ta sake sake ne a raina"

Ta fara kokarin kwantar min da hankali "kinga, ba wani abu bane ba, ba abinda muke magana akan shi bane ba. Amma kinsan Ummi bata gida yanzu ko? Kinsan ta koma gidan su ko?" Na gyada kai "sanda mukaje Lagos Aunty tace mana ta mayar da ita gida"

"Ba Aunty ce ta mayar da ita ba, guduwa tayi da kanta" Na bude ido "me yasa ta gudu?"

Tace "tun farkon zuwan Ummi gidan mu suka saba da Umar yana kulata sosai kamar yadda yake kula su Mufida, sai ta mayar dashi kamar abokin shawarar ta dan komai na Ummi in kana son ji to a gurin Umar zaka ji shi. To wai ashe ta dade tana gaya masa zancen wai tana so ta shiga Hausa film, kuma wai tana ta yi masa zancen wai Aunty tana takura mata tana cin zalin ta, ita ashe so ma tayi sanda kuka yi aure ya mayar da ita gidan sa shi kuma wai sai yaga bakya so shine yaki yarda. To wai yanzu bayan ta gama makaranta shine suka shirya zai saka ta a film din, wai akwai wani abokin sa daya san wani producer, shine suka shirya plan ta ringa daukar kayanta a hankali tana bashi yana boye mata har ta gama diban waɗanda zasu ishe ta kawai rana daya yazo gidan tace wai zata je gidan su friend dinta ashe zuwa tayi ta shiga motarsa da yayi packing acan gefe, shima ya gama abinda yake yi ya bi bayan ta suka tafi"

"Shiru shiru Aunty taga bata dawo ba, har dare, sai ta kira maman yarinyar da tace zata je gidan su sai aka ce ai bata je ba. In gaya miki tashin hankali, akayi ta kiran number din yarinyar nan wallahi taki dauka daga baya ma sai ta kashe wayar. Nema nema nema, kwana da kwanaki babu Ummi babu labarin ta. Baba yana Lagos lokacin dole ya biyo jirgi ya taho aka zo akayi ta nema. Kuma abin haushin har da Umar a neman ta kusan shine ma kan gaba a neman ta ashe yasan inda take"

Nace "amma Yaya, duk wannan abin ace bani da labari?"

Tace "to ai duk mun dauka kin sani, tunda mijinki ne yake ta kokarin nema dan haka ya za'a yi muyi tunanin bai gaya miki ba? Sai da aka kusan kwana goma sai kawai ga kira daga gidan su Aunty wai ga Ummi can taje gida ita da wani film producer wai yazo neman iznin iyayen ta zai saka ta a film, dama wai suna da

51 / 106