Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
tare da gogo ruwan jikin sumarsa ya watso min. "Tashi zabuwa, kije kiyi alwala tun kafin tawa ta karye" naji kunyar maganar sa sosai, oh Allah, dama haka auren yake?
Ya sake cewa "ki tashi mana, ko ni kadai akace inyi sallar banda ke?" Na hadiye yawu da kyar ina tattaro dukkan bravadon da nake dashi nace "bani da tsarki" ba tare da wata damuwa ba yace "kije kiyi tsarkin sai kiyi alwalar" na bude ido "na shiga uku, ba wannan tsarkin nake nufi ba fa" ya zauna a bakin gadon yana murmushi tare da daga gira daya "to wanne kike nufi?" Nace "ina nufin bani da tsarki ba zanyi sallah ba" ya sake bata rai cikin rashin fahimta, naji haushin sa a raina, a matsayin sa na doctor aiya kamata ace ya gane ko?
Na sake cewa "ina nufin, ba zanyi sallah ba saboda period nake yi" am sure dai ai ya san wannan kalmar kuma yasan abinda take nufi. Ai kuwa ya sani din dan yadda fuskarsa ta chanja kadai ya tabbatar min da cewa ya sani. "What?" Ya fada da sauri. Na ja baya ina sake komawa karshen gado. "Wallahi da gaske nake, na rantse da Allah"
Yace "wannan rantsuwar taki kadai ta isa ta tabbatar min cewa maganar ki ba gaskiya bace ba. Tsoron nawa har ya kai nan Jidda? Lallai muna da aiki a gaban mu ni da ke. Amma bara inzo inyi fata fata da tsoron nan da kunyar gabaki daya ones and for all"
Ya fara biyo ni zuwa karshen gadon, na dunkule a guri daya "wallahi da gaske nake Allah kuwa, ko Alqur'ani aka kawo min zan dafa" yayi dariya "kin kama kanki Baby girl, in ana period ba'a taba Alqur'ani, meaning ke ba kya yi kenan tunda kin ce zaki taba"
Na girgiza kaina kaina "ina nufin na rantse da Alqur'ani period nake yi" ya karaso tare da dora dan ya tsansa akan lips dina "ba'a rantsuwa da komai sai da Allah. Na san kin san haka, meaning kina sane kenan dan kinsan baki da gaskiya shine kika rantse da Alqur'ani" na girgiza kaina "please yaya Doctor. Wallahi dagaske nake"
"Then show me" na bude ido "me?" Yace "period din, show me. In da babu kasa ai anan ake gardamar kokawa ko?" Naji hawaye ya taho min "yanzu ta yaya zan nuna maka period dina? Na rantse maka amma kaki yarda kamar baka sanni ba, Umar Jidda ce fa" yace "Jidda Umar ne fa. Me yasa ke ba zaki yarda dani ba? Me yasa kike jin tsorona? Am not going to hurt you I promise you. Ni wannan abin da kike yi sai nake ji a raina kamar ba kya so na ma"
Nace "ina sonka mana, ka sani ina sonka sosai amma abinda kake so ba zai yiwu ba tunda ga halin da nake ciki. Ka bari, four days ne kawai ya rage zan gama shikenan" ya zaro ido "four what? Kina so in sheka barzahu kenan. Na share hawayen daya taho min "dan dai kwana hudu? Kayi shekaru ma babu wannan din menene laifin kwana hudu?" Yace "shekaru lokacin babu ke a matsayin matata ba. Shekaru lokacin bani da wannan right din" nace "yanzun ma baka dashi ai"
Ya mayar da hannun sa bayana inda ya saka dazu, but this time around maimakon hannun yayi sama sai yayi kasa cikin skirt dina. Na zaro ido da kokarin rike hannunsa amma sai shi ya rike nawa yana wani murmushin da yafi yi min kama da na mugunta. Na saka kuka "na shiga uku Umar me kake yi?" Yace "tabbatar wa bani da right. In na tabbatar sai in rabu da gurin in kama dukkan sauran bangarorin da nake da right a kansu ko?"
Na kwace hannu na daga rikon da yayi min sannan na rike hannunsa da hannu biyu ina kokarin fito dashi amma na kasa, ina jinsa yana yi min dariya tare da yi min tafiyar tsutsa a can. Na koma da baya na zauna akan hannun nasa dan in hana shi karasa wa inda yake son zuwa. Yayi kara "zaki balla min hannu fa" na daki hannun da karfi har da cize lips dan inyi masa mugunta, ya zare hannunsa yana sosa wa "sai na rama. Ki rubuta ki ajiye" na murguda masa baki ina share sauran hawaye na.
Ya tsaya yana kallon hannun sa "ni banga komai ba. Meaning babu komai a gurin kenan" nace "ai baka je inda yake da komai din ba. Na san kuma ka sani"
Ya mayar da hannun sa baya na amma banji saukar sa a bayan ba sai jin fitar zip din rigata nayi, ya zuge shi har kasa. Na yi sauri na rike rigar. "Na shiga uku. Me kake yi haka?" Yace "idan da gaske bani da right a can ai ina da shi anan ko? Can din ma kuma ban yarda ba" na kamkame rigata "dan Allah ka rabu dani. Albarkacin soyayya da kace kana yi min ka rabu dani" ya maimaita abinda nace yana kokarin rabani da rigar "dan Allah ki rabu dani, albarkacin soyayyar da kika ce kina yi min ki rabu dani"
Na sake kankame rigata, sai ya hadani ni da rigar ha rungume mu tsamtsam tare da kokarin tura ni baya in kwanta. Nayi saurin cewa "kaza ta. Ba ka dauko min kaza ta ba" farko yayi kamar bai ji ni ba, sai dana maimaita na kuma kara da cewa "in baka bani kaza ta ba kullum sai na yi maka gori ko yaya nawa zamu haifa" ya sauke ajjiyar zuciya sannan ya sake ni tare da dafe kai, sai kuma yace "ba dai kaza kike son ci ba? You know what? Guda biyu na siyo miki ma da yoghout, saboda a gurina kinfi karfin kaza daya. But tell me please, akwai abinnan ko babu"
Na girgiza kaina "babu. Ka dauko min kazar ka dawo" naga yadda fuskarss tayi lighting up, "da gaske? Okay ki tashi kiyi alwala kafin in dauko, in na dawo nima sai in sake sai muyi sallah" na gyada kai da sauri shi kuma ya tashi jikinsa cike da kuzari ya fita.
Na gyara rigata na zuge, na jiyo shi ya bude kofar waje ya fita sannan naji ya bude mota ya kuma rufe, ya sake dawowa naji yayi locking kofar palo,a lokacin ne na mike nima da sauri naje bakin kofa na saka mata lock sannan na zauna a gurin na jingina bayana da jikin kofar ina murmushin mugunta. Ba shi mugunta ba? Zai ga mugunta.
Ina jinsa ya shigo corridor din sannan ya murda handle din kofar dakin da nake ciki na kuma turo "damn it. Jidda open this door" nayi murmushi bance komai ba. "Na san kina jina, open this door idan ba haka ba in na kama ki sai na yayyanka neman ki na cinye" na danyi dariya still ban ce komai ba.
Waya ta da take cikin handbag dina akan dresser ta fara kara da ringtone dinsa, na mike na dauko ta na zauna a bakin gado ina kallon sunan sa akan screen din "Umarul Faruq" na murguda baki na ajiye wayar na sauki ledar pad a cikin jaka ta na tafi toilet. Nasan ina dauka zaiyi min dadin bakin da zai saka in bude masa ni kuma gaskiya tsoron yadda yake yi dinnan nake ji. Ta yaya zai ce min in nuna masa period dina? How on earth can I do that?
Na chanja pad, na wanke make up din fuskata sannan na fito na chanja kaya. Still wayar tana ta kida abinta. Na gyara gadon na kashe fitila tare da yin mika gami da hamma, zanyi bacci na mai dadi kamar yadda nayi niyya. Na hau gado na ja bargo tare da daukan wayar. Nine missed calls and counting. Sai dai bai kuma kira ba sai message daya turo min.
"Ko dai ki bude kofar nan ko kumada safe ki zama widow"
Nayi murmushi sannan na tura masa reply
"Naki din, waye yace ka saka min hannu a skirt kace sai kaga period dina"
"Na tuba nabi Allah da annabi na biki. Ba zan kuma tabaki ba ma. Ki bude min kawai kallonki zan zauna inyi tayi har gari ya waye"
"Haha. Ai ba yau aka haife ni ba"
"Kajin ki zasu huce"
"Na bar maka, ka cinye"
"Dan Allah ki bude"
"Period nake yi"
"To ni a ina zan kwanta?"
"A dakin ka"
"Kofar ta lalace bata buduwa"
"Ka kwana a palo to"
"Babu katifa"
"Ka kwanta akan kujera"
"Dan Allah ki bude, da gaske nake fa mutuwa zanyi kafin safe"
"Allah yaji kan ka, sai mun hadu a lahira"
"Dama ashe ba sona kike ba yaudara ta kike yi?"
"Goodnight"
Sai na kashe wayar gabaki daya na ja bargo nayi kwanciya ta. Amma kuma sai na kasa baccin, ko yayi bacci? What if da gaske yake ba zai iya baccin ba? What if da gaske yake dakin sa yaki buduwa?
Na jima ina ta juyi a kan gado, babu irin tunanin da bana yi. A karshe na yaye bargon na mike na tafi bakin kofar ina lekawa ta keyhole, babu abinda na hango sai kofar dakin sa. Na bude lock din na murda kofar a hankali na leka kaina. Babu kowa a corridor din. Na fita na tsaya a kofar dakinsa sannan na leka ta keyhole. Ban hango komai ba. Na dora hannuna a handle sai kuma wata magana daya fada dazu ta fado min a raina, na cewa zan zo inyi begging dinsa, yanzu ina shiga zai iya juya maganar yace abinda nazo nema kenan. Kuma ya samu abin tsokana ta kenan.
Na saki handle din amma duk da haka sai na saka kunne na ina saurare, babu komai sai hucin ac, na gyada kai. Yayi baccin sa ma ni ce na damu kaina a kansa har na kasa bacci.
Na juya na koma dakina na rufe.....
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Episode Fifteen : The New Couple*
Ina komawa daki na mayar da lock dina sannan na hau gado nayi kwanciya ta.
Sai dai duk da gajiyar da nake tare da ita, da tabbatar wa da nayi cewa he is okay amma sai na kasa baccin, ko dan bakunta ne? Yawanci in naje bakon guri bana iya bacci har sai na saba da gurin tukunna. Sai da gari ya kusa wayewa sannan na samu bacci mai nauyi ya dauke ni kuma saboda rashin sallah ta sai nayi dogon bacci sosai har gari ya waye. Sanda na farka har rana ta fito sosai, sai dai duk da haka banji baccin ya ishe ni ba.
Amma sai dai abu daya ne ya saka ni dole na tashi, wata azababbiyar yunwa da naji tana kwakular cikina. Na tashi na nemo sabon brush dina da na saka a karamar jaka ta, sai dai kuma babu toothpaste a toilet din kuma ban zo da shi ba. Haka na hakura na wanke bakin sai kuma nayi wanka na kawai gabaki daya na fito na gyara jikina na kuma shafa mai sannan na dauko doguwar riga zan saka sai kuma na fasa na dauko rigada skirt na atamfa na saka na feshe jikina da turare, ina tunanin sa a raina "ko ya tashi?" Nayi murmushi dana tuno da kalaman sa na cewa zai mutu kafin safe.
Sai kuma na tuno da kajin da ya shigo da su, nasan in ma zai ci ba zai iya cinyewa ba, Allah yasa basu yi komai ba in samu inci dan ba karamar yunwa nake ji ba. Har zan fita sai kuma na dawo na nemi hijab na saka, Umar ba kunya ce da shi ba babu ruwansa da cewa rana ce yanzu zai iya cewa zai taba ni.
Na murda kofar a hankali na leka na tabbatar baya corridor din sannan na saka kafa ta cikin sanda na fita, na bude kofar falon na shiga a hankali ina dosar hanyar da zata kaini kitchen, maybe acan ya ajjiye kajin.
Sai dai taku biyu nayi na ganshi.....
Yana kwance akan doguwar kujera, pillows every where, ya dauko standing pan ya tsayar da ita a kansa ga kuma uban sanyin acn da naji tana ratsa har cikin kashi na. Amma shi ko riga babu a jikin sa sai singlet da dogon wando, Daga yanayin kwanciyar sa na fahimci tun dare yake a haka bana jin ko sallah ya tashi yayi.
Sai na fasa zuwa kitchen din na taho inda yake, na kashe fankar na janye ta ina fargabar in ba sa'a yayi ba sai mura ta kama shi dan ni already sanyin palon ya saka ni ina jina kamar mai zazzaɓi. Sai kuma na tsaya ina kare masa kallo, zuciya ta tana yaba kyawun halittar sa da yanayin kirar jikinsa, Sannan kuma raina yana kara jin tsoron sa. A lokacin na lura duk harken fuskar sa da nake gani fatar jikinsa tafi hashe Sannan kuma raina yana kara jin tsoron sa.
Na koma side din kansa a hankali na daki jikin kujerar.
"Yaya Doctor?"
Na sake daga murya
"Yaya Doctor ka tashi fa.....ko kayi sallah ne? Rana ta fito fa"
Ya dan motsa kadan sannan yayi juyi, yana zubar da some of the pillows daya jejjera akan kujerar, na dauki daya daga ciki na dan dake shi kadan. "Ka tashi fa....assalatu khairun minal...." Ya juyo ya watso min kallon daya saka na yar da pillow din na ja da baya d sauri, banason wannan jan idon nasa.
Yace "go away. Kar ki sake min magana babu ruwana da ke"
Ya mayar da kansa cikin pillow sannan ya dauki wani ya dora a saman fuskarsa.
Na dauki remote din AC dana gani a kusa da shi na fara neman yadda zan rage ta.
"Ka tashi dan Allah, kayi wanka da ruwa mai zafi kar kayi mura"
Ya dauke pillown daya rufe fuskarsa da shi "don't act like you care. Bayan abinda kike yi min jiya"
Na langwabe kai, "kayi hakuri yayana. Nima ba'a son raina hakan ta kasance ba ai na fada maka uzuri na" ya kara hade rai "ba'a son ranki ba? Ba da kafafuwanki kika tashi kika saka hannun ki kika rufe min kofa ba? A matsayi na na ango ace na kwana a falo akan kujera tare da pillow?"
Na rufe baki na saboda dariyar data taho min, ya kankance ido, "okay dariya ma na baki ko?" Na daga hannu ina rike dariyar "sorry dear. Ba dariya nake yi maka ba kawai dai......kayi hakuri please.....na dauka a dakin ka ka kwanta ai" yace "bana gaya miki kofar ta lalace ba" na dafe kai "na dauka ba da gaske kake ba ai"
Ya juya min baya yana mita "You locked your door and switched off your phone. Ko muryar ki ma baki barni naji ba. You are very cruel"
Na zauna akan hannun kujerar ina jin babu dadi a zuciyata, he seemed to be truly angry with me. "To ba nace kayi hakuri ba, na gaya maka ai excuse dina tun jiyan amma kaki fahimta kace lallai sai ka gani. And you know me, ba zan ina nuna maka ba ka sani"
bai ce komai ba kuma bai juyo ba. Na dan saka pillow na dake shi kadan "kace ka hakura mana to......yaya zaka yi fushi dani ne wai washegarin bikin mu" ya juyo da sauri tare da mike wa zaune "ni kuma da kika rufewa kofa fa, on our first night, ki ka saka na kwana akan kujera" na sunkuyar da ido na kasa ina jin nauyin laifina "kayi hakuri please"
Ya danyi shiru bai ce komai ba, but ina jin idonsa a kaina. Sai kuma naji yace "okay let's make a deal, kina so in yafe miki ko?" Na gyada kai. Yace "then earn it" na dago kai "earn what?" Yace "yafiyar. Ba a yin komai for free ai ko? Do something sai in yafe miki" nayi sensing wayo zaiyi min, na juya ido na nace "me zanyi in yi earning forgiveness din?" Ya jawo ni daga hannun kujerar na fado kan cinyarsa, nayi kokarin mikewa da sauri "na shiga uku" ya zagaye ni da hannayensa yana kara jawo ni jikinsa "baki shiga uku ba Baby girl, not yet"
Na cigaba da kokarin mikewa tsaye, he tighten his grip dole na hakura na sauke ajjiyar zuciya ina kallon sa nace "to me zanyi a yafe min din?" Yayi murmushi, his first smile of the day "kiss me" na bude ido "what? Ya kashe min ido "simple. Kiss me, sai in tabbatar da gaske kina sona akwai kwakwkwaran dalilin da ya saka kika rufe min kofa".
Na girgiza kaina da sauri amma kafin inyi magana sai ya rigani yace "either you kiss me or I kiss you. Choose one" ya fada yana daidaita fuskarsa kusa da tawa, idonsa akan lips dina.
Na saka hannayena biyu na rike fuskar sa sannan na tura ta baya ina dariya "wait wait wait. I will do it" yace "uhum, yanzu kika yi batu" nace "amma kasan dai ina jin kunyar ka ko? You have to close your eyes"
Yace "okay. No problem" ya rufe idonsa har da kara jingina da jikin kujera yana relaxing, na tsara ina karewa fuskar sa kallo, ban taba kallonta so close to me ba sai ranar and sai naga tafi kyau up close, murmushin sa yana kara mata kyau,
Yace "waiting........."
Nace "ban yarda da kai ba gaskiya, kana kallona ta kasan idonka, ya bude idon yana dariya "na rantse bana kallon ki" na harare shi "ba wani nan, ban yarda da kai ba"
Sai na saka hannu na cikin hijab dina na ciro dankwali na sannan na ninke shi yayi kauri na daga shi nace "rufe idonka, sai na daure maka sannan zan tabbatar baka kallona"
He obeyed and closed his eyes, ni kuma na daure masa idon da dankalin har na cije lebe dan in tabbatar ya dauru sosai, yayi dariya "mugunta ko?"
Sai dana chuchchusa na tabbatar ba zai ganni ba sannan na kyale shi. Sai kuma na tsaya