Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
a gabana a yanzu haka, amma yadda har yanzu suka kasa fahimta ta shine yake damuna, shine kuma abinda nake so in fahimtar da Umma.
Sai data gama wayar ta ajiye tare da jan tsaki tace "Allah ya kyauta". Na kira sunanta a hankali "Umma" bata kalle ni ba tace "ina jin ki" nace "Umma kiyi hakuri akan abinda ya faru da ni, nasan ba haka kika so ba, Allah ya huci zuciyarki".
Ta juyo tana harara ta "kina sane ai da cewa zaki bata min din ai amma kika yi abinda kika yi din" na girgiza kaina nace "Umma na san ranki zai baci amma ina so ki san cewa nawa ran yafi naki baci akan maganar, tawa zuciyar tafi taki shiga damuwa akan maganar....." Ta katse ni "karya kike yi Hauwa'u. Idan ranki baya so me yasa kika yi. Mutumin nan babu abinda ya rage ki da shi. Mata nawa suke neman irin sa sun rasa? Mata nawa ne suke zaune da wadanda suka fishi munin hali suna hakuri saboda sun san bautar Allah suke yi? Sai ke yar gwal? Ke ce ba zaki iya ba?"
Na danyi shiru ina harhado maganar da zan gaya mata sannan nace "Umma aure ibada ne, hanya ce ta samun aljanna kuma at the same time hanya ta samun wuta" ta kalle ni da sauri "wuta? Jidda auren ne kike cewa hanyar shiga wuta? Anya kuwa kina da hankali?"
Na gyada kai na "Umma aure ibada ne, sunna ce mai karfi, amma kuma abinda za'a yi a cikin auren farilla ne, in anyi dai dai a dace da aljanna in anyi ba dai dai ba kuma a samu zunubin da zai iya kai mutum ga wuta. Umma na san kin sha jin labarai na matan da suka kashe mazajen su har lahira, shin wadannan aure ba wuta ya kai su ba? Ko kuma matan da suke zama da mazajensu shekara da shekaru ba tare da suna iya yi musu biyayya ba, ba tare da suna iya hada gado da su ba, shin wadannan aure ba wuta ya kai su ba? Ko kuma matan da mazajensu suke halayya irin ta Umar sai suma suka dauki halayyar a matsayin revenge suke yi dan su rama, shin wadannan suma aure ba wuta ya kai su ba? Umma ki zabar min, da in zauna a gabanki a matsayin bazawara da kuma in fada cikin jerin wadancan matan da na lissafa wanne ne dai dai?"
Na lumshe idona ina tuna marin da nayi wa Umar ranar da zan bar gidan sa da kuma yadda zuciyata tayi ta gaya min in dauki wuka in je in caka masa, tabbas na kusa shiga sahun wadancan matan.
Na goge hawayen da ya fara zarya a kuncina nace "Umma ni ban san komai ba game da rayuwa, dan ilimi na dan kadan nake da shi amma a cikin kadan din nan na san dai dai na san ba dai dai ba. Bani da sani sosai akan rayuwa, amma nasan duk matan da suke zaune da mazaje irin Umar ko kuma wadanda suka fi Umar munin hali to ba suna zaune ne da su saboda suna hakuri irin hakurin da Allah yace ayi ba, da yawa daga cikin su suna zaune ne dan babu yadda zasu yi, wadansu daga cikin su dan suna tsoron in sun rabu da su zasu rasa shinkafa da taliyar da zasu ci, idan kuwa har suna da sana'a ko aiki to dalilin zamansu shine dan iyaye ba zasu karbe su ba in sun koma gida dan wasu iyayen da yarsu ta fito gwara ta mutu dan bakin ciki, idan kuwa har iyayen zasu karbe su kuma still suke zaune to dan suna tsoron zawarci ne suna tsoron loosing sunan su na matar aure da kuma tunanin mijin da zasu aura nan gaba wanda ni a ganina ba dalili bane ba dan Allah ne mai zaben miji ba mutum ba, kamar yadda ya baka wancan haka zai baka wani ko da kuwa shima mai irin waccan matsalar ne ko kuma wata daban sai ka dauke shi shima a matsayin wata kaddarar ta daban. Idan kuwa har dukkan wadannan sharudan sun cika kuma still suna gayawa kansu suna zaman hakuri ne to watakila suna yin irin hakurin da nayi shekara shida ina yi ne, hakurin da babu lada a cikin sa "
"Umma mu'amala da fasiki haramun ne. Duk wanda kuwa ya san da haka amma yake cigaba da yi bisa wani dalili nasa yake gayawa kansa cewa hakuri yake yi to tabbas bashi da ladan hakuri, dan bana jin akwai lada a cikin aikin haram. Kuma ba dan Allah yake yi ba, kamar yadda na zauna da Umar dan ina son shi na cigaba da gaya wa kaina cewa zaman hakuri nake yi"
"Umma ina ganin ubangiji ya haramta mu'amala da fasiki ne saboda hikimomi irin nasa, na farko kamar yadda na fada ita halayya naso take yi, in kana abota ko auratayya ko ma wacce irin nau'in mu'amala ce da akwai chance na cewa kaima zaka dauki fasikancin sa wata rana, ko ba zina ba ko da salon magana ne in kana tare da mutum sai kaga ka koyi irin yanayin maganar sa ba tare da kai kanka kasan sanda ka fara yi ba, hikima ta biyu a fahimta ta ita ce shi fasiki kullum yana tare ne da fushin ubangiji da kuma tsinuwar malaiku, idan kuma ubangiji yayi niyyar saukar da fushin sa akan fasikin nan ba lallai ne masifar da zata same shi ta same shi shi kadai ba, zata shafa ne har da wadanda suke tare da shi, duk wanda ya zauna dasu har fushin ubangiji ya shafe shi shi ya jawo wa kansa tunda kiri kiri ubangiji ya haramta mu'amala da su. Hikima ta uku a fahimta ta itace idan ana kyamar su ana kin muamala da su ana kuma kin basu aure da kuma raba auratayya dasu hakan zai yi discouraging masu son joining dinsu, hakan zai saka rayuwa tayi musu kunci watakila kuma sanadiyyar hakan su samu shiriya. Amma in ana cigaba da zama da su ana cigaba da muamala da su ana nuna musu abinda suke yi ba komai bane ba kamar ana kara musu karfin gwuiwar cigaba da abinda suke yi ne. May Allah forgive me if any of the things I said is wrong but ni haka na fahimta"
"Umma ni ban san komai ba, amma na san banbancin halal da haram, na kuma san hukuncin kowanne daga ciki. Na san cewa rabuwar aure halal ce....." Na fada ina bude mata hannu na na dama a gabanta, "na san kuma auren fasiki haramun ne" na bude mata hannu na na hagu a gabanta sannan ina kallon ta nace "umma a matsayin ki na mahaifiya ta wanne zaki zabamin tsakanin halal da haram? Wanne ne kike ganin zai sa in dace a duniya da kuma a lahira?"
Ta jima tana kallona sai kuma ta dauke kai gefe tace "Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" na sauke ajjiyar zuciya nace "ameen Umma. Na gode" sai na mike zan shiga cikin daki.
Ta kira sunana "Jidda" na amsa tare da juyowa sai tace "Hajiya ta san maganar nan? Me tace akai?" Na danyi murmushi nace "Hajiya ta sani Umma, bata ce komai ba kuma ba zata ce komai ba, ubangiji ya riga yayi taking care of her for me"
Washegari muka bar kasar very relaxed and very satisfied. A jirgi na tuno da damuwar da na shiga ranar da zamu taho saboda ina tunanin rashin lafiyar Umar sai na fahimci yanzu babu ko rabin damuwar a tare da ni, na fahimci cewa Umar ya fara fita daga raina kamar yadda aurensa ya fice gabakidaya daga raina.
Muna zuwa muka tarar da yan taryar mu, Yaya Tahir da matarsa da babyn su, Abbah, da kuma Farhan. A gida kuma muka tarar Abba har da sakawa a gyara wa Umma dakinta, mun lura har kwalliya yayi ya saka kaya masu kyau, ni da Farhan muka yi ta gulmar sa muna cewa yayi wa amaryar sa kwalliya. Mun kuma tarar neman auren Farhan ya kankama har an kawo kuɗi dan ma tace Abba ne yake ta delaying maganar yace bai gama bincike ba, a raina nace "an sha Abba ya warke, ba zai kuma sake ba".
A sitting room na tarar da kayana, har furnitures din gabaki daya na bedroom dina dana falo dana dakin yara, an cika su a sitting room din an daina amfani da shi, sai Abbah yake ce mana wai aiko dasu aka yi daga gidan su Umar, ban ce komai ba na bar maganar.
Washegari na shirya yara suka da kayan su nace Amira ta kai su gidan kakannin su su kwana biyu tare da su, bata jima ba sai gata ta dawo, a ranar da dare kuma sai Mama ta kira ni wai yara sun ce a kira ni su gaishe ni, sai kace ba dazu muka rabu ba, bayan mun gaisa da su kuma sai ta karba tace min "su Yasmin sunyi kyau kamar ba su ba, har fari naga sun kara yi" na danyi dariya nace "watakila weather din garin ce ta karbe su" tace "haka ne. Allah ya sa zaku samu bikin Mufida. Tana ta nemanki a waya bata san yadda zata same ki ba tace a social media ma kina offline" sai naji babu dadi wai za'a yi bikin Mufida ban sani ba, nace zan kira ta a waya. Har munyi sallama kuma sai tace "gashi kuma su Yasmin basu samu babansu ba, amma na kira shi a waya sun gaisa" sai naji babu dadi da ban tambayi jikinsa ba nace "ya jikin nasa, ya samu sauki kenan tunda har yayi tafiya" tace "jikinsa da sauki. Amma yanzu ma yana asibiti a Dubai. Muna dai saka ran za'a sallame shi kafin bikin Mufida" nace "ayya, Allah ya kara masa lafiya" sai tace "zan turo miki number din da yake using a can sai ki kira shi ki duba shi, dan Allah" sai na kasa ce mata a'a, nace to.
Muna ajiye wayar sai ga number ta turo min mai code din Dubai, nayi saving da sunan "Dubai" amma ban kira ba kuma bani da niyya.
Washegari da safe na koma gurin aiki na, nayi cike ciken duk da ya kamata inyi sannan aka yi posting dina paediatric ward aka saka ni a duty roster sai na dawo gida, ina zuwa na tarar da Abba a tsakar gida na gaishe shi sai yayi min maganar kayana da aka zuba a sitting room, "ya zaki yi dasu? Dan babu dakin da zasu shiga a gidan nan" na danyi tunani sai nace masa "siyarwa zanyi" ya gyada kai "hakan ma dai dai ne, in an siyar din sai a ajiye kudin in Allah ya kawo wani auren kinga cikawa kawai za'a yi ayi wasu kayan" nayi murmushi kawai, shi Abba har ya fara yi min lissafin wani auren.
Sai kuma yayi min maganar inda zamu zauna ni da yara. "Ga daki nan ciki daya inda yaruwarki take, tunda ta kusa tashi ke sai ki zauna a ciki tare da yaran. Sai na samu kudi sai a danyi muku gyara a ciki a shigar muku da bandakin tsakar gidan nan zuwa cikin dakin saboda sanyi"
Na danyi murmushi ina jin dadi nace "Abba akwai wasu kudade a hannuna sai ayi amfani da su gurin gyaran" yace "ba wani gyara za'a yi da yawa ba ai, ɗan yadda zaku ji daɗin zama ne kafin Allah ya fito da wani mijin" na sake murmushi. Abba will never change.
Da dare ina kwance ina kewar yayana sai ga kira ya shigo waya ta, na duba naga "Dubai" sai nayi tsaki na ajiye wayar, I need to learn to say "no" and mean "no" bana son ayi ta kwan gaba kwan baya akan magana ta da Umar, an riga anyi an gama sai dai kuma labari, labarin ma watarana ba za'a yi shi ba
Ganin wayar tana ta kara har Umma ta fara kallon ta sai na dauka na saka ta a silent sannan na kife ta dan kar ta cigaba da haske. Sai da nayi bacci na farka sannan na duba wayar na ga 5 missed calls daga Dubai, da kuma message guda daya "Jidda. Umarul Faruq ne" na ja tsaki, as if I don't know. Na san shi din ne ai shi yasa naki dauka.
Washegari kafin in fita office na kira Abbah karami muka yi maganar gyaran dakin da Abba ya bani, plaster kawai za'a gyara inda ya danyi cracks sannan ayi fenti, sai toilet da za'a yiwa gyare-gyare a shigar da shi ciki, babu bata lokaci yayi min bill din komai na bashi aka fara aiki, cikin kankanin lokaci aka gama gyaran dakin fes kamar na amarya.
Sai kuma muka koma maganar siyar da kayan dakina, dan sunyi wa dakin girma. Tunanin farko da yazo kaina shine na wasu instagram accounts din da nake ganin suna siyar da second hand kayayyaki kuma na fahimci suna ciniki sosai saboda yadda nake ganin responses na mutane. Sai nayi tunanin why not inyi musu magana su zo su sayi nawa su siyar?
Sai kuma na sake wani tunanin, why not nima in bude irin wannan business din? Why not nima in siyar da kayayyaki na da kaina through the same process da naga suna using sannan kuma in cigaba da siya daga gurin mutane ina siyarwa?
I thought about it a lot and realized it wasn't such a bad idea, sai kuma nayi addu'a akan hakan na kuma gayawa Umma nace itama ta gaya wa Abba in samu amincewar su and I set up my mind to it, sai fatan Allah ya bani nasara.
Katifa kawai na dauka a cikin kayana na saka a sabon dakina na saka carpet a kasa tare da labulaye, sai kuma na bayar aka yi min wardrobe madaidaiciya wadda zata shiga dakin kuma zata dauki kayan mu, na zuba mana kayan sakawar mu ni da yarana, sannan a dakin ma na zuba mana abubuwan da nake ganin zamu bukata irin su shoe rack, standing fan, da dan karamin set na kujera da table wanda zamu iya zama akai muyi rubutu and I was happy with my new room, with my new life.
Naci sa'a Abba ya amince da maganar business dina sai dai da sharadin ba zan ke fita anyhow da sunan kasuwanci ba sai dai in samu mai yi min ni kuma ina funding. Na yarda da sharadin, sannan nayi masa godiya.
Abbah karami na samu da maganar business din da nake so in fara, kuma na nemi muyi hadin gwiwa ni da shi saboda shi namiji ne zai taimaka min wajen zirga zirga da kuma abubuwan da suke buƙatar lokaci da karfi, da yake shi mai business mind ne dan yafi son kasuwanci ma akan karatu sai ya amince. Muka yi yarjejeniyar zan ke bashi 30% na duk ribar da muka samu. Shi ya ringa fita da kayan cikin railer din kofar gidan mu yana daukan su pictures, furnitures din dakina dana falo da na dakin yara da dining table da kuma tv set, da su muka fara.
A take muka saka a whatsapp status din mu da kuma instagram accounts dinmu muka yi captioning as for sale. Nasan yan'uwa da friends zasu gani kuma zasuyi magana, mutane zasu fadi duk abinda suka ga dama akan siyar da kayan da zanyi but I don't care. Yes, bani na siya kayan ba amma ina ganin zaman auren da nayi da Umar da yayan da na haifa masa I deserve that, kuma bani na roke shi ba.
Ina saka wa mutane suka fara tambayar price, da yawa daga cikin masu tambayar na san ba siya zasu yi ba amma na biye musu na ringa fada musu price din da na saka wa kayan. It was hard at first, kamar ba za'a siya ba amma kyawun kayan da kuma quality din su dan banbancin su da sababbi kadan ne amarya ma zata iya using, sai gashi wata colleague dina a asibiti ta hada ni da wata mata da ta siya set din kujerun da kuma gadon ta kuma siyar min da nata da take son chanjawa, Abbah kuma aka siyi dining table a hannunsa. And that was the beginning of my business carrier..........
Daya daga cikin dakunan cikin sitting room muka roki Abba ya bamu sai muka bude shi muka yi extending dinsa zuwa railer din kodar gida, yayi girma sosai, anan muka zuba kayan kasuwancin mu, Abbah karami har da saka table da kujera wai office dinsa ne a matsayin sa na manager. Sai kuma na bude instagram handle musamman saboda business din na kuma saka masa suna "Used...to be reused" Sai nayi sharing link din zuwa duk sauran social media accounts dina na nemi mutane suyi following, na kuma nemi yan uwa da abokan arziki su taya ni sharing dan in kara samun followers, sai kuma na nemi wadanda nake kallo a matsayin social media celebrities suma na roke su suyi min talla a handles din su, wadansu sunyi min free wadansu kuma sai da na biya su something but it was worth it dan nan da nan followers dina suka fara counting in thousands, ni kuma na dage gurin daukan pictures din kayan kitchen dina, labulaye na, da kuma kayan matar da na siya wadanda Abba ya kai aka gyara su akayi musu sabon penti.
Ai kuwa nan take aka fara rububin siyan kayan kitchen dina da tv set da sauran electronics dina, kowa kuma in ya siya zan tabbatar masa da cewa in ya same su faulty zai iya dawowa da su ya karbi kudinsa, ina yi kuma ina cigiyar wanda yake son siyar da kayan sa. Ban jima ba na samu wata da zasu sake gida kuma zasu sake komai na kayan gidan, thought sababbi take so dan haka bata siya daga gare ni ba amma ta siyar min da komai nata, wanda kafin in gama siya sai da nayi wa account dina tas but it was worth it dan komai da na siya sai na gyara abinda yake bukatar gyara