Chapter 50 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   50 / 106

147K to 150K   out of 316K words

din kuma......"

Nace "tace in ban yarda ba aje asibiti a gwada, are you willing to do that?"

Sai a lokacin naga abinda tun jiya nake neman gani a fuskar sa amma yaki bani damar gani, guilt, for brief seconds yayi appearing sannan ya dauke da ace bana kallon sa ma da bazan gani ba, "asibiti? Gwaji? Haka tace? Me yasa baki fada min hakan ba tun jiya? Na riga na kona su tun jiyan da nasan tace haka da na barsu ko dan in tabbatar miki da cewa ba nawa bane ba"

Na danyi murmushin takaici sannan na juya na cigaba da aikina. Daga dukkan alamu Umar bashi da niyyar admitting laifinsa a wannan karon, ya jima a tsaye a gurin, jin bani da niyyar cigaba da biye masa sai naji ya fita daga kitchen din, jimawa kadan naji tashin motarsa ya bar gidan.

Sai dana karasa komai a kitchen din sannan na dawo falo, na lura da abincin da na zuba masa ko taba shi bai yi ba. Motsin su Yasmin da naji ya saka na tafi daki gurin su dan basu dukkan kulawa ta.

Har azahar ban yanke shawarar ta yadda zan tunkari iyayen Umar da wannan maganar ba, amma kuma ban chanja shawarar gaya musu din ba dan alokacin ina jin hakan shine mafita a gare ni.

Indomie kawai na dafa mana da rana muka ci ni da yara, sai laasar na dora dinner nayi tuwon shinkafa miyar taushe na gyara komai kamar yadda na saba ba zaka taba dauka da akwai wani miki a zuciyata ba amma bakikkirin nake jinta tamkar dunkulallen gawayi.

And to add more salt to my wound sai ga kira ya shigo wayata daga Maryam, yanzu tayi amfani ne da number din ta, na rike wayar a hannuna ina kalla inajin raina yana zafi gar ta katse ban iya dauka ba, na fara neman yadda zanyi blocking dinta sai wani kiran nata ya sake shigowa. Sai kawai wani tunani ya fado zuciyata. Me yasa zan kasa daukan wayarta har kuma inyi blocking dinta? Shin waye yayi abin kunya a tsakanin ni da ita? Waye ya kamata yake boye fuskar sa waye ya kamata ya kasa bacci?

Sai na daga wayar na saka a kunne na amma bance komai ba. Naji muryar ta  "Hello? Matar gold mai mijin diamond. Da fatan kin ga sako na. Da naji baki dauka ba na dauka kina gida kina yiwa Umma kuka" na gyara muryata na dan daga murya nace "Yasmin kira Daddy yazo za'a fara program din da yake so a TV" sai kuma nayi murmushi ganin Yasmin ta tsaya tana kallona dan tasan Daddy baya gida, amma sakon da nake son isarwa yaje inda yakamata yaje din.

Sai kuma nace "hello Mery G mai kike cewa? Sakon ki ko? Eh na gani kuma na karba har na adana su. Amma ina son yi miki tambaya guda daya, me kike so kiyi achieving da kika aiko min da wannan sakon? Uhmmm"

Tayi dariya, amma naji muryar ta ta rage armashi sannan tace "baki gane ba ke har yanzu sai nayi miki bayani dalla dalla? Ina so ki fahimci cewa you are not the only woman in his life dan haka ki daina wani cikabaki kina ganin kanki kamar wata mai muhimmanci ko wata daraja ta musamman, duk abinda kike gani nima na gani, duk kuma abinda kike ji nima naji"

Na lumshe ido nana bude ina kokarin kwantar da zuciyata. Nace "really? Ashe toshewar kwakwalwar ki har ta kai haka Maryam? Ta yaya zaki kwatanta darajar lu'ulu'un da aka adana a cikin gida a cikin ma'ajiyar ta musamman aka kuma samar masa guri na musamman a cikin zuciya da kuma shaddar gefen titin da aka shiga aka fitar da datti aka fito ba tare da an biya ko kwandala ba"

"Maganar sakon ki kuma na gani na kuma dauka sannan kuma na adana shi. Ba kinyi maganar yin test a asibiti ba? Tabbas za'a yi test kamar yadda kika bukata amma ba yanzu za'a yi ba sai ranar da kika gama yawo offices din maza kika gama bude musu kafafuwan ki kika samu wani garan yayi niyyar rufa miki asiri ya aure ki a lokacin zan dauko ajjiya ta in kira shi tare da iyayensa da naki iyayen muje asibiti ayi wannan gwajin da kike magana akai, dan tabbas in dai abinda kika bani daga jikin Umar ya fito a lokacin da yake tare da ke to tabbas a jikin condom din za'a samu dna din ki kema, then sai kiyi musu bayanin yadda yaje gurin. Dan haka sakon da kika aiko min da shi ba wai shaida ce gare ni ba shaida ce a kanki kema"

"Albishir na gaba da zan miki shine tun jiya na gaya wa Mufida abinda kika yi, kuma na tabbatar kin san halin budadden bakinta dan haka zuwa yanzu ina jin kusan rabin kawayen mu sunsan abinda kika yi, suma kuma zasu fadawa wasu wadanda zasu fadawa wasu suma. Dan haka sai kisan irin takun da zaki ke yi a cikin mutane. The stain will forever be on you"

"Bayan nan kuma ina so inyi miki wani albishir din, you have no idea who Umar is, da kin sani ko Maryam da ba zaki fara kokarin yin abinda kika yi ba. Ba ke bace ta farko ba, amma ina jin duk cikin su kinfi kowa kaskanci tunda bashi kanki kika yi kyauta ba tare da ko kwandalar sa ba, gwara ma wadanda yake bawa kudi at least sun tsira da wani abu, ke kuwa babu mutumci babu dajara babu kuma ko kwandala. A gurin Umar darajar ki daidai take data toilet paper din da yayi amfani da ita ya goge datti daga jikinsa sannan kuma ya jefar a trashcan. Wannan shine abinda zai yi miki, zai jefa ki a trashcan just like the trash that you are. Idan baki yarda ba ki jira nan da maximum of 24 hours ki ga abinda zaiyi miki sai kin yi regretting ranar da kika fara dora idon ki a kansa. And good luck finding a husband after this"

"Nonsense trash"

Sai kuma na dan janye wayar daga fuskata nace "Darling bara inzo in serving dinka karbka bata jikin ka"

Na katse wayar na ajiye, ina jin kusan rabin zuciyata yana yin fari. Sometimes it feels so good in anyi maka ka rama.

Yes, na wanke Maryam amma ba haka yana nufin nabi bayan Umar bane ba. Dan haka daya dawo da dare ma ko fuska bai gani ba a gurina har ya gama kame kamensa ya hakura ya rabu dani ya ja yayansa suka yi ta hirar su yana bawa Yasmin labarin makarantar da ya dubo mata. Suka gama ya dauke su suka fita sai gasu sun siyo school bag da lunchbox har da na Asad shima duk da cewa banda shi za'a saka a school din.

Sai da dare bayan na kwantar da yara ina shirin kwanciya nima sai ya shigo ya kama hannuna na "ki jira ni zuwa gobe, zan fada miki abinda zai saka ki bani hakuri akan zargin da kika yi min" na karbe hannu na na kwanta ba tare da nace komai ba.

Washegari ma da wuri ya fita, sai dai zuwa azahar sai gashi ya dawo ya tari yaransa ya dauki kowanne yadaga sama yayi kissing sannan ya basu chocolate. Sai Yasmin tace "Daddy baka bawa Mommy ba" sai ya taho kusa dani ya zauna yana murmushi sannan ya miko min chocolate din, na miko hannu zamy karba saboda idon yaran da suke kallon mu Yasmin tana ta zagba murmushi, a lokacin naga abinda yake hannun sa, band dina ne, na kama na zare shi daga hannun ina kallon sa.

Yayi murmushi "na karbo abina" naji raina ya fara baci sai nayi shiru bance komai ba, ya ce "baki tambayeni yadda nayi na karba ba?" Na daga kafada "ai kasan inda yake dama, zuwa kayi kace ta baka" sai ya gyada kai "hakane, amma bani naje ba, aikawa nayi, police na aika suka karbo min"

Na bude ido ina kallon sa, sai yace "na gaya miki I will find out yadda ta chanja min ko? Na gano yadda tayi tun jiya. A duk sanda zan shiga surgery ina cire shi tare da rings din hannuna in bar su a office sai na fito sannan in mayar. A ranar I accidentally left my office door open, ita kuma ta shiga ta chanja ni kuma dana fito ban lura ba na saka kawai na taho gida, kayan kuma nafi tunanin a cikin gidan nan ta shigo ta ajiye su dan bana barin motata a bude a office. Sai dai mai gadi yace bai ga shigowar taba, maybe ta faki idon sa ne"

Na rufe idona ina so inyi tunani sai ya cigaba "bayan nayi tunanin a office ta chanja min sai nayi reporting to security office na asibitin mu cewa anyi min sata a office, we checked the CCTV footage and we saw her entering the office. Na fada musu kawar kanwa ta ce sai na kira Mufida na tambayeta address dinta kuma ta bani ni kuma na basu suka he har gida suka kamata"

"Tana hannun su har yanzu, nace su rike ta har sai na gama bincika office din na tabbatar da abubuwan da aka dauka a ciki, na gaya musu dai wannan band din ne ban gani ba for now, suka tambaye ta inda yake ta kuma basu su kuma suka bani"

"Na dauka zata yi kokarin kala min sharri a gurin su kamar yadda tayi kokarin yi a gurin ki, but bata yi ba, maybe she is not ready to explain that to her parents, yanzu explanation din da zata yi shine na shiga office dina da tayi ta daukar min abina ba tare da izni na ba"

Ya rike fuska ta a hannun sa yana kallona, "please Jidda please ki ce min kin yarda dani, ki ce min kin yarda ba zan iya neman kawarki ba" na sunkuyar da ido na kasa, komai na labarin sa ya tafi dai dai amma ko kadan ban yarda da shi ba, tabbas yayi, tabbas wannan CCTV footage din da aka ga Maryam tana shiga office dinsa gurinsa taje, maybe a lokacin ne abin ya faru a tsakanin su, she may have went to his office and seduced him, babu cctv a cikin offices dinsu saboda privacy, a lokacin ne ta chanja band din bayan ya cire shi kamar yadda yace, a lokacin ne kuma abin ya faru a tsakanin su.

Na dago kai ina kallon sa sannan nace "na yarda da kai Faruq" yayi murmushi from ear to ear. "Saura ki bani hakuri kuma" na sunkuyar da kaina ina jujjuya band din da yake rike a hannu na nace "kayi hakuri mijina, Allah ya huci zuciyarka"

Sai ya jawo ni jikinsa ya rungume "thank you thank you my love" ya dago kaina "Mufida ta gaya min ashe kun samu matsala ne da Maryam din, tayi kokarin fadar maganar banza a kaina and you depended my honor. Nagode Allah yayi miki albarka, Allah ya raya mana Yasmin da Asad ya kawo kannen su lafiya" ya karasa yana kashe min ido.

Na zame jikina daga gare shi na shiga daki na kira number din Yaya Mubaraka.

"Salamu alaikum, Yaya barka da rana. Dan Allah ina son ganinki ne akwai maganar da zamuyi please. Tana da muhimmanci sosai. Eh duk sanda kika samu time ko ki shigo ko ki bani lokacin da kike gida sai ni in shigo. Okay shikenan. Nagode sosai. A gaida yaran"..

Lokaci yayi da zan shiga third step dina

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta idan kuma kin siya kar ki yi sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*The Third Step*

Na zauna a bakin gado ina jujjuya wayar a hannuna. Yaya Mubaraka zan gaya wa sannan in roke ta ta gaya wa Mama da Baba su shigo into the battle of rescuing their son daga kan hanyar da ya dauka.

Tabbas Umar baiyi admitting yayi ba, but deep inside me nasan cewa yayi din, duk da cewa maganganun sa gabakidaya sun tafi dai-dai babu karkacewa amma the guilt on his face shi ya gaya kin komai. Shi abinda bai sani ba shine, yawanci lokacin da yake yin karya, abinda yake cewa daban abinda fuskarsa take nuna a daban. Da bana fahimta, amma a hankali yanzu ina fahimta.

Bana bukatar bincika wa akan maganar kama Maryam da yasa akayi, that I am sure yayi din, dan bana jin a gurin sa Maryam ta kai darajar Zuwaira ko Zahra ko sauran wadanda ban sani ba, kamar yadda na gaya mata a gurin sa darajar ta daya take data toilet paper din daya goge datti daga jikinsa ya jefar a shara, ba ita ba kuma duk macen da zata nemi namiji ta kuma bashi kanta kyauta, ko kuma wadda namiji zai nema da alfasha kuma ta amince masa suyi, kawai dan yana da kyau ko kuma dan yana da kuɗi ko fame ko kuma yayi mata karya tare da alkawarin aure, in dai kika yarda kika bashi kanki, to darajar ki a gurinsa daya take da ta used toilet paper. Gurin ajiye ki shine shara. In maryam's case gurin ajiye ta shine bayan kanta.

Ba zata kuma iya bude bakinta ta karyata cewa ta shiga office dinsa tayi masa sata ba saboda an ganta tana shiga, kuma ba zata iya fadar abinda ta shiga tayi ba saboda stain din sai yafi karfi akanta akan akanshi. Ya nannade ta da jijiyoyin jikinta, babu yadda zata yi dole ta amshi laifin sata dan sai ya fiye mata akan laifin zina. It is left to him ya fadi abinda ta daukar masa kuma dole ta karba dan hausawa sunce na shiga ban dauka ba bata fitar da barawo.

Tabbas yanzu ta fahimci waye Umar, she have tested his wrath kamar yadda na fada mata. Tabbas yanzu ta san matsayin ta a gurinsa. Sai naji wani barin na zuciyata yana tausaya mata.

Ina nan a zaune sai gashi ya shigo da Asad a hannunsa, "wai kina daki dama, muna ta nemanki ni da Asad?" Nayi ajjiyar zuciya "eh ina nan, waya nayi"

Sai ya zauna akan gadon sannan ya kwanta tare da dora kansa akan cinyata "wannan pillow yana da laushi" na dauke kaina bance komai ba, sai ya saka hannu ya dan mintsine ni a cinya "na juyo da sauri" "ash!" Yayi dariya "ni bana so kina ta tunani haka, nafi son kina kallo na kina murmushi" na juya ido na sai ya kama hannuna ya dora akan fuskarsa irin yadda nake yi masa in ya dora kansa akan cinyata, nayi kokarin dauke hannun sai ya rike shida nasa hannun "wai tunanin me kike yi ne? Tunani na?" Ya fada yana kashe min ido, nace "ya zanyi inyi tunanin ka bayan gaka a gaba na kuma?" Ya sake tambaya "to tunanin wa kike yi?" Nace "tunanin Umma ta, na kwana biyu ban ganta ba" yace "you know what? The day is still young mu shirya muje mu ganta mana" na danji dadi a raina nayi murmushi sai shima yayi "that's it, gashi nan yanzu naga murmushin ki ai" nace "to naji, daga ni inje in shirya" sai ya kara kusa kansa jikina tare da jujjuya kafa kamar mai yin bori "ni ba zan tashi ba ni cinyar ki dadi" Asad da yake zaune akan cikinsa ya kalkale da dariya ya dauka wasa yake yi masa, ni kuma na tattaro kan na daga shi na zame sannan na dangwarar da shi akan dago, making sure cewa wuyansa ya amsa.

Ya rike wuyan kuwa "ouch" Asad ya sake yin dariya sai kuma ya kama yi masa chakulkuli "kake min dariyar mugunta ko? Sai na rama ko a kanka ko a kan babarka" suka cigaba da wadansu ni kuma na wuce su ma shiga toilet.

Bamu bata lokaci ba muka shirya tunda duk munyi wankan mu dama, sannan muka dauki hanyar gida, a hanya ya tsaya ya saki frozen chicken "kar muje mu shigar musu gida hannu rabbana" sai kuma ya sayi fruits yana murmushi "wannan na Amira ne, sarkin kwadayi" ni dai bance masa komai ba, duk wata hanya da za'a kama mutum Umar ya san da ita.

Muna zuwa gida muka tarar Abba yana kokarin fita, muka gaishe shi gabakidaya yana ta yiwa Umar fara'a karshe har da ce masa ya shiga cikin gida kar ya zauna a sitting room ai shima dan gida ne, sai ga Umar a falon Umma wadda nan da nan ta kawo masa abinci da abin sha ni kamar ma sunfi jin dadin ganinsa akai na dan yar kallo na koma a gefe a zaune, Amira ce mai zuba masa abinci tana tayi masa zance, Farhan ma ta shigo aka cigaba da ita, suna ta musu ita da Umar akan yace combination din da take yi a College ba mai kyau bane baita kuma tana kare kanta.

Sai da nayi mita nace ni babu wanda zai kula ni ballantana a bani abincin sannan suka juyo kaina suna min dariya, "wanne marar aikin yi ne zai zauna yana zuba miki abinci?" Inji Farhan, sai ya dauki chokali ya saka min a cikin plate din sa "zo muci kinji? Rabu da Farhan in kowa bai kula ki ba ai ni zan kula ki" Farhan ta bude baki "a gaban Umma ko?" Sai ya sunkuyar da kai yana shafa keya, Umma kuma ta tashi ta shiga daki tana murmushi, daga gani zuciyarta fes take jinta ganin mijin yarta yana kula da ita "uhm uhm kuci abincin ku".

Sai na dauki wani plate din na zuba sannan na saka Amira ta yanka mana fruits a cikin wadanda muka zo dasu. A lokacin ne Farhan take bani labarin cewa an fasa bikin yaya Jamila. Na ajiye spoon din

50 / 106