Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
mataki, ki dauki waya ki kira shi kice kina son ganinsa, in yazo ki tambayeshi game da Jamila ki kuma fada masa dangantakar da take tsakanin ku sannan ki tabbatar masa da cewa ba zaku zauna kishi ba, ki bashi dama ya zaba ko ita ko ke. Idan ke ya zaba to ki tabbatar masa cewa iyayen Jamila ba zasu bashi ita ba indai ya aure ki, tsakanin sa da ita sai dai mutunci a matsayin ta na yaruwarki. Idan kuma ita ya zaba to ya janye maganar aurenki ya kuma aiko a karbar masa kudinsa da sauran kayansa, ke kuma Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi".
Na gyada kai na da sauri ina yadda da hukuncin ta, amma kuma wani bangare na zuciyata yana cike da tsoro "what if ya zabe ta? Zan iya rayuwa babu shi anya kuwa?"
Na mike da wayata a hannu, sai Umma ta dakatar dani tare da nuna min kunun data zuba min, na zauna na shanye ina bata fuska kamar mai shan magani, ina gamawa na dauki waya ta na koma dakin mu. Missed calls din Umar na gani har guda biyar a dai dai time din daya saba kira na kullum dan yaji yadda na kwana.
Nayi dialing number din sannan na saka a kunne na. Seconds biyu ya dauka
"Hey Baby"
Na lumshe ido na na bude ina jin muryar sa tana taba zuciyata. "Hi" na fada da muryar da naji kamar ba tawa ba.
"What's up Baby. Naji muryar ki wani iri ko yanzu kika tashi daga bacci?" Na girgiza kaina kamar yana kallo na ina jin hawaye yana kawowa ido na, nayi kokarin boye emotions dina nace "lafiya lau. Kana ina?" Yace "ina office, nayi ta kira dazu ai kina ta bacci ko? Are you sure you are okay?" Nace "ina so ne in ganka yanzu, if you are free, akwai maganar da nake so muyi" ya danyi shiru sannan yace
"Baby, is everything okay?"
Sanyin da yayi min maganar da shi ne ya saka hawayen da nake rikewa suka zubo, can he really do it? Yana dating dina yana dating wata kuma daban? Ko da bai san yaruwata bace ba amma still.......
"Lafiya lau. Kazo kawai zamuyi maganar in kazo" "are you crying?" Ya tambaya, sai naji hawayen ya sake ballewa "oh my God, gani nan zuwa yanzu. I am about to go into surgery but zan ajiye yanzu in taho...." Na katse shi "no.. lafiyar patients dinka tafi duk wata maganar da zamuyi, ka gama kawai sai kazo" yace "wa? Ba dai ni Umar din ba, Jidda tana kuka kuma zan iya surgery? Ai tabbas zanyi barna ne a ciki. Ba emergency bane ba scheduled cs ne, zata iya jira inzo in ganki in dawo ko kuma wani doctor din yayi taking over amma ni ba zan iya ba Baby, not when you are crying"
Sai ya kashe wayar, na dora ta akan kirjina ina jin bugun zuciya ta yana vibrating a jikin wayar "can he really do it?" "Will he chose me?" Na tuna Yaya Jamila, zuciya ta tana lissafo min yawan abubuwan da ta fini, kusan ta fini komai da wayayyen hadadden namiji kamar Umar zai so a gurin matarsa.
Na tuna da wayar da take raba dare tana yi sanda muka je gidan su, da wa take waya? Umar?
Ina nan a zaune Farhan ta shigo dakin, ta zauna tana ta yi min labarin abokin mijin yaya Hudallah da take kokarin hada su "kinga katon cikin sa kuwa?" Ta fada tana dariya, daga dukkan alamu so take ta saka ni dariya amma ganin bani da niyyar yi sai ta fita ta bani guri.
Bata jima da fita ba ya kirani "ina waje" ban amsa ba na kashe wayar sannan na tashi na wanke fuskata a tsakar gida sannan naje dakin Umma na saka kwalli, bana so yasan how much nayi kuka a kansa. Amma gyaran fuskata bai yi komai ba wajen gyara zuciyata, dan a tsorace take sosai, ko wannan ne zai zamo gani na karshe da zanyi masa? Menene makoma ta idan na rasa Faruq? Har na fito daga dakin kuma sai na koma na dauko wayar Umma na fito da ita a hannu na.
Yana mota bai fito ba, har na fito daga cikin gidan bai fito ba nasan kuma hakan yana da alaka da saurin da yake yi dan lokuta da dama in yana sauri yakan zauna ne a mota.
Na zagaya na bude kusa da shi na zauna. Yana sanye da kayansu na doctors, wannan ita ce ranar dana fara ganinsa da kayan kuma sai naga kamar sunfi yi masa kyau akan kowane kaya, sai naga kamar yafi yi min kyau akan kullum.
But he looked worried.
"My God! Da gaske kuka kike yi Jidda" na girgiza kaina, trying so hard not to continue crying. Sai na dauko wayar Umma na bude sannan na nemo hoton Yaya Jamila na nuna masa direct nace
"ka san wannan?"
Na lura da yadda yanayin sa ya chanja a lokaci daya, sai kuma naga ya dawo dai dai sannan ya karbi wayar daga hannuna yana kara kallon ta kamar mai tunani sai yace "Jamila ko? Jamila something......na manta second name dinta" sai ya miko min wayar "a ina kika santa?" Na karba still ina kallon yadda yaki hada ido dani yana kallon waje, duk damuwa da seriousness din fuskarsa sun tafi, he looked uninterested"
"menene a tsakanin ka da ita?" Na sake tambayarsa. Ya juyo yana kallo na kamar mai mamakin tambayar sannan yace "wai wannan yarinyar? Ni kuwa menene hadi na da ita? Wani abun aka gaya miki? Is that the reason da kike kuka?" Nace "I will be the one asking the questions, and you will be the one answering" sai ya sara min kamar yadda ake yi wa masu khaki yace "yes ma" na lura gabakidaya ya mayar d maganar wasa.
Nace "menene tsakanin ka da ita?" Yace "nothing really, na santa a buk tun kafin in fita India, she is a friend of girlfriend din Bashir ta lokacin, so in na raka shi gurinta muna haduwa kuma most of the times in zai fita da ita suna tare kuma nima ina tare da shi. So bayan sun rabu ma muna dan gaisawa haka in mun hadu, shikenan...... please ki gaya min mai ya faru?"
Na ajiye wayar a tsakanin mu ina kallon gaba na, trying to think using my head but my heart is already jumping with joy cewa ba wai yana son Jamila bane ba, it was a misunderstanding.....
"Yayata ce" na fada "yar gwoggo Habibah ce...ita ce autarta" ya kalle ni "really? What a small world. Amma menene ya saka ki kuka a cikin maganar? Oh sorry ma, ashe fa kece mai yin tambaya ni mai amsawa" yayi dariya, shi bashi da wani problem.
"Dazu gwoggo Habibah tazo gidan mu da sassafe........." Sai na bashi labarin abinda ta fada na daga dangantakar da tace akwai a tsakanin sa da Jamila. Amma ban fada masa abinda Abba yace akan maganar ba.
Anan ne naga hankalin sa ya tashi "ya salam...... wannan yarinyar sharrin da zata yi min kenan? Yaushe ne muka yi haka da ita..." Na bishi da kallo kawai "ta cuce ni amma wallahi shikenan ta bata min suna a gidan ku" sai yayi kamar zai riko fuska ta sai kuma ya dauke hannun sa yana yarfarwa a gefe "na shiga uku. Wallahi Jidda karya take yi min babu wani abu mai shigen kama da wannan a tsakani na da yarinyar nan, ni ban taba cewa ina sonta ba ballantana har in yi mata alkawarin aure. My God!" Ya fada yana shafa gashin kansa
"Look Jidda, Wallahi karya take min. Look, ban damu da wasu su yarda ko kar su yarda da abinda nake cewa ba, but Please ki gaya min cewa ke baki yarda ba. You think zan yi miki haka? Bayan na same ki kuma Jidda mai zanyi da wata mace kuma?"
Na dauke kaina gefe a kokari nana kara jan zaren aji na, "tace jiya ma kuna tare" ya danyi frowning fuskarsa sannan yace "jiya? Jiya naje dinner ne ta bikin wani friend dinmu" sai kuma yace "ohh I remember seeing her there, sunje a matsayin kawayen amarya mun gaisa haka briefly but it doesn't mean muna tare as in kamar naje 'zance' gurinta" yadda ya fadi zancen kamar wani abun kyama.
Nayi shiru ina assessing maganar sa, ido na akan band dina da yake hannunsa. Ya sake cewa "idan baki yarda ba bara in kira Bashir, zai fada miki komai....." Na girgiza kaina "no need" ya dauko wayarsa tare da cewa "I insist. Bana son ko trace na wani abu mai kama da wannan ya shiga tsakanin mu" yayi dialing number sannan ta saka a handsfree tare da dora ta akan dashboard.
Ina jin Bashir ya dauka "hey namiji" yace "hey Bash. You are on speaker. Ina tare da baby na ne kuma ina bukatar taimakon ka. Please help me clear something out. Ka tuna yarinyar nan Jamila kawar Nafisa ta ka?" Yace "yeah. Na tuna Jamila, me ya faru" sai ya fada masa abinda na gaya masa a game da Jamila
Bashi yace "look Jidda,ba tun yau ba na gaya miki cewa guy din nan ya sace zuciyar yammata da yawa, amma tasa zuciyar ke kadai kike da mallakin ta, and it happens that Jamila is just one of those girls. Guy ka manta na taba gaya maka yarinyar nan kamar she is into you kace min ba haka bane ba?" Umar yace "yeah, anyi haka, da nasan zata bata ran baby na dana tare ta a hanya na kora mata jawabi tun a lokacin"
Bashir ya cigaba "to kinji, babu wani abu mai kama da wannan a tsakanin su. Ke kadai ke da zuciyar Umar. My guess is tana sonsa sai kuma ta ganshi a matsayin wanda zaki aura and she wants to break you guys up dan ta gwada tata sa'ar. Wannan shine gaskiya"
Ya dauki wayar ya saka a kunnen sa "thank you bro, I really appreciate this" sai kuma ya kashe ya mayar da ita aljihunsa ya juyo yana kallo na "I really hope kin yarda da magana ta yanzu, I also really really hope zaki yi dropping maganar nan and we will never discuss it again. Jamila ba budurwa ta bace ba, I don't and I will not love her talk less of marry her. Ni saurayin mace daya ne, kuma mijin mace daya, sunanta Hauwa'u Maijidda" ya karasa yana murmushi, nima na sunkuyar da kai na kasa ina taya shi murmushin a raina ina jin dadin yadda maganar ta warware ba tare da tayi affecting tsakani na da shi ba.
Tabbas biri yayi kama da mutum, yadda Jamila take da rashin kamun kai zata iya shirya sharri dan ta samu wanda take so, kuma na san gwoggo Habibah bata san fuskar samarin Jamila ba ballantana ta gane ko akwai Umar di na a ciki ko babu.
"Jidda" ya ambaci sunana, na dago ina kallon sa amma ban amsa ba sai yace "wannan ne misunderstanding da muka samu na farko, kuma am sure ba zai zama na karshe ba tunda aure zamuyi kuma shi aure akwai challenges da yawa irin wadannan a cikin sa. Sai dai abinda nake so dake shine ki saka a ranki Umar naki ne ke kadai, duk wata wadda zata yi kokarin saka doubt a zuciyarki ki karyata ta, dan ni bayan wadannan relationships din guda biyu da na fada miki ban taba zuwa wajen wata da niyyar ina sonta ba ballantana har ta kaimu ga maganar aure"
"Sai dai wadansu mata suna misunderstanding maza iri na. Ni ina da faran faran da mutane, in naga lady ina treating dinta as a gentleman should, misali sakin fuska gurin amsa gaisuwa, getting a seat for her, ko offering a helping hand when needed, su kuma wasu matan sai su dauka wannan soyayya ce, sai su fara tagging kansu as 'budurwa ta' when ni kuma babu wannan maganar a raina"
"Sai magana ta tashi kuma nace ba haka bane ba sai a fara fadar maganganu. I have been tagged as 'mayaudari' several times. Wannan shine dalilin da yasa Mama tayi kokarin hada ni da cousin din nan tawa da nayi miki bayani kwanan baya. Ladies need to understand that if a guy loves you he will say it out. Mu ba mata bane da zamuyi ta boye boye waiting for the other one to say it first. A guy smiling at you doesn't mean a guy is in love with you"
"Dan haka please, ko nan gaba ko bayan bikin mu in wata ta gaya miki magana irin wannan please kar ki tayar min da hankalin ki har kiyi min asarar hawayenki a banza, ki dauka kawai direct cewa karya take yi. Ni Umar mijin JIDDA ne ita kadai babu kari"
Nayi murmushi ina jin dadin maganar sa amma sai na girgiza kaina nace "dadin baki ko? Zaka yi min dadin baki ko? Umma ta gaya min ai ku maza are polygamist in nature, dan haka Umar is free yayi adding second, third and fourth wife after Jidda duk da dai hakan ba zai yiwa Jidda dadi ba amma zata yi accepting"
Yace "wai kina nufin Umma tayi comment akan maganar nan?" Nace "eh mana, ita ce ma ai ta saka na kira ka, tace in gaya maka ka zaba tun yanzu ko ni ko Yaya Jamila dan ba zanyi kishi da yaruwa ta ba" ya dan daki stirring "damn it, wannan yarinyar ta cuce ni ta bata min suna a gurin su Umma" nace "kar ka damu, zata fahimta in nayi mata bayani. Yanzu bara in barka ka koma gurin patient dinka" ya shafa kai yana dan murmushi "ni har na manta ma da zancen wani aiki, ni na manta ma ashe ni doctor ne, sunana ma kadan ne ya rage ban manta ba" ya karasa yana dariya, nima sai na taya shi dariyar and Jamila and all her problems went away with our laughter.
Bayan na koma gida na tarar da Umma a falo tana jirana, na zauna da sauran murmushi a fuska ta and I saw her relaxed, kamar hankalin ta ya dan kwanta kadan, tace "to ya kuka yi dashi?" Sai na bata labarin yadda mukayi, "yace shi ya dai santa a matsayin kawar budurwar abokinsa amma bai taba cewa yana sonta ba ballantana har suyi maganar aure" ta danyi shiru tana tunani sannan tace "to shi kenan, Allah ya kade fitina ya tabbatar mana da alkhairi" nace "ameen" amma sai na cigaba da kallonta ina lura da yadda kamar bata gamsu da maganar ba sai dai kuma bata sake cewa komai ba.
Da yamma na bawa Farhan labarin yadda muka yi da Umar, amma sai naga bata yi looking happy for me haka ba, na tambayeta "baki yarda da abinda yace min ba?" Ta girgiza kai "maganar yace sharri tayi masa ma bai taso ba, me zata yi gaining in tayi masa sharri? In dai da gaske babu komai a tsakanin su mai zata yi gaining in tayi masa sharri? Tunda ko ya rabu da ke ba zai aureta ba tunda babu wani abu a tsakanin su sai ma bata kanta da zata yi a gurinsa"
Nayi shiru ina jinta, ina jin haushin yadda take saka doubt a zuciyata a game da shi, nace "kina nufin karya yake yi kenan? Ke me yasa komai Umar zaiyi ba kya taba ganin farinsa kullum bakikkirin kike ganin sa?" Tace "tunda kanwarsa uwa daya uba daya ta kira shi da mayaudari who am I to argue with her?" Naji haushin me yasa na bata labarin maganar Mufida a kan sa, na bata rai nace "kina nufin yaudara ta yake yi kenan" ta girgiza kai "ko kadan bana doubting son da Umar yake yi miki, da gaske yana sonki kuma da gaske auren ki zaiyi, amma wannan bai goge masa wancan sunan a gurin sauran mata ba"
Ta cigaba "abinda na fahimta shine akwai wani abu a tsakanin su, ita ta dauka sonta yake da gaske kamar yadda ita din take sonsa da gaske, amma shi ba da gaske yake sonta ba yaudarar ta yake yi, bai san da alaka a tsakanin ku ba dan haka baiyi tunanin asirin sa zai tonu ba, my guess is daga yau ba zai kara kulata ba zaiyi acting as if abinda ya fada gaskiya ne, as if babu wani abu a tsakanin su"
Na mike ina karkade rigata "kanki ake ji wai mahaukaci ya fada rijiya, yace kanku akeji ni wanka na nake yi" tayi murmushin takaici "Umar dan yaudara ne Jidda, the earlier you get that into your thick skull the better for you" na fita daga dakin ba tare da na bata amsa ba. Sai kuma selfish zuciya ta take gaya min "in ma dan yaudarar ne tunda bani ya yaudara ba ina ruwana? How can that affect relationship dina da shi?".
What a selfish heart
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*Episode Twelve : A Blessing or a Curse*
Rayuwa ta cigaba kamar ba ayi komai ba, Umma bata kuma ta yar min da maganar Jamila ba haka ma Farhan tunda ta ga bana so bata kuma yi min maganar ba, tsakani na da Umar ma ko sunanta bamu kuma ambata ba sai ma wani shafin na soyayya da mu ka sake budewa. Mutum daya da take maganar ita ce Hajiya. Ita kuma a nata bangaren tana kokarin tabbatar wa cewa duk wamda yake family din mu ya san maganar Umar da Jamila. Haka kawai in tayi niyya sai ta fito tsakar gida ta saka kujera ta zauna ta dauko wayarta tana ta kiran yayanta suna maganar suna dariya. Raina ya kan baci in tana yin haka amma ban taba tanka mata ba kamar yadda nake yi kullum