Chapter 39 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   39 / 106

114K to 117K   out of 316K words

wannan kika siyo? Idan kina bukatar cream ne ba sai ki gaya min in na fita in siyo miki ba?"

Nace "sorry my dear husband, bukatar da nake musu ta gaggawa ce shi yasa na fita" na dauki roba daya a cikin robobin set din dana siyo sannan ba tare da na tsaya dubawa ko cream ne ko scrub ba na fara matsawa ina shafawa a jikina, ya rike hannuna "Jidda look at me, me yake damun ki ne wai" his face looked genuinely concerned.

Na tsaya ina kallon sa, ina jin ganin fuskar sa yana sakawa numfashi na yana tsayawa a iyakacin kirjina kamar yadda yake min idan zan samu attack, fuskar sa tayi min baki, wata irin tsana da kyamarsa tana shiga duk lokunan da soyayyar sa take ciki. Na kwace hannu na daga nasa da karfi nace "kana so kasan inda naje? Mai naje siyowa, man bleaching......" Yace "what?" Nace "eh man bleaching na siyo saboda ina son in zama fara, ina son fata ta ta koma irin wadda kafi so"

Naga yanayin fuskarsa ya chanja amma still ya sake pretending "what? Me kike nufi da irin fatar da nake so? Wacce iri ce fatar da nake so" sai na saka hannu a aljihunsa na dauko wayarsa, and I saw his face turned paper white, na bude na dubo hoton ba tare da ya motsa daga inda yake ba sannan na nuna masa "irin wannan fatar, irin ta nake so in koma"

Har lokacin bai motsa ba kuma bai ce komai ba idonsa a akaina, sai na jefar da wayar kan gado ina jin duk emotions din da suka yi folding kansu inside me suna unfolding. Nace "girman nonon kuma a matsayin ka na gynae, na san zaka iya bani wani maganin da nawa zasu yi girman irin wadancan din, dan in zama irin wadda kake so din"

Na fada numfashina yana kakkatsewa. Yayi taku biyu zuwa gaba na ya rike ni tare da saka bakin rigarsa yana goge min man dana fara shafawa a wuyana da kafada ta "inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Hasbiyallahu wa nieemal wakeel. Jidda that wasn't real. Dan kinga hoto a wayata shine zaki tayar da hankalin ki har haka? Har kina kokarin ki shafawa kan ki abinda zai cutar da ke?"

Na fara ture shi amma karfina kusan ya kare kamar yadda numfashi na ya kusan karewa. "Lier! Lier! Lier. Hypocrite! Ba hoto kadai na gani ba, hirar da aka turo hoton a cikin ta na gani, na kuma san dalilin da ya dawo da kai gida"

Ya fara girgiza kansa "Jidda you are sick, listen to me, calm down, duk abinda kike tunani ba haka bane ba. Dan Allah ki kwantar da hankalin ki ki rufa min asiri kar wani abun ya same ki. Bashir ne fa! Kin san yadda muke da Bashir we were just kidding, wasa ne muke yi fa, none of what we said is real!"

Nace "wasa? Wasa fa kake cewa? Kar ka raina min hankali mana Umar? Wasan ne har ya saka ka bata wandonka?" Ya sake ni da sauri sannan ya rufe bakinsa da hannayensa, jikinsa ya fara rawa kamar yadda yake yi aduk sanda hankalin sa ya tashi irin wannan. "I saw it! I smell it on you then I saw it a cikin wandon ka. Shi yasa na duba wayarka kuma na tabbatar da kuma san abubuwa da yawa daban sani ba"

Na nuna shi da hannu ina jawo maganganun da suke tsaye a kirjina ina fito dasu daya bayan daya

"kazami! Mazinaci! Makaryaci! Mayaudari! Maci amana!"

Wasu taurari masu haske naga suna ta zazzagayawa a dakin, bayan hasken su kuma bana ganin komai sai duhu, na dafe kirjina dan tsakanin hunhuna da zuciyata ban san wanne ne yafi daukan zafi ba, and a thought cross my mind, this is the end of me. Dama Umar ne sanadiyyar mutuwa ta shi yasa Allah ya hada ni da shi kuma ya saka min tsananin soyayyar sa a raina.

Nasan dai jiri ya debe ni, sai kuma na jini a hannun Umar yana jijjiga ni yana kiran sunana da karfi, nayi kokarin bude idona dan in kalle shi sai kuma nayi realising ashe idon nawa a bude yake already gani ne dai baya yi.

"Jidda! Na shiga uku! Jidda talk to me! Hit me please, ki dake ni Jidda ki zage ni just don't keep quiet"

A muryarsa sai naji kamar kuka yake sai dai bana iya ganin sa, na bude bakina da niyyar gaya masa sauran maganganun daban gama fada ba amma babu abinda ya fito sai sunan sa "Umar" and that was the last thing I said, and the last thing I heard. Sunan sa!

Sanda na farka ma fuskar sa na fara gani, sai dai ta chanja gabakidaya tayi jajawur idonsa ya kumbura. Yana tsaye a kaina yana magana amma bana jin abinda yake cewa kuma ban ga da wa yake maganar ba. Sai dai na fahimci a asibiti muke kuma na fahimci akwai oxygen mask a fuskata.

Na mayar da idona na rufe dan in na cigaba da kallon fuskar sa oxygen din ma ba zata yi min amfani ba.

Dana sake farkawa Mama na gani tana ta sharar kwalla, da wani abu a nannade a hannunta kamar dan jariri, na saka hannu a hankali na shafa ciki na sai naji babu, nayi kokarin saka daya hannun da in tabbatar sai na ji hannun a rike,na waiga side din sai na ganshi.

Ya rike hannuna daya da dukkan hannayensa biyu sannan ya kifa kansa a kai. Ba zan iya sani ba ko bacci yake yi ko kuma idon sa biyu ba kuma ban damu da in sani din ba. Na saka dukkan karfin da nake dashi na karbe hannu na daya cikin nasa, ya dago kansa da sauri.

"Jiddah"

sai na mayarda idona na rufe dan in akwai abinda bana son gani a duniya ta a lokacin shine. Sama sama naji muryar Mama, ban san me take cewa ba har na kuma komawa unconscious.

Farkawa ta uku da nayi babu mask din a fuskata kuma numfashi na yana fita sosai. Sai naji ni kamar wadda nayi wani dogon bacci sai dai jikina yayi wani irin nauyi kuma duk ciwo yake min, fatar cikina felt strange kuma kamar akwai wani abu daya makale min a cikin, na saka hannu zan taba inda naji abin sai naji an rike hannun nawa.

"Kar ki sosa Jidda"

Naji muryar Umma. Na bude idona na sauri na kalli inda naji muryar tata. Ita din ce kuwa, tana zaune akan kujerar gaban gadon marasa lafiya, "Umma!" Na kira sunan ta, ta rike hannuna "sannu Hauwa'u" naji motsi ta daya gefen nawa na juya sai naga Aunty Afia "Jidda! Alhamdulillah. Aira kira Umar maza, ki ce masa ta tashi"

Ta dawo kusa da Umma "yana bakin kofa a zaune zaman dirshan a kasa, ga kujera amma yaki hawa ya zauna a kasa ya hada kai da guiwa"

Na rufe idona ina hango shi a yanayin da ake ce yana ciki, sai kuma na saka replaying hirarsa da Bashir wadda already kwakwalwa ta tayi scanning ta kuma yi saving a wani gurina musamman wanda ba zai goge ba.

"Shegen duniya! Dama nasan kai baka wuce tayi shi yasa nayi maka"

"Her skin is so beautiful. Irin wadda nake so. Ka biya min please"

"Shit! U just mess my pants"

Ban san hawaye ne suke biyo wa fuskata ba sai da na jisu suna shiga cikin kunnena sannan suna sauka kan pillown da nake kwance akai.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" na fada cikin muryar kuka. Aunty ta rike hannuna "subhanallah, jiddah! Jidda me yake damunki? Ba zaki gode Allah ba! Mu da muka fara fitar da rai dake kuma sai gashi Allah ya dawo mana da ke? Kuma Allah mai kyauta da kari sai ya hada mana har da jaririn cikin ki duk lafiyar ku kalau? Me zamuyi wa Allah Jidda in ba godiya ba? In muka yi kuka ai kamar munyi masa butulci ne ko?"

Na sake kai hannuna kan cikina. "Baby na, Aunty ina yake?" Sai ta zauna akan kujerar da Umma ta tashi ta cigaba da rikon hannuna sannan ta ce "jinin ki ne ya hau sosai Jidda. Unconscious Umar ya kawo ki asibitin nan, preeclampsia Umar ya ce mana, ga kuma asthma dinki da ta tashi ita ma a lokaci daya, dan haka dole akayi miki aiki aka fitar da babyn dan a ceci rayuwar sa, ke kuma aka ci gaba da baki treatment. Kwanan ki biyu kenan, sai yau numfashin ki ya dawo dai dai, sai yau ne kuma jinin ki ya fara sauka. Jiddah har mun fara fitar da rai da ke"

Ta karasa maganar cikin karyewar murya. Na juya kaina kan Umma naga tana sharar hawaye. A lokacin Umar ya shigo dakin kamar wanda aka jeho shi daga sama.

"Jiddah!" Ya fada yana takowa zuwa gabana . Wani mugun kallon dana jefa masa ne yasa ya dakata sannan yayi taku biyu baya sai kuma ya juya da sauri ya sake fita. Aira da suka shigo tare ta bishi da kallo.

Na dafe kaina da hannu na daya, "Umma kaina ciwo yake yi, ji nake kamar zai tsage" na fada ina kara yin wasu hawayen, amma a zahirin gaskiya ba wai kan nawane kadai yake ciwon ba, dan ciwon da nake ji a zuciyata yafi wanda nake ji a kaina. Ganin Umar ne kuma ya sake rura wutar ciwo na.

Aunty ta taya ni dafe kan nawa, ta juya tana kallon Aira "ina doctor din? Ki kirawo shi mana ko zaiyi mata wani abu? Ko zai kara rarrashin ta ma ta daina wannan kukan kar jinin ta ya kuma hawa" Aira ta sake juyawa sai na daga mata hannu "kar ki kira shi. Ki rabu da shi kawai"

Umma tace "a rabu dashi? Saboda me? A kira shi mana ya ganki shima ko yaji dadi a ransa, kwana biyun nan bana jin yaron nan ya rintsa, anan bakin kofa yake wuni yana kwana kansa akan guiwowin sa" Aunty tayi murmushi "soyayyar Umar da Jidda ai sai Allah. Kuka fa yake yi, baya yi a gaban mutane amma kana kallon idonsa kasan kuka yake yi" Umma ta danyi dariya, da alama suna cikin jin dadi tare da murnar cewa yarsu tayi babban dace a gidan mijinta.

Na sake cewa "kar ki kira shi please" Aunty tace "shikenan Aira kar ki kira shi, kirawo Doctor Bashir abokinsa dan kullum shi yake taya shi zama" na  sake girgiza kai na "not that man please, bana son ganin Bashir"

Umma ta bata rai "me yake damunki ne wai, dole a kira likita ya duba ki Jidda, ko dai a kira Bashir ko kuma mijinki" na rufe idona ina jin ciwon kan yana karuwa, "Umar, a kira Umar din".

Sai dai na rufe idona dan bana son ganinsa duk da ba zan iya hana shi shigowa ba.

Naji muryarsa yana magana da su Mama, sai kuma naji kamshin turaren sa a kusa da ni. Ya jawo kujera ya zauna sannan ya kama hannuna ya rike

"Jidda. Sannu kinji? Allah ya baki lafiya" naji Umma tace "ameen" ban dube idona ba ballantana in kalle shi, naji ya daura min abin auna bp a hannuna sannan ya auna, sai kuma ya saka min wani abu a kirjina, daga dukkan alamu bugun zuciya ta yake aunawa amma still ban kalle shi ba har ya gama.

Sai kuma naji ya mike ya kama hannuna yana daura min drip sannan ya dafa goshina da hannun sa, ba zan iya banbance fatar waye tafi zafi a tsakanin mu ba. "Jiddah, talk to me please. Menene yake miki ciwo yanzu? Kiyi min magana please" naji muryar Aunty "kiyi magana mana? Ba naji kince kanki yana ciwo ba?"

Na juya side din da yake sannan na bude ido na akan sa "kaina yana ciwo" na fada a hankali, "amma ciwon da nake ji a zuciyata yafi wanda nake ji a kaina. But I guess you know that already"

Sai ya sauke idonsa daga cikin nawa, sannan ya dauko takarda yayi rubutu a ciki sai kuma ya mike "Umma bara in kawo mata drugs din nan, dama na ajiye su already" Umma ta bishi da "to, sannu Umar" Aunty tayi dariya "kai ma ina jin sai an kara maka ruwan" ya danyi murmushi ya shafa kansa sannan ya juyo ya kalle ni kafin ya fita.

Yana fita Aunty tace "in aka tashi kara masa kuma sai an hada da Maman sa,dan jiya anan na sameta ta zabga tagumi ta saka shi a gaba" Umma tayi dariya "ai na fahimci tana son shi sosai, son ne kuma ya shafi har Jidda da ƴaƴan ta, jaririn nan fa kafin a tafi dashi nursery da kyar ta bani shi na dauka" suka sake dariya "ohh Allah. Allah kasa sauran yayan mu mata su dace da mazaje kamar yadda Jidda ta dace"

Na rufe idona na juya kaina daga gare su a zuciyata nace "ba ameen ba, Allah duk mata na gari Allah ka raba su da mazaje irin Umar ya Rabbi"

Bai jima ba ya dawo, ya na ta rawar jiki ya ajiye magungunan da ya shigo dasu sai yayi kamar zai kama ni ya mikar dani sai kuma ya tsaya yana kallo na sannan yace "zaki iya tashi ki sha magani?" Na dauke kai na gefe, sai ya kalli aunty "ga magungunan ta nan, a batata sha please"

Aunty ta karba sai ya kuma sunkuyo wa yana dafa goshina "kina jin sanyi ne, naji kamar jikin da zafi" "bana ji" na fada saboda Aunty da take kallo na, ya dan daga rigata kadan zuwa can kasan marata ya taba inda nake tunanin nan aka yanka aka dauko jaririna. Sannan ya kalleni "da ciwo?" Nayi banza dashi, sai ya daga murya yadda su Aunty zasu ji yace "da ciwo gurin?" Na girgiza kai na kawai, ya gama dube duben sa a gurin sannan ya tashi. Aunty tace "abinci fa? A bata ta ci?" Ya girgiza kai yana kallon ruwan daya daura min. "Ba lallai ne ta ji yunwa ba, amma in ta nuna tana ji din za'a iya bata" ya sake kallo na sannan ya fita.

Bai jima da fita ba yan gidan su suka zo kusan kaf din su banda Baba banda Muhibbat wadda bata gari. Nan da nan gurin ya rude da hayaniya, manya suna nasu wanda bai wuce zancen sabon mijin su ba da ni har yanzu ban kai ga gani ba. Su kuma yammatan suka dawo gurina suna ta min sannu da kuma bani labarai wadanda kusan dukkan su na irin rudewar da Umar yayi bani da lafiya

"Mama! Mama ki zo ki taimaka min Jidda zata mutu. Mama na shiga uku nima mutuwa zanyi"

Mufida ta fada tana kwaikwayon muryar sa tare da leka wa ko yana kallon ta. Muhsina tayi dariya "kin tuna rigimar su da Mama? Gashi fa sam baya cikin hayyacin sa amma wai babu wanda zai taba masa mata, babu yadda Mama bata yi da shi ba akan ya bar Doctor Bashir yayi mata aikin amma yaki yace shi zaiyi da kansa, Allah ya taimake mu bai hada da hannun jaririn ba" suka sake dariya su kadai ba tare da na taya su ba dannia gurina babu abin dariya a maganar ni ban ma ga abin burgewa ba a maganar dan a gurina munafurci ne, zai nuna wa mutane yana kishina a bayyane bayan a badini babu wani abu mai kama da kishi na a zuciyar sa, idan har yana kishina kuma ya damu dani to tabbas ba zai aikata abinda yake aikata wa ba.

Na rufe idona ina tunanin abinda ya aikata din, ko kuma ince abinda yake aikatawa. Dan hirar su da Umar gabakidaya tana nuni ne da cewa ba ranar suka fara ba kuma ba'a ranar zasu daina ba dan tabbas sun riga sunyi zurfi a cikin abinda suke yi, bana jin ma a gurin su sun yarda da cewa abinda suke yi din ba dai-dai bane ba.

Na tuna abinda ya faru akan Zuwaira da kuma alkawarin da Umar yayi min, nuna min da yayi cewa ya daina da kuma nunawa da yayi kamar cewa wancan din ma kuskure ne, ni kuma,the stupid me, believed him, forgive him and trusted him again. Wannan yasa wannan din yafi wancan yi min zafi, musamman realization na cewa tun a wancan lokacin shi da Bashir din rami suka hada baki suka haƙa suka binne ni a ciki.

Na bude ido ina kallon jama'ar da suke dakin fuskokin su cike da fara'a da nishadi, su a ganin su they are celebrating me, su a ganin su taya ni farin ciki suke yi basu san cewa ni wadda suke tayawa din babu farin ciki ko kadan a zuciyata.

But I still have a reason to smile ko?

Na juya ina kallon Mufida "kina da hoton babyn?" Ta bude ido "wai baki ganshi ba? Kyakykyawa in gaya miki har yafi yasmin kyau" ta dauko wayarya tana dubawa sannan ta nuno min hoton dan mitsitsin yaron da daga ganinsa kaga bakwaini da yar mitsitsiyar kyakykyawar fuskar sa, na shafa fuskar ta screen din wayar and I did smile duk da halin da zuciyata take ciki.

"Yana nursery, amma nasan in yaya Doctor yaje zasu bashi shi ya kawo miki ki ganshi" sunan yaya Doctor din ya katse min murmushi na. Na mika mata wayar sannan na koma na kwanta.

A lokacin nurse ta shigo

"Doctor Umar yace a bawa mara lafiya guri dan tana bukatar hutu"

Auntyn su Mufida ta tafa hannu tana salati "la ha ila. Kiji marar kunyar yaro? Mu zai kora mu bar matarsa ta huta?" Mama ta shigar masa "ai da gaskiyar sake kuwa, wahalar da yarinyar nan ta sha ai tana da yawa kuma kinsan hayaniya tana saka wa jinin mutum ya hau ko da kuwa mai lafiya ne ballantana wanda dama bashi da lafiya"

Aunty Afia ta mike "lallai Jidda yar gatan Mama, kaunar ta bi jini ko kara ma ba'a yi mana" Mama tayi murmushi tana kallona sannan ta taso tana ta ba goshina "duk abinda Umar yake so nima

39 / 106