Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
iya rabuwa da shi?"
Ta girgiza kai "ai ba Sadauki ne mijina na farko ba Jidda"
Nace "but sanda aka ce mana anyi miki aure, lokacin muna jss3, duk mun dauka Sadauki aka aura miki tunda munsan yayanki ne kuma saurayinki"
Ta girgiza kanta yanayin fuskar ta yana chanjawa, da alama ta tuna da wani memory marar dadi, tace "ba sadauki aka aura min ba. Mijina na farko sunansa Saghir, cousin dina ne, yanzu ne nake auren Sadauki" na kuma kallon ina so in fahimci kam labarin ta amma sai ta dakatar da ni "don't let me bore you with labari na, just know that I went through a lot kafin in zo inda nake yanzu" na sunkuyar da kaina ina tunanin nima ai ina going through a lot a yanzu, but will I reach where she is ko kuma nawa destiny din ba irin nata bane ba.
Sai ta sake rike hannuna tace "look Jidda, you are my dear friend, nan kuma gidan mijina ne, in kina so you can stay here for tonight kafin gobe sai ki yanke hukuncin abinda zaki yi, but I advice you to call your parents ki gaya musu you are okay dan hankalin su ya kwanta. But choice din ki ne yin hakan. Ban ce lallai ki gaya min matsalar ki ba ko dalilin da yasa kika baro gidan mijinki ba, amma in kina son gaya min din I will listen, sannan kuma zan baki shawara dai dai da fahimtata. I won't judge you, because I am a woman, and women are supposed to be each other's keepers"
Na gyada kai kawai, sai ta sake tambayata "kin yarda? Kin amince zaki kwana anan gidan kafin ki yanke hukuncin abinda zaki yi?" Na sake gyada kai na tare da sauke ajjiyar zuciya "Nagode. Nagode sosai"
Ta mike tsaye tare da jan hannuna nima na mike "muje ciki to, ki samu kiyi sallah ki huta ki ci abinci. And then think about it. Gobe in Allah ya kaimu sai mu zauna mu san inda muka tsaya da kuma inda zamu tashi.
Na bita a baya, ina lura da kyau da tsarin gidan tun daga yanayin ginin sa har zuwa furnitures da decorations, akwai taste mai kyau gaskiya kuma akwai kudi sosai.
Wani daki ta kaini, daga gani zaka gane guest room ne dan babu alamar akwai mutum a ciki, sai ta bude wardrobe din ciki ta dauko min sallaya ta shimfida min sannan ta nuna min toilet na shiga, ina fitowa na ga wata yarinya tana yin shimfidar gado, ta gaishe ni sannan ta cigaba da aikin ta, ina sallar ta gama shimfida gadon ta kunna room heater sannan ta saka room freshener ta fita, bayan jimawa kadan ta dawo da tray dauke da abinci ta ajiye a gaban dan karamin carpet son da yake gaban gado.
Na idar na zauna addu'a, sai na samu kaina da yin irin addu'ar da Surayya ta gaya min cewa tayi na Allah ya ji min jagora akan abinda na saka a gaba yayi riko da hannu na kar ya barni ni kadai dan ni kadai ba zan iya ba, ya kawo min dauki.
Ina cikin addu'ar Diyam ta dawo dakin, na kammala na shafa tare da share hawayen da ya zubo min sanda ina addu'ar. Ta zauna a bakin gado tana kallona "kiyi hakuri Jidda. Insha Allah komai yayi farko zai yi karshe, Allahn daya dora miki wannan matsalar shi zai yaye miki if you believe and trust him kinji?" Na gyada kai sannan na mike tsaye ina kallon abin da ta shigo dashi a hannunta.
Duk da halin da zuciyata take ciki sai da nayi murmushi "babies!" Na fada "twins. Diyam twins kika haifa?" Tayi murmushi tana miko min daya, na karbe ta na daga ta sama ina jin sha'awar jarirai tana shiga zuciyata. "So cute wallahi kamar in sace ta. Dan Allah ki bani" tayi dariya "na baki. In dai wannan ce na baki ita. Da dai wannan rigimammen ne da sai inji tsoron kar ya hana ki bacci" ta fada tana yiwa daya jaririn da yake kan cinyarta wasa "ko ba haka ba abba na? Mai rigima irin ta babansa" na zauna a kusa da ita ina kallon kyakykyawan dan da yake cinyarta yana yi mata toothless dariya, nayi murmushi a raina ina fatan kar nawa yayan suyi halin nasu uban.
"Sannu Diyam!" Na fada "haihuwar twins ance da wahala ko?" Ta yi dariya "da wahala mana, ko wacce haihuwa ai akwai wahala. Amma ni ba su ne twins dina na farko ba na taba haihuwar wasu, na fari na, Allah yayi musu rasuwa amma a ranar dana haife su, ko kwana daya basu yi ba" ta fada tana murmushin takaici, daga dukkan akama har yanzu tana jin zafin mutuwar yayan nata.
Na sunkuyar da kai na ina wasa da hannuna sannan nace "Allah sarki. Allah yasa masy ceto ne" tace "ameen Nagode" sai kuma na kalli kofa ina tunanin nima nawa yayan amma bance komai ba, kamar ta san me nake tunani sai tace "su Yasmin suna can suna cin abinci, ko a kawo miki su nan ku ci tare?" Nace "eh" a raina nasan Asad zai iya cin abinci acan amma Yasmin ba zata ci ba, ko a gida bata cin abinci ita kadai sai mum hadu gabakidaya, sai dai ko in tea ne ko kuma wani snacks haka.
Jimawa kadan da fitar Diyam yaran suka shigo tare duk suka fado jikina "mommy anan zamu kwana ne?" "Mommy nan ne sabon gida mu? "Mommy daddy fa? Shima nan zai taho?" Na jawo tray din na fara zuba musu abinci "ku zauna ku ci abinci" Asad yace "an bani na ci. Ni yoghout zan sha. Ki kira Daddy ki ce in zai taho ya taho min da yoghout" nace "to babana, maza shiga toilet kayi fitsari kazo ka kwanta" ya shiga toilet da sauri ni kuma na dawo da hankali na kan Yasmin "sauko ki ci abinci"
Ta sauko ta zauna tana kallona "mommy anan zamu kwana?" "Eh na amsa mata ina juya mata abincin. "Mommy daddy shi kadai zai kwana?" Na dago kai ina kallonta "ban sani ba. Ki rufe min bakin nan naki kuma ki ci abinci" ta dauki chokali tana ta jujjuya abincin har Asad ya fito ya kwanta yana ta surutan sa shi kadai har bacci ya dauke shi. A lokacin Diyam ta kuma dawowa, wannan karon babu babies din a hannunta sai kaya, "ga kayan bacci, amma na rasa wanda zan bawa Yasmin da Asad,na Subay'a sunyi musu yawa," na karba ina murmushi, ina jin dadin kyautatawar ta "nagode, babu komai" Yasmin ta mike "na koshi da abincin mommy" sai ta shiga toilet.
Ranar da kyar na samu Yasmin tayi bacci, amma ni kuma banyi baccin ba, tashi nayi na sake yin alwala sannan na cigaba da kai kukana ga ubangiji, zuciyata a lokacin da hawayena duk sun kafe, addu'ar samun mafita kawai nake yi duk da cewa har lokacin ban san menene mafitar a gare ni ba. Abinda na sani kawai shine na gama auren Umar, abu na biyu kuma shine nasan indai na koma gida sai sun mayar da ni gidan sa, dan haka yanzu gidan zama nake tunanin inda zan samu. Diyam ta bani gurin zama na tsakanin yau da gobe, kawata ce ita amma rabon na da ita shekara da shekaru bazan zo rana daya kawai in zauna mata a gida in dora mata responsibilities dina ba, dole in nemi mafita. Shin ko gurin yaya Tahir zan koma in roke shi kar ya gaya wa Baba ina tare da shi? And then what? Ba zan cigaba da zama har abada da auren Umar a kaina ba Umar kuma bana jin ko bindiga aka saka masa a ka zai sake ni.
But he must, dan na gama da shi.
Ranar yadda naga rana haka naga dare, na saka yayana a gaba ina ta sakawa ina warwarewa. Har gari ya waye kuma ban saka abinda nake ganin shine mafita a gare ni ba.
Da assuba bayan nayi sallah ne na dauko wayata na kunna, ko gama kamawa batayi yi ba sai kiran ya shigo "Umma" sai kawai naji hawaye ya taho min, Allah sarki uwa, yanzu haka itama yau kwana tayi bata yi bacci ba tana kiran wayata, sai naji wani irin guilt, naji cewa bata chanchanci haka daga gare ni ba amma duk da haka sai naki dauka. Messages ma suka yi ta shigo min yawanci duk daga Umar, wadansu dogaye kamar mai rubuta labari wadansu yan kadan, babu wanda na tsaya na karanta a ciki sai naga wani ya shigo daga yaya Tahir
"Jidda call me"
sai na shiga nayi masa reply.
"I am safe. Ka gaya wa Umma"
Message din yana tafiya na kuma kashe wayar, a lokacin ne na yanke wata shawara, ban san inda zanje ba, ban kuma san me zanyi ba, amma ba zan koma gida ba har sai na tabbatar Abba yayi laushin da idan na koma zai tsaya ya saurare ni sannan kuma ya tsaya min akan maganar kamar yadda ya kamata iyaye suke tsayawa yayansu da suke cikin irin halin da nake ciki.
Gari yana fara wayewa Yasmin da Asad suka tashi, saboda sun riga su saba da tashi da sassafe saboda makaranta. Sai a lokacin tunanin makarantar su yazo min? Ya zanyi da karatun su? Na girgiza kaina, dole su hakura da karatu for now har sai al'amura sun warware mana, dan rashin karatun nasu a yanzu yafi musu alkhairi akan cigaba da zama da babansu, dan tabbas suna tare da Umar watarana zai iya neman mace a gabansu, ko kuma worst.
Nayi saurin kawar da maganar daga raina sannan na shigar dasu toilet nayi musu wanka na sa suka yi alwala suka fito na mayar musu da kayan jikinsu tunda basu da wasu kayan sannan suka yi sallah.
"Mommy yau ba zamu je school ba?"
"Mommy daddy ne zai zo ya dauke mu daga nan gidan ya kaimu school ko?'
"Babu school, anyi hutu"
Na fada shortly
Asad ya fara tsalle yana murna, Yasmin kuma ta zauna kawai tana kallona ni kuma nayi kamar ban ganta ba na cigaba da jan charbin hannuna ina yiwa Allah kirari tare da neman taimakon sa.
Bamu jimada tashi ba Diyam ta shigo, muka gaisa su Yasmin ma suka gaishe ta sai na tsokane ta "kika tashi da sassafe kika taho nan kika bar mijinki ko?" Tayi murmushi "lah! Baya gari ai, yaje Maiduguri, da yana nan ai da tun jiyan kun gaisa. Sai gobe nake saka ran dawowar sa"
Nace "Allah ya dawo dashi lafiya"
Sai ta kawo min kayan da nake tunanin nata ne ta ce in saka, "yara kuma na yi waya za'a kawo musu kaya" nayi saurin cewa "da kin gaya min ai da sai in bayar da kudin" ta harare ni "yayan nawa in zan siya musu kaya sai na karbi kudi a hannunki?" Nayi murmushi kawai tare da yi mata godiya amma bata amsa ba.
Tare muka fita, ta kai yara falo ta kunna musu TV sannan muka shiga kitchen muka yi breakfast tare, tana tabani labarin karatun da take yi a Oxford, "nan bada dadewa ba in sha Allah zan dawo Nigeria gabakidaya a matsayin lauya mai kare hakkin mata, insha Allah wannan shine burina, in share hawayen duk wata mace da take cikin halin kunci, in taimaka wa duk wata macen da namiji ko iyaye, ko al'umma suka danne mata hakkin ta, in fadakar da mata su san menene hakkokin su su kuma san abinda ya kamata suyi idan an danne musu hakkinsu, su san me ya kamata su dauka su san menene bai kamata su dauka ba. Wannan shine mafarki na. Wannan shine burina"
Nayi shiru ina tunanin wannan dogon buri na Diyam, sai nace "Allah ya baki sa'a akan abinda kika saka a gaba, amma babbar magana ce kika dauko Diyam, aikin ba karami bane ba bana jin zaki iya yi ke kadai dole sai kin samu hadin kan su matan da kike so ki taimaka wa din, some will rather die a gidan miji akan su bujirewa aure saboda sun riga sun saka akan su cewa sai a gidan miji zasu iya rayuwa, suna ganin sai da namiji zasu iya rayuwa su ba zasu iya defending da kansu ba, wasu kuma sunyi believing kamar zama a gidan mijin shi zai kai su aljanna, sun manta cewa ba wai yin auren ne yake kaiwa aljanna ba, a'a abinda ake yi a cikin auren ne either ya kai mutum aljanna ko kuma ya dangana shi da wuta"
Ta gyada kai " shi yasa suke buƙatar enlightenment, a fadakar dasu tare da nuna musu abinda ya kamata su dauka a addinance da constitutional rights, da kuma abubuwan da basu kamata su dauka ba dan zai zama illa ga either physical ko mental health dinsu, ko kuma ya zamo illa ga tarbiyyar yayansu, ko kuma ya zama illa ga addinin su dan wani auren zai kai mace wuta ne instead of aljanna"
Nayi shiru ina kallon ta amma ban ce komai ba sai ta cigaba "Duk auren da rashin zaman lafiyan cikin sa ya kai matsayin da mace zata ke daga muryar ta sama data mijinta, wani lokacin har ta kai da duka ko zagi ko cin mutuncin, ko ta ke gudun sa a gado, ko ta mayar da shi dashi da babu duk daya ne a gurinta, to wannan auren a ganina matar da take cikinsa hanyar wuta ta kama bata aljanna ba"
Nayi shiru ina tuno marin da nayi wa nawa mijin jiya. Amma da nayi marin ma ba wai huce wa nayi ba. Meaning akwai matan da in ransu ya baci irin haka suke abinda yafi mari, na tuno da matan da suke kashe mazajen su har lahira.
Sai naji Diyam ta cigaba da cewa "kinga akwai wadda naji labari, wai mijinta neman mata yake yi tayi tayi ya daina yaki dainawa sai kawai tace ita ta sallama shi ta bar wa duniya shi, yaje yayi ta neman matansa amma ita ba zata kwanta dashi ba, za dai ta cigaba da zama dashi a matsayin matarsa saboda kar ta fita al'umma su ce mata bazawara. Tun mijin yana binta yana nemanta har ya hakura shima ya barwa duniya ita. To Yanzu menene amfanin wannan auren? Wacce aljanna mai wannan auren take tunanin tana nema a cikin auren?"
Nace "most of mutanen yanzu ba dan neman aljanna suke yi komai ba, most of them dan duniya sune yi, dan duniya ake zaman gidan auren dan duniya iyaye suke matsawa yayansu kar su fito daga gidan miji, saboda kar duniya ta zage su, saboda kar su kunyata a idon makiyan su" na fada ina tuno da tawa uwar.
Sai Diyam tace "haka ne, wasu kuma ba dan haka ba. Wasu kuma dan rashin madafa ne. Mijin nan shine yake yi musu komai maybe har iyayensu shine yake yi musu komai idan suka rabu dashi, bar ta gurin zama, hatta abincin da zasu saka a bakin su gagararsu zai yi, sannan yayansu dole ko da ace sun san right din su na cewa yaya su addini ya bawa rikon su ba miji ba, amma rashin inda zasu ajiye yayan da abinda zasu ciyar da su dashi, da kuma tunanin zasu rasa wani mijin idan suka fito da yaya dan ba kowanne namiji ne zai aure ki ya haɗa da yayanki ba, to wannan tunanin shine yake time su saisu zauna da sunan zaman hakuri, amma in reality ba wai zaman hakurin suke yi ba fa, zaman babu yadda zasu yi suke yi"
Nayi shiru ina tunani, a raina ina lissafin to ko irin wannan zaman ne Aunty Afia tayi? Sai na tambaye ta "to yanzu menene kike ganin mafita ga irin wadannan matan?"
Tace "mafita shine su nemi abinyi, ko aikin yi ko sana'a, na farko in suka samu abinyi ba zama su dora ransu sosai akan mijin ba har wani abun nasa yadame su, damun da har zasu kai ga sainsa ko akai ga daga murya ko zagin da har za'a samu alhaki. Na biyu su kansu mazan in kina da abin hannunki bakya yawan ce masa bani bani to zaki ga bai fiya daga miki kai da fushi da sauran su ba, musamman ace kina dan taimaka masa da wasu abubuwa na gida, kin san nauyin nan shine wani lokacin yake kufular da maza su zo suna ta fadan babu gaira babu dalili, amma misali ace bai kawo cefane ba, ya dawo yana tunanin zaki yi masa mitar cewa bai kawo cefane ba sai ya tarar har kin siyo kinyi girkin kin kawo masa abincin, tabbas zaki ga yadda zai ji dadi, zaki ga yadda ko kinyi wani karamin laifi shima zaiyi overlooking, dan haka samun abinyi ga mace yana kara zaman lafiya sosai a gidan aurenta. Kuma in the case if extremist maza wadanda ba'a iya musu, da kuma masu manya manyan laifuka kamar zinace zinace da shaye shaye, luwadi, da sauran manyan laifukan da ko a addini zama dasu bai halatta ba, idan mace tana da abinyi rabuwar ma zata fi zuwa mata da sauki tunda tana da yadda zata kula da kanta da yayanta, kuma su kansu iyayen, da yawa daga cikin su tsoron responsibility ne yake sakawa su bar yayansu suyi ta shan wahala ba wai dan basa son su ba, amma in kina da shi zaki ga sai sun fi supporting dinki, kuma ko wani auren ne yazo mijin ba zai wani damu da rikon yayanki ba tunda yasan kina da abin da zaki rike kayan ki. Wannan duk ina magana ne akan idan ubansu bai sauke nauyin su ba, dan a shariance idan aure ya mutu uwa za'a bawa rikon yaya, shi kuma uba za'a saka masa kudin da zai ke bata duk wata ko duk sati na ciyarwa da sauran hidindimun yayan nasu, idan tana da ciki ko tana shayarwa har da nata hidimar"
Nayi shiru ina kallon bango, ina jin idonta akaina tana kallona, sai na juyo ina kallon ta nace "akwai matan kuma da baki fada ba, su kuma suna