Chapter 16 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 106

45K to 48K   out of 316K words

ba dan halin ta ba ko dan tsakani na da Farhan.

Abu daya da ya chanja shine gwoggo Habibah da yayanta kaf sun janye jikinsu daga gidan mu, sun kuma janye daga duk shirye shiryen bikina bayan an saba duk bikin da za'a yi a gidan mu tare da su ake yin komai. Umma tayi kokari gurin rarrashin gwoggo akan tayi hakuri ta manta da maganar amma taki tace ita ba wai auren ne bata son ayi ba, taso ne dai Abba yayi wa Umar fada ya nuna masa bai kyauta ba kafin ya bashi ni din. Tunda akayi abin bamu hadu da yaya Jamila ba, amma naji ance wai duk ta chanja tayi wani iri har makaranta ta daina zuwa, duk da ban tabbatar hakan ko gaskiya bane ba ko kuma exaggeration ne irin na Hajiya.

Mu kam shirin bikin mu muke tayi, Mufida da Farhan ne suka fitarda anko na kawaye kuma sune suka gayyaci duk kawayen mu na school da na unguwa da kuma dangi. Umar ma kuma ya kammala duk shirye shiryen sa, ya gyara gidan sa dai dai da yadda yayi suiting taste din mu ni da shi. Sannan muka tsara duk yadda muke so bikin ya kasance. Umar ya saka a saka daurin aure ranar Friday "saboda albarkar ranar so nake ta bi auren mu ni da ke har abada".

Allah ya dora Umma akan Abba biki saura sati uku ya bar ni na tafi gidan Aunty Afia na zauna a can, ita kuma ta bude min sababbin lessons take dora min kullum akan aure da duk abinda ya kunsa.

"Shi aure da kike ganin sa Jidda hakuri ne yake rike shi. Duk matar da kika gani a gidan mijinta to zaman hakuri take yi da shi haka zalika shima mijin hakuri yake yi da ita. Shi kuma namiji da kika ganshi to tamkar sarki yake a gidan sa, babu abinda namiji yafi so fiye da komai a gurin matarsa irin ladabi da biyayya. Wannan girman da Allah ya dora musu to har a cikin halittar su haka suke, su dai suna son ayi musu ladabi kuma babu abinda suka tsana irin a raina su. Komai son da mijinki yake miki idan raini ya shiga tsakanin ku sai kin fita daga ransa. Duk abinda yace miki kar kiyi masa musu ki bishi a haka in yaso daga baya a hankali cikin dabara sai kiyi masa bayanin yadda kike so bawai ki nuna masa ke lallai ba zaki yi abinda yace ba ke abinda kike so zaki yi"

"Ki zamanto mai rike sirrin mijinki ba mai kwakwazo da yada duk abinda yafaru tsakanin ku a idon duniya ba, musamman a gurin kawaye ko yanuwansa ko naki. Kar kuma kike nuna kwadayin abin hannunsa, in ya baki ki karba ko mai kankantar sa kiyi masa godiya in kuma bai baki ba sai ki hakura, kar ki yarda kike rokonsa abun duniya sai lallai abinda yake hakkinki ne yayi maki kamar ci da shada sutura, suma kuma kinsan dai dai aljihunsa kar ki dira masa abinda yafi karfinsa. Ballantana ma ke tunda ya samo miki makaranta kuma muna saka ran zai barki kiyi aiki, sannan aikin health albashin su mai kyau ne dan haka zaki ke daukewa kanki wasu yan tsarabe tsaraben na mata ba sai ma ya sani ba"

"Kar kuma ki dora wa kanki mugun kishi akan mijinki ki ce ke lallai dake kadai zai zauna ba zai kara aure ba, in yanason karawa ki barshi ya kara din in dai har je ya sauke miki naki hakkin da yake kansa shikenan. Kema kuma sai kiyi kokarin ganin kin sauke nasa hakkin da yake kanki wajen kula da tsaftarsa data gidan sa, kula da abincinsa, kare mutuncin kia cikin gida a makaranta da kuma wajen aikin ki, sannan da tabbatar da kin biya masa bukatar sa a kan gado"

Na rufe fuska ina jin kunya sai tayi dariya "to au wannan shine yafi komai muhimmanci a aure, na saka shi a karshe ne saboda ina son inyi miki bayani sosai a kansa. Kinga mazan nan? To da yawa daga cikin su babu abinda suke girmama wa a cikin aure kamar wannan abin, duk da dai halitta halitta ce. Wani yana da bukata sosai wani saffa saffa wani kuma bai ma damu da abin ba, amma majority sun damu da abin. Kuma kinsan babban sirrin abin?"

Na girgiza kai na tace "tsafta. Kar ki yarda ko da wasa mijinki yazo kusa da ke yaji wani wari ko wani karni. Ko mai son kusantarki da yake yi wannan warin zai gusar masa da sha'awar ki, kullum ki kasance cikin kamshi, ki samu kiyi hadin turare ya zamanto koda yaushe shi kike anfani dashi yadda zai kasance kamar wata signature dinki, a gurinki kadai zai zo yaji irin wannan kamshin musamman in kika hada din kika ji ya yaba to sai ki cigaba, wannan zai sa ya kara manne miki dan wani kawai zai zo kusa dake dan yaji kamshin ki hankalin sa ya kwanta"

"Sirri na biyu shine rashin nuna gazawa, kar mijinki yana kusantarki ki nuna masa kin gaji ko kiyi ta korafin ke ya takura miki ko something like that, ko yana tabaki kina ture shi, wannan shima zai cire mishi son abin daga zuciyarsa ko yana so din sai ya kasa nema tunda yana tsoron yadda zakiyi reacting. In ya nema ki bashi tunda hakkin shi ne, in bai nema bama in ke kina so sai ki nema kema tunda kema hakkin ki ne. Wannan shi ya kawo mu kan sirri na uku wanda shine kunya"

"Kunya ado ne mai kyau a gurin mace, kuma maza da yawa suna son mace mai kunya amma a wajen bedroom, in aka shiga daga ciki maza da yawa sunfi son macen da zata nuna sanda aka raba kunya ita bacci take yi a lokacin. Babu wani shamaki a tsakanin miji da matarsa, abinda kawai addini ya saka iyaka akai shine saduwa yayin da mace bata da tsarki da kuma saduwa da mace ta dubura, banda wannan komai zasu iya, komai. Wannan ne kuma ya dawo damu kan abu na farko da muka yi Magana akan sa, tsafta. In babu tsafta ko kuna son yin wasu abubuwan na ma'aurata ba zaku iya ba saboda kazanta. In kin cire kunyar ki a bedroom sa ki mayar da ita idan kun shiga mutane, wannan zai kara daga darajar ki a idon sa"

"Generally maza sunfi mata karfin sha'awa, a yanzu baki san yanayin mijinki ba sai kinje tukunna, duk da dai yawanci farkon auren nan da masu ƙarfin sha'awar da marasa karfin sha'awa duk suna yin na dokin nan, sai dai daga baya kuma a hankali zaki gane yanayin sa, idan ya fiki karfin sha'awa shine zaki bukaci supplements da zasu kara miki taki yadda zaki iya daukan nauyin mijinki, idan kuma ƙarfin sha'awar ku yazo dai dai to ba kya bukatar supplements, abunda kike bukata kawai shine cima mai kyau musamman fruits, shan isashshen ruwa da kuma hutu na jiki dana zuciya wanda zai saka mind dinki akan son abin"

"A yanzu ma dole zamuyi miki shiri sosai na taryar mijinki, a matsayin ki na budurwa ba kya bukatar kayan matsi sai dai na karin ni'ima kafin kuma in kinje kun fahimci juna ke da mijinki sai ki san wanne zaki cigaba da sha wanne ne kuma zaki daina. Amma dai koma menene ina kara tuna miki cewa wannan abin shine kusan rabin auren"

Daga nan sai ta fara loda min kaya, wadansu ta bani ta saka in yi amfani da su a lokacin wasu kuma sai dai tayi min bayanin yadda zanyi amfani da su tace in ajiye sai bayan biki tukunna. Tun ina jin kunyar ta in tana yi min wasu maganganu har na zo na saba na daina jin kunya sai dai in saurara amma dai bana iya bata amsa sai dai in bi umarnin ta kawai.

Tun kafin muyi nisa na fara fahimtar magungunan ta sun fara aiki a jikina, dan haka kawai in ina zaune sai inji ni a jike kamar wadda ta fara period sai na duba sai inga ba ita bace ba, haka zanyi ta faman saka pant ina chanjawa.

Tunda na taho gidan Aunty sai Umar ya mayar da gidan gurin zuwansa, babu wanda bai san shi a gidan ba a cikin yan kwanakin da nayi ya siye kowa da kyauta da kuma kyautatawa, hatta Alhaji sai da naji yayi comment akan Umar kuma ya nuna yayi masa. Kowa ya zauna dashi kuma sai ya fahimci yana sona sosai kuma sai yayi min murnar samun miji kamar shi. A haka gar satin biki ya kama.

Ranar Wednesday za'a fara bikin, za'a fara ne da ƙunshi wanda aka tsara za'a yi anan gidan Aunty, sai kuma kamu ranar Thursday a gidan gwoggo Habibah, wanda Umma ce ta matsa ayi hakan duk a kokarin ta na ganin an daidaita, da dare kuma za'a yi kamun ango a can gidan su. Friday daurin aure bayan sallar juma'a a masallacin juma'a na unguwar mu, a ranar kuma gidan maza zasuyi yinin su, da dare kuma ayi dinner. Saturday muma zamuyi namu yinin anan gidan mu sannan da magrib a kai amarya Jidda gidan angonta umar.

Tun ranar monday Farhan ta zo muka tafi saloon akayi min gyaran jiki, halawa da dilka, kyakykyawar fata ta ta sake yin luwai luwai, aka kuma gyara min gashina sannan aka min manicure da pedicure. Farhan ma anyi mata wannan, wanda duk daga aljihun Umar kudin ya fito dan shi yazo har gidan Aunty ya dauke mu ya kaimu kuma da muka gama muka kira shi yazo ya mayar damu gida. Kuma tun daga can yake ta yaba gyaran jikina duk kuwa da cewa na saka dogon hijab na rufe jikina amma haka yayi ta tsokana ta wai shima zai je ayi masa dan yayi min gayu irin wanda nake yi masa. Farhan tana ta kara zuga shi wai dan ma baiga yadda fata ta tayi kyau ba.


Washegari yazo ya kawo min dinkunan da zanyi amfani dasu da bikin, wanda duk shi ya kai mana dinkuna tare ni da shi na dukkan events din da za'a yi. Tare da Aira muka fito, niyya ta mu karba kawai mu koma ciki amma ya langwabe min lallai sai na shiga motarsa munyi magana. Na bawa Aira kayan ta shiga dasu ciki sannan na shiga na zauna ya tsare ni da ido "duk wani kyau kike tayi wallahi, ko duk amarcin ne haka" nayi murmushi kaima ai kana kara kyau sosai, gashi nan kaje kayi gyaran fuska" ya shafa fuskar sa "am glad you noticed. Ni ban taba jin kin yaba ni ba, I always thought bana burgeki ma ni kwatakwata"

Nace "inji wa? Ni dai bani na gaya maka haka ba" ya rage murya "to tell me otherwise. Ki sanar da ni kina sona ko ki gaya min ina da kyau ko ina burge ki ko wani abu mai dadi haka" na sunkuyar da kai "zan fada maka, amma ba yanzu ba" yace "sai yaushe? Sai kin kawo min ziyara?" Ya fada yana kashe min ido Nace "wacce ziyarar kake magana akai?" Yace "wacce kike kawo min kullum cikin bacci na, ko baki san duk dare sai nayi mafarkin ki ba" na bude ido "mafarki na kuma? To me nake yi maka a mafarkin?" Yayi murmushi yana lumshe ido "kina so ki sani? Zan gaya miki amma ba yau ba sai ranar assabar da misalin karfe goma na dare, ina gayyatar ki gida na kuma dakina, a can zan bayyana miki da baki in kuma nuna miki a aikace irin abinda kike min a mafarkin nawa"

Nayi saurin kama handle din kofa zan fita sai yayi locking. Na juyo ina kallon sa "kaga gida zan koma fa, Aunty tana can tana nema na" ya lumshe idonsa yana kallona kasa kasa, Aunty ta san kina tare da mijinki ai, dan Allah Baby ki barni inyi ta kallon ki" na langwabe kai "ni bana son wannan kallon da kake yi min, wani iri yake yi min" y danyi dariya "wanne iri yake yi miki" nace "irin kamar n yan shaye shaye" yace "ko? Baki san ni ma a bugen nake ba?" Na rufe baki na da hannu biyu "a buge fa kace?" Yace "eh mana, amma ba giyar da yan shaye shaye suke sha na sha ba, ni giyar son Hauwa'u na sha har tayi min illa"

Naji kunya "kai ko? Ba zaka fasa halinka ba ko?" Ya kara narkewa akan kujera "ki barni dan Allah, ko kamshin ki inyi ta shaka ina jin dadi" na sake kama handle "ni dai gida zan tafi. Ka barni in tafi" yace "to in dawo gobe in kuma ganin ki?" Nace "gobe kasan za'a yi kunshi, ba lallai in samu damar fitowa ba" yace "muga hannun da za'a yi miki kunshin? Show me" ya fada yana miko min hannunsa, kamar wata sokuwa sai na fito da hannun daga cikin hijab na jera a kusa da nasa daya miko min, bai kama hannun ba kamar yadda nayi tsammanin zaiyi, duk da cewa a lokacin a yadda nake jin sa a zuciya ta ko kama hannun nawa yayi ba lallai ne in iya hana shi ba.

Muka yi shiru muna kallon hannayen mu da suke a jere sai nace "wanne color din lalle kake so ayi min? Ja ko baki?" Ya danyi jim yana kallon hannun tare da tunani sannan yace "red. Duk zasu yi miki kyau but Ja zaifi kyau. Besides, red is sexy" mukayi dariya tare, sannan yace "but these long nails, ayi musu adon red and black din zasu yi kyau sosai" nace "an gama" sai kuma nayi dariya. Yace "what's funny?" Nace "hannun ka, kawai na lissafo ace kai aka yiwa halawar da akayi min jiya da ina jin sai kayi fitsarin wando" yace "inji wa? Ni fa jarumi ne. Kuma ba zaiyi min kyau ba ma" nace "saboda me?" Yace "saboda ni namiji ne, it is the rule of nature. Hannun maza is supposed to be like these, in ya zama irin naki then it wrong be attractive to you kuma, haka zalika in naki ya zama irin nawa then it won't be attractive to you too"

Na gyada kai cikin fahimta. Sai kuma na ɗauke hannuna na mayar cikin hijab tare da cewa "dan Allah ka barni in tafi gida, Aunty zatayi fada" yace "sai kinyi min alkawarin in na dawo gobe zaki fito" na juya ido "minti biyu kadai" yace "na yarda, in dai zaki fito shikenan" na bude motar na fita sannan na leko ta window "bye bye" yace "bye Baby. Sai munyi waya".

Washegari tun safe aka dauke carpet din palon Aunty, ana masu kunshin da aka gayyato suka zo suka fara yiwa mutane, masu baki nayi masu red nayi. Ni kuma a dakin Aira aka yi min nawa, nayi wa mai lallen bayanin yadda Umar yace kuma ta bani isashshen time dinta ta kuma baje basirar ta a hannayena da kafafuwana. Tun kafin a fara su Mufida suka zo su ukun dan suma duk za'a yi musu kunshin, sune kuma suka yi ta daukar hoton kunshin nawa suna turawa yayansu yayin da shi kuma ya addabeni da waya, dole na saka ear piece na saurare shi. Kusan tare da shi akayi lallen aka gama duk yana jin hirar mu.

Da yake ana fara da wuri wajen azahar har an gama nawa, sai duk suka fita palo ana yi musu a can ni kuma na zauna anan dan bai gama bushewa ba bana so a bata min shi. A lokacin ne kuma aka turo kofar aka shigo, na daga kai muna kallon kallo ni da Yaya Jamila.

Ta rame sosai, duk da glasses din idonta amma naga ramar ta. Gabana ya fadi sanda ta cire glasses din, nayi saurin sauke ido na kasa ina jin wani irin kunyarta a raina. "Amarya kin sha kamshi" ta fada tana karasowa kusa dani. Ta zauna tana dan taba kunshin hannuna daya fara bushewa "yayi kyau sosai. Allah ya sanya alkhairi" nace "ameen. Ya su gwoggo?" Tace "lafiya lau. Ya angon naki?" Sai nayi shiru na kasa amsa mata.

Tace "zuwa nayi muyi magana Jidda. Ina so in tabbatar miki da cewa ni banji haushin ki ba ko kadan, tunda ba wai kwace Faruq kikayi daga gurina ba, sanda yace yana sonki baki san yana zuwa gurina ba dan haka baki da laifi for falling for him. Baki da laifi. Kuma banji haushin ki da kika ki fasa aurensa bayan kinsan abinda yayi min, I would have done the same thing da ace ni ya zaba. I love him so much that I would have done the same thing"

Ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta "na san da kika gaya masa abinda Umman mu tace karyata wa yayi, dan baya son ya sirka soyayyar ku, baya son ya bata kansa a idonki. Watakila ma cewa yayi bai ma sanni ba. Watakila cewa zaiyi bai taba yi min magana ba. Tunda abinda yake pretending kenan tunda abin ya faru. Kuma nasan kin yarda da shi dan nasan idan ni ce nima zan yarda da shi saboda son da nake yi masa"

Ta dago kai tana kallona tace "watanku nawa tare? Bana jin kun kai shekara daya tare, imagine yadda kike jinsa a ranki. Imagine ace kun shekara uku a haka. Imagine yadda zaki ji shi a ranki then. To haka nake sonsa, haka ya saka min sonsa a raina. Then imagine rana daya yace shi baia taba saninki ba, yayi cutting duk wani link da yake tsakanin ki da shi."

Ta fara murza hannayenta. "Tun ranar da ya dawo dani daga dinner din abokinsa dana raka shi, ina shigowa ina duba chats dina naga video din sa dake wai shine mijin da zaki aura. Na gaya wa Umman mu, da sassafe ta zo ta fada a gidan ku, I guess ke kuma kika kira shi kika gaya masa, tun ranar yayi cutting dina off tamkar wata used and unwanted rag, yayi blocking number dina, yayi blocking

16 / 106