Chapter 102 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   102 / 106

303K to 306K   out of 316K words

kina cikin kunci, society kuwa su zasu fara dora tukunyar shinkafa a ranar da kika mutu, daga nan kuma su koma kan wata"

"But still, no matter how strong you have become you still need a man's strong sholder to rest on, kamar yadda shima namiji no matter how strong yake still yana bukatar a soft and gentle touch of a lady, muna bukatar su kamar yadda suma suke bukatar mu"

Na ture maganar ta gefe na shigar da maganar da bayan ganin baby ita ce ta kawo ni gidan, maganar motar da nake son siya. Sai ta ce min dama yanzu zasu fita da maigidan ta, in jira sai mu fita tare muje Abatcha motors in ga motocin da suke available ko da wadda za ta yi min a ciki.

Ta hau sama zata shirya ni kuma na zauna ina cin samosas din data kawo min ina duba waya ta amma a raina maganganun ta nake juyawa a raina. I can't even imagine me falling in love again, ni love din tsoronsa nake ji, maybe in naga ina son auren ko kuma in su Abba sun matsa zan iya cewa kawai su zabar min da kansu. That way sai Allah ya dubi biyayya ta ya saka in dace da wanda zai zama sanyin idaniya ta, and maybe, watakila, watarana, I may even be able to love him. 

Babu jimawa muka fita tare a motar Sadauki mijin Diyam, bayan na karbi kayan da na bata sako ta taho min da su daga UK. su biyu a gaba ni kuma ina baya, sun bar yaran duk a gurin Nanny din su tunda ba dadewa zasuyi ba.

Munje na ga the famous Abatcha Motors, proudly Sadauki da Diyam suka zagaya dani suna nunamin gurin tare da nuna min tarin motocin da suke gurin, Sadauki yana ta zuga ni wai sai na sayi mai tsada ni kuma naki nace ni daidai aljihuna zan siya kawai ina neman motar da zata ke kaini duk inda nake son zuwa, wanda baya wuce within Kano state. Shikenan.

Da kyar ya barni na zabi wata peugeot wadda tayi dai dai da aljihuna. Muka gama ciniki Diyam tana ta yi mana dariya wai ina jin kunyarsa naki neman ragi, shi kuma sai ya rage min kawai da kansa ya zabtare min kudade masu yawa har sai da naji kunya nace zan fasa siya gaskiya. Diyam kuma ta bata rai dole na hakura.

Daga nan muka dauki hanyar gidan mu, su zasu kaini a mota sai an rubuta receipt an yi clearing motar sannan za'a kawo min ita har gida.

Zuciyata tas nake jinta ina jin dadin siyan motar da nayi, duk da kasancewar ba wannan ce mota ta ta farko a duniya ba amma nafi jin dadin ta saboda wannan ni na siya da kudin da na tara da gumi na. Na biye musu muka yi ta nishadi a motar har muka je kofar gidan mu muka yi packing sannan nayi musu sallama na fita. Sai bayan da na fita sannan na tuna da sako na a booth din motar sai nayi musu knocking na tuna musu. Nufi na su bude min in dauka but sadaukin Diyam is too much of a gentleman for that, sai gashi ya fito da kansa ya dauko min.

A lokacin ne Umar ya shigo layin, ni na dauka ma ya koma Lagos tun sanda ya dawo da yara ashe yana nan. Yayi packing dan nesa damu kadan yana kallon mu. Sadauki ya fito da yar ƙaramar jakar ya miko min, na dan durkusa kadan na karba sannan nayi masa godiya bai amsa ba sai ya juya yana kallon gidan mu yace "amma try and get somewhere safe da zaki ke packing motar ki saboda security" na gyada kai nace "akwai wani gida anan bayan mu inda Abba yake ajiye motarsa lokacin da yana da ita, can zan ke kaita" yace "good. Gobe za'a kawo miki ita insha Allah" na sake yi masa godiya sai yayi dariyar sada take kara fito da kyawunsada kwarjinin sa yace "wai ke ba kya gajiya da godiya ne sai kace wata yar fulani da nasani a shekarun baya?" Ya fada cikin daga murya dai dai yadda Diyam zata jiyo, muka juya muna kallon ta ta kofar daya bari a bude sai ta harare shi ta kuma yi masa alamar zata kamashi.

Nayi dariya "ni kam babu ruwana kar a kama da ni gwara in shiga gida" sai ya shiga motar yana mata magana amma banji mai yace ba naga dai tayi kamar zata rankwashe shi sai ya kauce yana dariya, nima ina da murmushin sha'awar da suke bani, lallai da gaske soyayya akwai dadi idan kayi dace.

Na leka ta tagar shi da take a bude na sake yi mata sallama sannan na matsa ya tayar da motar sukayi gaba ina daga musu hannu.

Ni shaf na manta ma da motar da naga tayi packing a bayan mu sai da naji an zo da sauri kamar kububuwa an sha gaba na a dai dai kofar shiga gidan mu.

"Uban waye wancan din?"

Na dago kai cikin mamaki ina kallon Umar din da gabakidaya ya rikice kamannin sa sun chanja, idon nan yayi ja kamar in an watsa turaren wuta zaiyi kamshi.

Lokaci daya na gane abinda ya faru. Umar bai ga Diyam ba saboda tinted glasses din motar. Ya dauka Sadauki gurina yazo. Ya dauka hira da dariyar da muke yi zance muke yi. And I decided to rub more salt to his wound.

Na hade girarsama da ta kasa nace "ba uban kowa bane ba, kuma babu wani obligations a kaina na cewar sai na gaya maka ko waye, but tunda har ka wahalar da kanka ka tambaya zan baka amsa. Saurayi nane. Zance yazo gurina muka fita shopping. Sai menene?"

Ya fincike jakar hannuna yayi jifa da ita ya nuna ni da dam yatsa "na ga alamar kina so ki kashe ni ne da raina Jidda. And I will not let you. Tun wuri ki kore shi ki gaya masa kar ya kara ya kara zuwa gidan ku dan wallahi rayuka zasu baci, tell him that gidan mijinki zaki koma......"

Na bude baki "waye mijin nawa? Last time I checked bani da aure kuma bansan sanda aka daura min ba. Ina ka da damar da zan tsaya da duk wanda na ga dama. Kuma saboda me zance masa kar ya sake zuwa gurina bayan ina son sa? Bayan yanzu muka gama maganar zai turo neman aure na? Bayan yanzu fitar da mukayi har da akwatin kayan lefe muka siya?"

Ya jingina da jikin bango, daga alama neman faduwa yake yi, na dauki jakar da ya yar na rakube ta gefensa da niyyar shigewa ciki sai ya rike hannuna, and I felt the heat coming from his skin da tayi ja kamar yadda idonsa yayi.

"Kina gaya min Jidda......kina son sa....aurensa zaki yi?" Na fisge hannuna daga cikin nasa "why not? Ba ka ganshi bane ba? Ko ba ka lura da yadda ya hadu ba? Ko baka lura da irin kulawar da yake nuna min ba? Jiya ma fa ya sauka a kasar nan daga Canada inda acan ne zamu zauna bayan bikin mu kawai dan ya ganni duk da cewa kullum muna tare da shi a video call, but yana so ya ganni physically shi yasa yazo purposely saboda ni. To me yasa zan ki son sa? Me zai hana ni auren sa?"

Na juya sai kuma na sake juyowa na nuna shi da yatsa "and don't ever try to touch me again, kar ka sa mijinaya gani ransa ya baci. In ka kuma kuwa zanyi maka ihun gardi"


Bai ce komai ba har na shiga cikin gida ina murmushin mugunta. Yau wani zai kwana yana juyi. Duk da dai ban san yadda zan kare kaina ba kuma in ya ga ba'ayi auren ba.

Ina shiga kuwa na tarar da Abba. Na durkusa na gaishe shi as usual ya tambaye ni daga ina nake nayi masa bayani tunda dama nayi masa maganar motar da nake son siya kuma ya amince, dama yace baya son yawon da nake yi a motar haya kullum.

Sai kuma ya kama yi min fada "to ba kin fara da siyan mota ba, kar hakan ya sa ki cigaba da sakin jiki a gida, dan ni ba jin dadin ganin ki nake yi a gaba na ba dan dai kaddara ta gifta ne, ki fito da miji na gaya miki so nake kafin Allah ya dauki raina ya zamanto babu yata da take gida"

Na gyada kai "insha Allah Abba" har ya juya sai kuma ya sake juyowa "dan nace ki fitar da miji fa ba wai ina nufin ki kula kowanne shashasha ba." Na danyi murmushi na sake gyada kai "na gane Abba".

Washegari monday, evening nake dashi dan haka tun safe dana raka yara school a kafa ina kwance ina dan taba business kuma ina hutawa, sai kusan azahar sannan na tashi na dan taya Umma muka karasa abinci sannan naci na shirya zan fita. Luckily sai ga mota ta an kawo min, bayan su Umma sun fito sun gama gani sun gama saka min albarka sai na fita da ita zuwa office ina ta jin dadi a raina har da kunna kida inaji.

Dama lokacin a asibitin nasarawa nake, na shiga nayi packing na fito ina sauri dan na kusa makara sai ganin mutum nayi a gaba na.

"Hajiya Jidda manyan mata" na juya na kalli mai maganar saboda jin muryar da nayi kamar na santa

"Bashir?"

Na fadi sunan sa cikin mamaki.

Ya dan bude hannu. "Doctor Bashir. Dama ranar nan na ga wata kamar ki sai na saka aka bincika min aka ce min ke ce, ashe kina nan yanzu"

Na cigaba da tafiya tare da jan dan karamin tsaki. Ya biyo bayana "kina kallon kanki a madubi kuwa? Lallai abokina ba karamar asara yayi ba ina taya shi jaje, sai dai ina taya kaina murna" na dan juyo cikin mamaki ina kallon sa cike da tsana "murna? Menene gain dinka a ciki da zaka yi murna?" Yace "well, I have not gain anything yet, but I intend to in dai zaki bani hadin kai. Allah da gaske nake auren ki zanyi in dai kin yarda. Kinga zaki samu damar kona masa rai in kika auri babban abokinsa, ni kuma nayi gaining by getting kyakykyawar mata kamar ki, ke kuma kinga kinyi gaining saboda kin auri wanda yafi tsohon mijinki komai kuma an rufa miki asiri an dauke ki daga yawo a kwararo kullum....."

Na daga masa hannu ina jin cewa ba zan iya cigaba da sauraron muryarsa ba nace "save your breath, maybe zaiyi maka amfani later, and this is the first and last warning da zan baka, kar ka sake gangancin yi min magana" nayi masa kallon sama da kasa nace "ni kuma na san kafi Umar komai marar kyau, amma ko tafin kafarsa baka kamo a masu kyau ba"

Na wuce da sauri sai ya kamo hijab dina "don't walk out on me bayan ban gama magana da ke ba" na juya da sauri na kwace hijab dina da niyyar wanke fuskarsa da mari ko da kuwa hakan zaiyi sanadin aikina amm sai ganin Umar nayi out of nowhere ya sauke nasa hannun a inda nayi niyyar saukewa.

Ban tsaya sauraron me suke cewa ba nayi sauri na bar gurin dan bana son wata rigima ta tashi a saka sunana a ciki, can ta matse musu, sunfi kusa.

Sai dai kuma sai na samu kaina da mamakin me ya kawo Umar gurin. Was he following me? Has he been spying on me?

Ina shiga na tarar wadda zata tashi tana ta jira na, na bata hakuri na karbi aikin tayi min bayanin komai sannan ta tafi ni kuma na zauna ina yin cike cike sai kawai ji nayi an banko kofar office din an shigo, Umar ne ya tsaya a gaba na yana haki, gabakidayan sa a hargitse yake na lura tun kayan da na ganshi da su jiya ne a jikin sa.

Kafin yace komai na daga murya da karfi "security!" Ya sunkuyo dai dai fuskata.

"I am warning you. Idan na sake ganin ki da mutumin nan, da Bashir din nan, wallahi sai na kashe shi, sai dai in na kashe shi nima a kashe ni, and I bet that is going to touch your stone cold heart dan ko bakya jin komai a kaina dole kina ji akan yayanki"

Na kankance ido a kansa "are you threatening me?" Ya mike straight "yes, I am threatening you with my life, if that means something to you"

A lokacin securities din dana kira suka shigo, bai jira sun karaso ba ya juya ya fita tare da bugo kofa da karfi.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana idan baki siya ba kar ki karanta idan ykuma kin siya kar ki sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*The End*

*Alhamdulillah, komai yayi farko yana da karshe. The journey of six months have come to an end*

🎶you are a good soldier, choosing your battles, pick yourself up and dust yourself off and back in the saddle🎶

🎶You are on the front line, everything is watching, you know it is serious we are getting closer, this isn't over🎶

🎶The pressure is on, feel it, but you got it all believe it. When you fall get up ehh ehh, when you fall get up ohh ohh. Tsamina mina sam karewa, cos this is africa🎶

~ Rihanna

Sai da ya fita sannan nabi kofar da tsaki. Wai threat, wai zai kashe Bashir, to in ya kashe Bashir ni menene nawa a ciki? In ma saboda yayan da suke tsakanin mune zan iya sauke su away from all his scandals.

Ya manta sanda nace zan yiwa Bashir wanka da tafasasshen ruwa saboda tsanar da nayi masa? Ya manta da sanda nayi ta masa kuka akan ya rabu da Bashir din sai yanzu kuma zai zo yana wani kumfar baki da wasu empty threats cewa zai kashe Bashir. To sai me kuma? It will be a good riddance in ya kashe shi din ma shi kuma aka kamashi, at least al'ummar annabi sun samu sauki daga masifar da take cin su.

Ban kuma bi ta kan maganar ba har na tashi daga aiki a gajiye na tafi gida. Sai dai ban jima da dora hakarkari na akan katifa ba bayan na samu da kyar yara sunyi bacci sai Umma ta leko wai inje inji Abba. Tun da naji wannan kira da dare na san ba lafiya ba, sai dai kuma jikina yana bani ba zai wuce maganar aure ba amma kuma menene emergency a ciki da ba za'a bar maganar sai da safe ba?

Na tashi na saka dogon hijab akan kayan baccin jikina na hau saman na tarar da Abba a zaune a varandar yana jin radio da Umma a zaune a gefensa. Na zauna acan nesa na gaishe shi, sai yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan yace

"baban yaranki ne ya aiko min da sako a waya"

Gabana ya fadi na dago kai ina kallon sa. Baban yara na Umar kenan ko? Sakon menene ya aiko wa da Abba?

Kamar amsar tambayata sai Abba ya miko min wayarsa yace "shiga cikin sakonni ki dubo sai ki karanto a fili inji" na fara lalube a cikin wayar hannu na har rawa yake yi, ina budewa na gane number din da Umar yake min magana da ita a whatsapp, na bude messege din na karanto a fili.

"Assalamu alaikum. Abba barka da yamma tare da fatan alkhairi a gare mu baki daya. Abba na san ana iyakacin kokari akan iyali, ina kuma fatan Allah ya cigaba da jagora, sai dai a duk lokacin da ba'a kusa wani abu zai iya faruwa ba tare da an sani ba. Ina neman alfarmar a saka ido akan Jidda, tana shiga motar maza suna fita unguwa mara amfani, sannan kuma tana kula mutanen da bana kirki ba. Ina neman afuwa idan na shiga hurumin da ba nawa ba"

Wani bakin ciki da ya tsaya min a makogwarona shi ya sa na kasa magana, Umma ce ta fara rafka salati tana tafa hannu "karya yake yi Alhaji. Wannan yaro akwai makaryaci"

Abba ya daga mata hannu yana kallo na sannan yace "ina jin ki, zaki iya bayanin wadannan maganganun nasa?"

Na gyada kai da sauri sannan cikin nutsuwa nayi musu bayanin kawo ni gida da Diyam da mijinta suka yi min da kuma ganin mu da Umar yayi da Sadauki da abinda ya dauka. Sai kuma labarin babban abokin sa da yayi min magana dazu da yadda shi kuma yayi reacting har zuwa threats din sa.

Abba yace "to shi Umar din me yake yi a gurin? Tare kuka je da shi?" Na girgiza kaina da sauri "ban sani ba Abba. Maybe wani abun ne ya kai shi gurin maybe kuma tare suke tunda abokinsa ne"

Abba yayi shiru yana kallon gefe sannan yace "zanje gidan su gurin mahaifinsa inji dalilin da zai saka dan shi bashi da hali sai yake daukan kowa ma kamar irinsa ne. Zan nemi su ja masa kunne ya daina shiga lamuran ki idan kuma yaki ji sai mu dauki matakin hukuma akan sa. Shi kuma wancan abokin nasa kar ki sake tsayawa da shi idan kuma ya takura miki shima tabbas bai fi karfin hukuma ba"

Na yi murmushi ina jin dadin yardar da iyaye na suka yi da ni tare kuma da yiwa kaina alkawarin ba zan taba basu kunya ba.

Har nayi kokarin mikewa sai ya kuma dawo dani tare da kara yi min magana akan in yi kokarin fitar da miji inyi aure na in huta da irin wadannan abubuwan.

"Kishi ne ya ke yi. In ya ga kinyi aure dole ya hakura ya kara tabbatar wa cewa ba zaki koma masa ba"

Nayi

102 / 106