Chapter 23 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   23 / 106

66K to 69K   out of 316K words

gidan "Abba ya bawa yaya shamsu da yaya Aminu kudi zasu shiga kasuwanci da sunan sa, duk wata zasu ke kawo masa abinda aka samu na riba" na gyada kai cikin fahimta. Sai dai ina fatan bai yi mistake ba, saboda su din masu iyali ne kuma naji ance ba'a trusting namiji mai iyali da kudi, amma bance komai akan hakan ba dan bana son Farhan tayi min mummunar fassara.

Ni kuma na bata labarin yanuwan Umar da suka zo min ziyara da kuma zuwan mu gidan su. Ta matso kusa dani tana yi min rada "to wannan rashin lafiyar fa? Anya kuwa ta gaskiya ce?" Ta karasa tana kashe min ido, na dake ta a kafada ina dariya sai tace "dan Allah bani labari, ya kika ji? Da ciwo sosai" she looked concern sai na tuna da nima nawa tsoron.

Sai na girgiza mata kai, "ba irin ciwon da muke tunani bane ba fa, da ciwo dai amma ba sosai can ba. Ba irin wanda muke karantawa a novels bane ba, ba'a suma kuma ba'a wani fitar da jini kamar an yanka rago" mukayi dariya tare sannan ta kara matsowa "bani labari mana" na harare ta "ke zancen manya ne fa. Duk abinda kike so kiji zaki sani ne wata rana, duk kuma bayanin da zan miki ba zaki fahimta ba sai yazo kanki"

Ta tabe baki sai ta fara bani labarin irin damuwar da take ciki yan kwanakin nan da bana gida, kowa ya saka mata ido, dangi kowa zai tafi sai yace "ke yaushe ne naki bikin?" Ko kuma "saura ke, ai da an sani ma hada ku akayi aka huta" Abba kuma yakan ce "hada sun naso inyi ai, ita kuma taki fito da mijin"

Ta juya hannu, "ni makaranta ma nake so ya barni in shiga wallahi. Ga result dina yana da kyau, gashi bana komai a gida, ban san me yasa ba zai barni in yi karatu ba kafin Allah ya kawo mijin".

Sai nayi ta lalashinta da bata shawarar da nake ganin zata bulle mata "hakuri". Muka tashi muka gyara gurin muka tafi kitchen, tare da ita mukayi ta duba kitchen appliances din wadansu ma bamu san yadda ake amfani da su ba sai mu karanta manual, muna fitowa ta tambaye ni "amma dining table din nan ba Abba ne ya siya ba ko?" Nace "eh. Daddyn su Aira ne ya siya min a matsayin gudummawa" ta shafa shi "yayi kyau sosai".

Bayan mun zauna sai na tambayeta "Umar fita yayi ne?" Ta girgiza kai "kamar daki naga ya shiga" na mike da sauri "wayyo Allah. Yana can yana jin yunwa. Yanzu haka ko breakfast bai yi ba" ta bini da kallo "soyayya manja, na dauka ai da aka kar tsami kwarnafin ya kwanta" na harare ta "sai ma tashi da ya sake yi"

Har dare su Farhan suna nan, sun kawo min kayana da na bari a gida sannan suka bude lefena suka zabi abinda suke so, wasu na basu wasu kuma na hana su. Sai da muka ci abincin dare tare sannan Umar yace in dauko hijab dina mu kaisu gida. Ai kuwa har da rawar murna nayi zanga Umma ta tunda ban saka ran ganin ta kusa ba.

Muna zuwa gida na shiga da sauri na na rungume ta sannan na gaishe ta, itama tayi mamakin zuwa na kuma daga dukkan alama taji dadin ganin nawa dan sai bina take yi da kallo da murmushi a fuskar ta, yan samarin ta duk basa nan, sai na bada sakon lallai suma suje suga dakina. Ta saka ni na je na gaishe da Hajiya, ta amsa min babu yabo babu fallasa sannan tace "wannan wanne irin aure ne ko sati ba'a yi ba har an fara zarya a gida? Ko akwai wata matsala ne" na girgiza kaina kawai sannan nayi mata sallama na fita.

Na hau saman Abba da dokin son ganinsa amma ina shiga sai yace "ke! Me kike yi a gidan nan?" Na durkusa "Abba tare da.......tare da shi muka zo muka kawo su Amira" ya kama fada "su amiran basu da kafa ba zasu iya tahowa da kansu ba? Yaran yanxu kun dauki aure kamar wani wasan yara, ki tashi maza ki koma gidan ki kuma kar ki sake zuwa gidan nan idan ba da wani kwakwkwaran dalili ba"

Na mike jiki n a sanyaye, sai dana sauka sannan na tuna ko gaishe shi banyi ba. Ina shiga dakin Umma kafin in zauna ya leko ta baranda " Jidda? kin tafi ko har yanzu kina nan?" Na mike da sauri ina jin kwalla tana zuwa idona, Umma tace "kar kiyi, kar ki sake ki fita kina kina kuka. Ba kim gan mu ba sai menene kuma?" Na dauki jakata nayi mata sallama na fita kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki.

Ina fita waje Umar ya bini da kallo "har kin fito?" Na dauke kai na bance komai ba sai shima yayi shiru ya tayar da motar muka tafi gida.

Sati uku bayan bikin mu hutun Umar ya kare, kuma kusan a lokacin nima muka koma school na shiga shekara ta biyu. A cikin wadannan kwanakin ba soyewa ba in ma kone wa ne duk mun kone kan mu a gida, wannan yasa komawa aikin da school ya dan zame mana da wahala saboda sabawa da junan mu da muka yi.

Sai dai jin dadin mu shine hanyar mu daya, babu nisa tsakanin office dinsa da school dina dan haka tare mume fita ya ajiye ni shi kuma ya tafi, in na tashi ko bai gama ba kuma ya kan ajjiye aikin ya kaini gida sannan ya dawo, na nuna masa ya ke barina ina tafiya a adaidaita sahu amma yaki yarda. "Menene amfani na idan ban kai ki gida ba? Menene amfanin mota ta idan bata dauke ki ba? Da kin iya mota da sai in ke baki kina tafiya da ita, in yaso ni in na gama sai in nemi abin hawa"

That's the kind of person Umar is to me.......

Duk abinda nake so shi yake yi min, duk abinda ya fahimci ina so ko ban furta ba sai yayi min shi, duk abinda yayi tunanin zan so ko da bai ga alama a fuska ta ba sai yayi kokarin yayi min shi in da har bai fi karfin sa ba.

Gidan mu kullum a cike da kayan ciye ciye, tunda ya lura ina da kwadayi, besides ni nafi son kayan kwadayi ma akan solid abinci, dan haka kullum sai ya samu abinda zai siyo min, ko kuma ha dauke ni mu tafi yawon ciye ciye. Duk wani joint a kano da ake siyar da wani abin kwadayi mun san da zamanshi.

Watanni uku da auren mu ne akayi hutun yan makaranta. A lokacin ne kuma mukayi bakuwa. Ummi.

Ni tun zuwan mu gidan su naji suna zancen Ummi tana makaranta amma ban san wacece ita ba tunda ban taba jin sunan ta a bakin Umar ko a bakin Mufida ba. Sai gasu an kawo su tare da Afnan da Affan wai zasuyi mana hutu anan. Na tarye su sosai, yaran suna ta murna, itama kuma Ummin ta gaishe ni na kuma saka ta kai musu kayan su guest room.

Yarinya ce zan iya cewa kusan sa'ar Amira, koma Amira ta dan girme ta kadan dan ta gaya min a js3 take, Amira kuwa lokacin tana ss1. Abinda ya bani mamaki shine muna zaune tare da su a falo Umar ya shigo,sai kawai naga ta mije ta gudu taje ta rungume shi shi kuma har da dan daga ta sama kadan sannan ya ajiye ta yana dariya "ya naji kin kara nauyi? Me suke baku a school din?"

Sai daya ajiye ta sannan ya tari kannensa. Sai naji hakan bai yi min ba, ai ba karamar yarinya bace ba dan akwai nono a kirjinta dan haka zan iya kiranta da balagaggiya. A lokacin bansan menene alakar su ba shi yasa nayi shiru tukunna.

Daga baya ne Umar yake min bayanin ta "kanwar Aunty ce, tun tana karama Aunty take rikon ta har yanzu kuma a hannun ta take. She is like a sister to us" na gyada kai kawai amma a raina ina jin bana son ta duk kuwa da cewa bata yi min komai ba.

Sun kwana biyu anan, kullum in mun fita zamu barsu a gida kuma zan iya cewa tana taimaka min sosai da aikin gida dan kamar yadda take da shegen surutu haka take da aiki. Amma duk da haka zuciyata bata kwanta da ita ba sai dai ina iyakar kokari na wajen boye mata hakan. Sai kuma na fara tunanin ko kishi nake da ita shi yasa nake jin haushinta?

In dai har Umar yana gida to tana kusa da shi, ko magana zata yi masa sai ta rike hannunsa, ga shagwaba, magana daya ta fara yi masa shagwaba tana girgiza jiki shi kuma yana yi mata dariya.

And then ranar da suka yi sati da weekend na kwanta ina bacci da rana a dakina, na farka nayi sallah sai nace bara in duba Umar ko ya tashi yayi sallah shima dan ya riga ni kwanciya baccin ma.

Sai dai ina shiga dakinsa na gansu tare. Yana kashingide ya jingina bayansa da bed frame ita kuma tari ruf da ciki a tsakiyar gadon tana kada kafafuwa a sama da wayarsa a hannun ta da alama game take yi. Na tsaya a bakin kofar ina kallon su, zuciya ta a wuya na.

Ya dago kai yana kallona "Baby. Kin tashi" ya miko min hannu. Ban amsa ba kuma ban je ba sai bata rai da nayi. Yayi min sign da hannunsa "what?" Na kara hade rai nace "Ummi, ban wayar nan" sai ta juyo ta kalle ni sannan ta kalle shi shima tare da fara shagwaba.

Na jira in ji abinda zai ce sai naji yace "ki bata mana, ko baki ji abinda tace ba?" Maimakon ta mika min sai ta mika masa, ya karba ya miko min, ban karba ba nace mata "tashi ki je waje" ta zumbura baki tana kallon sa, and I half expected yace kar ta fita amma sai naji yayi shiru har ta tashi ta wuce ni ta fita tana kunkuni, nabi bayanta da kallo sannan na tura kofar.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Seventeen: The Visitors*

Ya ajiye wayar a gefe sannan ya nuna min kan cinyarsa, "come Baby, zo ki fada min waye ya taba min ke da tsakar ranar nan" na tafi naje na zauna a inda ya nuna min, na kwantar da kaina a kirjinsa sannan nace "wannan yarinyar, bai kama ta take shigowa dakin ka har ta kwanta akan gadon ka ba"

Ya dago da fuska ta yana kallona "wai Ummi? But why? She is like a sister........" Nace "like a sister, not a sister. Matsayin ta shine kanwar kishiyar Mama. Babu dangantaka ta jini ko kadan a tsakanin ku" sai yayi murmushi "kishi, kishi, kishi, I feel honored" na ture shi. "Ba kishi bane ba gaskiya ce. Dakina ko gadona duk zata iya shiga ta kwanta amma gadonka ba gurin zuwan ta bane ba. Ba ita ba ko su Mufida da kuke ciki daya dasu bai kamata su zo su kwanta akan gadon ka ba ko da ace baka dakin ballantana kuma kana nan sannan kai ma kana kwance akai"

Ya mayar da kaina kan kirjinsa ya kwantar "shikenan, sorry Baby, ba zata sake shigowa ba tunda ba kya so. In ba kya son ta zauna a gidan ma yanxu sai in kai ta gida tunda ba gidan ubanta bane ba" na dago kai "a'a ni bance ka mayar da ita gida ba, in nayi haka Aunty ba zataji dadi ba, kawai dai ina son boundary a tsakanin ku, bana son yadda kake bari tana taba ka a duk lokacin da tayi niyya dan kai ai ba muharramin ta bane ba kuma shaidan babu zuciyar da baya shiga even the purest of hearts"

Yace "Allahu Akbar. Ya ustaziyya Hauwa'u"

naga alamar wasa yake so ya mayar da maganar, na mike "eh naji ni ustaziyya ce. Ka tashi kayi sallah" na fada half hopping inji yace min yayi amma sai naga ya mike ya shiga toilet, na kalli agogo, almost three o'clock na rana amma bai yi azahar ba.

Ni a gidan mu na saba maza masallaci suke tafiya, in ba wani uzuri mai karfi ba da wahala ki ga wani yayi sallah a gida amma Umar sau da yawa a gida yake abarsa, a gidan ma wani lokacin sai nayi ta tuna masa musamman in yana wani abu sai yace sai ya gama.

Na danga chanji a lamarin sa da Ummi, ya kan cire hannun ta daga jikinsa in ta rike shi ko kuma ya matsa in ta zauna a jikin sa, sai kuma na lura gidan duk ya ishe ta duk tana ta kunci kwana biyu bayan nan ma tace tafiya zatayi gida.

Umar ya siyo mata doguwar riga da takalmi ni kuma na bata mayafi da kayan kwalliya muka kaita gida, amma sai twins suka ki zama suka ce  biyo mu zasuyi mu dawo gida.

Sai naga Mama ta bata rai "ku kun fiya rikici wallahi. Kawai dan kuje su saka su wahala ba kunyi kwana goma a can ba? Shi yana aiki ita tana karatu waye zai zauna daku a gida? Ita kuma Ummi da zata zauna daku din tace ba zata koma ba ya kuke so suyi daku?"

Na danyi murmushi "babu wahala ai Mama, gobe sunday bani da school shi   kadai ne zai fita, jibi kuma in zamu fita sai mu biyo mu ajiye su anan tunda hanyar mu ce"

Ta bata rai. "ba wani hanya, lokacin da zaku bata gurin shigowa da su ai yaci ace kunyi wani abun. Kuma keda ba ke ce mai driving ba ai ba ke ce zaki wahala ba"

Sai naja bakina nayi shiru amma bana jin dadin yadda yaran suka yi kamar zasuyi kuka. Ga Aunty tana Lagos a lokacin. Na daga kai na kalli Faruq da yake ta danne danne a waya kamar ma bai sannan maganar da ake yi ba. Na dan dungure shi da kafata. Ya kalle ni sai na marairaice masa. Ya juya ido sai kuma ya mike yana saka wayar aljihu yace "su taho mu tafi, monday din sai mu dawo dasu"

Muna tsaye a bakin gate muna jiran maigadi ya bude mana gate sai ga bakuwa munyi, Maryam kawata. Tun da ta doso motar take washe baki tana kara sauri, nima nayi mata murmushi sannan na daga mata hannu ina nuna wa Umar ita "ga Maryam nan, kawar mu ni da Mufida, ka gane ta?" Sai naga ya dauke kai kamar bai ganta ba sannan yace "eh" tana karasowa ga mamaki na sai naga ta zagaya ta window dinsa

"Yaya Doctor sannun ku da dawowa, ashe na kusa in daki gurbi na kusa in tarar ba kwa nan" sai naga ya nuna ni da yatsansa "kamar kinyi batan kai, ga kawar taki can" sannan sai ya daga mirror dinsa.

Sai naji a raina banji dadin abinda yayi mata ba, duk da ita ma rawar kanta yayi yawa ina ita ina zuwa window dinsa tayi masa magana in banda neman magana? Ni ce kawarta kamar yadda ya fada, guri na tazo dan haka ni ya kamata tayi wa magana.

Kafin ta zagayo window na mai gadi ya bude mana gate, Umar bai jira komai ba yaja mota ciki sannan yace da mai gadi ya rufe gate. Shi kuma mai gadi bai san tana waje ba kawai ya tura gate ya rufe.

Nayi sauri na bude kofa na fita sannan na tafi na bude mata karamar kofa. Na tarar ta hade rai kamar zata fashe "mijin ki dan wulakanci ne" na girgiza kai. "Kiyi hakuri kawata, wallahi bashi da wulakanci kawai dai ina jin a gajiye yake ne" na kama hannun ta "zo mu shiga ciki" ta zare hannun ta daga nawa "ni ba zan shiga ba ballantana ya kara wulakanta ni, sai anjima"

Ta zare hannun ta daga nawa ta tafi ranta a bace, sai naji banji dadi ba. Tabbas yayi mata wulakanci amma ai laifin ta ne rashin kamun kanta ne ya jawo mata. Kuma a ganina ai tunda gurina tazo babu ruwan ta da abinda Umar yayi mata musamman tunda na fito har waje na bata hakuri.

Na juya jiki a sanyaye na koma gida. A  palo na tarar dasu sun baje shi da twins yana raba musu abinda muka siyo a hanya. Na wuce su na dauko kayan su daga guest room na shiga dashi cikin bedroom dina, tunda Ummi ta tafi gwara su dawo kusa da mu.

Ina dakin ya shigo babu sallama kamar yadda ya saba sai kamshinsa ne ya sanar da ni shigowar sa. Ya tsaya a bayana ya zuro hannayensa ta cikina ya jani jikinsa, ya saka fuskar sa a wuya na yana goga min sajensa a fuskata. Na saka hannu na kare ina dariya "ka ga duk zaka min scratches a fuskata"

Yayi dariya "au haka ma zaki ce? To bara in miki scratches din abinda yafi fuska" ya juyo da ni yana goga fuskar sa a kirjina" na fara ja da baya ina dariya "wannan ai chakulkuli ne" yace "chakulkuli? Bara in nuna miki yadda ake chakulkuli" sai ya zura hannunsa a rigata ya fara yi min ni kuma ina dariya ina ture shi nace "ka daina, kaga bamu kadai bane a gidan, akwai yara"

Ya bata rai "in zasu takura min sai in mayar dasu gidan ubansu. Haka kawai ban ajiye ba ba za'a takura min ba" ya fada yana shafa mara ta "saura wata tara da kwana goma ki haifa min baby mai kama da ke" nayi murmushi "ni nafi son mai kama da kai. Kuma tun kafin a samu cikin har za'a fara lissafin ranar haihuwar sa?" Yace

23 / 106