Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
ya dauki takardar ya mike tsaye yana cewa da Mufida. "Gobe zamu fita, gobe zamu samo Jidda" ta mike itama tana kallon sa, "how do you know?" Yayi dan murmushin gefen baki "Allah yana sona. Yasmin ce ta kira ni dazu da wayar Jidda, tace suna gidan wata kawar Jidda mai suna Halima" Mufida ta bude baki cikin mamaki da farin ciki, sai ya dan daki cheek din ta kadan "goodnight sweet sister" daga nan ya fita ya koma dakin da yake zaune yanzu.
Ya ajiye takardar sai ya koma ya kwanta yana kallon ceiling, remembering the days da yake tare da iyalinsa, remembering yadda kullum da daddare suke cin dinner together sannan suyi wa yaran su wanka tare su kuma kwantar da su tare, sannan su tafi nasu dakin, remembering how kullum shi yake musu addu'ar bacci ya shafa a jikinsa sannan ya shafa mata, yadda mostly in yazo shafa matan yake mintsinin ta a gefen cikin ta, ita kuma tace sai ta rama shi kuma yaki barin ta ta rama din har a karshe su kama kokawa akan gadon, kokawar da most of the times leads to something else, something sweet, something unique. Later kuma sai tayi mitar cewa ya bata mata shimfidar gado tunda shi ya jawo shimfidar ta hargitse, then sai su tashi su gyara gadon tare kowa ya kama side din bedsheet daya su shimfida kowa kuma ya cuccusa side din sa, abinda suke gasa aga wanda zai riga gamawa, price din wanda ya riga gamawa shine pillow din da yafi laushi akan gadon, kusan kullum shi yake rigata gamawa saboda baya tsayawa ya cusa bedsheet din sosai, she will then accuse him of cheating amma sai yaki karbar laifinsa ya dauke pillow mai laushi ya bata mai tauri ita kuma tayi jifa dashi ta kwanta akan kirjinsa, nan ne pillow din ta.
Ya jawo pillow ya dora a kirjinsa tare da rungume wa da duk karfinsa yana jin kamar zai tsaga kirjinsa ya saka pillown a ciki ko zai cike mass emptiness din da yake ji a cikin zuciyarsa. It has been the toughest month of his life. Kuma cikin wata gudan nan ko kallon mace da sigar sha'awa bai yi ba, abinda ko a mafarki bai taba tunanin zai iya ba amma yanzu gashi involuntarily yayi, there are better things a mind dinsa than sex. Yayi loosing libido dinsa gabakidaya kamar ta hada da shi a cikin kayanta ta tafi dasu, maybe sai ta dawo zata dawo masa da shi, but then it will be only for her.
Yasan ba zai iya bacci ba, amma sai ya kwanta da pillow rungume a kirjinsa and his eyes closed yana replaying memories din su together, their bedroom memories, and hoping ina ma dai zata zo masa ko da a mafarki ne? That's in yayi baccin kenan.
Washegari da safe ya sanarwa da Baba da kuma Mama abinda ya faru, sun nuna jin dadin su sosai dan yanzu har ita kanta Maman da take jin haushin Jidda ta fara damuwa da rashin ganin nata, yayi ignoring Aunty da take zaune a gurin amma bata ce komai ba, yanajin haushin yadda tunda abin ya faru bata yi masa jaje ba.
Daga nan ya dauki Mufida suka kuma biya ta gidan Bashir suka dauke shi sannan suka fara zagaya duk gidan jen wadanda suka ware, but har suka gama basu samu wadda suke nema ba, suka zauna a wani restaurant suka ci abinci tare da dauko wadancan tsofaffin lists din suna adding more suspects suma suka sake bibiyarsu amma babu wadda tayi fitting characteristics din da suke nema, babu mai auren mai kudi mai zaune a gida mai kyau kuma at the same time take goyon twins. A karshe suka yanke shawarar su je gidan su Jidda su nemi taimakon Farhan, tafi kowa sanin Jidda tafi kowa sanin kawayen ta tun daga yarinta har zuwa yanzu.
A sitting room suka zauna, Farhan din ta gabatar musu da ruwa da lemo sannan suka sake bitar abinda Yasmin ta fada da kuma guraren da suka je so far.
Umar yace "da akwai something da muke missing, da akwai someone da babu a list din mu" ya kalli Farhan "ta yaya kika hada list din ki?" Tace "na rubuta friends din mu tun na kuruciya, na unguwa na islamiyya da kuma na cikin yan uwan mu" ya juya kan Mufida "ke kuma fa?" Tace "ni nayi using photo album din mu ne da akayi mana sanda zamu yi graduation a secondary school, duk wanda muka yi school tare tana ciki" ya dafe kansa "babu kuma wata Halima wadda ba'a saka a cikin album din ba? Wadda maybe baku gama school tare ba" and he saw some light come into her eyes, sai ta juya tana kallon Farhan wadda itama take kallon ta da budaddun ido, a tare suka fadi sunan da yazo kansu
"Halima kollere" ya zauna straight da sauri yana kallon su "Diyam" ya fada shi kuma, realising wadda suke nufi. Sai ya mike tsaye ya fara zagaya gurin yana magana da sauri "how can I even miss this? Tabbas ta na fadar sunan wannan halimar, tace sunyi jss tare sai aka cire ta aka yi mata aure".
Mufida tace "shi yasa ni ban san ta ba saboda sai a ss1 na shiga school din. Kuma har yau ban taba ganin ta ba ina dai ji sukan yi maganar ta da sauran kawayen mu" ya dawo ya zauna a gabanta "yanzu wa zaki nema a cikin kawayen ku wadda tasan wannan Diyam ɗin?" Without thinking twice tace "Ramla. I heard them talking about her ranar da muka yi reunion, ranar da Jidda suka yi fada da Maryam, naji Ramlan tana gayawa Jidda cewa ta hadu da Halima kollere har ta karbi number din ta, amma ta gaya mata zata yi tafiya zata bar kasar zata tafi karatu"
Umar yayi murmushi "gida mai kyau da swimming pool ya dace da masu zuwa kasar waje karatu" sai Bashir yace "call her Mufida, ki ra mana ita wannan Ramla din ki ji ko tana da labarin Diyam din? Ko ta san ta harfi twins? In ita ce ki nemar mana address din ta a gurin ta"
Mufida ta dauko wayarta ta nemo number din Ramla sannan ta kira, ba bata lokaci ta daga suka gaisa
"ya gida? Ya yara da baban yara?"
Tayi dariya "kar ki damu, nan ba da jimawa ba za'a kira ku ku shigar da ni daga ciki"
Umar yayi tsaki "abinda akace tayi daban abinda take yi daban"
A cigaba da wayar
"Dan Allah Ramla labari nake nema akan Diyam. Ta dawo Nigeria kuwa?"
"Okay kun hadu wancan watan? Ohh ta haihu kenan. Twins wow. Allah ya raya"
"Dan Allah ko kinsan gidan ta kuwa? Okay yi min kwatancen gidan auntyn tata sai inje in samu address din acan"
"Okay na gane, Nagode"
Sai ta katse wayar tana kallon su da murmushi a fuskar ta. Umar ya mike tsaye tare da daukan wayarsa yace "gotcha. Let's go"
Babu bata lokaci suka je gidan auntyn Diyam wadda suke kira da Mama kamar yadda Ramla ta kwatanta mata, suka yi packing a kofar gidan sai Umar ya juyo yana kallon Mufida da Farhan yace "ku shiga ciki and pretend ku kawayen Diyam ne da kuka yi taura science tare, kun jima kuna neman ta sai yanzu aka yi muku kwatancen nan gidan aka ce gidan auntyn ta ne, sai ku roke ta ta baku address din Diyam din kuna so ku kai mata surprise visit. Kar ku karbi phone number, address kuke so saboda kuna so ne kuyi surprising din ta. Got it?" Suka gyada kai a tare sannan suka fita.
A cikin gidan suka samu mama, tana zaune tana kallon shirin akushi da rufi a tashar Arewa 24 suka gaishe ta ta amsa cikin rashin fahimta sannan suka yi mata bayani kamar yadda Umar ya koya musu, tayi murmushi "ai kuwa zata ji dadin ganin ku dan duk ta rasa kawayen ta na taura" Mufida tayi murmushi "muma zamu ji dadin ganinta dan rabon mu da ita tun da aka cire ta aka ce anyi mata aure" Mama ta gyada kai tana kara yarda da cewa kawayen Diyam din ne amma kuma duk da haka sai tace "Allah sarki, ai mukan je mata visiting a lokacin da take can, ya ma sunan wannan principal din taku ta lokacin?" Direct Mufida tace "Hajiya Safiya Muhammad? Ai ta bar taura yanzu, sanda muka yi candy Hajiya Rabi ce PC" Mama ta gyada kai tana kara yarda dasu.
A lokacin wani saurayi ya shigo, su Farhan suka gaishe shi ya zauna yana kallon su da alamar tambaya sai mama ta gaya masa su waye da abinda ya kawo su, sai kuma tace "kun ci sa'a, dama yanzu nake shirin aiken Sadiq ya kai mata sakon daddawa da kuka da kubewar da tace in hada mata, da yake daga ita har mijinta babu abincin da suke kauna irin tuwo, bari in bashi sai ya tafi daku ya kai ku har gidan"
Suka kalli juna amma sai Farhan tace "ai bamu kadai muka zo ba, akwai driver yana waje. Kuma sai gobe muke son zuwa dan akwai wata da zamu tafi tare da ita"
Mufida ta gimtse dariyar da tazo mata tana hango reaction din Umar idan yaji an kira shi da driver. Sai wanda aka kira da Sadiq yace "babu komai. Sai a baku address din kawai" Mama ta mike tana cewa "basu to, ni ba iya kwatance nayi ba, bara in dauko maka sakon kayi maza ka kai mata" daga nan ta shiga ciki shi kuma wanda aka ce ya bada address sai ya dauko wayar sa ya mika wa Farhan yana murmushi "a bani number, sai in turo address din dan kar ku manta" ta karba ta saka masa number din ta tana kallon hoton sa da yake kan screen din sannan ta mika masa kan ta a kasa bata son ya fahimci hoton nasa ya tafi da ita. Mama ta fito da leda a hannunta ta bashi su kuma suka yi musu sallama suka fito.
Basu dade da shiga mota ba sakon address din ya shigo cikin wayar Farhan, ba tare da ta karanta ba tayi forwarding zuwa number din Umar, ya karanta a fili, a karshe address din an kara da
"Save my number please. The name is Sadiq"
Umar yayi tsaki Bashir kuma yayi dariya.
Farhan suka fara saukewa, ta fita ta tsaya tana kallon su sai Umar yace "mungode sosai Farhan, I am going to get her back to us" ta girgiza kai, ta jima dama tana son gaya masa magana amma matsayin sa na mijin Jidda yana yi mata shamaki, yanzu ta samu dama, tace "ban shiga maganar na taimaka saboda ina so Jidda ta koma gidan ka ba, na shiga maganar ne saboda ina son Jidda ta dawo gida, zabin komawa gidan ka ko akasin haka nata ne, personally ma ni bana son ta koma din. I know all about you. I know all about halin ka da yasa ta fito, na jima dama kuma ina gaya mata ta fito din"
Umar yaji wani irin bacin rai, matsayin da take da shi a gurin Jidda ne kadai ya hana shi fitowa ya wanke fuskarta da mari, amma sai Bashir ya zuciyo ya bude kofa zai fito, Umar yayi sauri ya rike hannunsa, Farhan ta juya idonta kansa sannan tace "what? Me zakayi? I know all about you too and I think it is a good riddance for your ex wife da ta rabu da kai"
Da kyar Umar ya lallashi Bashir ya shiga mota suka bar unguwar, amma suna fita titi yace ya sauke shi ya tafi gida da kansa ba saboda yayi zuciya, shima kuma Umar din ransa ya baci sosai da maganganun Farhan din musamman da ya kasance ta yi su ne a gaban Mufida, ta zubar masa da mutuncinsa a gaban kanwarsa. Sai yaji yana jin haushin Jidda da ta gaya wa Farhan halin da suke ciki, ita ta jawo masa wannan wulakancin, kuma ya tabbatar yanzu ma already ta gayawa that Diyam of a person.
Sai daya sauke Mufida a gida sannan yayi tracing address din da aka turo masa ya je har kofar gidan da yake tunanin shine inda matarsa da yayansa suke ciki a yanzu, yayi ta tambaya a unguwar yana so ya samu information akan gidan da masu gidan amma bai samu komai ba sai sunan mai gidan "Aliyu Umar Abatcha" sai ya juya ya koma gida tare da yanke shawarar zai dawo washegari, ya rasa dalilin da yasa ya kasa shiga gidan a lokacin duk kuwa da tabbatar wa da yayi cewa nan ne inda rabin rayuwar sa suke ciki.
Sai da ya koma gida yana wanka sannan ya fuskanci abinda ya hana shi shiga gidan, tsoro yake ji, tsoron haduwa da Jidda yake yi.
Ya tuna maganar da Bashir ya taba gaya masa cewa tsoron Jidda yake ji, yau ya kuma yarda da hakan amma kuma ba wai ita yake tsoro ba a'a maganganun da ya tabbatar zata gaya masa in sun hadu, ya tuna wadda ta gaya masa kafin ta tafi cewa ko akuya aka daurawa zani aka shafa wa jambaki in ya ganta sai ya bita.
Sannan kuma yana tsoron abinda zai biyo bayan haduwar ta su, yadda zasu kare da iyayen su, dole za'a zauna sharia in ta dawo, me zata gaya musu? Me zai gaya musu? Me zasu yi? Mai zaiyi?
Wannan yasa ko da gari ya waye din ma bai iya zuwa da sassafe ba duk kuwa da tsananin son ganin iyalin nasa da yake ji, ya dai tura mata sako cewa yana zuwa, amma zuwan is easier said than done.
Sai da rana tayi sosai sannan yaje. Kamar yadda dama tun jiya ya lura da gidan cewa akwai security, amma shi ba tsoron security din yake yi ba abin da yake tsoro yafi security din ban tsoro. Yayi horn a bakin gate din expecting za'a zo a bude masa gate amma sai yaga mai gadi ya leko yana tambayarshi waye shi kuma wa yake nema? Ya fito daga motar yana jin haushi, ya tsani introducing kansa musamman a gurin wanda yake ganin bai isa ba kamar mai gadi, dan haka yaki yi sai yace matarsa yake nema kuma ya tabbatar tana cikin gidan nan, sunan ta Jidda. Yana jin mai gadin ya kira waya cikin gidan ya sanar da zuwan sa sannan kuma ya miko masa wayar, yaji muryar Jidda sosai, kuma sosai jin muryar tata ya ratsa har zuwa inda bai yi tunanin rashinta ya je ba a jikinsa, yayi kokarin ta saurare shi amma ta ajiye wayar bayan ta gaya masa magana kamar yadda yayi tsammani.
Wannan ya fusata shi, ya za'a yi shida matarsa da kuma ƴaƴan sa amma wasu banzaye da bai ma san ko su waye ba su saka wani katon gate a tsakanin su? Yayi kokarin yi wa maigadin bayanin cewa matarsa ce fa, amma yaki bude masa yace sai dai idan masu gidan sun ce a bude masa ko kuma ita matar ta sa ta fito ta same shi a waje, amma shi ba zai bude masa gate ba, daga haka ya rufe yar karamar tagar da ya leko yayi masa maganar ta ciki.
Wannan ya kara sa bata masa rai ya yayi bala'i iyakacin bala'i amma babu ma wanda ya kula shi. Yayi nadamar da bai taho da Bashir ba, amma kuma zuwa da Bashir zai kara dagula tsakanin sa da Jidda ne in ta gansu tare, but ai akwai hukuma, akwai hukumar da zasu saka dole a bude gate din nan kuma a fito masa da matarsa da yayansa.
Wannan yasa ya juya zuwa nearest police station kuma ya fadi bukatar sa ta a bashi police ga wasu can sun rufe iyalinsa a gida sun ki fito da su sun kuma hana shi shiga gurin su.
Babu bata lokaci aka bashi police guda biyu ya tafi dasu, suna zuwa gidan suka sake yin horn mai gadi ya sake lekowa ta karamar tagar sa, police din suka je gurin sa suka yi magana, jin babu alamar za'a bude gate din ya saka Umar ya fita dan yaji mai suke cewa "har yanzu ba za'a bude ba? Har yanzu ba za'a bani iyali na ba? Ga police nan ku bude musu su shiga su bincika, suna ciki matata da yayana"
Aka bude kofa karama sai wadansu securities guda biyu suka fito suka gaisa da police din sannan suka tambaye su abinda suke bukata su kuma suka maimaita abinda Umar ya gaya musu "muna so mu shiga mu duba gidan dan mu tabbatar ba sa ciki din" security din yace "babu damuwa, amma muna bukatar ganin ID cards din ku da kuma search warrant signed by a judge, cewa an baku damar shiga kuyi searching gidan" police din farko suka fara hayaniya, basu da search warrant din kuma suna so su nuna power din su, amma kuma daga jin sunan mai gidan sai Umar yaga jikin su yayi sanyi sun fara shafa kai suna ja da baya
Umar ya sake zuciya "what? Ba zaku shiga ba? Ba kune hukuma ba" suka fara jan sa gefe "yallabai kayi hakuri, in muka shiga gidan nan mune a ruwa, muje station yanzu ka rubuta statement sai mu aika da maganar sama......" Ya karbe hannunsa da karfi sannan ya juya zuwa motarsa a zuciye ya shiga sannan ya nuna police din da yatsansa "kwa mayar da kanku zuwa inda na dauko ku" sai ya ci taya da karfi ya bar kofar gidan.
Ransa a tsananin bace yake driving, shi ba'a taba wulakanta shi irin yau ba kuma shima ai da gatansa ba wai zauna gari banza bane ba. Zai sake dawowa ne kuma a yau ba gobe ba, amma da shirinsa zai dawo, ya dauko wayarsa ya fara neman number din Baba, tabbas Baba zai san wani wanda yake a sama wanda zai saka lallai a bude wannan katon gate din. Sai dai yana cikin neman number din sai ga kira ya