Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
dina in dai har na fita daga gida kamar na bar su a gidan ne bani da wani tension in na zama busy sosai har mantawa nake yi da cewa mijina yana da wani problem. Bani da wani lissafin inda yake ko abinda yake yi. Farhan har cewa tayi nayi kiba wai, kuma na zama less moody, more focused.
Zuwa aikina bai hana min sauke duk wasu hakkokin Umar ba, musamman na shimfida, kula da gida ma da girki da sauransu ina iyakacin kokari na duk da ba zan ce kamar kafin in fara aiki ba, amma kasancewar bama zama sosai a gidan sai ya rage aikin gidan sosai.
Bayan wani lokaci ne Asad ya fara rashin lafiya, mura mai tsanani da zazzabi, kwanan mu biyu a asibiti kafin ya samu sauki a sallamo shi ya dawo gida.
Bayan mun dawo gida ne Mama tazo gidan tare da wata yar budurwar yarinya. Umar yana nan, nima ina nan, muka gaishe ta ta amsa mana ciki ciki sai tace yarinyar ta fita waje ta jirata sannan ta dauki Asad tana yi masa sannu shi kuma ya langwabe mata yana ta mata complain din bashi da lafiya duk kuwa da cewa ya warke.
Ta kama fada "ba dole kayi ciwo ba Asad tunda iyayenka basu dauki rayuwar ka da muhimmanci ba, ai suna sane, sun sani sarai cewa ba lafiya ce ta ishe ka ba amma uwarka ta tsiri wani zuwa gurin aiki na banza da wofi, dan tana ganin tafi karfin a hana ta abu in tayi niyyar yi, tun sanda tace zata fara aikin sai da na kira ka ai nayi maka maganar bana son aikin nan da zata fara" ta fada tana addressing Umar, "amma saboda kafi girmama maganar ta akan tawa sai ka saka kafa kayi ball da maganar tawa ka nuna ai babu komai ai waye waye, ga shi nan zata yi maka asarar Da ai, duk da nasan ko mutuwa yayi ma ba dai na zuwa aikin zata yi ba tunda ta riga ta saka kanta, bayan babu abinda aka rage ta da shi".
Umar yace "Mama please now, menene hadin aikin ta kuma da rashin lafiyar Asad, ba fa dashi take zuwa office din ba ballantana ya dauki kwayoyin cuta a can ko wani abu" tace "rufe min baki, sallamamme, ko yawon da take yi dashi kullum a mota ba zai saka masa ciwo ba? Ko gidan nasu da take kai shi kasan abinda yake ci ko sha acan?" Umar ya dafe kansa "Mama" ta nuna shi "kar ka sake kiran sunana. Wallahi a kirji na nake jinka Umar kar ka bari in amayoka, kai ba ka ganin laifin matarka kuma baka so wani ya gane maka, ta shanye ka tas babu abinda yayi saura sai fanko. Bata so kowa ya rabe ka sai ita kadai, bata son kowa ya more ka sai ita kadai. To wallahi baki isa ba" ta fada tana nuna ni "na gaya miki ranar nan kuma zan sake gaya miki wannan yaron da kike gani wanda kika aura bayan ya riga ya zama mutum ba ki san wahalar da nasha da shi ba kafin ya zama mutum, shi kadai Allah ya bani a matsayin da namiji dan haka sama ta ka ba zaki zo ki karbe shi ki raba shi da kowa ba. Dole inyi magana kuma dole a bita a gidan nan. Ga yarinya nan..... Sunan ta Asabe, yar Malam Musa ce (maigadin su), ni na roke shi ya bani ita saboda na yaba da hankalin ta gata nan na kawo muku zata ke zama da yara a gida ba za'a ke watangaririya da su ba. Sai ki zaba, ko ki bar aiki ko kuma ku dauki yar aiki. Zabi ya rage ya naki amma dole cikin biyu zaki dauki daya" ta mike tsaye sannan ta nuna shi tace "saura kuma ta saka ka ka kore ta kamar yadda ta saka ka kori yan uwanka kwanan baya, saboda tsabar kishin bata son kowa ya rabe ka sai ita kadai"
Ta ajiye Asad ta fita da sauri shi kuma ya mike ya bi ta a baya.
Na bisu da kallo sannan na dawo da hankali na kan yatsun hannuna ina kalla, ba wai dan suna burge ni ba sai dan ina son in rike hawayen da yake neman zubo min.
Tabbas bana son yar aiki, tun ina amarya bana son yan aiki, ina kallon su a matsayin kazamai kuma in na var musu gidana zasu yi kin kazanta, ni kuma babban abinda na tsana shine kazanta. But then ina son aikina, dan ina jin tun da muka fara samun matsala da Umar ban taba jin peace irin wanda nake ji yanzu da na samu abinyi ba. Bana jin zan iya barin aikina gaskiya.
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, in baki siya ba kar ki karanta, in kin siya kuma kar kiyi sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Limit*
*Masu karanta littafin nan ba tare da kun siya ba, ina tuna muku da cewa na siyarwa ne. Lokaci na da kwakwalwa ta da data ta da nayi amfani dasu gurin hada labarin nan, rubuta shi, typing da kuma posting na siyarwa ne, idan kuma baki biya ni a duniya da kudi ba tabbas zaki biya ni a lahira da sallar ki da azumin ki*
Ina na zaune har ya dawo, ya zo zauna a kusa dani "am sorry Jidda...." Nayi saurin katse masa magana "don't be. It is okay. Mama ta fadi abinda yake ranta ne kuma ni ko menene zata fada bazan taba mayar mata ba saboda kamar Umma nake ganin ta, nasan kuma ta so ni farkon auren mu yanzu ne dai ta kasa fahimta ta, ina kuma saka ran watarana zata fahimci cewa ni da ita are on the same side" sai na mike na leka waje na kira yarinyar, ta shigo na tsaya ina kare mata kallo ina jin raina yana baci ina tambayar kaina anya kuwa zan iya barin yayana a hannun wannan kazamar?
Daga inda take tsaye ina jin warin da yake tasowa daga jikinta, ko dai in ajiye aikin ne? Na girgiza kaina da sauri, gaskiya ba zan iya ba.
Na zauna na sake tambayarta sunan ta tace "Asabe" na gyada kaina "ina kayan ki suke?" Tace "suna waje" sai nace taje ta dauko.
Umar yace "ina za'a saka ta?" Nace "dakin yara mana, ina kake tunani?" Ya girgiza kai "no way, in tana da wani ciwo fa ko wani parasite a jikin ta wanda zasu iya dauka" nayi dariya "gyara ta zamu yi ai, in ma tana da ciwo ba gidan likitoci ta shigo ba? Sai ayi mata magani" ya sake girgiza kai "uhm uhm, ba dakin yayana ba gaskiya" cikin gatse nace masa "to ina zataje? Dakina?" Yace "definitely no" sai yayi shiru yana tunani sannan yace "a gyara mata store din can tunda ba amfani ake yi da shi ba"
Babu yadda banyi da Umar ba kar a ajiye yarinyar nan a store amma yaki yarda, na nuna masa cewa dakin yaran ai ba a can suke kwana ba amma still yaki yarda, haka ya kira mai gadi suka fitar da kayan da suke store, ni kuma na saka Asabe ta fitar da jakar kayanta waje na bata sabulu ta sake wanke su ta shanya a rana, na saka mata ƙaramar katifa a store din na bata bedsheet da pillow sannan na kawo mata standing fan din dakin Umar, yayi ta mita nayi kamar ban ji shi ba dan babu fanka a store din kuma ga taga karama ni kuma ba zan iya barinta ta kwana a haka ba ina ganin akwai cin zali a ciki.
Sai da muka sake wani rigimar da Umar, yace wai sai dai take fita toilet din mai gadi ni kuma nace gaskiya ba zata je ba, tana mace ba zata ke fita waje tana shiga toilet din maza ba gwara ta shiga na dakin yara, shine har da jan yaran gefe da ja musu kunne wai kar su shiga toilet din dakin su zasu dauki cuta, in suna son shiga toilet su taho dakina ko nasa
A haka zaman Asabe da mu ya fara, Umar ya takura mata sosai, ni har tausayi take bani a lokacin, bata da damar ko da giftawa ta hanyar da yake, in dai yana gida to tana dakinta ko kuma dan filin da muke dashi a baya, nan ne ya koma gurin zamanta, ko a kitchen ya ganta sai yayi mata bala'i, sai da ya saka na ware mata cup da plate da spoon tare da rokon dan Allah kar inke barinta tana taba mana namu.
A nawa bangaren ni kuma duk da tsantsani na haka na dage gurin gyaran yarinyar nan dan dai kawai in iya zama da ita kamar yadda mahaifiyar sa ta bukata, na bata toiletries kuma na koya mata amfani da su, na koya mata amfani da water system dan bata iya ba, sannan na jaddada mata yin amfani da sabulu in ta gama using toilet da fatan hakan zai rage mata warin da take yi. Har turare na bata, roll on da na kaya masu dan karfi da zasuyi overcoming warin jikinta. Sannan na debi kayana na bawa wani tailor a bakin layin mu ya rage mata su na bata na cire wadanda suka zama tsumma a cikin nata, na siya mata pants da bra guda bibbiyu na ja mata kunne akan take chanjawa akai akai tana wankewa.
Kullum sau biyu nake matsanta mata tayi wanka kuma ta wanke bakin ta da har bana so tayi magana a kusa da ni saboda warin da yake yi.
A hankali a hankali ta fara dawowa mutum, sai na fara koya mata aikin gida kamar shara da wanke wanke da moping, iyakacin falo da kitchen da dakin yara dan ko corridor din da dakunan mu suke bana barinta ta shiga ballantana ta shiga daki na ko na Umar, in Umar yana nan kuwa ko falo bata zama, tana yin aikin ina gani kuma ina gyara mata har ta koya duk da dai ba kamar in ni nayi da kaina ba amma ina barinta tayi musamman in ina sauri.
A hankali sai na fahimci bata da matsala, tana da son yara sosai kuma tana son su Yasmin duk da dai Yasmin ko kallo bata ishe ta ba, Asad ne mutumin ta kullum yana gurinta yana yi mata surutu ita kuma tana biye masa suyi tayi suna dariya, kun san ance mai da wawa, sai naji nima ta kwanta min arai, na kuma cigaba da kyautata mata a hankali har na fara barin mata yaran a hannun ta sannan na siya mata yar karamar waya na kuma koya mata yadda zata ke amfani da ita na saka mata number ta nace in bana nan in suna bukata ta sai da kira ni, nima kuma sai nake kiran su akai akai inajin yadda suke ciki.
Kullum idan morning duty ne dani zan fita da Yasmin, ita kuma ita zata je ta dauko ta a Napep sannan su ci abincin da nake dafawa in ajiye musu sannan su shirya su tafi islamiyya tare, ita ma na saka ta tare da Asad, in evening ne dani haka zasu dawo su zauna su jira ni in dawo, in morning ne kuma usually kafin su tafi islamiyya ma na dawo.
A bangaren Umar har yanzu muna nan, tun case din Mammy bamu sake yin wani case da shi ba kuma ban taba gani ko jin wani abu da zai sa inyi tunanin bai daina ba, amma na rasa dalilin da yasa deep inside me nake ganin bai daina din ba, ko dan ya saba yi min alkawarin ya daina kuma yazo ya sake? Ko wannan ne dalili? Ko kuma wani dalilin ne daban?
Amma ban taba nuna masa ina tunanin bai daina din ba, na cigaba da kokarin kyautata masa da kuma kai kuka na ga Allah da rokon kar ya sake maimaita mana abin daya faru a baya, dan na sani, na riga nayi wa kaina alkawari cewa next case da zamuyi da Umar, that's in muka yi kenan, is going to be our last dan na gama zama dashi ko da kuwa shine autan maza, ko da kuwa zan ke kwana a gefen titi ne.
Umar ya sayi wata motar ko ince Baba ya siya masa wata motar, da tawa muke sharing, da yayi sabuwar luma most of the times tawa yake hawa yabar min ta sa. Sai dai in na riga shi fita ne sai in dauki tawa in bar masa ta sa.
Ina jin dadin aikina sosai, bayan debe min kewa da keeping dina busy da yake yi ga kudade da suke shigowa aljihuna. Kuma kudaden da dan kaurin su babu laifi, kuma gashi Umar bai rage komai na daga abinda yake yi min ba, bai kuma taba neman inyi masa wani abu da kudina ba, abinda nake yi da kudin kawai shine taimakon iyayena, dan da gaske yanzu Abba yana cikin matsala dan yan kudin nasa da ya bawa yayansa su juya masa sun cinye, yanzu gidan mu ya zama sai dai wannan ya kawo shinkafa wancan ya kawo taliya, kuma duk da haka fama ake yi kowa a cikin mazan yana complain cewa yana da iyali shima, matan kuma duk babu wadda Abba ya tsayawa tayi karatu sai ni dana samu Umar ya barni, dan haka tunda na fara aikin nake siyan kayan abinci ina kaiwa, sannan kuma in bawa Umma kudi itama ko zata bukaci wani abu duk da dai yaya Tahir yana iyakacin kokarin sa na daukar dawainiyar ta, Abbah ma ya fara neman kudi yanzu yana dan samun na kashewa. Amira kuma Umar ne ya nema mata school sannan ya dauki nauyin kudin makarantar ta har kudin kashewa yake bata saboda transport da sauran tsarabe tsaraben karatu. Wannan ne ya kara kafa gwamnatin sa a gurin Umma.
A lokacin ne akayi bikin yaya Jamila, Finally Allah ya nufa lokaci yayi ta samu miji matansa biyu da yaya shida, amma gidan ta daban ya samar mata ga kuma aikinta tana yi, dan haka duk bamu damu da kasanewar sa mai iyali ba sai fatan Allah ya basu zaman lafiya ya hada kawunan su.
A bikin sai na zama tamkar wata tauraruwa a cikin sauran yan'uwa, kowa kallo na yake yi, Umar ya kashe kudi wajen siya min suttura mai tsada wadda zan shiga biki da ita, sannan a gurin bikin bini bini ya kira ni wai ya nake? Babu problem? Har tsokana ta matan gurin suka fara yi daga anji karar wayata za'a ce gashi nan ya kira, wai battery dinsa yayi low ya kira in masa recharging, ni kuma sai inyi dariya kawai, sai kuma aka dauko hirar matsalolin aure kowa tana fadar nata, wannan tace masifa ne da mijin ta waccan tace kulle, waccan tace rashin kulawa, da yawa kuma matsalar su rashin nuna soyayya, ni kuma sai nayi shiru kawai ina bin su da kallo dan babu abinda zan iya cewa a cikin hirar tasu, to ince me? In ce ni nawa mijin neman mata yake yi a ciki harda yar mu Mammy? Ko kuma ince ita kanta amaryar da ake bikin ta mijina ya taba kwanciya da ita?
Yaya Hudallah ta kalle ni "Jidda fa? Ke baki da wata matsala ko?" Na danyi murmushi "babu wanda bashi da matsala yaya, but all I can say is alhamdulillah"
Suka yi dariya "baki da matsalar kenan ai yarinya, da kina da ita sanda zaki fada ma babu wanda zai tambaye ki, ko a jikin ki ko a gidan ki da sai an gani" sai suka fara hira ta, kowa tana fadin albarkacin bakin ta akan abinda taji ko ta gani na irin kulawar da mijina yake bani.
Sai na tashi kawai na bar gurin, bana son hirar tayi nisa har in fadi abinda zanyi regretting nan gaba. Sai na koma gurin yammata na zauna tare da Farhan hoping zanji dadi amma sai ta dauko min hirar nata problem din
"Jidda ni ina jin duk wanda yazo neman aure na kawai zance masa ya fito ne, ke ni bani da zabi fa yanzu, ko mai matan ne irin na yaya Jamila Allah auren sa zanyi" nayi dariya "zabin Allah dai Farhan. Duk gaggawar ki ba zaki yi aure ba sai lokacin auren ki yayi, kuma duk saurin ki mijinki dai zaki aura ba zaki auri mijin wata ba, ko kince ya fito in dai ba shine mijinki ba to ba zai fito din ba, ko kuma in ya fito din ma sai anzo daurin aure a fasa, mijinki yana nan somewhere, zai fito da kansa insha Allah"
ta fara bubbuga hannu "to yayi sauri ya zo mana me yake jira, ko so yake sai al'umma sun cinye ni da raina? ni da nasan inda yake da naje na kirawo shi" nayi dariya "lokaci Farhan, lokaci yake jira. Sai kiga yazo kunyi auren ku kun zauna lafiya har mutuwa, It is better to marry late than to marry wrong" na fada ina jin wani iri a zuciyata. Ko wa yana kallon na kamar nafi kowa dacen miji, ni kuwa ni kadai nasan what I am going through.
Wannan bikin ma na gayyaci yan uwan Umar, kuma kamar wancan Mufida ce kawai da yaya Mubaraka suka zo min kuma ban damu ba, yaya Mubaraka sharp sharp tazota tafi wai tana da wani bikin, Mufida ce muka zauna tare har aka kai amarya sannan na kwashi bataliya ta muka tafi gida tare da ita. Tace a gidana zata kwana sai da safe zata koma gida.
Da safiyar ne tana toilet dina tana wanka ni kuma na shigo neman chanji zan aiki mai gadi sai na dauki handbag dinta ina dubawa ko zan samu, and then I