Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
like ita ta kawo kanta da kanta.
But why?
Dukan Bashir din yake yi kamar Allah ne ya aiko shi. Duk da cewa Bashir din yana ta kokarin kare kansa da kuma rama wa amma kasancewar Umar din a kufule yake a kuma rikice, sannan kuma kirarsu dama ba daya bace ba, wannan ya saka cikin kankanin lokaci Bashir ya ji jiki a hannun Umar.
Ganin hakoran Bashir din basu da niyyar fita ne ya saka Umar ya sunkuya ya dauki piece din mirror a kasa da niyyar yiwa Bashir zane a fuskar sa, in bai zubar masa da hakora ba tabbas zaiyi masa zanen da zai ke gani kullum yana tuna abinda yayi, yana tuna cin amanar da yayi, amma dama anya kuwa akwai amana a tsakanin su?
A lokacin ne Mufida taci nasarar zura doguwar rigar da tazo da ita a jikinta sannan nayi sauri ta rike hannun Umar fuskar ta cike da tsoro matsananci, bata san wanne ne yafi tashin hankali a cikin abubuwan da suke faruwa ba. Kamata da umarta mahaifiya tayi tana aikata alfasha da abokin yayanta ko kuma kamatan da yayan nata shima yayi? Ko kuma halin da Maman ta ke ciki a yanzu wanda bata tabbatar ba ma ko tana da rai ko akasin haka, ko kuma kisan kan da yayan nata yake kokarin yi.
Tayi saurin rike hannun Umar, duk sauran abubuwan sun riga sun faru babu yadda zatayi ta chanja su amma zata iya kokarin hana wannan,
"yaya Doctor!" Ta kira shi da karfi yadda zai ji, ya juyo yana kallon ta da wani irin yanayi daya razanata ya saka ta saki hannun nasa, sai kuma ya yar da mirror din sannan ya kifa mata maruka guda biyu a jere kuma duk a kunci daya. Karfin marin ya saka ta durkushe a gurin hannunta biyu rike sa kuncin da ta tabbatar sai ya samu nakasu, ko dai kunnen ta ko idonta wani sai ya nakasa a ciki. Ya saka kafa yayi ball da ita ta bugu da jikin bango. Ta daga kafa zai sake dukanta sai kuma ya tambayi kansa, was it really entirely her fault?
Sai ya tsallake ta da sauri ya tafi gurin Mama, Maman da baya jin har duniya ta tashi zai kuma iya sake hada ido da ita. Amma kuma a yanzu so yake yi yaga ta bude idonta, ko da bata kalle shi ba so yake yi ya ga ta bude idonta ta kuma yi magana ko da ba dashi zata yi maganar ba.
"Mama" ya fadi sunanta cikin murya mai kama da kuka amma ba kukan bane ba, wannan muryar tafi kukan zafi tafi kukan ciwo a zuciya.
"Mamana!" Ya sake fada cikin yanayi na tashin hankali saboda jin da yayi babu alamar motsi a tare da ita. Shikenan ta faru ta kare, shikenan ya rasa mahaifiyarsa a sakamakon mummunar dabiar sa, shikenan kallon da tayi masa na karshe shine mafi munin kallo da ta taba yi a rayuwarta.
Yana kokarin daga ta Mufida ta zo tana jijjiga ta ita ma tana kuka da fuskar ta da already ta kumbure. "Wayyo Allah na shiga uku. Mama dan Allah ki tashi"
Umar ya lissafa kalmar shiga uku da ta fada, anya kuwa shi ba tara ya shiga ba? In da akwai shiga tara sai tara to duk ya shiga. Kuma a sanadiyyar abi daya. A sanadiyyar zina. Wannan kuma a duniya ne. A duniyar ma kuma ya tabbatar Allah is not done with him yet. Ballantana kuma in anje lahira.
Tunanin zuwa lahira ya saka wani irin tsoro a tsirga masa tun daga kwakwalwar sa har zuwa kafafuwan sa, yaji ya kasa daga Maman da yake kokarin dagawa saboda yadda guiwowin sa suka sage babu karfi bakinsa kuma ya bushe. Da kyar ya daga ta ya fita da ita da sauri ya saka ta a motar sa da take baya a zuciyarsa yana tuno da cewa exactly a week ago ya dauki Baba shima ya saka shi a motarsa a irin wannan yanayin, kuma duk akan abu daya, duk akan sa, duk saboda zina.
Har zai kunna motar sai kuma ya fahimci cewa babu riga a jikinsa sai ya koma cikin gidan da sauri, a falo yaga yarinyar da yazo da ita, yarinyar da ko sunan ta bai sani ba, tana tsaye da yar fingilgilar rigarta a jikinta ta rike kugu, a kofar daya dakin kuma mufida ce tana ta sheshshekar kuka. And it hurt him to see them together, to know they are here for the same thing, yadda ya dauko yarinyar daga gidan baban ta dan ta biya masa bukata haka Bashir ya dauko mufida daga gidan Baba, gidan Baban sa, dan ta biya masa bukata.
Ya wuce su ya dauko rigar sa a dakin ya saka sannan ya juyo da sauri zai koma motarsa sai yarinyar ta rike rigar ta sa "ina zaka tafi baka bani kudina ba?"
Ya rintse idonsa yana jin bacin ransa yana ninkuwa especially da yayi realising a gaban Mufida ne. "Wallahi ka bani kudina ko in tara maka jama'a a gidan nan dama ai an gaya min cewa makon kudi ne da kai shi yasa naso ka bani tun kafin a fara amma kace min wai babu matsala ga matsalar nan ai na gani da ido na, ni ba da kudi ba ni va da satisfaction ba"
Mufida ta tsaya tana kallon su, kudin menene yayanta zai bawa wannan matar mai kama da karuwai, amma kuma dakin dara fito daga ciki nan ya shiga ya dauko rigarsa, ma'ana daga nan ya fito babu riga kenan, ma'ana..........
"Wallahi ba zan cika ka ba na gaya maka sai kabani kudina, ba Mama zaka kira ba ko Baba ne sai ka sallame ni ko kuma su wadanda kake kira din su sallame ni tunda su suka haife ka bani ba ballantana in dauki asara"
Ya juyo a zuciye da niyyar itama ya daki ya daki banza amma kuma har ya daga hannun sa sai kuma ya sauke a ransa yana tambayar kansa menene laifin ta? Me tayi masa da zai dake ta? Tabbas duk da kasancewar ta karuwa in ya dake ta yana da alhakin ta kuma Allah ba zai yafe masa ba harcsai ya nemi gafarar ta ita kuma ta yafe masa, shi kuma a yanzu baya fatan abinda zai sake sakawa su hada hanya shi da ita ma ballantana suyi magana.
Ya fara kokarin controlling kansa sannan ya dauko wayarsa yace "fado account number" ta sake cakumar rigarsa. "Kutumar uba, ni zaka yiwa bura uba? Wallahi dama limcy tace min ranar nan da ka dauke ta kace babu cash sai dai kayi mata transfer, har yau transfer din bata zo ba, to wallahi in ita ta kyale ni ba zan kyale ba, wallahi sai na ............"
Murya suka ji daga bayan su.. muryar Mufida..,
"Nawa ne kudin naki?"
Ya rufe idonsa yana jin tamkar rufin dakin ne ya fado masa aka, yana jin ta tana gayawa Mufida sannan yaji alamar lissafin kudi sannan kuma yaji ta saki rigarsa, bai juya ya kalle ta ba ballantana Mufida ya fita yana jin cewa ita ma mufidan ba zai kuma iya kallon idonta ba.
Ya shiga cikin motar tare da juya wa baya inda ya kwantar da Mama yayi checking pulse dinta da yake jin sa can ciki, ya dauke idonsa daga kanta yana tunanin duk duniya babu uwar da bata yi dacen da ba kamar ta, duk duniya babu dan da ya ci mutuncin uwarsa kamar shi. Duk duniya babu wanda yayi asarar rayuwa kamar yadda yayi asarar ta sa.
Ta dauko key din motar yana kokarin kunna ta amma karkarwar da hannun sa yake yi ya saka key din faduwarsa biyu kafin ya samu ya shiga jikin motar. Sai kuma yaji an bude bayan motar an shiga, ya juya suka hada ido da Mufida sai yayi sauri ya juyar da kansa tare da tayar da motar.
Mufida ta jawo Mama ta rungume ta tana sheshshekar kuka, shima Umar din kukan yake so yayi amma ya kasa, burinsa a lokacin shine ya kai mahaifiyarsa asibiti mafi kusa wanda za'a bata taimakon gaggawa. A haka suka fita daga gidan, fitar da Umar ya tabbatar har cikin zuciyarsa ita ce fitar sa ta karshe daga gidan gonar, baya jin zai kuma bin koda hanyar gidan gonar ne ballantana ya kuma shiga ciki, sai dai ya sani cewa ba zai taba goge memories din mummunar rayuwar sa a gidan ba.
Ya gyara mirror din motar yana kallon Mama ta ciki, a ransa yana fatan zata samu wani problem da zai goge mata abinda ta gani daga kwakwalwar ta dan ya tabbatar bayan abinda ta gani rayuwarta ba zata taba dawowa dai dai ba, kuma duk a dalilin sa.
Asibitin da ya kai Baba yau ma nan suka je, yayi packing sannan ya fita da sauri, ko minti biyu ba'a yi ba suka dawo tare da nurses da kuma kujerar tura marar lafiya, suka fito da Mama da alokacin ta fara dawowa hayyacin ta suka tura ta zuwa ciki, Mufida ta bisu a baya hesitantly tana waigen Umar tana fatan shima zai taho tare da su amma sai taga ya tsaya a jikin motar sa yana bin su da kallo har suka shige ciki, ya runtse idonsa tare da dafe kansa da hannu biyu, a ransa yana jin wannan shine gani na karshe da zai yiwa mahaifiyarsa da kuma yaruwarsa, baya jin zai iya sake hada ido da su ko kuma duk wani wanda ya shafe su.
Ya bude mota ya shiga sannan ya sake kokarin tayar da motar amma ya kasa, abinda ya faru ne kawai yake ta replaying kansa a cikin kwakwalwar sa, ya girgiza kansa yafi sau a kirga amma kuma ya kasa kawar da hoton abin a zuciyarsa. Gashi nan a kwance a saman mace, Maman sa kuma a tsaye a gabansu idonta a kansu. Anya kuwa akwai wanda ya taba shiga irin halin sa ya ke ciki? Anya kuwa akwai masifar da tafi wannan muni?
Da yasan abinda zai faru kenan da baiyi ba, to wai ma me ya saka shi yi ne? Shi da ya gama sakankancewa cewa ya daina? Rabon sa da yi fa tun Jidda tana gidan sa, ya dauka da gaske ya daina, me ya kai shi ya sake yi ne wai? Me ya kai shi?
Ya tuna sakon da Jidda ta tura masa yau da assuba cewa tana so ta ganshi, ya tuna da irin farin cikin da sakon nata ya saka shi a ciki dan dama ya dade yana saia rai tare da zuba idon ganin sako kamar sa, ya san cewa Jidda tana son sa, kuma soyayya tana tafiya tare da tausayi, wannan yasa yake zuwa unguwar su kullum tare da fatan zata ganshi kuma taji tausayinshi.
Dan haka sanda ya samu sakonta, sanda ya kira ta ta dauka, ya dauka burinsa ne ya cika, ya daukar soyayyar da take yi masa ce ta rinjayi fushin da take yi da shi, ya dauka tana son su sasanta ne ta dawo gidan ta. Wannan yasa maganganun da tayi masa suka zama tamkar mari a fuskarsa ne ga zuciyarsa.
Sai dai kuma yanzu da yayi bitar maganganun na ta sai ya fahimci cewa gabakidaya gaskiya ne a cikin su, amma sanda tana fada bai fahimta ba, lokacin kawai jin su yake tamkar bakaken maganganun ne ta ware take gaya masa, cewa tafi karfin sa cewa shi mazinaci ne ita kuma mumina, cewa zata iya auren wani bayan shi kuma ta zauna cikin farin ciki.
Wannan ya ingiza zuciyarsa zuwa ga aikata abinda a lokacin yake ganin idan yayi zai tabbatar wa kansa da cewa shi ma zai iya rayuwa babu ita.
But now that everything is lost saboda abinda yayi sai ya fahimci cewa it is not worth it. Now that all his life is lost sai ya fahimci cewa gabakidayan barikin ma is not worth it.
Ya lissafo dukkan rayuwar sa da mummunar harkar sa, all the forbidden pleasures da ya samu a cikin harkar, just few minutes of pleasures, and now they have completely destroyed his life.
Kuma shi kansa ya san wannan abin da ya faru is just the beginning, the beginning of his torment a duniya ka dai sannan ga eternal turture a lahira. Yace ba zai iya sake kallon mahaifiyar sa da yan'uwansa ba, but what of Ubangijin sa? Mai zai ce masa ranar da ya tsayar da shi a gabansa ta tuhume shi da laifuffukan sa? Bayan kuma ba rage shi da komai ba sannan ya bashi mata ta ke ce raina wadda ba kowa ya bawa irinta ba.
Yanzu daya duba rayuwar barikin sa da kuma matan da zai iya tunowa wadanda yayi mu'amala dasu a barikin sai yaga babu wadda za'a ita jera ta tare da matarsa a matsayi daya na kyawun halitta ballantana kyawun zuciya, yanzu da yake duba abin sai ya fahimci he have never been truly satisfied sexually idan ba da matarsa din ba, amma still yake komawa ya bita kudibsa ya sake yi, duk da cikin zuciyarsa ya sani cewa masifa ce da bala'i yake siyawa kansa da kudin sa.
Gashi nan masifar ta fara saukowa kansa a yanzu, sai dai tashin hankalin sa shine ba wai kansa kadai masifar zata sauko ba, har kan ahalinsa. Lallai Annabi yayi gaskiya.
Ya tuna da ganin da yayi wa Mufida yau.......
Ya tuna da ganin da Mama tayi masa yau ......
What is next.
Kuma wannan a duniya ne kadai.....
Duniyar da yaji ta fita daga kansa baki daya, so yake ya barta a yau, mutuwa yake so yayi ya huta da wannan abin kunyar.
Amma in ya mutum mai zai tarar a lahira?
Ya tuna da ayar da take bayani akan azabar da ubangiji ya tanadarwa mazinaci a lahira.
Take wanj tsoro, mugun tsoro ya shige shi, ya dunkule a kan kujerar motar tare da fara wani kuka wanda yaje cike da tsantsar nadama da dana sani mai tsanani.
"Astagfirullah!!!"
Ya fada daga can cikin zuciyarsa. Kalmar da tasa yaji wani sabon tsoron ubangijin sa ya sake shigarsa.
"Astagfirullah!!!" Ya cigaba da maimaitawa cikin kukan da yake jin sa yana tahowa daga zuciyarsa yana vibrating a dukkan jikinsa.
Yafi awa daya a wajen a cikin wannan halin sannan ya tuna da sallolin da yake wasa da su, ya tuna cewa bai ma yi sallar azahar ba gashi har ana kiran laasar, ya tuna sanda ake tafiya masallacin sallar juma'a a lokacin ne shi kuma yake yake tafiya gurin aikata alfashar sa, sai yaji kunyar ubangijin sa ta kama shi, ya tuna cewa yana kallon sa a lokacin da yake tafiya kuma yana kallon sa a lokacin da yake aikatawa, yana kallon sa a duk lokutan da yake aikatawa. Wanne uzuri zai bayar idan ya tambaye shi? Yanzu da zai mutu a yanzu wanne uzuri zai bayar na dalilin da yasa bai yi sallar azahar ba?
Ya bude motar da niyyar zuwa masallaci yayi azahar sannan ayi laasar din tare da shi sai kuma ya tuna cewa sai yayi wankan tsarki. Ya koma ya zauna yana jin kunyar duniya gabakidaya ta kama shi. Kunyar ubangijin sa yake ji kamar zai nutse a gurin.
Yanzu mai zai ce da Allah idan ya mutu kafin yayi sallar?
Ya kunna motar sannan ya share hawayen idonsa ya taka ta a hankali ya fita daga harabar asibitin. A hankali yake tuka motar, a lokacin babu abinda yake tsoro irin mutuwa, gani yake zai iya mutuwa ko wanne second kuma shi kansa yasan makomarsa idan ya mutu a halin da yake ciki. A hanyar ya yanke wani hukunci a ransa cewa idan ya shiga cikin gidan sa ba zai kuma fitowa ba, ba zai kuma hada ido da wani ba, zai yi dedicating sauran rayuwarsa ne zuwa neman gafarar Ubangijin sa har sai ya karbi ransa.
Yana zuwa gidan mai gadi ya tare shi "yallabai dazu Hajiya tazo tare da baki baka nan" gabansa ya fadi, "wacce Hajiya?" Yace "Hajiya karama ta babban gida" ya fahimci Aunty yake nufi, sai kawai ya rabu dashi ya shige ciki.
Yana shiga toilet ya wuce yayi wanka, wankan da ya dauki lokaci yana yi yana ji kamar yanaso ne ya kankare fatar jikinsa ya zubar, maybe ko zai rage dattin najasar da take tare da shi, sai da ya fahimci lokacin sallah yana cigaba da wucewa sannan ya fito ya chanja kaya ya saka wadu sababbi wadanda bai taba sakawa ba, ji yake kamar sauran kayan nasa duk najasa ce a jikin su.
Yayi sallah, azahar da laasar, amma sai ya kasa yin addu'a, ya rasa abinda zai roka a gurin ubangiji, ya rasa da bakin da xai nemi gafara a gurin ubangiji dan tabbas a lokacin gani yake yi babu wanda ya kai shi munanan aiyuka. Maimakon ya daga hannun yayi addu'a sai ya mayar da goshinsa kasa yayi kuka, kuka mai yawan da yake jin bai taba yin irinsa ba a duniya, kukan kuma da yake jin yana fitowa da ga cikin zuciyarsa.
Sai da ya zama exhausted babu wani sauran karfi a tare da shi sannan ya kwanta a gurin ya rufe idonsa yana cigaba da sake bitar laifuffukan sa. Mai yasa ya kasa dainawa ne? Ya jima yana cewa zai daina amma kuma ya kasa dainawa, tun kafin yayi aure yake cewa zai daina idan yayi aure, da yayi auren kumaya dauka ya daina din sai da wannan shegiyar zuwairan ta bishi Lagos ta hillace shi, daga nan ya kuma cewa ba zai kara daga kanta ba amma kuma sai gashi ya cigaba, duk sanda yayi saibya gayawa kansa na karshe ne amma wani opportunity din yana sake zuwa masa zai sake yi ya kuma cewa na karshe ne.
Sai yanzu ya gano dalilin kasa dainawar tasa.......
Saboda ba dan Allah yake so ya daina ba... .
Amma yanzu ya gane kuskuren sa, he has learned the hard way but he is greatful for learning, ya gode Allah ya ya nuna masa ayar sa tun a duniya har kuma ya juyo da hankalin sa zuwa tuba na gaskiya, ya gode Allah dabai dauki ransa ba tare da ya tuba ba. Yanxu