Chapter 54 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   54 / 106

159K to 162K   out of 316K words

ta kuma kara min kwarin guiwar zuwa din, ta zo har gida ta dauke ni a motar ta muka tafi tare, and she got me involved a dukkan al'amuran da ake yi, sai dai ko amsa gaisuwa ban samu matsayi ba daga gurin Mama, amaryar ma kuwa dama ko inda take ban dosa ba. Nima kuwa wannan karon ban gayyaci kowa daga gidan mu ba ba kamar lokacin bikin Muhibbat ba da har da surukan gidan mu sai dana gayyata, wannan karon ko Farhan ban gayyata ba sai da ga baya da taji anyi bikin tayi ta min mita ni kuma sai nayi dariya kawai.

Bayan an gama bikin Muhsina sai mu kuma muka fara bikin yaya Tahir, wannan karon abin nawa maganin a kwabe ni dan haka na zage na sha hidimar bikina sosai.

Ranar da za'a fara bikin auncle Muhammad yazo tare da matarsa da yayansu uku, cousins dina da ban taba gani ba sai a hoto. Ahmad, Layla da Abdoul. Murnar da muka yi ranar babu irinta, a take na kira Umar na sanar masa da labarin zuwan su kuma na roke shi alfarmar idan ya barni zan kwana a gida tare da yan uwana yadda zamu ji dadin raba dare muna hira. Yayi ta min dariyar yadda nake ta murna sannan yace min babu komai zan iya kwana din, har da tambaya ta in da akwai abinda nake bukatar ya kawo mana ni da yara nace ya bar shi kawai babu komai, tunda ya barni shikenan dama haka kadai nake so.

Sai dai....

Muna tsakiya da hirar mu muna ta raha, ina ji na tamkar bani da wani problem a duniya sai Abba ya leko daga saman sa "Aysha! Kamar muryar Jidda nake ji a gidan nan?"

Naji gabana ya fadi, duk muka yi shiru, ya sake magana "Jidda ke nake yiwa magana fa, ko kin zama kurma ne ban sani ba?" Na taso na fito tsakar gida ina kallon samansa inda yake tsaye akan baranda.

"Me kike yi har yanzu baki tafi gidan mijinki ba?" Naji alamar kamar zanyi kuka, "Abba dama.....na tambayeshi kuma ya barni......" "Saboda baki da hankali? Shi kuma ya biye miki? Ina kika taba ganin mace ta bar gidan mijinta ta taho gidan su ta kwana bayan ba a wani garin take daban ba, kawai saboda ana biki a gidan su. Na dauka da nayi miki aure zaki yi hankali ashe har yanzu da sauran ki. To ki hada kayanki maza ki zo ki koma gidan mijin ki yanzu yanzun nan" 

Naji hawayen ya karaso "Abba dare ......." Kafin in kai karshe naji yana waya "kazo yanzu ku tafi, in kana barinta kwana wata ranar ma babu bikin da akeyi zata ce zata zo ta kwana kuma ba zaka iya hanata ba tunda ka riga ka sabar mata, na fahimci da Umar yake waya sai kawai na juya na koma daki na dauko mayafi na da jaka ta, raina yayi bala'in baci na ma kasa yiwa duk masu tambayata bayanin abinda ya faru sai wadanda suka san halin Abba ne kawai suka fahimta, haka ina ji ina gani Umar yazo na bishi muka tafi gida na bar yan'uwa na da nake ta doki da murnar gani.

Farko Umar da yazo ya dauke ni dariya yake min yana tsokana ta, sai daya  lura da gaske raina a bace yake sannan kuma ya koma rarrashina tare da kokarin faranta min "kinga, yanzu tunda Baba yace ba zaki kwana ba dole muyi masa biyayya, amma gobe in Allah ya kaimu sai ki dawo da wuri ku wuni tare in dare yayi sai ki dauko su duk ki taho dasu gida su kwana a gurinki, ku raba dare kuna hira kamar yadda kike so, kin yarda?" Na gyada kai ina dan sakin fuska ta, yace "to kiyi murmushi in gani in dai kinji dadi, nayi masa murmushi tare da cewa "thanks" ya yi murmushi "anything da zai saki farin ciki shi zanyi. Yanzu dai tunda an koro mu kuma mun bar yara a can sai muje gida muyi sabon amarci".

Na harare shi "sai dai ka biya sabon sadaki" yace "bayan wanda na biya?" nace "kamar gaske, wani sai ya dauka shi ya biya da kansa bayan biya masa akayi, kai fa auren gata akayi maka, I doubt in ka san ma nawa ne kudin sadakin" ya shafa kai "nawa ne ma?" Nayi dariya "na sani da ma, ko adadin su baka sani ba, dan gatan Mama da Baba"

Yayi dariya "to shikenan, a lissafa min wasu in sake renewing" na juya ido na "sai dai kayi renewing kazar amarci, ina jin ita kadai ce abar da ka siya da kudin ka" yabata rai "bayan kajin nawa ma barin mu kikayi muka kwana tare a falo ke kuma kika rufe kofarki" nayi dariya "au baka manta ba?" Yace "ya za'a yi na manta, baki san irin dogon burin da naci wa daren nan ba amma kika yi min wayo kika rufe kofarki kika barni na kwana a falo tare da ledar kajina"

Nayi dariya sosai nace "abin tausayi, me yasa wai baka je dakin ka ba ko guest room sai ka zabi kwana a falo" ya langwabe kai "saboda in kika gan ni a falo zaki fi tausaya min, zaki fi gane halin da kika saka ni a ciki" na sake dariya sai ya ja kumatu na "matsoraciya kawai. Ban taba ganin mutum mai tsoro irin ki ba" nima naja kunnensa "ni kuma ban taba ganin mutum mai naci irin ka ba" ya kama kunnen "ouch, kin takurawa kunnena wallahi"

Na juya ido na "dadin tabawa ne dashi, laushi" yayi dariya "kin yiwa kanki, da har nayi niyyar siya miki kazar amma na fasa yanzu" na tura baki "nima da nayi niyyar baka special treatment amma na fasa yanzu" ya bude ido "ina ne gurin da ake siyar da kaza mafi kusa?" Nayi dariya "sun tashi ai yanzu, dare yayi" ya kalli ogogo, it was after 11 na dare, yace "ai kuwa sai an nemo ta duk inda take a kano ko da kuwa mai rai ce sai in fige miki da kaina" muka yi dariya tare.

Sai da ya nemo kazar kuwa, ni kuma na bashi special treatment din dana ce zan bayar.

Bikin sai ya zamanto kamar ya rabu kashi biyu, duk matasa sai suka koma gidana iyaye kuma suna gidan mu, and we really did enjoyed ourselves, Umar ta sakar min sosai ni kuma na sakarwa baki na. Kowa yazo gidan sai ya yaba, dan cima duk irin wadda kake so zaka samu sai dai in iyayi zakayi, wannan ya kara fito min da tauraruwa ta a cikin dangin mu.

Na gayyaci yan gidan su Umar bikin, amma Yaya Mubaraka ce kawai tazo tare da Mufida ranar yini suma kuma na tabbatar ba da sanin Mama suka zo ba, ba nuna musu komai ba na karbe su na basu kulawa ta musamman a matsayin su na bakina na musamman.

Bayan an gama biki mun dauko amaryar mu Yusra mun kaita gidan angonta sannan aka fara watsewa. Sai naji bana son rabuwa da yan uwana musamman su Layla da nasan zan jima kafin in sake ganinta. Ranar da suka hada kayan su zamu kai su gidan Aunty Afia inda daga nan zasu tafi, Nace "amma zaku dawo bikin Aira ko? Kun ga bai fi wata uku ba ya rage" tace "ba zamu dawo ba, sai dai in kuma kunje mana tukunna sai mu dawo tare" naji babu dadi sai nayi shiru, Umar da yake driving yace "are you daring us? To kuwa zamu baki mamaki, zamu zo when you least expect" tayi murna "da gaske?" Yace "da gaske" nima na bude ido nace "da gaske?" Yayi min murmushi "yes Baby, da gaske. I promise" and with that, he did made my day.

Ina baku wadannan labaran ne dan kusan irin kyautatawar Umar a gare ni ku kuma fahimci irin tsatstsauran position din da na samu kaina a ciki.

Bayan bikin Yaya Tahir ne nayi baki guda uku wadanda suka zo min da magana kusan daya amma a mabanbanta lokaci, kuma maganganun nasu masu conflicting juna ta yadda har na rasa menene matsaya ta kuma wacce hanya zan bi?

Bakuwa ta farko da nayi ita ce Farhan. Ta roki Baba ya barta tazo min weekend, ya barta da kyar bayan ya gama wanke ta tas akan har yanzu bata samu miji ba. Tazo tana ta yi min mita kamar kullum. "Ni ban san inda zan saka raina ba. Ni ban san me mutane suke so su mayar da ni ba, kin san yanzu wai duk wanda na gamu dashi sai kiji yana tambayata wai yaushe zanyi aure? Ko akan baban su nake a zaune ne ni ban sani ba. Ina ruwan mutane da aure na ko da rashin aure na ne wai?"

Sama sama nake jin ta dan hankali na yana wani gurin daban, nima tawa matsalar nake lissafawa, kwana biyu dai Umar shiru, shin ya daina ne ko kuma ban kama shi bane ba?

Ta taba ni, "wai tunanin me kike yi ne Jiddo?" Na girgiza kaina ina so in tattaro hankali na guri daya "babu komai" na fada tare da gyaran murya. Ta girgiza kai "bayan getting away from surutun mutane for two days, na zo gidan nan ne musamman saboda in tambaye ki, are you okay?"

Na kirkiri dariyar da ta tsaya a muryata "kin ji ki Farhan da wata magana. Ciwo kika ga ina yi ballantana ki saka ni a gaba da tambaya? Ni lafiya ta kalau"

Ta girgiza kai "you are not okay Jidda, ko wanda bai sanki ba yasan hakan ballantana ni. Akwai abinda yake damun ki tabbas tun da dadewa, na baki chance ki gaya min da kanki amma kin ki, kuma na tabbatar baki gayawa Umma ba, hakan yana nufin baki gaya wa kowa ba kenan ke kadai kike rike abinki a zuciyar ki. Kin dai san bature yace "a problem shared is a problem solved" kuma nasan ko banyi miki solving dinsa ba zaki ji dadi idan kika gaya min kuma maybe in muka hada kan mu ni da ke zamu iya solving dinsa"

Na sake girgiza kai, but this time not as convincing as the first, "babu komai na gaya miki Farhan, in akwai wani abu ai zan gaya miki ko?" Tace "anya kuwa kina kallon mudubi Jidda? Kin ga yadda kike bushewa kullum kuwa? To ko sanda kike boarding school baki yi irin wannan ramar ba wallahi. Kuma ba abinci kika rasa ba, dan haka definitely wani abun ne yake damun zuciyarki, da ina tsammani ne ban tabbatar ba, yanzu kuwa na tabbatar" sai ta dauko robar magani ni ta miko min, nayi sauri na karba ina kallon ta tace "na samu wannan a dakin ki, nayi browsing kuma naga maganin masu hawan jini ne, hawan jini ne da ke Jidda?"

Sai na sunkuyar da kaina ina jin hawaye yana taho min, na tsani wannan saurin kukan nawa amma halitta ta ce haka. Sai ta dawo kusa dani ta zauna tare da dafa ni, cikin karyewar murya ta sake cewa "Jidda ki gaya min, Me yake damunki? Miji ne ko dangin miji? Ko kuma aure Umar din yake nema?"

Nace "duk tambayoyin da kika yi min zan iya amsa miki da eh, kuma zan iya amsa miki da a'a, dan ban san ma matsayina ba Farhan, Farhan ni kaina ban san me nake ciki ba kuma ban san me zanyi ba" na fara kuka sosai, ta  jawo ni jikinta na dora kaina a kafadarta na fara kuka na, sai da nayi na gama sannan na bata labarin, na bata labarin komai ba wai dan ina saka ran zata samar min mafita ba sai dan kawai nasan kaf gidan mu bayan Umma da Abba bani da kamar ta, ko wadanda muka fito ciki daya bana ji dasu kamar yadda nake ji da ita.

She was shocked. Shocked beyond words. Sai kuma ta taya ni kukan da nake yi muka yi tayi tare. "Jidda yanzu wannan maganar kike rikewa a cikin ki? Jidda yanzu mijin irin Umar kike zaune da shi?" Na bude hannu na "Farhan ya zanyi? Nayi iyakacin kokari na Farhan Allah ma ya sani ina iyakacin kokari na. Ban san menene kuma zanyi ba, ban san menene zanyi ba Farhan"

Cikin fada tace "ki bar masa gidan sa. Gani yake yi kamar ba zaki iya rabuwa da shi ba shi yasa yake cigaba da abinda yake yi, gani yake kina sauraron sa shi yasa yake cigaba da yi miki karya, gani yake yana cin bulus shi yasa yake yi yake karawa. So yake ya cigaba da samun ki a gida sannan ya fita waje ya samu wasu, he wants to eat his cake and still have it. He is sooo selfish. Ki fita ki bar masa gidan sa ai ba anan ne kadai zaki cigaba da rayuwa ba, idan kin bar gidan sa ba mutuwa zaki yi ba. Idan kin zauna ne ma zaki mutu dan na tabbatar in dai baki bar gidan nan ba wannan mutumin sai ya kashe ki an fitar da gawarki"

Nace "Farhan ina zan je in na fita? Ina zanje Farhan? Kin fi kowa sanin halin Abba kin san babu yadda zanyi in je gidan mu da sunan yaji, Abba kora ta zaiyi, ko kuma ma yayi min mugun baki, ba zai tsaya ya saurare ni ba, Umma ba zata iya yi min komai ba sai dai ta dora damuwa ita ma a ranta har ta samu hawan jinin da za'a bata gado a kusa da nawa. Bayan gidan mu kuma ina zanje?"

Tace "try. At least try. Ki gwada zuwa gidan ki gwada yi wa Abba bayani watakila ya fahimta, with Abba you can't really tell, sai kin gwada tukunna" na goge hawaye na nace "abinda zanyi kenan Farhan. Na riga nayi wa kaina alkawarin the next time da zan kama Umar da irin wannan laifin to zanje gidan, zuwa gidan mu shine next step dina kuma zanyi. Bana fatan zuwan ranar saboda bana fatan sake kama Umar da laifi mai kama da wannan, amma in ya sake, in na saka kamashi tabbas zan je gida Farhan. Ban san me zan tarar a gidan ba amma nasan zanje insha Allah"

Ta gyada kai tana share nata hawayen "yanzu Jidda in dai har Umar duk da son da yake miki da kuma son da kike masa, duk da kyan da Allah ya baki, duk da yadda kike kokarin kula dashi shima yake kula da ke, duk da yayan da kika haifa masa, in dai har zai iya yi miki haka then who is safe kuma a wannan zamani?"

Nace "ba haka bane ba Farhan, abin ba'a soyayya bane ba ko kyau ko wani abu, abin a hali yake, sai ki ga kuma wadda mijin baya sonta kuma baya bata kulawa kuma bata da wani kyau amma mijinta baya neman mata. Haline kuma kaddara ce, ba gazawa bace ba daga matar"

Ina ma ace matan waje na banza zasu fahimci cewa wannan namijin da yake zuwa gurin su suna alfasha, watakila yana da matar da ta fi su komai, kuma tana iyakacin kokarin ta ba wai ta gaza bane ba, kuma yana sonta fiye da tunanin su, maybe da sun daina daukan kansu da wani muhimmanci

Farhan bata yi kwana biyun da tayi min alkawari ba sai ta hada kayanta tace tafiya zata yi "bayan abinda na sani, bana jin zan iya budewa Umar baki inyi masa dariya in yazo gidan nan, zan iya ambaton sunan Mama in zaga, gwara in tafi tun kafin in kunno miki wuta a gidan ki" ta cigaba da hada kayan ta tana mita. "Ni dama tun asalin Umar din nan ba son shi nake yi ba, ni dama tun farko bai yi min ba, he is just too much, tun farkon gani na da shi yayi min kama da playboy, ashe ya wuce duk inda nayi tunani" ta juyo tana kallona "ita kuma wannan mokadaddiyar Maryam din sai na karya wannan karkatacciyar kafar tata duk ranar dana kuma ganin ta a kusa da ke"

Ni dai ban ce mata komai ba har ta gama hada kayanta sai na kira Umar na tambayeshi zanje in kaita gida, yayi ta tambayar dalilin da yasa ta fasa kwana sai kawai nace masa Abba ne ya fasa barin ta, da yake yasan halin Abba sai kawai ya bar maganar.

Bakuwa ta biyu da nayi kwana biyu bayan zuwan Farhan ita ce Surayya, matar Bashir. Rabon ta da tazo gidana tun sanda nayi wa Bashir iyaka da gidan mu kuma nasan shine yake hanata zuwa, ni ma kuma tun daga lokacin dama ban kuma zuwa gidan su ba sai dai mukan yi waya mu gaisa ko kuma mu gaisa ta WhatsApp.

Ranar sai gata tirtsi tirtsi da ciki. Na tarye ta da fara'a da komai muka gaisa tace wai tazo sada zumuncin da na tsinke a tsakanin mu. "Ko menene dalili?" Nayi dariya "kinji ki da wata magana, kawai dai yanzu ne bana samun lokacin fita unguwa wallahi gabakidaya. Kafin mutum ya tashi ma ya gama aikin gida ga yara, nan da nan sai kaga lokaci har ya tafi. Unguwa yanzu ai sai ku amare" na fada da sigar tsokana sai naga bata wani yi dariya ba ta tabe baki "wa yaga amare, ke ma dai da tsokana kike wallahi" nace "as long as baki haihu ba, amarya ce ke. Ni kuwa fa? Na gama zama cus"

Sai tayi shiru kawai. Muna tare Umar ya fito daga daki, da yake ranar bai fita ba tun safe yana daki shi da Asad, suka gaisa sama sama, yana acting kamar ma bai gane ta ba sai ya dauki Asad yace zasu je unguwa, na raka shi bakin kofa yace "cook something delicious kafin mu dawo, in akwai abinda kuke bukata sai ki kira ni ki gaya min in taho dashi, zan biya in dauko Yasmin daga school ba sai kin fita ba. Ki huta sosai kiyi bacci. I love you, bye" sai yayi kissing cheek dina daya.

Naji kunya saboda bakuwar da take gurin kuma nasan

54 / 106