Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
na kasa cigaba da zama, na rasa dalilin da yasa ma kasa yin abinda nayi niyya, sai na tashi na saka hijab dina na dan gyara fuska ta na fita.
Yana zaune tare da su ya kawo musu drinks, suna magana da Bashir amma daga gani kasan his mind is not there, na ga yadda ya sauke ajjiyar zuciya da ya ganni sai na tafi gurin yammatan guda biyu.
"Sannun ku da zuwa. Amarsu ta ango sha kamshi" na lura da waddata sunkuyar da kai da kuma wadda tayi dariya, na zauna muma gaisa sannan na juyo na gaishe da Bashir briefly. I was not in the mood for chatting, suma kuma yammatan kamar ba masu surutu bane ba sai naji sunce zasu tafi, muka mike gabaki daya muka fita compound ina saka ran inga sun shiga motar Bashir sun tafi sai naga sun kama hanyar gate shi kuma yayi musu sallama yace sai sunyi waya, nayi mamaki sosai dan Umar ko sanda yake nemana ba zai yi min haka ba ballantana yanzu da in da ace mota ta zata samu problem zai iya bar min tasa shi ya hau ta haya.
Ban iya shiru ba sai nace "ba gida zaka kai su ba?" Ya daga kafada "noo, dama na gaya musu zan tsaya inyi wani abu anan, so, zasu nemi abin hawa ne kawai" na gyada kai kawai na juya zan koma ciki sai yace "baki tambaye ni abinda zan tsaya inyi anan din ba?" Na juyo "maybe zakuyi magana ne da abokin ka or something, I don't know"
Yayi murmushi "eh magana zamuyi, amma da ke zamuyi ba dashi ba" na tsaya ina kallon sa sannan na juya ina kallon Faruq wanda shima ni yake kallo, sai na girgiza kai nace "babu da wanda zanyi magana, bada kai ba bada abokin ka ba. You think zan yarda da maganar sa bayan naki yarda da taka? Abokin ka ne fa? A guri na komai kayi da sanin sa"
Ya hadiye wani abu sannan yace "baki tsaya kinji maganar tawa ba ma ai ballantana ki yarda ko ki ƙi yarda" na juya na cigaba da tafiya nace "bana bukatar ji dan ko naji ba zan yarda ba" Bashir ya biyo ni a baya "ta yaya za'a samu fahimtar juna in dai har ba'a zauna anyi magana ba?" Nace "bana bukatar samun fahimtar juna in dai da shi ne, na riga na fahimci dukkan abinda ya kamata in fahimta"
Ina shiga falon suka shigo duk su biyun, Umar yayi saurin shan gaba na, "please please Jidda dan girman Allah ki tsaya. Ki tsaya muyi magana dan Allah" na fara zama frustrated. "Dan Allah" ya sake cewa. Na juya ina kallon Bashir sai ya nuna min kujera yace "dan Allah ba dan ni ba ko dan shi" na kalli hanyar dakina "yata zan dauko" sai Umar yace "ki zauna, zan ne in dauko ta"
Na koma na zauna ina kallon Bashir, ina so inji wacce karyar kuma Umar ya hada masa shi kuma zai hada min? Nayi folding hannuna ina kallon sa nace "ina jin ka"
Sai ya zauna shima sannan yace "Umar ya gaya min abinda ya faru, ya kuma gaya min komai da komai duk da dai already na riga nasan wani part na abin da ya faru. And I totally believe kina da every right da zaki yi treating dinsa yadda kike yi koma fiye da haka, saboda bashi da wani excuse na abinda yayi. Na kuma zo ne nan gurin ki badan in baki hakuri ba akan abinda yayi din dan na gaya masa shi yayi creating mess dinsa shi ne kuma zaiyi cleaning. Nazo ne dan in gaya miki gaskiya, gaskiya to the best of my knowledge. Sannan kuma nazo ne saboda zan iya cewa akwai wani part na laifi na a cikin maganar"
Na gyara zamana "Umar ya kan yi rantsuwa akan karya. Ban sani ba ba ko kaima halin ka ne hakan? Tunda abokin ka ne?" Ya girgiza kansa "ban san a ina ne yayi miki rantsuwa akan karyar ba, dan haka ba zance dai dai ne ko ba dai dai bane ba, amma ni yan zu na rantse miki, wallahi, duk abinda zan gaya miki shine gaskiyar magana"
Nace "menene gaskiyar abinda yake tsakanin Umar da Zuwaira?"
Yace "budurwar sa ce. Tun muna buk suke tare, he thought he was in love with her, then realized the kind of person she is and broke up with her. Amma ita a lokacin bata shirya rabuwa da shi ba sai suka cigaba da kasancewa tare on and off, shi yasan cewa ba aurenta zai yi ba and itama deep inside her tasan cewa ba auren ta zaiyi ba amma sun cigaba da rayuwa a haka"
"Labarin sa ne ba nawa ba, and like I said am not here to clean up his mess but to tell you the truth. And the truth is, he finally broke up with her lokacin da ya hadu dake and fall in love with you and decided to settle down. Yayi cutting every ties da ita. That am very sure of. Kafin bikin ku zan iya cewa sunyi watanni basa tare. We even though ta hakura dashi finally"
"But jin labarin auren ku shine ya rikita ta, she realized cewa da gaske yake ba aurenta zaiyi ba and blamed him for all that has happened in her life. Wannan ne yasa tazo gidan nan, har ta fara dasa zargi a tsakanin ku, kuma ta ganshi yana bacci a reception din Mahmud ranar nan ta kuma turo miki sakon cewa suna tare, but am telling you the truth, and the truth is basa tare a ranar nan"
"Tare da ni muka je har inda take aiki a saloon din Mahmud, aikin da Umar din ne ya samar mata tun sanda tayi dropping out of school, kuma ya buga mata warning sosai a kanki saboda ransa yayi balain baci a lokacin musamman akan sharrin da tayi masa"
"Maganganun daya gaya mata ni a lokacin na dauka ko mai sunansa ba zata kuma kalla ba, wannan shi ya kara min mamaki last week data turo min message tana nemansa ni kuma na gaya mata cewa baya gari yana Lagos"
Na dago kai ina kallon sa sai ya gyada min kai yace "yes, ba tare suka tafi ba, Baba ne ya aike shi wata harkar business dinsa, and I accidentally told her yana Lagos and she followed him"
Sai ya dauko wayarsa yayi danne danne sannan ya miko min
Hira ce a tsakanin shi da Zuwaira, na gane ita ce saboda through Facebook ne da profile din data yi min magana and it goes like this
"Hi"
"Hi"
"Nace idan babu hello ai akwai hi ko? Amma ku babu hello din ma a gurin ku ballantana hi din"
"Tuba muke yi ranki ya dade"
"Ni na isa! Ransu ya dade dai su masu matsayin"
"Lol. You are funny"
"Funny ko gaskiya. Naji ance ma har an haifa muku Baby. Babu sanarwa m ballantana ma mu saka ran zamu samu naman suna. To maje mu karba da kan mu"
"Don't even try that, kin san dai abinda yace last time da kika je gidansa ko?"
"Yeah I know. Amma ya zanyi da raina? Mai sonka ai shi yake bibiyar ka ko?"
"Eh haka ne. Kinyi gaskiya. Mun gode"
"Yana ina ne? I have been trying to contact him in yi masa barka na kasa samun sa"
"Baya gari, yaje Lagos wani business"
"Lagos? A can ake jegon kenan?"
"No, shi kadai ya tafi. Jiya"
"Okay. Shikenan. Thank"
"Yeah. Bye"
Na sake komawa sama na ga date din hirar, and it shows washegarin tafiyar Umar. Na mika masa wayarsa bance komai ba, ya karba yace "wannan shi yasa nace part of it laifi na ne. Ban san me ya faru a tsakanin su a Lagos ba, yace ta turo miki some pictures, ban san menene a pictures din ba and I am not saying ko menene yayi a can din yayi dai dai, but koma menene yayi nadama and I think he deserves a listening ear from you. Ruwan ki ne ki yafe masa ko ki ƙi, but I am begging you, listen to him"
*wannan littafin na siyarwa ne, idan baki siya ba kar ki karanta, in kin siya kuma kar kiyi sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*
*The Confession 2*
Na dago kai ina kallon sa, trying to study him, sai kuma na juya na kalli Umar wanda ya fito tun dazu daga daki da Yasmin a hannun sa yana tsaye a bakin kofa yana kallon mu, na sake mayar da dubana kan Bashir sannan nace "for all I know bakin ku daya, for all I know tare kuka zauna kuka shirya maganar da zaku gaya min"
"Na yarda cewa ba tare suka tafi ba, na yarda kuma bashi ya gayyaceta cewa ta bishi ba, duk that doesn't change anything, that doesn't mean anything, taje gurinsa yayi welcoming her with open arms, kuma bani da wani abun da zai bani guarantee cewa gobe ma ba zai koma mata ba, ko kuma in tazo ba zai karbe ta ba, ko kuma......"
Ya katse ni "ba zai je ba, ita ma kuma ba zata je gurinsa ba, for that I am very sure of" nace "menene hujjar ka ta fadar haka? Dan ka ga yana nuna kamar yayi nadama? Da farko ai ba taba tsammanin zaiyi ba kuma yazo yayi din"
Ya girgiza kai, "tabbas yayi nadama, amma yanzy ba ina magana ne akan nadamar sa ba, ina magana ne akan abinda ya aikata ga Zuwaira sanadiyyar sakon data turo miki"
Nayi shiru ina kallon sa bance komai ba, sai ya dauko wayarsa for the second time yayi danne danne sannan ya miko min "kalli nan ki gani. Ban sani ba ko zaki gane wacece wannan?" Na karba na duba.
Facebook ne, wata ce tayi posting hoton wata tana nema mata addu'a daga gurin mutane akan tsautsayin daya same ta. Na kalli matar cikin hoton, Kallon farko ban gane taba, sai daga baya na gane ta, Zuwaira ce, sai dai zan iya cewa babu wani abu na fuskar ta wanda bai chanja kamanni ba, gabaki daya fuskar ta kumbura suntum idonta daya ma ya rufe saboda kumburi ga kuma dinki da akayi mata a kasan idon nata da gefen kunnenta. Fuska ce kadai, banga sauran jikin ba.
Na dago kai. "Menene hadin abinda muke magana akai da kuma tsautsayin da ya same ta?" Sai yayi murmushi "ba tsautsayi ne ya same ta ba, mijinki ne ya dake ta"
Na daga kai da sauri na kalli Umar sannan na sake kallon hoton hannuna, na kuma yin scrolling through dan in tabbatar cewa it is for real. Sannan na shiga gurin comment naga ana ta yi mata jaje, wadanda suka santa suna ambatar sunan ta.
Na sake dago kai ina kallon sa sai ha daga kafada yace "he told me ya bata mata kamanni kamar yadda ta bata shi a gurin ki. I never knew how bad sai dazu naga friend dinta tayi posting"
Na mika masa wayarsa sannan nace "ya burge kenan? A ganinsa dan ya dake ta zai burge ni kenan? Ko kuma dukan ta zai goge abinda yayi" ya girgiza kai "am sure bai burge ki ba kamar yadda ni ma bai burge ni ba, but that doesn't matter, abinda nake so wannan ya fahimtar dake shine how deep his love for you is, abinda ya faru a tsakanin su will never match abinda yake a tsakanin ku. And that should mean something to you. That should make him deserves a listening ear from you"
Na juya na sake kallon Umar sai ya sunkuyar da kansa. Bashir ya mike ya dauki wayarsa sannan yaje ya mika masa hannu suka yi musabaha sai yazo ya fita.
Falon yayi shiru bayan fitarsa, ni sai naji ma kamar har kukan tsintsayen da suke waje da kuma karar motocin da suke wucewa duk sun tsaya. Ya tako ya taho inda nake zaune, sai ya ajiye Yasmin a gefe na, ban kalle shi ba sai kawai gani nayi ya saka guiwowin sa a kasa yayi kneel down a gaba na, ya kamo hannayena biyu ya rike a cikin nasa biyu sannan ya hade su a kirjinsa tare da dora fuskar sa akai.
"Ban san me zance miki ba Jidda"
Nace "start with the truth"
Yace "ita zan gaya miki, the whole of it"
"Ka yarda kenan ka amince cewa Zuwaira karuwar ka ce bata Mahmud ba? Ka yarda ka amince cewa ka kawo ta gidan nan ta zauna tsahon lokaci saboda bukatar gangar jikin ka? Ka yarda ka amince cewa you cheated on me with her a Lagos?"
Na fada ina kuka, kuka sosai wanda na dauka na gama yin irin sa amma yanzu sai ya dawo min sabo. Ya dago kansa yana kallona, ga mamaki na sai naga shima kukan yake, and that's something I never expected from him, I never thought it possible for someone as strong as him yayi kuka, I thought kuka na iri na ne mata kuma masu rauni. Sai naji tawa zuciyar ta kuma tsinkewa, automatically na rintse hannayensa da suke cikin nawa
"Me yasa kayi min karya?" Na fada ina kara volume din kuka na. "Me yasa tun farko da na tambayeka ko ka santa ka ce min ba ka santa ba" ya ja hannayena zuwa sides din fuskarsa, ina jin yadda hawayensa ya jika fuskar ta sa, ya sake jan guiwar sa yana kara shiga tsakanin kafafuwana sannan yace "me kike so in ce miki a lokacin huh? Me kike tunanin zan iya ce miki? Cewa I have a bad past her? Shine gaskiyar da kike tunanin zan iya gaya miki? Sannan in zauna in kalle ki cikin kunan zuciya? Regretting marrying me kamar yadda kike yanzu?"
Na fara kokarin kwace hannu na amma ya hana ni, yana kara matse su a kan fuskarsa "yes I had a bad fast with her in haka kike so kiji daga bakina, yes na bata gida na ta zauna a ciki lokacin da iyayen ta suka kore ta, and yes na sama mata aiki a gurin aboki na sanda aka yi withdrawing dinta daga school, is that what you want to hear? Me wannan din zai karar damu a zaman auren mu?"
Na rintse idona ina jin zafi mai yawa a cikin zuciyata, I asked for the truth amma yanzu dana same ta it doesn't sound so good but it is still the truth.
Na karbe hannuna daya na dafe fuskata dashi ina sheshshekar kuka. Amma duk da haka sai na sake tambaya "and you told her duk abinda ta gaya min cewa ka gaya mata?" Ya girgiza kai "wallahi Jidda ban gaya mata ba, I cut all ties with her tun sanda nayi niyyar auren ki, wallahi ban taba maganar ki da ita ba" na girgiza kai "but then you cheated on me with her a Lagos. In kayi cutting all ties with her ya akayi haka ta faru? It doesn't look as if she forced you"
Ya saki hannu na yana kokarin kama kafada ta, na ja baya sai ya kifa fuskar sa akan cinyata yana kuka mai sauti. "I don't know Jidda, I don't know what came over me, she knows me and she seduced me" na ture fuskarsa daga jikina ina kara shigewa cikin kujerar, wani irin kishi mai daci yana ratsa jikina har cikin bakina
"Don't touch me, kar ka sake taba ni. Nan gaba kadan ma cewa zama yi raping dinka tayi" ya kama hannuna daya ya fara dukan kansa dashi "hit me, in zuciyarki zata huce hit me all you want amma kar kice ba zaki yafe min ba dan Allah. Abinda nayi miki is unforgivable kuma bani da wani excuse da zan baki. Na karbi dukkan laifuka na. Ki yafe min dan Allah ki bani second chance, ki bawa auren mu second chance dan Allah Jidda"
Na karbe hannuna daga nasa na hada dukkan hannayen biyu na rungume a kirjina inda nake jin tamkat zuciyata zata fado kasa in ban rike ta ba, I love him so much shi yasa betrayal dinsa take hurting dina too much.
"Me na gaza banyi maka ba Faruq? Akan gado da kuma a waje menene bana yi maka? Why did you chose to betray my love for you? Dan kaga ina son ka? Is that it? Dan kana tunanin ba zan iya rabuwa da kai ba saboda ina sonka? Shine takamar ka?"
Ya hawo kan kujerar tare da jawo ni jikinsa "ba zan ce nasan abinda kike ji a zuciyarki ba, ba zan iya misaltawa ba amma believe me zafin da nake ji a tawa zuciyar ban taba jin irinsa ba, saboda ganin ki cikin wannan halin and knowing nine silar saka ki a ciki. Saboda Jidda I love you, I love you with all my heart and soul, more than I love myself"
Na dago kaina ina kallon sa "kana son nawa fiye da kanka kuma kayi min sharri, kayi min sharri a gaban iyayena dan ka kare kanka ni kuma ka dora min laifi kuma ka zauna kana saurarensu suka yi min fada? Wannan shine naka kalar soyayyar?" Ya kamo fuska ta na ture hannunsa "Jidda I did that for us, for me and you and our children. Kina tunanin zanyi confessing a gabansu ne akan wannan maganar? Mu zamu iya daidai ta wa muyi putting what happened behind us amma su ba zasu manta ba and they may tell someone else who may tell someone else and before you know it our family will forever be stained with my mistake. Shi yasa na gaya musu haka. Case din duba waya is the most popular marital problem nowadays, shi yasa na gaya musu saboda maganar ta mutu ba wai saboda inyi hurting dinki ba....."
Nace "but you did hurt me. Me yasa baka kirkiri wata maganar da zata nuna cewa kaine mai laifi ba yadda kai za'a yi wa fada bani ba? In dai har da gaske kana sona yadda kake fada" yayi shiru bai ce komai ba, na ture shi daga jikina "kayi deleting hotuna daga wayata, but they will forever be