Chapter 55 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   55 / 106

162K to 165K   out of 316K words

in dai tana kallon mu ta gani, sai nayi kissing Asad ni kuma sannan nace "a dawo lfy" suka fita ni kuma na dawo gurin bakuwa ta na zauna sai tace "Jidda kinji dadin ki ke kam" nayi murmushi "dadin me naji?" Ta sunkuyar da kanta yana yin ta yana nuna zuciyarta babu dadi "ni har mamaki nake yi in naga maza suna yiwa matansu magana irin haka. Sai inyi ta sha'awa ince ko yaushe ni ma turn dina zai zo? Ko yaushe Bashir zai kalle ni irin yadda naga Umar yana kallon ki?"

Na girgiza mata kai nace "wannan fa duk ba shine zaman lafiya ba Surayya. Halayyar kowa daban. Zaki ga wani mijin vaya sakar wa matarsa fuska irin haka amma hakan ba yana nufin wai baya sonta bane ba ko kuma basa jin dadin zama da juna ba, a'a halayyar sa ce haka"

Ta dago kai tana kallona kamar mai shirya maganar ta sannan tace "akwai kuma wadanda basa sakin fuskar, basa sakin aljihu, sannan kuma ga mummunar halayya mai cike da cutarwa ga iyalin su" na danyi shiru nima ina jera tawa maganar sannan nace "hakan kuma ba yana nufin su wadanda ake sakarwa fuskar suna cikin jin dadi bane ba. Za'a iya yin mamaki sosai idan aka san halin da suke ciki a sirrance. Watakila akwai abinda yake cin su ta ciki wanda ko da zasu furta ba lallai ne a fahimta ba" ta kama hannuna a natada naji shi da zafi "kin sani kenan Jidda? Kin san halayyar mazajen mu?" Na dago ina kallon ta, sai naji sanyi a raina, at least na samu wadda take fuskantar the same kalubale irin nawa, wadda na tabbatar zata fi kowa fahimta ta.

Na gyada kai "na sani Surayya, na sani tun ina amarya, tun kafin in haifi Yasmin" ta rufe baki da hannun ta, idonta yana kawo kwalla, "amma kullum kallon ki nake yi kamar hankalin ki a kwance yake, kamar vaki da wata matsala shi yasa ban taba ko da yunkurin gaya miki ba dan kar in tarwatsa farin cikin ki" nace "wani lokacin ba lallai ne abinda idon mu yake gane mana ya kasance shine gaskiya ba. Kowa da akwai battle din da yake fighting a rayuwarsa, ni na saka a raina wannan shine nawa kaddarar"

Ta girgiza kai "amma taki kaddarar da sauki Jidda, taki rayuwar da sauki sosai dan zan iya cewa ke a aljanna kike idan nayi comparing da kaina. Bansan yadda yanayin muamalar auratayyar ku take ba amma na tabbatar Umar yana baki kulawa kuma yana baki lokacin sa, ni kuwa fa? Jidda ko kallo ban ishi Bashir ba. Bashir ya kanyi sati biyu zuwa uku ba tare da ya bukace ni ba. Tsakani na dashi shine ya ajiye min kayan abinci ni kuma in zauna a gida in kuma amsa sunan matarsa"

"Jidda ban san ya kuke da Umar ba amma nasan yana gudun bacin ranki, yana kokarin boye miki halayyar sa, amma Bashir a fili yake abinsa babu ruwan sa da in gani ko kar in gani, babu ruwan sa da me zanyi in na gani, in ma zuciya zan hadiya in mutu shi babu ruwansa shi dai rayuwarsa kawai yake yi tamkar wanda bai yarda cewa akwai mutuwa kuma akwai hisabi ba"

"Babu irin chats dinsa da bana gani tare da mata, su tura masa hotunan tsiraicin su ya tura musu nasa, wayarsa da laptop dinsa a cike suke tap da pornography, kuma babu ruwansa da wai zan dauka in gani babu abinda ya dame shi. In na bishi daki ma na nuna ina bukatar sa zai iya tashi ya fito falo yayi kwanciyar sa yana sexting mata har yayi releasing kuma ya ajiye min wandon sa in wanke"

Na toshe kunne na ina taya ta kukan da take yi "ya isa Surayya ya isa, wannan wanne irin tashin hankali ne muke ciki? Ya zamu yi da rayuwar mu ne wai?" Tace "na gaya wa iyaye na, har shaida na dauka daga wayarsa na nuna musu cewa ga abinda yake yi amma sai suka ce me yasa na taba wayarsa? Ina ruwa na da abinda yake yi a wayarsa ai ni na jawo wa kaina bakin ciki tunda na duba masa waya. Wai ai kazantar da baka gani ba tsafta ce. Suka kuma kara da cewa zan bata zumunci, auren da aka yi dan a karfafa zumunci ni kuma zan bata shi. Sun dai ce sun kira shi sunyi masa fada amma ni banga chanjin komai ba, sai ma masifa da yayi min wai zan hada shi da mutane zan zubar masa da mutuncinsa. Daga nan kuma ya cigaba da kara daure min fuska. Yanzu nace gurin iyayensa zanje kuma in gwada can in gani"

Nayi saurin girgiza mata kai "don't try that. Ni ta can na fara kuma hanyar bata bille da ni ba sai ma kuma afkawa cikin matsala da nayi" tace "to ya zamuyi kenan? Wacce hanya zamu bi? Wacce ce mai bullewar? And the society and our families expects us to be good and obedient wives to such husbands. Abinda ake so muyi shine muyi ta hakuri, muyi musu ladabi da biyayya, sannan muyi ta addu'a. Mu daina bincike akan su ballantana muga kazantar da bamu san da ita ba, sannan kuma in mun sani ma kar mu nuna musu bacin ran mu mu danne zuciyar mu, wata rana zasu daina. What a selfish society! Amma kuma a tsakanin iyayen mu ko nasu ko kuma a cikin society din da wahala a samu wanda zai zaunar dasu ya nuna musu cewa abinda suke yi ba dai dai bane ba sannan kuma ya gaya musu su zama good husbands to us"

What a selfish life!

Mun jima muna wannan hirar da ita, a cikin hirar ne take sanar min da cewa farkon samda ta fara gane halayyar mijinta sai ya nuna mata laifin Umar ne, yace Umar ne ya koya masa kuma shi yake gada shi da mata tun a jami'a. Sai ni kuma nace mata "ba zan ce Umar ne yake koyawa Bashir ba, kamar yadda ba zan ce Bashir ne ya koya wa Umar ba, abinda kawai nasani shine kowa a cikin su halinsa ne sai kuma suka hadu suke abota. Ni a bangare na abinda nayi shine nace wa Umar ya rabu da Bashir, though ban tabbatar ya rabu da shi ko bai rabu da shi ba amma ni da shi bamu kuma yin hirar Bashir ba har yau. Ke ma a naki bangaren kiyi mana kokarin ganin kin matsawa Bashir ya rabu da Umar"

Ta rike baki "rufa min asiri, ni na isa ince da Bashir ga abokin da zai kula ga wanda ba zai kula ba? Kamar yadda na gaya miki, ba kowanne miji ne irin naki ba dan haka you should cherish what you have".

Tana gidan har su Umar suka dawo tare da yara gabakidaya, sai kuma tace zata tafi ni kuma naji tausayin ta ga tsohon ciki kuma nasan wannan mijin nata ba zuwa zaiyi ya dauke ta ba, sai na roki Umar ya barni na kai ta har gida a mota ta. A motar ma sai da tayi comment "ki duba kiga motar ki Jidda, amma ni in samu arzikin da zai dauke ni a tasa motar ma abu ya gagara"

A hanya ina dawowa sai na fara lissafa rayuwar Surayya da tawa, sai na fara tunanin tabbas kamar yadda ta fada a gurinta ni kamar a aljanna nake, in ana jin irin nata complain din bama za'a saurari nawa ba. Kuma at least ni na zaba wa kaina Umar, ita kuwa zaba mata Bashir aka yi, maybe ma da akwai wanda take so aka hana shi aka bawa dan uwa dan a karfafa zumunci.

I felt blessed for some days bayan zuwanta, sai kuma bakuwa ta uku ta zo min ta kwance min dukkan lissafi na.

Bakuwar itace Aira. Ta shigo min gida a firgice kamar wadda aka koro ta. Na tashi da sauri na rike ta ina tambayarta abinda ya faru "Aira wani ne ya mutu? Wani abin ne ya faru?" Sai ta rungume ni ta saka kuka. Nima na rungume ta ina jin kamar zanyi kukan duk da cewa ban san abinda take wa kukan ba.

Sai data gama ta dago sannan na zaunar da ita akan kujera na bata ruwa ta sha na kuma tambayar ta "me ya faru Aira? Ke da waye? Waya sauke ki a mota?" Ta goge hawayen ta tace "Musaddiq ne" (wanda aka saka ranar auren su) nace "fada kuka yi da Musaddiq din?" Ta girgiza kai "na raka shi kasuwa ne, muna hada kayan lefe, shine......shine.....shine..... " Ta cigaba da kukan ta, gaba na ya fadi, kar dai wani abin banza yayi mata a hanya, na shiga uku.

Nace "ki gaya min Aira mai Musaddiq din yayi miki?" Ta dakata da kukan ta "babu abinda yayi min Jidda, mun shiga Well Care ne muna siyayya sai kawai na ga yana dariya, sai ya nuna min wasu wai ga wani gara nan wata kilaki tana wanke shi, Jidda kin sa wa na gani?"

Ban amsa mata ba saboda yawun bakina da ya tsaya chak. "Jidda Daddy na na gani tare da wata da kallon farko na tabbatar wa kaina da cewa karuwa ce. Ta sha attachment da muguwar shiga, tana kuma makale da jikinsa suna ta raha da dariya" ta karasa tana cigaba da kukan ta

Naji kaina yayi wata irin sarawa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Aira kin tabbatar da abinda kike fada? Daddyn ki fa kika ce?" Tace "Jidda Daddy na ne wallahi. Musaddiq bai san fuskarsa ba tunda ba gurinsa suka je neman aure na ba gurin auncle din mu suka je"

Ta dauko wayarta tana budewa tace "na daki idon Musaddiq na dauki hoton su. Wallahi sai na nuna wa mommy ta ga abinda yake yi. Yanzu ni yaya zanyi da raina, yaya zan kalli Musaddiq idan ya fahimci tsohon da ya gani da karuwa shine mahaifina? Jidda na shiga uku. Jidda fasa auren nan zanyi gabakidaya dan na tabbatar wata rana sai ya goranta min. Kuma wallahi ina sonsa" ta karasa tana sake fashewa da kuka.

Na karbi wayar daga hannun ta, wayar da kuka ya hana ta karasa budewa ballantana ta miko min, na bude sannan na shiga gallery na nemo pictures din da tayi yanzu. Daddyn na dafa ganewa dan fuskarsa ta fito fes yana ta washe baki, sai kuma na gane matar da take makale a jikinsa, Zuwaira.

Bazan taba mantawa da fuskar ta ba kamar yadda bazan taba mantawa da murmushin da yake kan fuskarta ba, irin wanda take yi a cikin hotunan su data aiko min ita da Umar a Lagos. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" na sake ambata tare da ajjiye wayar.

"Kin gan su ko?" Aira ta fada "wallahi sai na nuna wa mommy" sai na mike batare da na ce mata komai ba na shiga daki na zauna tare da rufe fuskata da hannu na. Na tuno maganganun Aunty Afia.

"Nima na taba shiga irin matsalar da kike ciki a yanzu Jidda, amma da nayi hakuri na kuma dage da addu'a yanzu ba gashi komai ya wuce ba?"

Sai kuma na tuno da maganar daddyn Aira "ki bani sunan yarinyar, ni zanyi bincike akanta daga dabi'un ta zan gane gaskiyar lamarin, sai mu san yadda za'a shawo kan maganar"

Binciken da har yanzu ba'a kammala ba.

Ashe ba bincike yake yi ba, ashe kansa ya samarwa sabuwar kamu......

Ashe bai daina ba kamar yadda Aunty Afia tayi tunani, ashe ya kara kwarewa ne kawai wajen boye mata halin sa.......

Ashe role model din da nake bi har yanzu a cikin ruwa take tsundum bata sami fita ba ballantana ni da nabi hanyar ta in samu fita ni ma.

Na tashi na koma falo na tsaya ina kallon Aira, ina tunanin abinda zan ce mata, sai kawai naga a idona ta koma min Yasmin, Yasmin ta girma ta kama babanta in the act, me zance mata? Kiyi hakuri nima hakurin nake tayi? Sai naji a raina tabbas wannan ranar tana nan zuwa indai abubuwa basu chanja ba.


Forgive the typos please..........
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki sharing, in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*Mammy*

Na koma na zauna a kusa da ita sannan na dago kanta ina share mata hawayen ta. "Kiyi hakuri Aira. Kiyi hakuri ki daina kuka dan Allah" tace "ni yanzu yaya zanyi? Yanzu Jidda ashe wai Daddy na ne yake da wannan mummunar dabi'ar?" Na girgiza mata kai "kar ki ce haka Aira, Daddy ne fa, maybe ma ba abinda kike tunani bane a tsakanin su da wannan matar maybe abokiyar aikinsa ce ko something like that" ta girgiza kai da sauri, "baki gansu bane ba Jidda, baki ga matar nan ba kina ganin ta zaki san ko ita wacece daga yanayin shigarta, kina ganin yadda suke yi zaki fahimci abinda yake tsakanin su" sai ta sake wani sabon kukan. "wai babana. Jidda babana ne. Mutumin da duk mazan duniya babu wanda ya kai shi kima da mutunci a idona, mutumin da har addu'a nake Allah ya bani miji kamarsa saboda yadda yake kula da mu da mahaifiyar mu amma ashe da akwai abinda yake aikatawa a boye bamu sani ba. Shin anya ma kuwa akwai wadda tafi kowa rashin dacen uba a duniya iri na?" Na rufe mata baki da sauri "menene haka kike cewa Aira?" Sai naji hawaye ya taho idona, na rasa dalilin da yasa nake kwatanta Aira da Yasmin. Will Yasmin one day find out about her Daddy ita ma? Will she say tafi kowa rashin dacen uba itama? Will she ask me me yasa na zaba mata shi a matsayin uba? Wacce amsa zan bata then?

Ta sake tambaya ta. "Jidda me zanyi? Ta ina zan bullowa wannan lamarin? Yanzu dole sai na rabu da musaddiq dan ba zan iya nuna masa tsohon da ya gani tare da karuwa a supermarket kuma yayi wa dariya ya kira shi da gara in gaya masa cewa shine babana mahaifina da kullum nake nuna ina takama da shi ina takama da kasancewar sa mahaifina ba. Ya zanyi Jidda?"

Na sunkuyar da kaina ina tunani, sai kuma na dago ina kallon ta nace "nima bansan abinda zaki yi ba Aira. Bansan ta yadda za'a warware wannan lamarin ba. Amma ina ganin shi wanda ya kulla komai shine ya kamata ya san yadda zaiyi ya warware komai" Tace "ban gane ba" nace "Daddy. Shi zaki kaiwa pictures din nan ki luma gaya masa abinda ya faru. Ki kuma nuna masa yadda kike ji a zuciyar ki a game da shi. Tsuntsun da ya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. In kin gayawa Aunty kin nuna mata pictures zata tashi hankalin ta taji kunya bayan ba ita ta aikata abin kunya ba, zata shiga damuwa da kunci bayan ba ita ce mai laifi ba. Za ta fara neman maganin matsalar da ba tata bace ba. Problem dinsa ne dan haka let him face it by himself. Kar ki matsawa Aunty tayi miki bayani akan laifin da ita ba ita tayi ba, rather ki matsa masa shi da yayi laifin shi yayi miki bayani kuma yasan solution din dazai samar miki a matsalar da shine ya saka ki a ciki"

Ta yi shiru tana kallona, daga alama maganganu na sun shige ta sai kuma ta dauki wayar ta da sauri ta mike. "Nagode Jidda, zanje in same shi kuma sai yayi min bayanin dalilin da yasa ya zabi ya kunyata mu mu ƴaƴan sa a idon duniya, sai ya gaya min dalilin da yasa zai zama sanadiyyar da dole zan hakura da auren Musaddiq"

Tayi hanyar waje da sauri ranta a tsananin bace, na sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen fuskata a raina nace "good. Yau zaiyi facing abinda maybe bai taba tsammani ba. Maybe kunyar wannan abin ya zama sanadiyyar shiryuwar sa".

Ranar har dare duk zuciyata babu dadi, har Umar yazo na gama sallamar sa na kuma gama da yara kawai sai na tafi daki na bar su tare a palo, a haka har suka yi bacci sannan ya shigo yace inje in kwantar dasu shi kuma ya shiga wanka. Ina kwantar dasu a dakina na dawo na kwanta a dakinsa na juya bayana na rufe ido na, a raina ina lissafin rayuwar da Aunty Afia tayi a baya da kuma irin alkawarirrikan da na tabbatar daddyn Aira yayi mata na cewa ya daina, maybe tun bata yarda ya daina din ba har tazo ta yarda kuma ta cigaba da yarda har yau. I can't even imagine how broken she will ve in wannan labarin ya same ta. I can't imagine how broken I will be idan ni ce a matsayin ta.

Har dare ranar bana cikin walwala, har Umar ya dawo na sallame shi na kuma gama da yara suma sai na tafi daki nayi kwanciya ta na barsu a falo, sai da suka yi bacci sannan Umar ya zo ya ce inje in kwantar dasu, na kwantar dasu a dakina nayi musu addu'a sannan na dawo dakin Umar na tarar yana wanka sai na kwanta na juya bayana na rufe idona, hoping in ya fito zaiyi kwanciyar sa dan ni kam bana cikin mood kuma bana jin duk dadin bakinsa akwai abinda zai yi ya sakani in the mood.

Ina kwance ya fito, naji ya watsamin ruwan gashin kansa a fuskata. Na bude ido ina kallon sa yace "nasan dama ba bacci kike yi ba. A penny for your thoughts?" Na danyi murmushi kawai na mayar da ido na na rufe. Naji ya hawo kan gadon na sake bude ido na ganshi kwance ruf da ciki yayi tagumi da

55 / 106