Chapter 3 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 106

6K to 9K   out of 316K words

rana daya yazo yace ya samo mata miji, dan tsohon abokinsa, five months later tana dakin mijinta, shekara ta zagayo da baby a kan cinyarta. Naji cikina yayi karar tsoro.

Ta cigaba da magana "idan kika yi karatu kuma kika ci exams dinki, kina da chance da zaki tafi school kiyi ilimi, ki kara warewa ki kara class ki kara kyau ki kara shekaru. Add these to your beauty, wannan wanda kike so din zai iya lasar takalmin ki dan ki bashi minti daya yayi magana da ke" na gyada kai, already ina hango Dr Umar yana bina a baya kamar jela ni kuma ina ja masa aji son raina, yes, wannan tunanin kadai ya isa ya saka in maida hankali na kan karatu na.

And it did.....

Ban ce na daina tunanin Umar ba amma tunanin nasa sai ya zama shi yake kara min kaimi wajen ganin naci exams dina dan in same shi.

Farhan bata zo ba kamar yadda tayi min alkawari a letter din da ta rubuto min, haka zalika su umma basu zo ba kamar yadda Abba yayi min alkawari, sai dai da muka yi waya a wayar wani copper da ya kan bamu waya a boye mu kira gida, sun bani hakuri cewa basu samu dama bane ba, ni kuma nasan ba wai dama ce basu samu ba tunda dai babu abinda suke yi a gidan, babu aiki babu sana'a, nasan dai Abba ne bai bar su suzo ba, zai ce ne bashi da kudi ko kuma yace za'a shagwaba ni ko kuma wani excuse din da shi kadai zai fahimci ma'anar sa.

Farhan kuma da yaya Mukhtar da Aunty Halima, nasan Hajiya ce zata hana su zuwa. Wannan bani da ko shakka akai.

Lafiya lau muka cigaba da exams din mu, na cigaba da rike kambu na, na cigaba da tabbatar wa cewa Mufida bata san cewa akwai wani abu a zuciya ta a dangane da yayan ta ba. A haka har muka zana final paper din mu. Hausa language. Ranar da ta zama ranar graduation din mu. Ranar kuma da nayi masa gani na biyu a rayuwata. Ranar kuma da ya yi ban ruwa akan shukar daya riga yayi a cikin fadarsa dake zuciyata.

Tun saura sati daya graduation din mu aka fara shirye-shirye, ana ta gabatar da programs na yin bankwana da mu, kowanne club yana shirya wa members dinsa dinner da kuma dan entertainment haka sannan kuma a bayar da gifts, a ciki nima na dan samu rabo na babu laifi. Kyautar da na samu ta farko ita ce ta tsafta kuma dama kusan duk shekara ina samun wannan kyautar, ba wai nafi kowa tsafta bane a set din mu ba, a'a, ni abinda nake ganin ya sa ake bani wannan kyautar bayan tsafta ta wadda na san ina da ita to akwai gayu kuma. Gashi dai ni ba yar masu kudi sosai can ba amma ina da daukar wanka ko da kuwa a cikin uniform ne ballantana a gida. Kuma sanyin jikina sai yake karawa gayun nawa kyau, komai a nutse nake yinsa a tsare. Wannan ya saka aka bani health prefect, sannan kuma yanzu da zamu yi graduation aka sake bani kyautar tsafta.

Bayan ita ma kuma na samu kyautar third overall student, sannan in-coming health prefect ita ma ta bani kyauta kamar yadda yake al'ada ta makarantar. A harkar sports ma an raba kyaututtuka, amma ni ban sami komai ba saboda hardly in yi sport ko ranar sport day ne, sai dai in an matsa min sai inje inyi table tennis, dan ni duk abinda zai saka ni wahala bana son sa.

Amma duk da haka sai aka raba mana wani hand band wanda akayi customising dinsa kowa da sunansa da kuma sunan makaranta da graduation year a jiki, an yi masa ado mai kyau haka kamar saƙa da different colors masu daukan ido. Ana bani nawa na karba ina karantawa "JIDDA. Beauty Queen" sai kuma sauran rubutu, nayi murmushi ina jin a raina ina son abin, na bare shi a ledar sa na saka a hannuna, naga ya danyi min yawa kadan amma a raina nace in naje gida naci abincin gida na huta nasan zanyi kiba kuma zaiyi min dai dai.

Ranar da za mu bar makarantar, paper din mu ta karshe ita ce hausa dan haka ba wani karatu mukayi sosai ba, da daddare ana ta kitson candy da lalle masu hada kaya nayi masu kukan rabuwa da juna nayi nasu kida da table da rawar murna nayi. Ni dai ranar na wuni dakin su Maryam kawata.

Maryam kawata ce, dan zan iya cewa a lokacin bayan Mufida sai ita a layin kawaye na, babban abinda ya hada mu kawance da Maryam shine gayun mu da yake kusan iri daya, amma ita kasancewarta yar talakawa futuk sai ya zama gayun nata ya zama kamar karya dan tana daukar wa kanta abinda yafi karfin ta ne, wannan ya saka tamu tafi zama daya da Mufida, ita kuma yar masu kudi ce sosai amma kuma down to earth, funny, and sweet, sannan kuma tana so na.

Tun safe ina kwance gadon Maryam ina ta cike slum books din da ban zauna na cike ba, masu su suna ta bina suna hada ni da Allah da Annabi, sai a ranar na cike musu wasu kuma na bawa Maryam ta taya ni cike wa dan sunyi min yawa, muna yi muna hirar mu da nishadi.

Bayan mun gama ta wanke min kaina, muna ta rigima dan ni babu abinda na tsana irin a taba min gashina, sannan bayan tayi towel drying gashin tayi oiling sannan ta fara min kitso inata mita ina cewa tayi min manya ita kuma tace kanana zata yi min, ai kuwa ita kanta sai da jikinta ya gaya mata saboda gashina cika ne dashi in ina kitso kamar ba zai kare ba, jelar ma kuma in tayi rabi sai ta saka band ta daure ta ta barta a haka dan in bata daure ba warwarewa zaiyi.

Haka muka zauna har bayan magrib, taje tayi sallah ta dawo muka cigaba, da yake ni ina off, har ishai muna abu daya, sai ga Mufida tazo ta zauna a gurin mu ita ma sannan da kyar aka gama kitson. Yan ƙanana, kitson da ina jin ban kuma yarda anyi min masu kankantar su ba.

Kusan kwanan zaune mukayi a ranar muna hira, muyi hira muyi kukan murna muyi kukan bakin cikin rabuwa sannan kuma muyi dariyar jin dadi. Da assuba muka kammala hada duk wasu sauran kayayyakin amfanin mu dan kusan komai mun bayar dashi sai few abubuwan da suke da muhimmanci muka dauka. Da sassafe muka kai kayan mu bakin gate din makaranta muka koma ciki sannan muka yi wanka muka shirya a tsanake muka fito daga hostel bayan munyi bankwana da metrons da sauran daliban da muka bari a bayan mu, muka tafi exam hall muka zauna, sai a lokacin ne muka danyi karatu kadan kafin a shigo mana, ana shigowa kuwa muka ajiye komai muka rubuta final paper din mu.

Kowa yana gamawa, daga mai ihu sai mai tsalle sai masu rungume juna suna kukan dadi da kuma na rabuwa, amma ni sai na samu kaina da tunani.

Wannan fa shine kamar wata border a rayuwa ta, kamar with this final paper na ajiye duk wani childhood dina kenan. Na zama cikakkiyar budurwa, kamar yadda nake kallon wadanda suka yi candy a matsayin manyan yammata nima na shiga cikin su kenan yanzu.

And my battle begins......

Neman admission, samari, aure ko karatu, yaushe zaki yi aure, samari yan yaudara da yan iska......duk yanzu zanyi facing dinsu in full scale. Am I ready?

Ni dama haka nake a rayuwata ina da tsoron chanji, na gammace in ta jure halin da nake ciki akan in nemi chanji sai imta jin tsoron irin kalubalen da zan fuskanta a sabon babin da zan bude, but wannan babi ne da dolen dole in bude shi, ba wai shawara ta bace ba, a'a dole ne.

Tunanin cewa aure yana daga cikin abinda wannan sabon babi na rayuwata ya kunsa sai ya dawo min da tunanin sa, though dama ba wai tafiya tunanin yayi ba, but sai naji son ganinsa ya dawo min sabo, sai na ji a raina ina addu'ar ina ma yazo daukan kanwarsa? At least nasan zan raka ta mota ko kadan ne sai in samu damar satar kallon sa ko da kuwa bamuyi magana ba.

Mufida ce ta katse min tunani na ta hanyar zuwa ta dane min jikina tana ihun murna, daga nan komai ya rike ce, muka fara bin malamai muna yi musu sallama su kuma suna yi mana nasiha akan rayuwa, wadanda already aka zo dauka suka fara tafiya. Ana ta exchanging phone numbers musamman a gurin wadanda suke da waya, mu kuma wadanda bamu da ita sai muke bayar da wayar wani da za'a same mu tare, ni dai wayar Umma nake bayarwa.

Muna cikin haka aka zo kiran Mufida, nan take naji cikina ya murda sosai kamar zanje toilet, Muka kama hannun juna muka fito daga hall din tare, a raina ina son in raka ta ko Allah zai saka shine yazo daukanta sai in ganshi, har munyi nisa sai kuma na ja na tsaya ina tambayar kaina ina aji na yake? Ai ba dan Allah nake da niyyar raka tan ba sai dan in ganshi, in dai har shine yazo daukan ta zan so ace shima yana son ganina dan haka shi zai aiko a kira ni ba wai ni inje kafin ma ya neme ni ba.

Sai na saki hannunta ina girgiza kaina "kije kawai Mufida, na tuna nayi mantuwa a hostel kuma nasan an kusa zuwa dauka na, ki je kawai zamuyi waya in na je gida" ta tsaya tana kallona, daga dukkan alama bata ji dadin magana ta ba kuma na saka ran zata yi retaliating amma sai naga ta gyada kai tace "shikenan. Allah ya kiyaye hanya. Ki kira ni fa kina zuwa gida. Ki gaida Umma da Amira" nace "zasu ji. Ki gaida kowa" a raina ina son ko sakon gaisuwa ne in aika masa amma pride ya hana ni, na juya na koma inda na fito.

Sai dai ban gama sauraron labarin da Maryam take bani ba, duk da ba fahimta nake yi ba, sai ganin Mufida nayi a gaba na. Gaba na ya fadi, muka tsaya muna kallon juna sannan muryar ta can kasa tace "ki zo wai.....inji Yaya Doctor" gaba na ya fadi, har wani gumi naji ya karyo min, kafin in bada amsa Sai ta juya ta fita, wani side na zuciyata ya ce min inyi zamana kar inje, wani kuma, inda already dama yake daukin ganin sa ya fara tsallen murnar ganinsa, nasan babu yadda zanyi in rarrashe shi ya hakura dan haka na tashi na bita a baya.

Har tayi nisa saboda sauri take yi, ni kuma ban iya sauri ba kuma ba zanyi saurin zuwa saurayi ba dan haka na cigaba da catwalking abina. Sai kuma naga ta tsaya can nesa kadan da inda naga mota irin wadda rannan suka zo a cikinta. Na karasa kusa da ita na tsaya nima bance komai ba, a raina ina jin babu dadi abinda tayi min, ta juyo tana kallona sannan tace "daga Abuja yake, suna can shida Daddy, yaji yau zan yi graduating shine ya dauko hanya tun asuba ya taho dan yana so yazo ta ganki, ba wai dan ya dauke ni ba" na bita da kallo, ina jin zakin maganar ta kamar suga a zuciyata, amma kuma bana jin dadin yanayin da take yi min maganar da shi.

Ban ba ta amsa ba ya bude kofar motar ya fito, numfashina da bugun zuciya ta duk suka tsaya a tare, ya saka shadda ruwan zuma kansa da hula ba kamar ranar nan ba, sai naji na kasa tantance yaushe ne yafi kyau, ranar nan ko kuma yau?

Na taka a hankali na tafi inda yake, dan nasan ni yake jira kuma nasan in banje ba zai iya tahowa kuma inda muke tsaye ana iya hango mutum tun daga exam hall din da sauran daliban suke ciki.

Kafin in karasa naga ya zagaya daya side din motar ya bude kofar gidan gaba sannan ya tsaya a bakin kofar tare dayi min nunin cewa in shiga da dayan hannunsa, fuskar sa dauke da irresistable murmushi. Naje gabansa na tsaya idanuna a cikin nasa, sannan a hankali na sauke idona kasa. Naga kofar motar daya bude na kuma fahimci me yake nufi da hakan amma nayi ignoring. "Sannu da zuwa" na fada da sassanyar muryata. "Yauwa nagode" ya amsa, "bismillah" ya fada yana sake nuna cikin motar da hannun sa, na daga kai ina kallon fuskarsa amma ban shiga ba sai yace "ba cinye ki zanyi ba fa, I promise, ina so muyi magana ne amma bana son muyi a nan saboda........" Ya nuna jama'ar da suke ta zirga zirga a wajen.

Na gyada kai na. Zan so inji abinda yake so muyi magana akai amma ba zanso Abba ya shigo ya ganni a tsaye tare da wani wanda bai sani ba. Ƙwaƙwalwa ta tayi kokarin tuna min da cewa gwara ya ganni a tsaye tare da wani akan ya ganni a cikin motar wani, amma sai zuciyata tayi saurin kawar da warning din, dan tana so ta farantawa abin son ta.

Na sunkuya na shiga motar na zauna tare da dora yar karamar jakar hannuna a kan cinyata, idanuna akan hannayena, ina jin sa ya rufe kofar sannan ya zagayo seat din driver ya bude ya shigo tare da rufewa.

Na rike numfashi na ina jin rashin dacewar zaman mu har cikin zuciya ta, I had never been so close to namijin da ba muharrami na ba kamar haka. Na kasa dago ido in kalleshi amma ina jin idan sa a kaina, na dan ja hijabi na ina kara rufe cinyoyi na da suka bayyana kasancewar wandon uniform ne a jiki na kuma hijabin mu bashi da girma sosai. Sai kuma na tuna cewa ban gaishe shi ba. "Ina kwana?" Na fada da muryar da naji kamar ba tawa ba. Bai amsa ba sai kallo na daya cigaba da yi, na fara tunanin in bude motar in fita sai naji yace "wai dan Allah in tambaye ki Jidda, ke wacce tribe ce?" Na dago da sauri muka hada ido, sai dai banyi mamakin tambayar tasa ba saboda na sha jin irinta a gurin mutanen da basu san ni ba.

Yace "ina ganinki ranar nan sai nayi tunanin bafulatana ce, sai dana kalla sosai naga cewa ba ita bace ba and definitely not Hausa and not kanuri, nooooo bayin nan basu da wannan kyan, and I thought about shuwa but idanunki ba irin nasu bane ba, idan ma sune to an samu mix, ba dan kalar fatar ba kuma zan iya cewa Arab but skin din ba tasu bace ba" ya dan rage ido yana kara kallon fuskata, sai na kama kasan hijab dina zan rufe fuskar sai kuma na tuna hakan yana nufin bude cinyoyi na, sai na saki hijab din na rufe da hannu na.

Ina jin shi yayi dariya kadan. "Please ki gaya min mana, it kept me awake at night, inyi ta tunani, har pictures din girls from different tribes nake browsing ina comparing da taki fuskar dana riga na dauki hotonta na kuma yi saving anan...." Ya fada yana nuna kirjinsa. Na bude fuskata inajin maganganun sa kamar busar sarewa a kunne na saboda dadin su, amma na dage wajen kin nuna hakan a fuska ta.

Nace "kace zamuyi magana, ina dan sauri ne kar azo daukana ayi ta nemana. Wacce maganar zamuyi?" Ya dan gyara zama da serious murya yace "taimako nazo nema gurin ki Jidda" naji gaba na ya fadi nace "taimako kuma? Wanne irin taimako?" A take zuciya ta ta fara lissafo irin abubuwan da zan iyayi dominsa, sai ya dan langwabe kai "bani da lafiya, magani nazo ki bani" na kalleshi da sauri, a idona sai naga yayi kamar mara lafiyan gaske, kamar ya dan rame akan wancan ganin da nayi masa, nace "me yake damunka? Ni bani da magani ai, kai ba Doctor bane ba ka duba kan ka mana?"

Ya danyi murmushi still idonsa cikin nawa yace "nayi kokarin treating kaina na kasa, har allura nayi wa kaina duk da bana son allura amma ban warke ba" na danyi shiru ina assessing maganar "to ka fada mana a gida sai a kaika gurin wani likitan ya duba ka? Ni ai ban iya duba marasa lafiya ba, me yasa zaka taho guri na?" Ya sake fadada murmushin sa, idanuwan sa suna sake yi min kyau, na kasa dauke idona daga kansa a hankali kamar mai rada yace "saboda kina da nasaba da abinda yake damuna" nima nayi magana a hankali "zazzabi ne yake damun ka ko mura? In zazzabi ne zan baka paracetamol in mura ce kuma...." "Nan ne yake min ciwo" ya fada yana nuna kirjinsa, ɓangaren da zuciyarsa take, "kuma bana iya bacci, in na rufe ido na sai inyi ta ganin ki kina yi min murmushi, irin wanda kika yi min ranar nan da kuna tafiya ke da Mufida, shine na dawo in roke ki Allah da Annabi ki sake yi min wani irinsa, ko wanda ya fishi"

"Wannan shine maganin ciwo na, shine abinda zai warkar dani, shine abinda ya saka yau nayi driving seven hours straight dan in ganki, ina fatan ba zaki hana min ba" na cire idona daga cikin nasa na mayar dasu kan hannayena da absentmindedly suke wasa da strings din jakata, a raina ina tunanin ko dai mafarki nake yi? A cikin ire ire-iren mafarkan da nake yi nasa, amma it felt sooo real, kalaman sa felt as real as kamannin sa.

"Please......" Ya kuma roka, "please kar kice nayi zuwan banza, ko fake smile ne a bani ina so a haka, amma nafi son real din, in son samu ne a hada min harda dariya ko yar karama ce"

Ban san yaya akayi ba sai kawai jin murmushi nayi akan fuskata,

3 / 106