Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
Nace "saboda a cikin mata nake kuma banyi tunanin wani gardi zai shigo ya rufe kofa ya tsaya yana kare min kallo ba"
"Gardi?" Ya maimaita, nace "ba shi bane ba?" Ya nuna kansa "I am Umar, your husband" ya fada yana nuna kansa kamar mau tunanin ban gane shi ba. Nace "point of correction. Ex husband. Now if you will excuse me kamar yadda na fada maka ina sauri ne zan tafi gidan dan baba na baya barina inyi dare a waje"
Ya dan matsa baya kadan ni kuma na bude kofar da dan karfi making sure ta dake shi sannan ba tare da na kalle shi ba ballantana in yi masa sannu na fita falo.
Sai dai ina fita naji motsinsa da kamshin sa a bayana, na matsa gefe da sauri sannan ya samu damar shiga palon sosai. Sai a lokacin na lura cewa zuwansa kenan gidan daga airport dan yadda sisters dinsa suka fara rige rigen zuwa su rungume shi. Sauran yanuwa da basu gama tafiya ba suma duk suka mike ana ta murna tare da tambayar sa jikinsa, abokan wasa suna tsokanar sa da "gawa ta ƙi rami" wasu kuma da basu san mun rabu ba suna zolayarsa da cewa daga shigowa gidan sai ya tafi gurina maimakon yazo gurin Mama ta fara ganinsa tukunna.
Na lura da yadda ya durkusa nesa kadan ya gaishe da Mama da kuma Aunty, sabanin da yadda yake zuwa ya rungume Mama ko ya kwanta a jikin ta, itama kuma tana zaune a i da take tunda ya shigo bata yi irin rawar kan da take yi akan sa ba.
Ni dai na wuce su na shiga dakin Aunty inda sauran kawayen mu suke jira na na kawo musu soveniers din su. Naga Asad da Yasmin suna game a wayar Mufida, casually nace musu, "kids! Ku je falo ga Daddy can ya zo" suka juyo da sauri suna kallona da budaddun idanuwan su kamar basu yarda da abinda nace ba sai na kara cewa "da gaske nake fa, ko ya koma ne?"
A guje suka yar da wayar hannunsu suka zuba tsere zuwa falo, na bisu da murmushi sannan na juyo ina kallon Mufida wadda nayi tsammanin da ita za'a yi tseren zuwa taryar Umar amma sai naga ta dauki wayarta da suka yar tana gogewa tana murmushi. Nace "ke ba zaki taryar yaya Doctor din ba" bata kalle ni ba tace "munyi waya ai. Ni na ce masa kina kitchen" na harare ta sai tayi dariya. But still nayi tunanin zata je amma bata je ba. And I wondered me yasa suka zama distant.
Ina gama hada kayana na fito zam tafi tare da yiwa Mufida alkawarin zan dawo washegari daurin aure da kai amarya duk da nasan ba cika alkawarin zanyi ba dan bana son abinda zai kuma hada ni da Umar a cikin gidan su, koma ina son dawowar na tabbatar Abba ba zai bari ba. Sai dai ina fita falo na ganshi zaune akan carpet hannayensa biyu rungume da yayansa da suke bashi labari su biyu at the same time, shi kuma sai murmushi yake yana shafa kitson Yasmin. Ban so mu kuma haduwa ba amma dole in bi ta falon idan zan fita, kuma in nace zan bari sai ya tafi to tabbas zan kara dare inyi laifi a gurin Abba.
Na dan tsaya daga gefe nayi wa Mama da Aunty sallama, naga alamar Mama bata ji dadin hakan ba tana ta kallon sauran matan gurin da suke kallona cikin alamar tambaya. Ni kuma ko a jiki na dan ni banga amfanin boyewar ba.
Sai kuma tayi saurin cewa "Umar kaje ka kaita gidan mana, sai ka dawo" ban ce komai ba na fita amma nasan ba abinda zai shigar dani motar Umar. Sai dai ba zan yarfa ta a gaban mutane ba.
Ya mike a hankali yana cije lips dinsa alamar har yanzu baya jin dadi. Ya biyo baya na su Yasmin suka biyo mu suma Asad yana rike hannunsa "Daddy muma zamu bi ku" Yasmin tace "mommy gidan mu zamu tafi ko?" Ban kula su ba dukkan su na fita compound sannan na kama hanyar gate ina zabga sauri. Ya dan kara sauri ya kamo ni su Yasmin suna dan baya kadan yace "ba zaki zo in kai ki ba ko?" Nace "eh. And don't insist in ba haka ba zaka jawo hankalin mutane kan mu" ya gyada kai "it is okay. Just give me the time da zamuyi magana. I tried communicating to you several times amma ba kya responding. Tunda na fara shirin dawowa alla I can think of is seeing and talking to you. Ironing things. Shi yasa ina sauka na kira Mufida na tambaye ta inda kike tunda ina saka ran kinzo bikinta. Please Jidda, na san kin tsane ni yanxu and all that but just hear me out....."
Na dakata da tafiyar da nake yi na juyo ina kallon sa ina jin raina yana baci nace "I don't hate you Umar. I just don't care. I don't want to talk to you. I don't want to hear anything from you. Ina yi maka fatan alkhairi. That's all"
Ya juyo sosai muna facing juna ta cikin sauran hasken gari da bai gama tafiya ba. Yace "ko ba zaki ji komai ba ina so kiji dalilin da yasa na rubuta miki wannan takardar. Dalili biyu ne. Na farko dan ina so in nesanta ki da kaina, ina so in cire miki title na mata ta dan ina tsoron kar cikin bakaken kaddarorin da suke fada min a lokacin su fada a kanki. Na biyu kuma ina so inyi respecting wishes dinki na rabuwa da ni. Ina so ki fahimci cewa na yarda zaki iya rayuwa babu ni kamar yadda kika sha fada min. Sai dai kuma a watanni hudun nan na fahimci cewa ni din ba zan iya rayuwa babu ke ba kamar yadda nayi gangancin fada miki ranar nan....."
Na juya na cigaba da tafiya ina jin dacin da na jima ban ji shi ba yana kawo ziyara makogwarona. Ya cigaba da tafiya a gefe na "Jidda ciwon zuciya nake fama da shi. Incurable. Na samu sauki amma ba zan warke ba har abada dashi zan tafi kabari na" na juyo da sauri nace "kamar yadda nima hawan jinin da ka saka min dashi zan tafi kabari na. At least gwara kai, kai ka jawo wa kanka ciwon ni kuma bakin cikin ka ne ya saka min. Na riga na wuce wannan babin, na rufe wannan bad chapter din ta rayuwa ta, yanzu na bude sabuwa fil mai cike da farin ciki da albishir na tarin alkhairai, please Umar let me be. Save every the heart ache and face your life, kaje ka kula da matarka da abinda yake cikin ta Allah ya baku zaman lafiya ya kawo albarkar aure"
Naga alamar fuskarsa ta chanja, na juya zan tafi ya rike gefen hijab dina "what did you just said?" Na yi masa kallon sama da kasa nace "cikin ka na jikin Asabe nace kaje ka kula da shi. Menene abin mamaki a ciki?"
Ya saki hijab din sannan ya gyara tsayuwarsa yana kallona "ita tace miki tana da ciki?" Nace "ni naga tana da ciki. Ko bata gaya maka ba? Ohh sorry na shiga maganar da ba tawa ba. Maybe ma ba cikin bane ba, maybe dan tana kara samun kulawar kane a matsayin ka na namiji shi yasa na ga ta kara cika. In ba cikin bane ba ma ina fatan Allah ya kawo cikin"
Sannan na daga kafa da sauri na karasa gate ina jiyo muryoyin su Asad suna masa tambayoyin mai yasa ba zai kai ni gida ba kuma yaushe zamu koma gidan mu.
Ina fita na tari adaidaita na shiga muka tafi, sai da muka danyi nisa sannan na rufe fuska ta da hannu na na fara kuka a hankali.
*Umar*
Ya bi bayanta da kallo har ta fita daga gate din sannan ya dawo da dubansa kan yayansa da suke gabansa suna ta jera masa tambayoyin da ba fahimta ma yake yi ba. Ya sunkuya ya dauki Asad yayi kissing cheeks dinsa. "Sarkin surutu. Ka koyawa mamana magana ko?" Sai kuma yaran suka fara musun wanda yafi wani surutu a cikin su. Daga nan sai ya nufi dakin da yake matsayin nasa a gidan, dana already yace a kai masa kayansa can.
"Muje in baku tsarabar ku" nan da nan suka manta da waccan maganar suka fara murna. Sai dai bai iya karasa wa dakin da Asad a hannunsa ba dole ya ajiye shi yana haki tare da dafe kirjinsa, sai kuma ya rike hannayen su suka tafi.
A dakin ya dauko musu jakar da yayi musu tsaraba ya ajiye musu yace kowa ya dauki nasa shi kuma ya zauna yana kallon su suna ta rabo, wani lokacin kuma ayi fada, amma kuma a zahiri ba wai kallonsu yake yi ba hankalinsa yana wani gurin ne daban, yana tuna yadda rayuwarsa ta juya lokaci daya kamar yadda mai suyar waina take juya wainar ta a cikin tanda. Sannan ta cigaba da gasuwa kamar ana babbaka kan rago.
Cikin sauki ya rubuta takardar ya kuma bata cikin minutes ya fita daga falon amma abin da ya biyo baya is far from sauki. Ya tura mata message dan yana tsoron kar ta dauka ya sake ta ne saboda ya daina sonta ko wani abu irin haka, amma amsar data bashi a lokacin ta kara saka masa tsoron anya ita din bata daina son sa ba.
"Ba so nake inyi proving cewa zan iya rabuwa da kai ba, so nake inyi proving zan iya rayuwa babu kai"
Sai yanzu bayan watanni hudu daya ganta sannan ya tabbatar she meant what she said.
Ta chanja gabakidaya tayi kiba ta kara kyau har da wani glowing da fatarta take yi wanda shi dai tunda take gidan sa bai taba ganin tayi irinsa ba ko da kuwa tana da ciki ne. A cikin wata hudu kachal. Sannan da akwai wani atmosphere of confidence a tare da ita wanda da bai san tana da shi ba. Akwai kuma wani kwarjini da tayi masa na musamman.
Ya tuna lokacin da tana gidansa babu irin mitar da Mama bata yi mata "kin ƙi kwantar da hankalin ki kiyi kiba. Sai fama kike kullum a kanjame kamar kazar mayu". Sai dai shi a lokacin ya jingina rashin kibar tata da cewa haka yanayin jikinta yake "jikinta ba mai kiba bane ba". But now he knows better.
She said she is beyond caring and he understands. Ya tuna sanda take zama tayi kuka kamar ranta zai fita saboda shi. Ya tuna sanda tayi ta fama da hawan jini kamar zata mutu saboda shi. Ya tuna lokacin da ta kusa samun depression saboda shi.
A lokacin ya sani ya san cewa she is depressed amma ko professional care ya ƙi nemar mata saboda son kan sa, saboda tsoron kar asirin halayyar sa ya tonu, yayi ta gaya wa kansa cewa she will fet better knowing too well cewa there are chances that she won't, there are even chances that zata iya rasa hankalin ta baki daya but he still chooses rufin asirin sa. And now she chooses her happiness. And no matter how much he tried ya san bata da laifi.
But now he knows cewa yana wasa ne da wuta kuma yanzu ta kama jikinsa tana ci. Yasan waccan yarinyar da ta fita daga gate bayan ta gaya masa maganganu, da ita ce kadai zai iya rayuwa a matsayin mata da miji. Ita ce kadai matarsa or else zai mutu marar aure.
"Ex-husband"
Ya tuno abinda ta kira shi da shi. Ex. Title din da shi ya rubutawa kansa ya saka hannu sannan ya buga stamp akai. Ta yadda zaiyi kuma ya cirewa kansa wannan title din a yanxu bai sani ba. Ta yadda zaiyi kuma rayuwa da wannan tittle din bai sani ba.
Shi mijin Jidda ne. Shine abinda ya sani. Mijin Jidda ita kadai.
Wannan maganar ta tuna masa da maganar da Jiddan ta fada kafin ta fita, cewa Asabe tana da ciki. Ya mike zaune yana jin wani tunani yana zuwa masa. Jidda might be wrong duk da cewa ita maaikaciyar asibiti ce kuma ta haihu har sau biyu, but yana fata har cikin zuciyarsa cewa maganar Jiddan ta zama gaskiya. Yana fatan ya kasance ciki ne a jikin munafukar yarinyar nan. Tabbas in hakan ta kasance ya samu hanyar warware daya daga cikin matsalolin sa.
The last four months has been rough on him. Daga inda yayi packing ya aikawa da Jidda message bai iya fitowa daga motar ba sai fitowa da shi akayi, wani bawan Allah da yazo wucewa ya tarar dashi yana fisgar numfashi hannunsa dafe da kirjinsa da yake jin sa kamar ana hura balloon din a cikinsa.
Daga nan mutumin ya kai shi asibiti, wanda kafin su karasa ma yayi loosing conscious dinsa, wannan ya sa sai daya kwana biyu a asibitin kafin a gano yanuwansa saboda kasancewar wayarsa da password, sai da aka koma motar sa aka samo ID card dinsa a ciki.
Duk da cewa a lokacin bai san inda kansa yake ba amma bayan dawowarsa hayyacinsa ya fahimci irin tashin hankalin da iyayensa suka shiga a sanadiyar rashin lafiyar sa, sai ya fahimci ashe dai suna sonsa har yanzu, ashe dai bai rasa su ba kamar yadda yake fadawa kansa. Ashe dai babu abinda da zaiyi da zai saka iyayensa su guje shi.
Su suka yi jinyar sa har ya farfado ranar da Jidda da yaransu zasu bar kasar, he expected sympathy daga gare ta, he expected tayi cancelling flight din ta taho tayi jinyarsa daga nan su mayar da auren su. Amma ko duriyarta bai kara ji ba. Wayoyinta basa shiga, and she is offline a dukkan social media accounts dinta, gashi bashi da number din kowa nasu a can, kuma bashi da guts din zuwa gurin Abba ya nemi layin da zai same su. Wannan ne ya sa ciwonsa yaki ci gaba yaki ci baya kullum jiya i yau, ko an sallamo shi daga asibiti baya kwana biyu zai sake komawa, tun yana kawaici da alkunya har ya fara fitowa yana tambayar yan'uwa su nemo masa Jidda da yaransa.
He never thought she can go through months without hearing from him, musamman tunda ta san ba shi da lafiya. Sai ya fahimci tabbas Jiddan da ya sani a da da kuma Jiddan yanzu are two entirely different jiddas.
Worsening din ciwonsa ya saka dole likitan da yake duba shi a Nigeria yayi referring dinsa to wani likitan a Dubai wanda ya kware a bangaren zuciya. Mama ta so tafiya tayi jinyarsa da kanta amma Baba ya hana ta yace shi zai je tare da shi. Shima kuma yafi son suje da Baban dan Mama har lokacin ba iya kallon cikin idonta yake yi ba duk da cewa ita din tana iyakacin kokarin ta a gurin jinyar ta sa.
Bayan sunje Dubai din ma kullum cikin waya yake Nigeria yana tambaya ko Jidda ta dawo? Har rokar yaya Mubaraka yayi ta je gidan su Jidda ta jiyo masa labarin su amma taki tace "ba dani za'a yi wannan abin kunyar ba".
Then one day bayan ya fara samun sauki Mama ta kira shi tace Jidda ta dawo Nigeria har ta turo yara suyi musu kwana biyu. Ta kuma bashi yaran suka gaisa a waya and he felt sooo good. Sai dai kuma Jidda bata kira shi ba kamar yadda Mama tace masa zata kira, wannan yasa shi din ya gwada number dinta kuma ta shiga amma bata dauka ba, ya kira ta har sau biyar bata daga ba, ya tura mata da message cewa shine, dan yana zargin ko bata dauka bane saboda bata san number din ba amma shiru kamar an aiki bawa garin su. And he thought
"Jidda bata sona yanzu. Ta tsane ni"
And he thought
"Maybe in ta ganni, maybe in ta saurare ni, maybe, zata tausaya min"
But now he is not sure about that either.........
Amma ya sani, gabakidaya abinda ya faru duk laifin sa ne kuma ya dauka. Yanzu abinda yake son sani shine ta yadda zai gyara laifin nasa.
Ya dawo da hankalin sa kan yaransa da suke gwada kayan da ya siyo musu, duk da bashi da lafiya sai da yayi sparing time and energy ya yi wa yayansa tsaraba.
But now at least yasan first step dinsa, zaiyi confirming akwai ciki a jikin asabe ko babu? Amsar ita zatayi leading dinsa unto the next step.
Washegari aka daura auren Mufida. Jidda bata zo ba sai ta turo mata da sakon taya murna da kuma ban hakurin cewa Abba ya hana ta fitowa. Da kuma alkawarin zata je gidan ta nan ba da dadewa ba.
Da yamma aka kai Mufida gidan ta zuwa dare gidan ya watse sai wadanda suka zo daga nesa. Zuwa safiyar litinin kuwa sai yan gida kadai. A lokacin ne ya samu ya ga abinda yake son gani daga asaben da take ta binsa duk inda yayi a bisa shawarar kakarta.
Bayan tabbatar da zargin Jiddan da yayi sai ya gaya wa yaya Mubaraka yace ta gaya wa Mama yana son a sake zama a sake maganar Asabe. Two days after that aka kuma kiran wani zaman irin wancan da akayi a watannin baya.
Bayan an zauna ne Umar ya fadi zarginsa na cewa Asabe tana da ciki. Baba ya juya ga kakar Asabe yace "haka ne? Da gaske ne" ta daga kafada "gwara da Allah yasa ya gani da kansa kunga yanxu sai a gaggauta ta tare tun kafin cikin yafi haka girma kowa ma ya gani azo aji kunyar da ake gudun ji. Asirin da ake rufewa ya tonu"
Umar ya gyara zamansa sannan yace "alhamdulillah. Allah shine abin godiya, tunda har kun amsa cewa akwai cikin, dama nayi niyyar idan baku yarda da cikin ba sai in nemi alfarmar aje asibiti a gwada dan a tabbatar. Alhamdulillah na jima ina addu'ar Allah ya kawo min hanyar da zan warware wannan matsalar ba tare da na kara bata tsakani na