Chapter 88 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   88 / 106

261K to 264K   out of 316K words

abinda ya rage masa shine neman yafiyar Ubangijin sa, amma gani yake yi kamar sauran kwanakin sa a duniya sunyi masa kadan yayi concentrating for his sins.

Karar wayarsa ce take ta breaking into his thoughts, ko kallon inda take baiyi ba dan yasan ba zai wuce yan gidan su bane ba suke nemansa, maybe duk sunji abinda ya faru, shi kuwa ba zai taba zuwa inda suke ba ballantana ya iya hada ido da su baya shi din ya zamanto tamkar annoba ne a gare su.

Sai kuma ya jawo rigarsa ya ciro wayar daga aljihunsa yana duba missed calls din sa, yawancin su daga Aunty ne sai kuma wasu daga yaya Mubaraka. Sai kuma message daga Aunty tun da rana

"Umar kana ina? Muna neman key din gidan ka dan iyayen amaryar nan sun ce gobe zasu kawo ta"

Ya ajiye wayar kusa da shi ya cigaba da sauraron kidan ta as they kept calling.

Sai dai daga baya ne kuma yaji wayar tayi kida na daban wanda ya saka shi saurin dago kansa ya kalli inda wayar take. Kidan daya saka wa number din Jidda. Rabon da yaji wayarsa tayi kara da wannan kidan tun Jidda tana gidansa, sai lokacin da Yasmin ta kira shi.

Ya dauke kansa daga inda wayar take, me take nema? Ko itama taji labarin abinda ya faru ta kira shi tace masa "I told you so?" In ba haka ba baya jin bayan rabuwar da suka yi dazu akwai dalilin da zai saka ta kira shi. Yana ji kiran ya katse wani ya sake shigowa still daga gare ta. Sai da tayi masa kira biyar sannan ya tashi ya dauki wayar jikinsa yana bashi babu lafiya, ko dai Mama ce ta rasu? Ko dai mahaifiyarsa ce ta mutu da bakin cikin sa?

Ya dauki kiran ya saka a kunnen sa amma yakasa cewa komai sai yaji muryarta, but she sounded as if she is crying.

"Umar! Kana ina?" Ya mike zaune. "Jidda? Lafiya kike kuka?" Ta kara sautin kukan ta "Umar babu lafiya, yanzu aka kira ni wai daga police station ta gwauran dutse, wai sun tsinci Yasmin, wai sun kaita asibiti, wai in tafi asibitin yanzu"

Ya mike tsaye, hankalin sa a matukar tashe "Yasmin? Me ya samu Yasmin Jidda? Me ya samu ƴata?"

Cikin kuka tace " wai wani ne ya tsince ta ya kaita gurin su, wai sun kaita asibiti, ka taho dan Allah Umar"

Yaji jiri yana neman daukar sa "kina ina? Wane asibiti suka ce?" Ta gaya masa sunan asibitin sannan tace "ina hanya na tafi can, dan Allah Umar kazo, tsoron abinda zan tarar a can nake ji, dan Allah kazo"

Bai karasa jin magiyar ta ba ya katse kiran ya dauki key din mota ya fita daga gidan a guje, gidan da yace ba zai kuma fita ba sai dau a fitar da gawar shi.

A guje yaje asibitin, a rikice, yana packing ko rufe kofar motar baiyi ba ya fita ya shiga cikin asibitin, a reception ya hango ta, ta taho da sauri itama fuskar ta kacha kacha da hawaye, direct ta wuce kirjinsa tana kara sautin kukanta, ya dago tada sauri "ina Yasmin din? Me ya same ta?"

Ta nuna masa wani daki a gefe "tana ciki....." Ya sake ta da sauri ya wuce ta ya shiga dakin da ta nuna.

Tun daga bakin kofa ya lura da fuskar yarinyar tasa, a kunbure kamar an dake ta a fuska, goshinta anyi mata dinki. Ya karaso gabanta ya tsaya sannan a hankali ya saka hannunsa ya dauki hannunta daya ya rike yana kallon dan karamin wrist din ta. Zagayen wrists din sunyi jajawur da wani zane mai kama da na igiyar shanya. Kana ganin hannayen kasan daure ta akayi da igiyar shanya.

Ya juya da sauri a lokacin da Jidda take shigowa dakin itama, cikin budewar murya yace "me ya faru da ƴata!?"

Kafin tayi magana doctor ya shigo tare da police a bayansa, police din ya na magana ya nuna Yasmin yace

"yauwa wannan itace rape victim din"


Wadannan sune kawai kalmomin da suka daki kunnen Umar, kalmomin da yaji su tamkar saukar tsawa a lokacin damina, suka kuma tarwatsa zuciyarsa kamar yadda tsawa taje tarwatsa bishiya idan ta sauka a kanta.

Sune kuma kalmomi na karshe da Umar yaji, kafin ya fadi kasa sumamme.


*Jidda*

Tun bayan tafiyar Umar nake zaune a sitting room din cikin halin rashin jin dadi, banji dadin yadda maganar mu da Umar ta kasance ba, ban kuma ji dadin yadda ya fita daga gidan mu ba, ina jin tsoron kar ya yi wani abu, kar yaje yayi hatsari a yanayin da ya fita.

Ina nan zaune har aka sauko daga masallacin juma'a, a lokacin ne yaya Tahir ya shigo mukayi maganganu akan shirin tafiya ta Ethiopia, daga nan ya tafi ni kuma na koma cikin gida nayi sallar sannan na kwanta da niyyar inyi bacci zuwa laasar amma na kasa yin baccin, zuciyata duk babu dadi nake jin ta.

Na mike na dauko wayata na kira Diyam muka danyi hira na bata labarin latest abubuwan da suka faru da kuma yadda muka yi da Umar yau, ta bani shawarwari tare da kara min karfin guiwa kamar yadda saba. Mukayi sallama na tashi na ci abinci sannan nayi sallar laasar na kunna tv na zauna ina jiran dawowar Asma'u daga makaranta dan ta dan ɗebe min kewar su Yasmin da nake jin ta dame ni.

Sai dai ban jima ina kallon ba kira ya shigo waya ta daga number din da ban sani ba. Sai dai true caller ta nuna min "DPO Gwauron Dutse" na yi mamaki tare da jin tsoron mai police suke nema a gurina, abu na farko da ya fara zuwa raina shine Umar yayi accident. Na dauka da sallama cikin tsoro da fargaba.

Yace "yauwa, dan Allah ina magana ne da babar yarinya mai suna Maryam wadda ake cewa Yasmin?"

Na mike tsaye cikin firgici, ina jin kamar zanyi fitsari a tsaye "eh ni ce, Yasmin yata ce. Me ya faru? Me ya samu Yasmin?"

Yace "ki kwantar da hankalin ki Madam, yarinyar ki tana lafiya tana hannun mu amma yanzu zamu tafi da ita asibiti sai dai ki same mu a can"

Na fara kuka "me ya samu Yasmin? Me take yi a hannun ku? Me yasa zaku kaita asibiti?"

Yace "farko zan yaba wa kokarin ki na saka yarinyar ki ta haddace number din ki, wannan yana da kyau sosai iyaye su saka ƴaƴan su su haddace number din da zasu iya kiran su da ita idan wani abu ya same su, kuma yana taimaka mana mu jami'an tsaro yana saukaka mana bincike. Abu na biyu kuma yarki tana lafiya, wani bawan Allah ne ya kawo mana ita wai yaji ihunta a cikin wani kango a kusa da gidan sa, sai ya shiga ya tarar wani lalatacce ne yake neman haike mata, wancan din ya gudu amma muna neman sa, lafiyarta kalau kamar yadda na gaya miki sai dai dan dukan da yayi mata dan ya hanata ihu, sai kuma buguwar da tayi a ka"

Na ajiye wayar jikina yana karkarwa kamar mazari, yace kar in tayar da hankali na amma hankali na ya kai kololuwar tashi. Babu abinda nake kira sai innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ban jira komai ba na saka hijab dina, sai a hanya sannan nakira Abba na gaya masa abinda ya faru, sai kuma da na shiga adaidaita sahu sannan na kira Umar, ji nayi ina bukatar sa a lokacin, ina so shima ya kasance tare da Yasmin.

Nayi ta kira da kyar ya dauka, na san fushi ne yake yi akan abinda ya faru dazu, sai daga baya ya dauka na gaya masa kiran sa akayi min kuma na nemi ya taho shima mu hadu a asibitin.


(Na so in rubuta cewa da gaske an yi raping Yasmin din amma zuciyata ta kasa 💔, amma ina so mu sani abubuwan da suka fi wannan ma suna faruwa, har babies ana raping ballantana masu wayo kamar Yasmin. Allah ya kyauta ya tsare mu da iyalin mu baki daya. But let it be our little secret🤫 kar mu gaya wa Umar. Lol. Let him keep thinking cewa anyi din🤭)


Forgive the typos...............

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana. Idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki yi sharing, idan kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*

*Hospitalized*

Ina ganin faduwar Umar na fahimci abinda ya faru, na tuna cewa ban gaya masa cewa ba'ayi ba kuma abinda yaji police din yana fada ya nuna masa kamar anyi ne, ina kallon doctor din tare da police din suka yi kansa da sauri suna jijjiga shi tare da kokarin bashi taimakon gaggawa amma ni kuma sai na wuce su zuwa gaban gadon Yasmin na tsaya ina kallon ta, remembering the first time I saw her ranar data fito daga cikina, how much she looked and still look like her father.

Na zauna a kan kujerar gaban gadon nata na rike hannunta da hannu na daya sannan na shafa gurin da yayi shati akan farar fatarta ina kallon fuskarta, so small, so innocent, babu abinda ta sani a duniya in banda soyayya da kulawa dan abinda kawai muke nuna mata kenan daga ni har mahaifin ta, bata san wani abu tashin hankali ba, wannan yasa rayuwar da muka samu kan mu a ciki a yan kwanakin nan ta ke tabata sosai, and now this.

Wannan wanne irin rashin imani ne?

Wannan wacce irin rayuwa ce?

Yanzu me za'a dauka a jikin wannan tatsitsiyar yarinyar da ba ma ta san menene abinda akayi niyyar yi mata ba? How can a sane person try to do something like that with someone like Yasmin? Ya yaya?

Wannan wanne irin cin zali ne?

Na shafa fuskarta da take rudu rudu da shatin yatsun azzalumin mutumin, na fara sheshshekar kuka "Allah ya isan ki Yasmin. Allah ya saka miki" amma a raina sai naji bana bukatar yi masa Allah ya isa, ko ban fada ba sai Allah ya saka mata, ko ban fada ba nasan duk wanda zai iya aikata cin zali irin wannan to kuwa tabbas ba zai gama da duniya lafiya ba, zai iya ya tuba Allah ya yafe masa amma wannan cin zalin tabbas Allah ba zai yafe masa shi ba sai ya fitar wa da Yasmin hakkinta a kansa.

Tunowar da nayi da Allah sai naji kamar ban yi dai-dai ba da nake wannan kukan kamar wadda aka yi wa mutuwa, kamata yayi in gode masa, kamata yayi in saka goshina a kasa inyi masa godiya akan kubutar min da yarinya ta da yayi daga mugun nufin wannan bawa nasa, ba dan Allah ya bata ikon yin ihun da har wani ya ji ta ya zo ya taimaka mata ba da yanzu wata maganar ake yi, maybe da ta rasa ranta, ko da bata rasa ranta ba da tabbas rayuwar ta ba zata taba dawowa da dai ba.

Na saka hannu na na goge hawaye na amma a take wasu suka kuma fitowa "alhamdulillah" na fada "alhamdulillah. Allah na gode maka daka kare min ita da kariyar ka, Allah ka cigaba da tsare min su gabakidaya a duk inda suke ka hana su fadawa cikin halaka".

"Sai hakuri Madam. Allah ya kiyaye, sai kuma fatan Allah ya kiyaye gaba" na dago kai ina kallon dan sandan nace "ameen Nagode" yace "amma kuma Allah ba zai kare taba sai kema kin kula sosai, duniya yanxu azzalumai sunfi nagari yawa, yarinya kyakykyawa, kosashshiya, lafiyayyiya kamar wannan a gurin wani tamkar nama take. A kula a daina barinta tana yawo, a saka ido sosai dan su yaya amana ce da Allah ya bamu kuma tabbas zai tambaye mu a bisa amanar da ya bamu"

Na gyada kai da sauri "haka ne officer, mun gode sosai, da zamu ga mutumin da ya taimaka mata da mun gode masa shima" ya girgiza kansa "babu wani abu, da akwai takarda da za'a saka hannu, ke zaki saka ko babanta?" Ya fada yana kallon daya side din dakin inda har yanzu doctor yake kan Umar da suka kwantar a kan daya gadon da yake cikin dakin, kafin in amsa sai ya sake min wata tambayar "shine babanta?" Na gyada kai sai ya kuma kallon ta yace "yeah, suna kama sosai. Shine mijinki kenan?" Nayi mamakin tambayar amma sai na amsa masa "eh shine" yace "ohhh, naga kamar baki damu sosai da halin da ya shiga ba, kinfi son yarki ko?" Ya karasa maganar cikin kokarin yi min wasa but I was in no mood for wasa. Jin bance komai ba sai yace "babu komai, duk sanda kuka samu dama sai daya daga cikin ku ya je station din mu ya saka hannu" na sake yi masa godiya ya sake yi min jaje sannan ya fita

Yana fita shima doctor din ya bar gaban Umar ya taho gurina da takardu a hannunsa ya mika min yana lissafa min kudaden da zanje in biya da kuma magungunan da zan siyo na Yasmin da kuma na Umar, ya kara da cewa "kar ki damu dashi, he is just in a shock, zai dawo hayyacin sa soon insha Allah kinji" na gyada kai kawai sai kuma ya lura da yadda nake kallon Yasmin, bana son fita in barta sai yace "ki kira wani a gida sai yazo ya taimaka miki" na zauna tare da sake rike hannunta da hannu daya na dafa kanta da dayan, ta dan bude ido kadan a tsorace tace "daddy! Wayyo mommy"

Na hau gadon tare da janta jikina na rungume ina hawaye, a raina ina lissafin duk da cewa ba'ayi mata abinda akayi niyya ba an riga an bata mata kuruciyarta da wani memory marar da di wanda zai cigaba da hunting dinta maybe har karshen rayuwar ta.

Na tuna kokarin da na ringa yi for years na ganin cewa yayana basu samu bakin pentin laifin mahaifin su ba, but ashe dai duk wahala ta ta banza ce, ashe their father's sin will forever haunt them, ashe dai wannan bakin fentin ba zai taba goguwa daga gare su ba.

Na tuna da maganar annabi ta cewa duk wanda yayi zina da yar wani sai anyi da ta sa, in yayi da matar wani ayi da tasa, in yayi da uwar wani ayi da tasa, na tuna da yawan matan da nasan Umar ya nema kuma bisa la'akari da yadda yake kokarin boye min harkokin sa na tabbatar wadanda ban sani ba sunfi waɗanda na sani yawa, na kuma san tabbas dukkan su yayan wasu ne tunda dai ba daga sama suka fado ba, kenan duk wadannan bashi ne Umar ya ci wanda za'a fanshe akan yarsa, Yasmin.

Na sake rungume ta a jikina, "Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah mun tuba Allah"

Na tuna da shekarun dana dauka ina zaune da Umar duk da nasan halinsa, duk da nasan wannan hadisin, shekarun dana dauka ina gayawa kaina cewa zaman hakuri nake yi, are they really worth this? Are they really worth my daughter's dignity? Shin soyayyar da nake yiwa Umar ta kai darajar Yasmin a gurina?

Na kalli kumburarriyar fuskar Yasmin da wani busasshen jini a gefen bakinta, a hankali nace "am sorry Yasmin! Am really sorry!" Sai na dora goshina akan nata na cigaba da kukana.

But is she really safe? Da yayanta da jikokin ta da yayan Asad? Tunda waɗanda Umar ya nema jikokin wasu ne suma. Ni dai nasan ba zan iya kare yayana da jikoki na ba daga wannan musiba da ubansu ya jawo musu, na san kuma maganar Annabi bata taba tashi amma nasan zanyi iyakacin kokari na, na farko abinda zanyi shine zan dauke su as far away from Umar as possible, na biyu zan dedicating dukkan time dina gurin basu tarbiyya da dora su akan tafarkin Allah da kuma cusa musu addini da kyawawan dabi'u a cikin zukatan su, sannan kuma zan dage da addu'ar nema musu kariya babu dare babu rana dan idan akwai abinda zai chanja kaddarar mutum daga marar kyau zuwa mai kyau to tabbas addu'a ce. In nayi haka sai kuma in ga yadda rayuwa zata yi damu, insha Allah yadda taci albarkacin addu'a yau haka zasu cigaba da cin albarkacin addu'a har karshen rayuwar su.

Karar wayata ce ta dawo dani daga tunani na, na goge hawaye na na dauko wayar a cikin handbag dina da take ajjiye a gefe na ga number din Aunty ce, ko me zasu ce min kuma?

Na dauki kiran amma magana ta kasa fitowa daga makogwarona, naji muryar Aunty, kamar a cikin tashin hankali take magana "Jidda, Hello, kina jina?" A hankali nace "ina ji Aunty" tace "dama tambaya muke yi ko Umar ya kawo miki Yasmin?" Na danyi shiru, wato sai yanzu ma suka san bata gidan, nace "Yasmin kuma Aunty?" Tayi salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Basu zo ba? Kinga kar ki tayar da hankalin ki na san suna tare da Umar, muna ta kiran wayarsa ne yaki daga wa dama shi yasa na kira ki"

Na juya kaina na kalli Umar da yake kwance a kan gadon har yanzu, ina lura da yadda yake jan numfashi sama sama. Ta cigaba "wallahi kinga ni na fita, babanku ya hada ni da uhmmm da mutane zamu je... zamuje unguwa, ashe itama Mama sun fita ita da Mufida sun tafi biki sun bar yaran da yan aiki, su kuma yan aikin basu saba da yaran ba sai suka manta da su, shine wai a yadda Asad yake gaya mana wai sai yake kuka shine Yasmin tace ya zauna zata je ta kira daddyn su yazo ya kawo su gurinki, to tunda ta fita bata dawo ba, babu wanda yaga sanda ta fita daga gidan, ni nafi tunanin ma a cikin gidan suka hadu da Umar ya dauke ta a

88 / 106