Chapter 43 Reading Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama READ HAUSA Novels

Jidda Sirri da zai iya rushe komai by Maman Maama

Author :  MAMAN MAAMA Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 106

126K to 129K   out of 316K words

na taso na dawo kan cinyarsa na zauna nace "to menene da zariyan, uhm? Ji nake aikin ka kawai zaka je kayi ka dawo? Kai da ba yawon shakatawa zaka je ba?"

Ya shafa fuskata "tunda aka fara wannan program din nake shirin tafiya da ku Abuja, mu je mu dan shana haka. Kin ga nan yanzu ko dan fita ma ba ma samu muyi saboda aiki yayi min yawa." na rike hannunsa "to ba sai mu bika zariyan ba? Ai nasan zasu baku accomodation ba sai mu zauna ba, ko ba komai ai mun samu chanjin muhalli kuma ai shanawar a tare da mu take ba'a gurin da zamu je ba" na kashe masa ido amma sai ya bata rai.

"Akwai sauro wallahi. Kar muje Asad ya dauki malaria or worst. Dole ni kadai zanje" na fara bubbuga kafa ina masa shagwaba "dan Allah dear ka tafi da mu. Ni sai in bar Asad dinmaa gurin Umma, ai zai iya shan madara kafin mu dawo, ni bana so ka tafi ka barni"

Sai ya fara rarrashi na "yaron nan kin san lafiya bata ishe shi sosai ba, ba zamu ji dadin tafiyar ba ma in muka tafi muka barshi. Kwana uku ne kadai zanyi in dawo" na kirkiri hawaye sai ya fara goge min "kin ga, karshen shekarar nan zan dauki annual leave sai mu tafi Abuja mu shana acan, transcorp kike so ko ina?"

Na sake matse kwalla "ni kai nake so......" Ya kwaikwaye ni "nima ke nake so ........."

A haka dai dole na hakura, Thursday da sassafe ya tafi. Yace sunday da yamma zai dawo.....

Kuma Sunday din ya dawo da daddare can bayan sallar isha. Na tare shi da murna da kwalliya da abinci. Ya kuma karbe ni shima da murna da ษ—oki, hannayensa cike da ledojin tsarabar da yayo mana ni da yara. Muka ci abinci tare da yara a kan carpet a cikin plate daya, Yasmin akan cinyarsa yana ci yana bata tana masa surutu ni kuma ina musu dariya tare da bashi labarin abubuwan da yayi missing na daga sabbin abubuwan iyayi da Yasmin take fitowa da su kullum, just like a happy family. Sai da muka gama komai
sannan muka kwantar da yaran mu tare kamar yadda muke yi kullum, sannan na hada masa ruwan wanka kamar yadda nake yi kullum, half expecting ya jani mu shiga wankan tare amma sai naga bai yi hakan ba, kafin ya fito na fitot masa da kayan bacci a raina ina tunanin nasan halin mutumi na ma ba lallai ne ya saka kayan ba sai dai da safe in dauke abina.

Yana fitowa na shiga nima, half expecting him to follow me ya sake wani sabon wankan dan nasan halin abuna. Cikin sauri nayi wanka na na fito tunda ba wani datti ne a jikin da zan wanke ba kawai dai dan dadin bacci ne, ina ta lissafin irin tarbar da zan samu a gurin mijina saboda kwana ukun da yayi bama tare, musamman kuma saboda hade haden da nayi wa kaina na taryar sa.

Sai dai me..........

Ina fitowa na tarar da shi ya kai dubai a baccin sa. Na tsaya ina kallon sa da mamaki. Ina so ku fahimci cewa a ranar nayi mamaki ne saboda hakan bai taba faruwa ba, ranar ce rana ta farko da Umar ya fara yin bacci ba tare da ni ba, a matsayi na na wadda ban saba da haka ba, da kuma already abinda yake a raina a game da shi dole inyi mamaki.

Umar ba zai taba bacci ba ya barni a ranar da ya dawo bayan yayi kwana uku ba tare da ni ba. Except if.......na girgiza kaina da sauri, bana son saka zargin mijina a raina, not again......

Sai na hau kan gadon sannan na juyo dashi daga ruf da cikin da yayi na mayar dashi rigingine sannan na haye ruwan cikinsa "gaskiya ka tashi, har wani nan ma bacci kake nufin zakayi bayan kasan nayi missing dinka" na fada kamar zanyi kuka.

Ya dan bude ido yana kallona sai ya dan shafa bayana kadan "bacci....." Sai ya daga ni chak ya ajiye ni a gefe sannan ya kuma juya min baya tare da cewa "just sleep".

Na jima ina zaune inda ya ajiye ni ina kallon sa fuska ta cike da mamaki. Har da kara sunkuya wa in leka fuskarsa dan in tabbatar Umar din ne da gaske ba wani can daban ba. Na kuma lura peacefully yake baccin sa. To ko dai da gaske yake gajiyar ce tayi masa yawa, but he didn't seem all that tired tun da yazi banga alamun wata muguwar gajiya a tare da shi ba dan ya gaya min ma bashi yayi driving din ba wanda aka tura su tare ne.

And I did what most will think ba dai dai bane ba but only wadanda suke cikin shoe dina ne zasi fahimta, it is something that you can't resist a irin wannan situation din, I checked his phone for the second time a auren mu.

Tana kasan pillow dinsa, na saka hannu a hankali na dauka sannan na shiga toilet na rufe kofa na zauna akan shadda sannan na bude ta. Whatsapp na fara shiga kamar yadda nayi wancan karon, kuma kamar wancan karon din, tarin unsaved numbers ne suka yi min welcome. A ranar na bisu ina dubawa a hankali sai dai babu wani abu da na tsinta a ciki. Daga sallama sai hello sai hi. Babu wata da na ga doguwar magana sai wata da naga an turo masa reply

"Haba da gaske? Haka kake cewa ai kullum amma ni banga alama ba har yanzu"

Na sake duba wa sai naga banga shi abinda yace din ba da aka bashi wannan amsar ba, sai na fahimci cewa goge wa yake yi. Yasan nasan pin dinsa, yasan kuma abinda ya faru the last time da na duba wayarsa, in ya chanza pin zanyi zargin wani abu shi yasa yake koke messages dinsa sai ya bar gaisuwa kadai kuma baya saving numbers ballantana in gane.

Amma sai na bi su ina ta duba WhatsApp names dinsu kuma na fahimci yawancin su mata ne, daga hotunan su da kuma sunayen su. But bani da wani dalili da zan tuhume shi akansu dan babu wani abu da na gani kuma yana da right din da zai yi magana da mata a social media.

Nayi searching Bashir sai naga kusan wata guda ma basu yi magana ba.

Na fita daga WhatsApp. Sai kawai wata zuciyar ta ce min in duba messenger duk da nasan ba amfani yake da ita sosai ba. And I checked it.

Chats din su da Bashir na fara gani a can

Message din umar ne karshe, an emoji
๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹

Sai na shiga ciki, naga dazu da safe ne suka yi maganar

Bashir ne ya tambaye shi

"Mutanen Zariya, ya kayan da na aiko maka dasu? Babu feedback?"

Sai Umar yayi replying
๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹

I then became curious to know kayan menene suke magana akai? Sai nayi scrolling up. Up to five days ago. Ranar da Umar ya zo min da takardar tafiyar su Zariya. Da dare, ma'ana bayan mun gama magana da Umar na gama rokon shi akan ya tafi da ni yaki

Shi ya fara turawa da Bashir message, sai suka yi hira kamar haka

"Zaria fa suka tura ni mutanen nan"

"๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ. Babu batun Abuja kenan"

"Kai dai barni kawai wallahi duk raina ya baci"

"Kwana nawa zakuyi ne?"

"Uku fa. Sai sunday zamu dawo, sunday din ma sai dare"

"Aiya sorry"

"Ni ba sorry ba, ka aiko min da wani sako mana da zan tafi dashi can๐Ÿ˜ฉ, kasan ba zan iya kwana uku ni kadai ba"

"๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ. Ka kira Zahra ta ka, ina jin tana Kaduna"

"๐Ÿคฎ๐Ÿคฎ๐Ÿคฎ๐Ÿคฎ"

"๐Ÿ˜ณ. Wulakanci. Zahran kake wa amai?"

"Please not her.๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ. Anyone but her"

"Saboda me? She was once your favorite pet"

"Duk balloons din kirjin sun sace๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ"

"๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ"

"๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ"

"Amma kai wallahi ban taba ganin dan iska irin ka ba"

"๐Ÿ˜. Allah da gaske nake. Maimakon inke kamasu sai dai in ke tattaro su kamar kaya"

"๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ"

"๐Ÿคท๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ. Ka samo min wata kawai. Mai dan kwari kwari haka. Young๐Ÿ˜‹"

"Kar in kira maka wata kuma kace g**d** yayi slack"

"๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚"

"Eh ai kai din ne baka da kai kamar sigari"

"Ni din? Kai biyu ne fa dani kana cewa bani da kai?"

"Daya ne yake aiki dayan a toshe yake๐Ÿ˜‚"

"๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚"

"Tunda kayi aure ka koyi shegen taste da iyayin banza. Ka tafi da matar taka mana in ba tsoro ba"

"Ina ruwan ka in ban tafi da itan ba? Bana son iskanci"

"Zan turo maka number din wata da aka hada ni da ita. Tana kaduna ita ma. Saura kayi mata iskanci"

"Godiya nake oga bros"

"๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„"

Sai kuma sakon yau da safe

"Mutanen Zariya. Ya kayan nan dana aiko maka dasu, babu feedback?"

"๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹"

Na kife kan screen din a kasa sannan na sauko daga kan shaddar da nake zaune na dunkule a guri daya kamar mai zazzabi ko kuma mai ciwon ciki. Duk yadda zan kwatantawa mai karatu halin da zuciyata ta shiga ciki a lokacin ba zai gane ba sai dai wadanda suka ta ba shiga irin wannan halin wanda bana yi wa wadanda basu shiga ba fatan shiga. Na jima ina jan numfashi da kyar sannan na fara ambaton sunan Allah ina neman daukin sa da fatan numfashina tare da tunani na zadu dawo gare ni. Ban san mintuna nawa na dauka a kwance a kasan toilet din ba ko kuma hours, amma kuma kukan da ada yake matsayin abokina sai na neme shi na rasa a lokacin da nake bukatar sa dan samun sassaucin zuciyata.

A karshe na mike zaune sannan na jawo wayar na sake karantawa sai kawai kamar daga sama naga Bashir ya hau online.

Without thinking twice na tura masa sako.

"Bashir Jidda ce take magana"
"Ina so in sanar maka da cewa nasan duk abinda kuka yi kai da Umar, na sani ba tun yau ba"
"Na fahimci cewa jahilci ne yake damun ku duk ku biyun, baku san girman abinda kuke aikatawa ba, baku san kuma illar abinda kuke yi a gare ku da kuma mu da muke tare da ku ba. Idan kuma har kun sani kuke takewa to ba zan kira ku da jahilai ba sai dai dakikai"
"Banzaye, dakikai, jahilai, kazamai, munafukai, mazinata, makaryata masu hali irin na dabbobi"
"Ba za muce muku Allah ya isa ba, ba wai dan ku ba sai dan zata iya dawowa kan yayan da Allah ya riga ya bayar a tsakanin mu. Amma ku sani ko bamu fada ba sai Allah ya saka mana, abinda kukeyi sai ya dawo kanku indai har baku tuba kun daina ba, fatana dai kawai shine in ya tashi dawowar ya dawo kan ku ku kadai ya murkushe ku da duk wasu masu hali irin naku"
"Wannan shine kadai magana tsakani na da kai da kuma shi dayan munafikin"

"Maganata ta karshe kuma gare ka ita ce, ka bude kunne kuma sosai kaji wannan, in na sake ganin ka a gidan nan wallahi sai nayi maka wanka da tafasasshen ruwa. Munafiki"


Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Wannan littafin na siyarwa ne a bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing in kika yi ke da Allah*

*The Second Step*

Naga alamar ya karanta, ban saka ran zaiyi kin reply ba kuma ban jira reply din nasa ba tunda dai ya karanta shikenan buri na ya cika.

Na tashi daga kasan toilet din na koma cikin bedroom din na tsaya ina kallon Umar da yake kwance shame shame yana ta shirgar baccinsa. Sai naji a raina tamkar duk duniya babu wanda na tsana irin sa, tsana irin wadda ake yiwa rikakken makiyi dan bana jin Umar yana daga sahun masoyana a duniya, yafi dacewa da in saka shi a sahun munafukai masu fuska biyu wadanda suk fi makiya zama abin tsoro.

Sai na tuna da mata da sule kashe mazajen su a lokacin da suke bacci, were they in my shoe sanda suka aikata? Then ashe suma suna da tasu hujjar aikata abind suka aikata din. Nayi saurin kawar da tunanin daga zuciyata sannan na jefa masa wayarsa, not minding cewa a kasan pillow na dauke ta dan na tabbatar ko na mayar da ita din zai san na gani dan zai fa sakon dana bar musu shida Bashir a messenger. Dan sakon nawa bana Bashir bane shi kadai, har da Umar din, shi yasa ban goge ba.

Na saka hannuna na dauki Asad da yake ta baccin sa sannan na fita daga dakin na koma dakina, na kwantar da Asad a kusa da Yasmin sannan na zauna ina a bakin gadon ina kallon gadon, remembering our first night

"my heart and my body belongs to only you"

Naji kamar yanzu yake gaya min maganar.

And then,

"Karya take yi min, ni ban san taba"

Sai kuma

"Kuskure ne Jidda. She knows me and She seduced me"

Daga nan kuma...

"Tun ranar da nayi tunanin na rasa ki,ย  ranar haihuwar Asad, tun ranar nayi wa kaina alkawari kuma yanzu ma ina miki alkawari cewa ma daina. It will never happen again"

And then this.....

Yanzu kuma me zai ce min? Sai naji bana ma son jin mai zai ce min din dan babu komai a cikin maganganun sa sai karya sai kuma kalamai na yaudara. Ya gama yaudara ta, na gama sauraron maganganunsa.

But menene option dina?

In sake fita? Ina zanje? Gidan Aunty Afia?
She will definitely send me back bayan doguwar nasihar yin hakuri da kuma ta daukan kaddara, ta kuma kara da bani misali da irin rayuwar da tayi a baya da yadda yanzu komai ya wuce take cin ribar hakurin ta

Maybe ma har in samu tukuicin fada akan daukan wayar Umar da nayi, watakila ta kara da cewa

"Wayar miji tamkar albasa ce, kana dubawa kana hawaye"

Ko kuma

"Kazantar da baka gani ba ai tsafta ce"

Sayings din da ni sam ban yarda dasu ba. Idan har ban ga kazantar ba ta yaya zan gyara ta? Ko kuma shikenan dan ina tsoron ganin kazanta sai inyi ta zama da ita har sai tayi yawan da zata zama cutar wa a gare ni ko kuma ga family dina? My children, my poor innocent children.

To ko gidan mu zan tafi? Bayanin me zanyi musu a gidan? In ce menene ya hada ni da Umar? In ce shi mazinaci ne shi yasa ba zan cigaba da zama da shi ba?

Knowing Abba, da zarar Umar yaje ya shirya masa magana shikenan ta sa maganar zai dauka ba zai ma kuma saurara ta ba, dan shi a gurin sa maganar namiji is worth ten times than maganar mace. Musamman in yaji cewa a wayar Umar din naga cewa yana neman matan, na tabbatar zai dora laifin duba wayar Umar din a saman laifin neman mata da Umar yake yi. And Umma, Umma zata dora wa kanta damuwa ne da tashin hankali bayan kuma babu abinda zata iya yi min maganar.

And then that means tonuwar asirin Umar, and no matter what Umar yayi ba zai chanja masa tittle dinsa a gurina na mijina kuma uban yayana ba. Staining sunan Umar will forever mean staining sunan yaya na. Musamman abu mai datti irin wannan, musamman a yanayin da gidan mu ya ke ciki, za'a yi ta dragging maganar ne har girman su kuma har sai an kai ga goranta musu watarana.

I can't imagine anzo neman auren Yasmin nan da shekaru ashirin anyi digging out cewa ubanta mazinaci ne, wasu ma zasu iya kara gishiri su ce shegiya ce. I can't. I can't do that to me children.

Ina ma Umar zaiyi wannan tunanin? Ina ma zai tuna da Yasmin da Asad a duk lokacin da yayi niyyar aikata aika aikan sa?

Kenan ita uwa bata da zabi a irin wannan lamarin, kenan duk matar da mijinta yake aikata aiki irin na Umar ko makamancin da Umar bata da zabin tona masa asiri saboda gudun kar ta bata sunan yayanta, and a mother can do anything for her children.

Sai naji wani irin feeling ya nannade zuciya ta, wani feeling da nake tunanin irin sa ne wadanda aka yi sentencing to life imprisonment ba tare da sunyi laifin komai ba suke feeling, saboda ni dai as far as I know babu laifin da nayi I am innocent amma yanzu I am sentenced to living with Umar and hiding his dirty secrets saboda yaya na.

Wannan tunanin ya saka wani kuka ya taho min finally, amma sai nayi saurin kifa fuskata akan pillow ina kuka na a haka, wato shi kansa kukan ma bani da freedom din yinsa yadda nake so sai dai in boye shi dan kar yayana su jini ina kuka su tambayi dalili, dan kar makota suji su yi tunanin menene dalili, dan kar yanuwa na su gani su fara guessing dalili. Saboda ni uwace. Saboda yayana.

A cikin daren I did a lot of crying, a lot of praying and a lot of thinking. Na duba step one din da na dauka na gyaran Umar and how it blew up in my face, sai kuma nayi tunanin next step din da zan dauka da kuma irin challenges din da zan fuskanta a kansa. But still keeping in mind that my first step will still remain second step din kamar dora wa zanyi akan wancan din inga kuma yadda abubuwa zasu cigaba da zuwar min.

Sai kuma nayi addu'a, nayi doguwar addu'a akan Allah ya baki karfin daukan abinda zanyi din, ya kuma saka hakan shine abinda zai fi zana min alkhairi ni da yaya na.

Akan sallayata nayi bacci, lokacin har assuba ta fara gabatowa. Na tashi na sake alwala sannan na fita zuwa dakin Umar da niyyar tashin sa yayi sallah, kamar yadda na yi alkawarin zan cigaba da step one dina.

Yana kwance kamar yadda na barshi, daga alama ma ko juyi baiyi ba saboda dadin baccin da yake yi. Na zagaya ta side din fuskarsa ina kallon sa, hirar su da Bashir

43 / 106