Author : MAMAN MAAMA Category : African Stories & Novels
suka shafe shi. Yayansa da matarsa kuma sune farko tunda sunfi kowa kusanci da shi.
Maganganun su Mama ne suka dawo dashi hayyacinsa "Umar ina Baban naku" "yaya Doctor are you okay" "Faruq mai ya samu Alhaji? Mai ya faru da shi?" "Yaya ina Baba?"
Ya girgiza kai yana so ya dawo da tunaninsa zuwa gare shi. "Uhmmm. Yana ciki. Ku taho. Bara inje in duba"
"Da tahowa kai waje ka barshi shi kadai? Me kake yi a wajen to? In kuma yana neman wani abu fa? In doctors din suna neman wani abu fa?"
Aunty ta kama fada cikin nuna tashin hankali da takaici, yayi tunanin Mama zata shiga ta tare masa kamar yadda ta saba amma sai ya ga tayi shiru bata ce komai ba, sai yayi musu jagora zuwa ciki, zuwa kofar emergency room din da Baba yake ciki sannan yace musu su zauna a waje shi kuma ya shiga ciki yana dauko medical license dinsa in case ko zasu hana shi shiga, amma sai ya tarar har sun gama bawa Baba dukkan gudummawar da zasu bashi har bacci ya dauke shi, sai suka yi masa bayani "jininsa ne ya hau sosai" suka gaya masa readings din, ya dafe kai cikin tashin hankali, one of the doctors ya dafa shi "Allah ya kiyaye ai, abin yazo da sauki da bai samu stroke ba, but har yanzu ba wai sauka jinin yayi ba mun dai yi stabilizing dinsa ne for now, but I will advise cewa kar a dame shi kuma ayi avoiding duk abinda zai bata masa rai, a barshi ya huta sosai"
Umar ya gyada kai sannan ya basu hannu suka gaisa kuma yayi musu godiya, sai suka tura shi inda zai je ya biya bill, ya fito ya sake wuce su Mama yaje ya biya komai ya dawo, sai a lokacin aka turo gadon da Baba yake kai aka fito da shi zuwa dakin da aka bashi, su Mama suna ganin shi unconscious sai kuka, kowa kuka, da kyar Umar ya rarrashe su suka yi shiru aka kaishi dakin amma sai Umar ya ce su ganshi kawai su fito,
"ba'a son a dame shi dan ana son jinin nasa ya samu ya sauka"
"Jininsa ya sauka kuma? Jininsa ne ya hau?" Aunty ta tambaya cikin tashin hankali "yaushe Alhaji ya samu hawan jini kuma bamu sani ba?" Mama ta tambaya amma duk babu wadda Umar ya amsa wa a cikin su har sai da ya kammala saka masa drip din da doctors din suka bar masa ya saka sannan ya fita ya basu guri.
Can wani lungu ya samu ya zauna ya dafe kansa, sauro yana ta cizon sa amma ko a jikinsa kuma shi kansa bai san abinda yake yi a gurin ba har sai da dare yayi sosai sannan ya koma dakin da Baba yake, ya tarar har driver ya mayar da Mufida da sauran yara gida sai Mama da Aunty, sai kuma Muhsina da tazo a lokacin tana zaune tana ta faman rusar kuka kamar wadda aka cewa Baban ba zai tashi ba, yayi mata tsaya "kiyi wa mutane shiru ko ki fita daga nan, so kike ki tashe shi kuma ki kara masa wani ciwon?" Tayi shiru tana goge hawayenta, sai kuma wani tunani yazo masa "will she have obeyed him like that idan tasan abinda yake aikatawa, in tasan dalilin da baban nasu ya yanke jiki ya fadi?
Ya sake duba Baba sai kuma ya dauki iyayen da Muhsina duk ya tafi dasu, ita ya ajiye ta a gidan ta su kuma ya kaisu gida sannan shi kadai ya juyo ya dawo asibitin gurin Baba.
Ranar haka ya kwana a kan kujera a gaban gadon Baba, checking his vitals lokaci zuwa lokaci amma baya samun wani result mai kyau duk da da doctors report ya nuna sun bashi duk abinda ya kamata su bashi. Babu abinda zaiyi for now sai dai ya jira, sai kuma ya tuna cewa he can do more than jira, he can pray.
Yaje yayi alwala sannan ya fita motarsa ya dauko sallaya yazo ya shimfida, a ransa yana tunanin ranar da Jidda tayi rashin lafiya makamanciyar wannan, ranar da jinin ta ya hau kamar yadda na Abba ya hau, a lokacin tana da tsohon cikin Asad, ciwon da ya jawo aka haifi Asad prematurely, shima kuma lokacin shine sanadin ciwon ta. Ya tuna da alkawarin da yayi wa kansa a lokacin, alkawarin da yayi wa Allah a lokacin da kuma alkawarin da yayi maya bayan ta samu sauki ya daina halinsa, kuma a lokacin bai taba tsammanin zai sake ba, amma shima kansa bai san sanda ya sake din ba. What went wrong?
Sai yaji ya kasa yin wata addu'ar, ya kasa yiwa Ubangijin sa wani alkawarin saboda yana kunyar wancan alkawarin da yayi kuma ya karya ba tare da wani dalili ba da ya wuce son zuciyata da kuma satisfying his body cravings, cravings din da they never seemed satisfied.
But koma ya samu satisfaction din was it really worth it? Satisfaction din few minutes da illar su take staying har karshen rayuwa. Satisfaction din da suka saka shi a halin da yake ciki a yanzu yadda ko daga ido baya iya yi ya kalli mahaifansa, ballantana surikinsa wanda baya jin har abada zai iya tsayawa a gabansa.
Sai dai kuma idan bai tsaya a gaban nasa ba bai san yadda zai yi ya roke shi ya dawo masa da matarsa ba.
Sanda ya gama adduoin sa lokacin har asuba tayi dan haka ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya sake dawowa, ya tarar Baba ya tashi yana kokarin sauko wa sai ya je ya taimaka masa ya sauko ya kai shi toilet yayi alwala sannan ya shimfida masa abin sallah yayi, all the while avoiding his eyes, har sai da ya bashi magungunan sa koma ya kwantar dashi sannan Baba yace "ka rubuta? Ka rubuta wa Jidda takardar ta ka kaiwa babanta kamar yadda ya nema?" Umar yayi shiru bai ce komai ba kansa a kasa sai Baba ya sake cewa "ka zama kurma ne kuma?" Umar ya girgiza kai "Baba ba ka da lafiya, kayi hakuri ka bar maganar nan dan Allah"
Baba ya fara kokarin tashi "sanda ka aikata ai baka damu da cewa zai bata min rai ba ko? Ko ka sani? Ko kuma ka sani baka damu ba? Ko nine idan suruki na yayi min abinda kayi masa dole zan ce ya sakar min ya in yaki kuma in kai shi kara tunda ina da hujjar da alkali zai raba auren a take. Dan haka zabi ya rage naka, ko ka sake ta cikin lumana da rufin asiri ko kuma su kaika court ka sake ta bayan an tona maka asiri a gaban mutane, the choice is yours"
Umar ya zame daga kan kujerar zuwa kasa ya rike hannun Baba "Baba dan Allah. Wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba Baba. Baba ka taimaka min ka bashi hakuri" Baba ya zare hannunsa daga nasa "ni ba zanje in bayar da hakuri ba, ni ba zan ma iya sake hada ido da shi ba. Kai da ka aikata abin da ka aikata sai kaje ka bashi hakurin in ya hakura shikenan, in yarinyar itama ta hakura shikenan. Amma ni in nine ba zan hakura ba na sani. Ba zaka iya rabuwa da ita ba amma ai ka iya neman yarta ko?"
Umar ya zauna a kasa dabas! "Abba wallahi ban san nayi ba, ni inajin ma Mutanen nan asiri suka yi min dan wallahi ban san na aikata ba sai daga baya aka gaya min. Wallahi Baba asiri suka yi min" Baba ya girgiza kai cikin takaici "asiri Umar? Menene dalilin da zai saka suyi maka asiri? Duk mazan duniya su rasa wanda zasuyi wa asiri sai kai da kake surikin su? Kai kana ganin akwai iyayen da zasu yi asirin da zai saka a lalata musu yar su? Idan da ace baka auren Jidda sai a iya yin tunanin suna so su makala maka ita ne dan ka aureta, amma ta yaya zasu ce ka aure ta bayan kana auren babarta?"
Umar yayi shiru yana jujjuya kansa, shima it doesn't make sense to him amma yasan gaskiya ce, gaskiya ce amma wadda babu wanda zai yarda dashi a kanta dan bashi da wata shaida akan hakan. And that hurts him a lot.
"Baba wallahi" ya sake attempting, Baba ya daga masa hannu "ka daina rantsuwa akan karya Umar, kuma ka tashi ka fita ka bani guri".
Ya jima a zaune, sannan ya tashi yayi waje da sauri sai dai yana kaiwa bakin kofa Baba ya sake kiran sunan sa, ya juyo da fatan Baban ya sauko ne zaije ya rokar masa Abba amma sai yaji baban yace "ka shirya rana ita yau za'a daura auren ka".
Da sauri ya fita ya rufo kofar, a ransa yana aiyanawa in dai zancen Asabe ne ana gama daurawa a gurin zai rubuta mata saki uku ya damka wa waliyin ta, sai dai sama da kasa su hadu. A stairs ya hadu da Aunty da Mufida suna hawowa, "Umar ya maijikin, muna ta kiran wayarka ba ka daga ba" "da sauki" kawai yace mata sannan ya karasa fita, Mufida ta bi bayansa "yaya Doctor ga abinci nan an taho maka dashi, kazo kaci, Mama tace in gaya maka ka ci" ya juyo a fusace ya nuna ta da yatsa "ki shiga hankalin ki, ko in sassaba miki a gurin nan" tayi baya da sauri fuskar ta cike da mamaki sannan ta bishi da kallo har ya shiga motarsa ya bar gurin.
Gidan sa ya nufa direct, mai gadi ya bude masa ya shiga sannan ya taho da gudu yana gaishe shi tare da yi masa tuni cewa wata ya kare har an shiga wani amma bai ji dumus ba, Umar yaji kamar ya rufe shi da duka, amma sai ya shafa aljihun sa yace "yi hakuri da Allah, na manta ne wallahi kuma yanzu babu kudi a jikina amma in na fita zan dawo maka dasu" bai jira amsar sa ba ya wuce ciki.
Direct dakin Jidda ya tafi ya fada kan gado yana jin sauran kamshinta da har yanzu bai gama barin dakin ba. Ya jawo pillow ya dora a fuskarsa, so yake yi ma ya samu yayi kuka irin wanda takan zauna tayi tayi amma shi ya kasa yi ko kadan ne ballantana yaji dadi.
Yanzu menene abin yi? Abubuwan da suka faru sun ruga sun faru sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba amma menene abin yi? Shi dai yasan ko da wuka a wuyansa ba zai saki Jidda ba. Kuma yasan ba zai iya zuwa ya durkusa ya bawa Baba hakuri ba dan a yanzu ma in ya tuna haduwar su ta jiya ji yake yi kamar zai narke a inda yake, ji yake yi duk ya tsani kansa.
Yanzu mafita a gare shi kawai ita ce ya san hanyar da zai bi ya samu ganin Jidda kafin iyayenta su riga shi ganinta, ya samu ta saurare shi ta fahimci seriousness din halin da ake ciki ta fahimci irin halin da yake ciki ya san zata tausaya masa, zata iya cewa ta yafe masa kuma zata dawo gidan sa, in ta fadi haka babu alkalin da zai raba musu aure, idan har ya samu ta dawo gidan sa then everything will be ok for him, with her by his side he will be ready to face the world.
amma ta yaya?
Ta yaya zai ganta har ta ta saurare shi har kuma ta yarda da shi har ta dawo gidan ta. Ta ina zai fara?
Wayarsa tayi kara, ya daga yana kallon sunan a take kuma yawun bakinsa ya kafe. Waliyin Jidda ne.
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ajiye wayar a gefe yana kallon ta kuma yana sauraron karar kidan ta har ta katse sannan wani kiran ya sake shigowa shima ya katse sai wani.
"Idan fa baka dauka ba kana karawa kanka laifi ne"
Wata zuciyar ta gaya masa, ya dauki wayar a ransa yana aiyanawa "ko ya sani shima?"
Ya amsa kiran sannan ya saka wayar a kunnensa
"Hello salamu alaikum. Kawu barka da safiya"
"Yauwa doctor barka kadai, ya mahaifan naka?"
"Lafiya lau kawu"
"Yanzu ai ake gaya min ashe ka gano inda yarinyar nan take mai taurin kai, to alhamdulillah, shine na kira dama ka gaya mana inda take sai muje mu taho da ita gida kafin kuma a zaunaa duba maganar aga abinda ya faru da kuma yadda za'a bullo masa"
Umar ya sauke ajjiyar zuciyar da yake rikewa. Bai sani ba. Amma yasan Abba ne zai gaya masa yasan inda Jidda take shi kuma Farhan ce ta gaya masa, shine zasu kira su tambaya dan su je su dauko ta. Tana shiga hannun su kuwa shi da ganinta sai ranar da Allah yayi.
Yace "haka ne kawu, tana gidan wata kawar ta ne anan unguwa uku, nima dai ban ganta ba naje jiya taki fitowa"
Yace "to ai in taki fitowa gurin ka mu in muka je dole ta fito dan kaniyar ta, zata hadu da mu ne ai, duk ta bawa mutane wahala. Ka zo an jima gidana ka dauke ni sai muje mu dauko ta"
Da sauri Umar yace "to kawu, insha Allah" sannan ya katse kiran tare da dora wayar a kirjinsa yana fatan ina ma ranakun baya su dawo, ranakun da Abba ma yake yi masa magana kamar haka, amma a ransa ya gama kudirewa ba zai je ya kai shi gurin ta ba har sai ya samu ganin ta first.
Ya mike tsaye, yaji wani jiri yana neman mayar da shi kwance, sai a lokacin ya tuna rabonsa da abinci tun na breakfast din jiya, ya kuma tabbatar idan bai ci abinci ba ba zai iya zuwa inda Jidda take ba ballantana ya ganta ɗin.
Ya kuma yin kokari ya mike tsaye sannan ya bi dakin da kallo, remembering all the memories da suke cikin dakin. Ya lura da pieces din kayan ta dana yara da suke kasa waɗanda suka zube a lokacin da take hada kayan su. Ya tuno yadda ranta yake bace a lokacin, ya tuno maganar da ta gaya masa
"Wanne Allahn kake rantse min dashi? Allahn da kake sabawa a duk chance din da ka samu?"
"Please ni ba ma game me kake cewa nake yi ba, ka tafi dakinka ko palo ko dakin Asabe, anywhere but where I can't see you har sai na tafi then you are free to do anything, ka kawo mata ma har gidan ka ba zan takura maka ba"
Ya danyi murmushi yana shafa inda ta mare shi, "ke kadai zaki dawo gidan ki Hauwa'u. And everything will be ok. Kawai dai I need you to trust me again"
Sai kuma ya tuna cewa tayi trusting dinsa time and time again.
Ya wuce kitchen ya hada tea amma ko rabin cup bai iya sha ba saboda baya wucewa ta makogwaronsa, ya ajiye sannan ya shiga dakin sa ya chanja kaya ba tare da ko ruwa ya zuba a jikin sa ba ballantana ya shafa mai. Sannan ya shiga motarsa ya sake komawa gidan Diyam, da niyyar sake gwada sa'arsa akan Jidda.
*Jidda*
A ranar haka kawai na tashi zuciyata naji tayi min dadi, irin feeling din da zaka ringa jin ka cikin farin ciki ba tare da kasan dalili ba. Na tashi da wuri na shirya na shirya yarana sannan muka zauna ina dora musu karatu kamar yadda nake yi musu kullum da safe dan kar a wuce su a islamiyyar su. Muna yi muna ta wasa abin mu, ina jin dadin yadda yau naga Yasmin tana cikin fara'a ko dan fadan da nayi mata jiya ne?
Muna kokarin kammalawa Asma'u kanwar Diyam ta shigo dakin itama tayi joining din mu muka cigaba tare. Sai da muka gama na tambaye ta ko Diyam ta fito? Sai ta tabe baki "yau fa weekend, Hamma yana gida, kar ma ki saka ran ganin ta yanzu gwara ma muje mu nemi abinda zamu ci tun kafin ulcer ta kama mu" nayi murmushi, kawai sai naji ina tunawa da yadda weekend ta kan kasance a gidan mu, yadda Umar makale min yace lallai sai munyi baccin safe tare bayan ni kuma ba baccin safe na iya ba, haka zanyi ta kwanciya a jikinsa har sai Allah ya cece ni Yasmin ko Asad sun tashi sannan zai barni in tashi dole in je gurin su.
Na kawar da tunanin na mike muka fita tare da Asma'u muka shiga kitchen, mai aikin Diyam daya ta taya mu muka shirya breakfast muka ajiyewa lovebirds din nasu mu kuma muka dauki namu muka dawo palo muna ci da yara, Asad yana ta yi mana surutu muna dariya, surutun da duk sentences sai an hada da sunan Daddy a ciki, shima yana missing dinsa sosai kawai dai bai kai Yasmin rigima bane ba.
Muna cikin ci Diyam ta sauko, da niyyar ta zata kai musu abinci sama ne har ta nemi Asma'u ta taya ta sai kuma ga yallaban nata ya sauko ya zauna shima a kasa kan carpet aka kawo musu abincin suka fara ci tare da matarsa, ni duk sai naji na kasa cigaba da cin nawa, irin feeling din kamar kana trespassing. Bayan na gaishe shi ne yake cewa "Diyam ta gaya min ai maigidan ki yazo, sai kuma yaji tsoro ya gudu" Diyam ta harare shi "ba fa guduwa yayi ba, zuwa yayi zai je ya dawo. Ai ja da baya a gurin rago ba tsoro bane ba shirin fada ne"
Yace "accept it, guduwa yayi, dama tunda aka ce min bafulatani ne na san cewa guduwa zaiyi dan fulani matsorata ne"
Sai na fahimci abinda yake faruwa, Diyam yake tsokana dan ita bafulatana ce, Asma'u tace "kai Hamma, kai ma fa bafulatanin ne" Diyam tace "rabu dashi. Ina ma Umma zata ji ka, zata ji abinda kake fada akan Fulani bayan fulanin sune kan ka ya dawa" yayi dariya "ta sani ai, tunda ta haife ni tasan ni ba bafulatani bane ba tunda ni ba matsoraci bane ba"
Diyam tace "ai kuwa za'a ware su waye